← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 13 OF 18

PART 25 AND TWENTY SIX

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Salim dik halin da za a kasance Ina buqatar nainah a raye ina buqatar ta,kallon ta yayi yace mommy amma da haka Kika ce a fasa bincikarta,to yanzu kuma nace a bincike ta Salim ko bani da ikon haka ne,aa mommy kina da right ma sannan zan binciketa amma Ina buqatar ganin babe,domin ita kadai ce zata iya fada min inda sukaje da nainah,fitowa sukayi daga parlorn kai tsaye dakin babe sukaje,a zaune akan gado suka tarar da ita tana wasa da teddy,gaba kuma ga video nan tanayi ita kadai,salim ne ya shiga ya zauna yayin da hajiya areefah ta tsaya daga bakin kofa,salim ne ya kalli babe yace babe Ina Kika he da wannan matar,cikin yar hausarta ta furta Unguwa ya salim,murmushi yayi yace ai nasan dama Unguwa amma Unguwa Ina,shiru tayi tana wasa da wani teddy blue color,kalle kalle take yi take idanunta suka sauka akan television da sauri ta nuna da hannu,kallon wajen Salim da mommy sukayi sannan suka kalli juna,daga bisani kuma suka Fi ce daga dakin,zama sukayi hajiya areefah ce ta kasa dannewa yanzu kenan Salim kasar waje sukaje,murmushi yayi yace aa mommy babe ba nan ta nuna ba kamar Kaduna naga ta nuna saboda tashar Hausa ce,amma ko ma Mene bazamu yadda da zancen babe ba zamu bincika da kanmu domin Nemo nainah,daga haka ya Mike to mommy zan tafi idan an samu wata maka ma zan miki magana,shikenan Salim ka gaishe min da hajiya,zataji mommy.
Oga dik yawancin hospital na garin nan mun duba amma ba ita ba alamunta,kai banza fadin mutumin da ya harbine nainah an gaya maka zataje public hospital ne,private hospital zakuje,sannan inaso ku rarrabu zuwa mota daya
domin so nake na kamata a yau,ok oga daga haka dikkan motocin suka sauya akala.Nainah ce ta farka ganinta a wani daki ya tabbatar mata da cewa asibiti take,da hanzari ta mike ta dauki Jakarta,ganin magani akan drawer yasata dauka ta Fi ce daga dakin,dai dai lokacin data fito ne yasata ganin giccin mutumin da suka biyota dazu har suka harbeta,tsayawa tayi tana kallonsa sai kuma taga na 2 da mugun sauri ta juya akalar tafiyarta zuwa kofar baya tana tafe tana waiwaye,ganin zasu kamata ne yasata Jan rigar doctor ta dora take ta fice daga asbitin.
Tafiya take dik da batasan ma yanzu Ina zata nufa ba,wani tinani ne ya fado mata take ta tsaki da mai taxi tabar asibitin take,tafiya yake da ita ganin taki fadin inda zai kaita ne yasa shi yin parking hajiya amma baki gayamin inda zan kaiki ba,sai a lokacin ta juyo shikenan barni anan ma,hannu tasaka ta zaro wasu kudade masu yawa da Mika masa,amma hajiya wannan kudin ai ya isa kaje kawai dika na baka,da murmushi a fuskarsa ya mata godiya sannan ya juya sai tafi,sai kuma ta ce masa Dan aramin wayar ka azo a daukeni,mika mata wata keypad yayi number ta fara dialling,sannan ta kira,ni ce nainah kazo ka daukeni zan tura maka address din,tana gama wa ta tura masa address sannan ta Mika masa wayarsa sukayi sallama.
Oga tabbas munganta a wannan hospital din abinda yasa muka ga kamar ba ita bace na hangeta da rigar doctor,kuma sai da kafin ya karasa ne ya sakar masa mari,cike da takaici ya furta are you mad kana ganin ta ta tafi kuma kazo kana fada min,shin kayi hauka ne Daaz,kasan wacece ita idan muka bari ta tayi wallahi kasani dikanmu bazamu Sha ba,daaz ne ya kallesa yace to Ina ruwa na ni kai dai oga kai ne a matsala,domin kwa mu bamu Santa ba,kai ka Santa tinda kai ka Santa kasan kai za a kama,kallon sa yake yayin da yake masa magana cikin kunar rai ya furta daaz ka fice daga dabata kar na sake ganin fuskarka,dazz ne ya kallesa and so what aminu na tafi dama banyi tinanin wannan danyen aikin za ka sakani ba da wallahi bazan ba,kuma kaga tafiya ta wucewa yayi yana huci kamar zaki.Bayan wucewar sa ne ya kalli sauran guys din yace zamu ci gaba da Neman ta ne har sai mun kamota,amma Ina da magana ga dik Wanda ya kamota zan bashi kudin da zasu isheshi rayuwa Dan haka ku bazama ku Nemo ta,da ok sir suka furta kowa na mai yin addua Allah yasa ya Nemo nainah a bashi kudi.
Hammad ne ya karyo da motarsa cikin asibitin da aka kwantar da nainah,parking yayi sannan ya fito yana mai nufar dakin da aka kwantar da nainah,t urus yayi yana mai ganin dakin ba kowa,da sauri ya juya ya koma wajen doctor din a zaune ya same shi,doctor ganinsa ne yasa shi mikewa kallonsa Hammad yayi yace ina mara lafiyar da na kawo maka,tana dakin ta mana,wane dakin dakin da na kwantar da ita,cike da takaici Hammad yace to bata nan,d a sauri likitan ya kallesa yace kamar ya,hammad ne yayi gaba shi kuma na binsa a baya.Dakin suka shiga likitan ya kalli dakin tare da furta ya salam Ina ta tafi kuma,hammad ne ya shigo kamar ya Ina ta tafi bayan anan wajen na barta a kwance,doctor ne ya kallesa yace Hammad ka kwantar da hankalinka please insha Allah zan nemota,domin nasan dai akwai dalilin da yasaka ta tafi,sannan kuma kai tinani domin harbinta akayi,kaga ya zama dole ma akwai wata a kasa amma zan nemota,badan ya gamsu da bayanan sa bane yasa shi fita daga dakin ya huce zuwa bakin motarsa,tada ta yayi sannan ya fice daga asbitin.
Faisal ka tabbata da cewa wannan gidan yana da dik wani abu da nace,nainah wannan gidan fa Wanda aka saya ne kwanaki,har Kika ce idan an samu mabukata a mallaka musu amma nake ganin kidan zauna nan da kamar kwana 3 sai ki tafi ko,faisal nasani bama zanyi kwana ki 3 ba,sannan karka damu akwai Wanda zan bawa gidan ma,kawai ka bani key da takardun gidan insha Allah komai zaizo da sauki,ka zauna bara na hada maka koda tea ne,aa nainah Ina da abinda zanyi,amma zan dawo ko zuwa anjima ne na kawo miki takardun sannan wannan shi ne mukullin,ajiye mata yayi sannan ya fice yana tinanin wai wacece nainah,meyasa take wasu abubuwa haka kamar daga haka kuma ya Fi ce daga gidan.
Remote din television din ta dauka tare da kunna tv,gefe ta dawo ta zauna tana kallo,sai kuma ta janyo Jakarta,ganin komai yana ciki ne yasata fadin alhamdulilah,hannunta ta kalla sannan ta fito wayar ta,Faisal natura maka card ta WhatsApp ka siyo min wannan magungunan ka taho min da su,amma nainah naga da magani a wajenki,ya isa Faisal kai wai wane irin mai tambaya ne,kayi abinda nace,daga haka ta katse.Hankalinta ta maida kan television take taga hotanta a sama,yana wayo a kasa kuma an saka wanted,cike da bacin rai tace dama nasan za a yi haka,amma yanzu abinda ya dace shi ne na dawo kan Alhaji mahboob.
ASHU ce
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABON LITTAFI
.....Based on Creative Story....
Chapter 13 · 0% Book details