← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 18 OF 18

PART 35 AND THIRTY SIX

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Muniba tin asuba ta tashi ta fara shirye shirye kasancewar ummu ta sanar mata cewa flight din nasu na karfe 8 ne,shiryawa take sai da ta gama tsaff sannan ta kira zuby a waya,waya suke tana fadin ke zuby yau ne fa tafiyar mu,zuby ce Tai murmushi tace aikin banza kuma shi ne zaki tashe da sanyin safiyar nan,haba zuby ba dole na tasheki da sanyin safiya ba tinda kinsan yau dole na cika buri na akan ya hammad,tsaki zuby taja tace wallahi muniba kina ban mamaki,kina cusa kanki inda ba a sanki,kalleki fa da kyanki da komai amma kin tsaya hammad yana wulakanta ki akan wata wadda bai san inda take ba,nifa da zaki bi shawara ta ki kyale wannan hammad din kawai ki nemi wani,muniba ce taja tsaki ke dallah matsa baki san Yaya hammad ba ga kudi ga kyau,ga ilimi ga iya daukar wanka,zuby ce ta katsesa da cewa to ke kenan dik baki da wadan nan abubuwan da Kika lissafa ko,gajiya tayi sannan ta katse wayar tana mai jin haushin zuby domin ta tsani a kushe hammad ko ba komai ai akwai sa da kudi.
Fitowa sukayi yayin da kowa ke a falo hammad,ummu sai Muazzam,muniba ce ta fito tana kallon kowa Dake dakin,ummu ce ta kalleta yawwa 'yata Zo nan Ina da magana Dake,cike da mamaki muniba ke kallon ummu,matsawa tayi ta zauna tana gaisar da Muazzam da kuma hammad,amsawa sukayi,ummu ce ta kalleta muniba shin kinason zama a wannan kasar ko,muniba daga kai tayi domin ita dik tinanin ta ai zata aura mata hammad ne,yawwa ummu ta furta to dama namiki miji ne,cikin sunkuyar da kai tace to ummu waye,vazan fada miki ba har sai kin dawo daga taraba,ko kina da Wanda kikeso,kai ta girgiza mata sannan hammad ya katse hirar da fadin ummu ki kyaleta mu tafi,zamu makara ba,shikenan ummu ta furta tare da mikewa,wasu ledoji ta mika mata tace ta kai musu tsaraba,muniba cike da murna ta fita tana mai farincikin ba tare da tasha wahala ba gashi zata auri hammad,motor suka shiga,ganin hammad ya shiga baya ne yasa zata bi sa,muazzam ne yace aa hajiya muniba ni kadai zaki bari a gaba ne,ki shigo mana ko ba komai ai munyi hira ko,badan ta so ba Dan sai da ta tabe baki sannan ta bude gaban motar ta shiga,ummu na daga musu hannu daga nan suka zarce aminu kano international airport.
Sir wallahi nayi dik yadda zanyi wajen naimo ta amma nakasa,yarinyar ce kamar aljana,wata muryace ke furta aminu ba aljana bace sannan ka sani yarinya ce karama,sannan abinda nakeso da kai tinda ka kasa kamota to kawai ka tafi na sallameka,sanann inaso ka dawo min da mukullin motata,da mukallayen gidaje na da suke hannunka,aminu ke fadin sir Dan Allah kayi hakuri,look aminu yanzu ba lokacin bada hakuri bane tinda harka kasa farautar ta,nizan farauce da kai na,domin a gobe zan shigo NIGERIA,indai har ba kashe ta ba,to tabbas Ina cikin matsala,wannan shine magana ta ta karshe dakai,dan haka ka saurari zuwana,daga haka ya katse wayar,wata kara aminu ya saki yana furta no Alhaji wannan yarinyar ta ja mini asara,nayi rashin babban abu,cike da bacin rai take wannan surutan.
Salim ne a cikin office din police din dayake aiki anan,a zaune yake yayin da yaji wayarsa tana ringing,dubawa yayi yaga an saka private number,da kamar bazai daga ba sai kuma ya daga yana mai fadin hello,jin muryar abeed ce yasa shi saurara da takardun gabansa,yana mai kallon wayar sannan ya kara yana fadin abeed,daga can bangaren ne abeed ke furta Salim ka kyale nainah na Riga da na fada maka ka kyaleta amma kaki ko,to kasani nan gaba kadan zaka gane kuskuranka kamar yadda nima na gane kuskurena a kanta,amma abeed meyesa kuka,yanzu kana Ina,mommy tana tambayar shin kazo wajena,salim yanzu ba lokacin wannan tambayar bane amma nidai na fada maka sannan Ina mai baka tabbacin cewa ko da ka kama nainah sai dai ka saketa domin ba abinda zaka iya yi mata,daga haka ya katse wayar tasa,salim na kokarin binsa anan ya gane ASHE da private number ya kirasa,dukan table din gabansa yayi yana mai furta hitt,fitowa yayi daga office tare da shiga motarsa ya bar station din tare da hucewa gida.
EGYPT
Zaune suke su 3 akan kujeru,yayin da dikkan su ke shan shayi,alhaj mahboob nai nasara ganewa,alhaji mahboob ne ya kallesu yace ina mai fadamuku ban taba tinanin yana da yarinya ba,a wannan takin da tamin hacking sai na rasa naira billion 100 dama kuma gaskia kudin kunsan ta yadda aka samesu,daya ne ya kallesa yace ai Kaine banza amma taya za ai yarinya karama tayi maka wayo,to kai kana mai,kallonsa yayi yayi murmushi sannan ya numfasa yace bazaka gane ba Alhaji Habib domin yarinyar hatsabibiya ce,dik wannan hirar da suke zubawa dayan ko tatafasa bai ce ba,sai da suka gama sannan ya kallesu ya zama wajibi mu zauna,mu san ta yadda zamu shawo kan wannan matsala domin tabbas,bayyanar yarinyar nan abin tsorace,dadin ta daya ma bata da wani evidence akan mu,yanzu Ina Alhaji kabeer,mahboob ne yace ai yana France domin dazu muka gama magana da shi akan cewa zai sauka Nigeria gobe,saboda ya Nemo yarinyar nan ya kashe ta kowa ya huta,amma Alhaji muhsin meye shawarar ka akan wannan Batu,nufashi ya furzar sannan yace ku kyalesa mugani ko zai yi abinda ya fada din,idan aikin ya gagaresa ai kaga sai mu sauka akan ta,tinda kunce hatsabibiya ce.
Bacci take akan bed din dayake dakin,kiran wayar ne ya tasheta dagawa tayi tana fadin hello faisal ya dai,nainah dama nace ko na turo miki doctor ne,murmushi tayi tace aa faisal ka barshi kawai kasan bana ganin doctor,cike da damuwa a muryarsa yace amma Harbin hannun naki ya warke ne,eaa faisal ya warke karka damu da wannan,kawai inaso ne na huta yanzu anjima zan fita,to ko na kawo miki car din ki,aa faisal ka barni kawai zan hau taxi domin labari yazo min cewa ana nemana a cikin gari to Ina ganin hawan taxi din yafiye min da Hawa mota ko,shikenan to,nainah ce taja numfashi Ina zuwa faisal ana kira na,katsewa yayi,sai da ta duba kiran a wannan lokacin gaban ta ne yayi matukar faduwa,domin a saman screen din number India ce,da sauri ta tashi ta rufe dakin sosai sannan ta dawo,kiran ta daga a wannan lokaci ne fuskar wata Kykkyawar yarinya ta bayyana,fuskar nan dauke da murmushi,itama murmushin take zuba mata,addah yarinyar ta furta amsa wa nainah tayi,bayan dik sun gaisa ne sannan take ce mata to alkawari dai ya cika addah domin kinsan gobe zakizo ko,da murmushi tace Ina sane kanwata zanzo kinji my raudah ta,da dariya itama take kallonta tana fadin shikenan addah amma kuma jikin,shittt tai mata alamun tayi shiru,hakan yasa tai saurin kama bakinta ki shiru da bakinki idan nazo gobe zamuyi magana kinji shalelen addah,sauri tayi ta katse wayar ta,sanann ta mike sai a wannan lokacin ta tina da cewa zata fita ma.
Aminu kano sukai parking hammad ya Riga fita sannan muniba da take kokarin fita,kallonta Muazzam yayi yace Dan Allah inaso muyi magana da ke koda na minti 2 ne,kallonsa tayi a wannan lokacin kuma taji ya mata kwarjini,kallonsa tayi tace inajinka,muniba tabbas Ina sonki,wallahi kuma idan Kika amince min zan turo domin azo ayi maganar aure,da sauri ta dago kai ta kallesa a wannan lokacin ne ta kasa magana,cike da fadin nama ta bude kofar ta fice batare da ta bashi amsa ba,ranta a bace ta nufi cikin port din,a can zaune taga hammad yana jiran layin tantancewa yazo kansa,kusa DASHI taje ta zauna tana maida numfashi,bai kalleta ba bare ma yasan da cewa ai taba wajen,kawai ya ci gaba da aikin danna wayarsa.
SECRET WRITER
ASHU
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
WPS Office
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Default Paragraph Font
Times New Roman
Times New Roman
SimSun
Symbol
Symbol
Arial
Arial
SimSun
SimHei
Courier New
Courier New
Wingdings
Wingdings
Z&!),.:;?]}
Normal.wpt
db048de713584fa6b178f99aedfd2fb9
Chapter 18 · 0% Book details