← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 15 OF 18

PART 29 AND THIRTY

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Karfe 8 na safe ummu ce ta shiga dakin Hammad a zaune ta tadda shi,bisa sallaya nemar kujerar tayi ta zauna tana kallon Dan nata cike da soyyaya,hammad dago wa yayi yace ummu Ina kwana,lafiya Lou Hammad ya jikin naka,da sauki ya amsa yana kallonta,ummu dama doctor ne yace zaizo shisa nazauna jiransa kuma naga har yanzu baizo ba,zai Zo Hammad ai kasan yanzu garin ya waye,ya kake jin jikin naka yanzu,da sauki ya bata amsa,hammad kayi hakuri kaji komai yayi farko zaiyi karshe,nasani ummu to taso muje kai breakfast kaji,da to ya amsa sannan ummu ta mike ta fice,wayarsa ya janyo tare da dialling number hello Doctor kasami wani bayani game da Juwairiiyya,shikenan kittt ya kashe wayar yana bin wayar da kallo cike da kulewa,tashi yayi ya fito parlorn tin daga nesa ya hango muniba zaune akan dining taci wanka tana danna wayarta,zuwa yayi ya zauna kallonsa tayi tace ya hammad Ina kwana cike da kulawa yace lafiya lou,daga haka bai kara cewa kala ba,sai abincin da yakeci sama sama kamar Wanda bayason cin abincin,wayarsa yaji tayi kara,shikenan ka shigo mana ai Muna parlorn,ummu ce ta kallesa yace mata doctor ne,daga haka ya shigo parlorn.
Hey baki abinda ya fito daga bakin nainah,cike da takaici ya kalleta yace ke shashasha ba sunana baki ba,sunana Vitt meye kike min wannan kiran,tabe baki nainah tayi tace taya akai kukasan cewa zanzo kuma meyasa kuka kamani,dariya yayi yace auuh ke baki sani ba Kenan,eaa ta bashi amsa tana kallonsa,d dariya yayi yace ai sai ki bincika yammata,ko kallonta bai kara yi ba,agogon hannunta ne yake haske,kalla tayi yayin da tayi Maza ta rufe shi da hannun rigar ta,kallon Vitt tayi tace zanje bandaki,kallon ogansu yayi yace oga wai zataje toilet,ok shikenan alama yayi mata da bandakin da yake cikin dakin,dole haka ta mike ta wuce,wucewarta bandakin ne yasata gyara agogon tare da dagawa,inajinka Khalid daga dayan bangaren ne naji ance,madam mun samu address din wannan matar a garin Niger take amma yanzu an tabbatar mana da cewa ta bar kasa ta tafi Ireland,ok Khalid Kaci gaba da bincika wa,madam na kira wayar ki naji switch off karka damu da wannan kawai dai ka bincikamin komai zamu hadu nan da wani week din,fitowa tayi Kamar ba ita bace yanzu ta gama waya,kujera ta samu ta zauna tana tinanin kuma yanzu meye mafita.
Hammad ne ya fito sanye da kananan kaya sunyi matukar yi masa kyau,ganin parlorn ba kowa ne yasa shi hucewa dakin ummu,a bakin kofar dakin ya tsaya yana knocking,shigo aka bashi amsa,shiga yayi yana kallon ummu a zaune bisa sallaya,gaisawa sukai sannan yace ummu zan tafi aiki ne,amma hammad maimakon ka huta yanzu haka zaka tafi,aa ummu ai jikin nawa da sauki sosai,shijenan hammad yawwa ummu inason magana Dake ne,inajinka hammad ummu naga Juwairiiyya,dago kai tayi tace dama hammad ka ganta mana a television,aa ummu naganta wallahi a zahiri ni da kai na na kaita asibiti,hannunta na zubar da jini kuma likitan ya tabbatar min da cewa harbinta akai,hammad kayi hakuri zaka ganta very soon amma ummu,ya isa hammad ka ga time na wucewa tashi ka wuce kaji,ummu ai ba kimin addua ba fa,s shikenan tashi kaje zan maka,tashi yayi yana dariya domin dai yaga da gaske korarsa take.
Muniba ce ke waya a dakin ta da aka bata,Rabi'ah bazaki
gane ba,ina mugun sonsa wallahi,dik wani abu da nake masa Dan ya kulani ne amma wai akan wata budurwa can har ciwonsa yayi kokarin tashi,rabia ce tace kinga idan da dama mu hadu mana kawai sai mu tattauna matsalar,shikenan ki tura min address din gani nan zuwa,daga haka ta katse wayar ta kishingida tana tinanin hammad,domin tana mugun jinsa a ranta.
Dakin ummu ta nufa a lokacin hammad ya fita daga gidan,ummu ce tace to muniba lafiya cike da kulawa tace ea ummu dama zan fita ne zanje wajen kawaye na,cike da mamaki ta kalleta tace muniba yaushe kikayi kawaye,a social media ta bata amsa,shikenan muniba ki kula and ga mukullin motar,karba tayi tana nagode ummu da haka ta fice daga gidan ta hau kan titi,a take ta kure sautin motar da wakar ayra.
WACECE MUNIBAH
Cikakken sunanta Saudatu Jamil inkiya muniba,ya ga attajirin mutum mai company daga nigeria har zuwa karsashen waje,miniba ta taso cikin gata dik da cewa mahaifinsu su biyu ya Haifa amma dayake ita ce ta fari sai so ya koma kanta,akwai kanenta mai suna Muhammad,alhaji Jameel ya kasance Yaya ne ga Hajiya Fatima wato ummu,mahaifiyar hammad,sannan yana zaune ne a Abuja Wanda daga baya kuma sai suka tattara DASHI da matarsa mai suna Zainab suka koma Switzerland da zama,acan muniba taci gaba da karatun ta anan tai degree and tana aiki a daya daga company mahaifinta,sannna kuma tana karatu dik da cewa online takeyi.muniba tana matukar son hammad tin daga yarinta kasancewar ta gansa kyakkyawa,ko da tayi wayo taga ya fisu kudi sai ta kara son hammad,muniba ta kasance yar karya domin bata daukar raini,ba laifi tana da kyau daidai misali,amma ba wani can ba,amma dayake kudi sun zauna sai gaba daya ta chanja ta koma kamar wata baturiya.
A wani katon eatery tayi parking fitowa tayi tare da karewa wajen kallo,sai kuma ta shiga kanta tsaye,zama tayi a daya daga kujerun wajen,wayarta ta ciro daga jaka,sannan tai dialling number,batare da an daga ba wata budurwa ta zagayo tana fadin,basai kin kira ba gani nan ai naga shigowar ki,zama tayi tare da kallon waiter da yazo Kansu,abinda suke so suka fada masa,sannan muniba ta kalli yarinyar zuby ya kike,lafiya Lou muniba,da Kika ce zakizo ban yadda ba wallahi,ashe kin dawo daga Switzerland din,da dariya ta kalleta tace ai na kusa komawa,saboda naga alamun buqata ta bazata biya ba sai na hada kai da iyayena,zuby ta kalleta tace wace buqata kardai kice min har yanzu hammad bai bada kai ba,dariya muniba tayi tace eaa bai bada kai ba zuby,narasa ya zanyi DASHI,shikenan muniba shawara ba zakije kauye ba,kiyi dik yadda zakiyi ku tafi tare,zuby kuma kina ganin zai yadda,tabe baki zuby tayi tace ke a tinaninki mahaifiyarsa zata yadda domin ai kakaninku daya,murmushi muniba tayi bama sai kin karasa ba zuby nadau haske,dariya suka sa gaba daya harda shewa.
Sunfi 1hour sannan sukai sallama,muniba na ganin cewa tabbas shawarar zuby zata yi mata aiki,domin tasan da cewa ummu zata yadda da buqatar ta,da wannan tinanin ta iso gida a lokacin ana kwala kiran sallar magariba,dakin ta ta nufa tare da gabatar da sallah,sannan ta kira mahaifiyarta da mahaifinta,sai kuma kanenta sai da suka gama video call dinsu cikin farinciki sannan ta tashi ta nufi falo,a parlorn ta tarar da ummu,muniba har kin dawo abinda ummu ta fada,murmishi ta yi eaa ummu,dama inaso muyi magana ne,inajinki muniba lafiya,so nake dama ya hammad ya shirya muje Taraba domin naga kamar ya dade baijeba,da murmushi ummu ta kalleta da kuwa kin kyauta muniba,domin ya dade baijeba,sai dai su in sun gaji basu gansa ba suzo,kibari zamuyi magana da shi zakuje din,cike da farinciki ta zauna domin ganinta buqatar ta zata biya akan hammad.
Salim ne tsaye Ina wannan number ta nuna,cike da kulawa daya daga cikin jami'i ya kallesa sir wannan number tana garin kano,sannan an kashe ta ranar laraba da karfe 5 na yamma,yallabai number dai tabbas tana garin kano,da kyau Ali nagode da wannan information din,and juyawa yayi yana kallon agogon hannunsa,ganin lokacin tafiyarsa yayi ne yasa shi juyawa ya ce Ali ka turo min bayanan ta WhatsApp daga haka ya fice daga office din,yana mai murmushi tare da fadin nainah Sharwaz gani nan kanki.
SECRET WRITER
ASHUUU
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABON LITTAFI
.....Based on Creative Story....
Chapter 15 · 0% Book details