← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 14 OF 18

PART 27 AND TWENTY EIGHT

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dai dai kofar parlorn ne ya hango muniba a zaune,tsaki yaja yana kallon gefensa domin ya Riga daya dano jirgin muniba, shigowa yayi da sallama a bakinsa,amsawa tayi tana ya hammad sannu da zuwa,yawwa ya bata amsa lokaci daya,remote din television din ya dauka yana danna wa,dai dai wata Tasha da aka rubuta Lucky TV ya tsaya,sakamakon abinda idanunsa suka gane masa,hoton nainah ne da aka zana da pencil,a kasa an saka wanted,a wani zabure ya Mike ya fara kwala kira,ummu! Ummu!! Da sauri ta fito daga kitchen tana fadin haba Hammad kamar baka girma ba,ganin hannun sa tayi yana nuna mata television,kalla tayi yayin da muniba ta zama yar kallo,a sauri ummu ta dago tana fadin wannan ai Juwairiiyya ce Hammad,kallonta yayi sai kuma ya zauna yana fidda numfashi,ummu ta sauri ta bude fridge din bayan ta ta dakko ruwa,a hankali ta dawo kusa DASHI ta zauna tana Mika masa ruwan,sha yake yana maida numfashi tamkar wani mara lafiya,ummu ce ta kalli muniba tace je ki kular min da girkina,da to ta amsa tana fadin to wai me ya faru,wacece ita har zata zama yana kallonta ciwonsa na kokarin tashi.Ummu ce ta kallesa taga alamun kamar bacci yakeji,mike Hammad a hankali ya Mike idanunsa a rufe,dakinsa na kasa ta nufa,shiga dakin sukayi sai da ta tabbatar daya kwanta,sannan ta masa addua ta fito ta koma kitchen,muniba ce ta kalleta tace wai ummu menene,wacece ita,bqnason tambaya muniba kawai ki aikin ki daga haka bata kara magana ba.
Faisal muje ka sauke ni gidan Alhaji mahboob,amma nainah me zakiyo gidan Alhaji mahboob,murmushi tayi tace bazaka gane ba Faisal muje,ajiye min takardun anan,fita sukayi sannan suka fice daga gidan,tafiya suke nainah ce ta kalli Faisal tace yawwa Faisal dama inaso muyi magana akan wannan kudin,eaa nainah dama naso nai miki magana dazu amma kuma naga kamar kina sauri ne,ok shikenan Faisal ya kamata a fitar da wani kaso daga ciki,a bawa masallatai sannan a Gina massalaci,makaranta,borehole and so on,to nainah zamuyi lissafi kamar nawa kike ganin ya dace a fitar,zamuyi magana akai,idan ka samu space ka ajiyeni,amma kuma nainah wannan ciwon naki fa,dariya tayi tace karka damu domin ni nan bana tsoron dik wani mutum daga haka ta fice daga motar.
Alhaji SALMANU har yanzu ba wani labari a game da yarinyar nan fa,alh DAYYIB ne ya kalli system din yace to yanzu kake so muyi da wannan zancen,musaka kudi sannan musaka a kowa ce state yadda zata zaga state,alhj DAYYIB ne yace kodai musaki kudi a bazata a duniya, domin kasan bazan taba yafe mata ba,kamal fa ta karya karas,wannna abu ne da bazai taba yiwuwa ba wallahi Dan haka nasan me zanyi Salman ka bar min komai a hannuna,daga haka ya katse ya Mike ya bar wajen.
Tsayawarta ne yayi daidai da shigowar kira,kallon wayar tayi sannan ta daga hello,ok shikenan ka tura min da address,knocking ta farayi,gate man ne ya bude yana murmushi,hajiya hajiya dariya tayi sannan ta shiga,mai gidan yana nan,yana washe hakora yace yau dai kam kinci sa'a yana nan,ok wucewa tayi zuwa cikin gidan,dai dai kofar parlorn ta tsaya tana knocking kamar baza a yi magana ba taji ance yes! Shiga tayi take idanunta suka ci karo da wasu bodyguard bakake da su sunci bakaken kaya,kallonta suke one by one,zauna daya daga cikin su ya furta hakan,take daya ya ciro bindiga ya saita kan nainah,nainah cike da mamaki take kallonsa,waya ya daga yes mai gida ta kawo kanta har gidanka,ok sir ya katse,kasan bindigar ya saita ya dakar mata kai take ta tafi luu ta Sume.
Abeed yanzu mommy tace na kamo mata nainah Sharwaz kai meye shawararka,to salim me zance yanda tayi,kudi ne ta riga da taci,yanzu Salim ko nace ka kamota iyawa zakayi ne,yarinyar data Fi mu sanin kanmu,lokaci guda take bacewa kamar mai layar zana, look abeed tinaninka ba zan iya ba,to Salim idan zaka iya kayi mana,ni kaina inaso na ganta amma badon na kashe ta ba,sai da na tambayeta dalilin da yasa ta kashe min mahaifi,amma kwata kwata ta fimu wayo,ta fimu iya taku fa,bazamu iya kamata ba,abeed tinaninka bazan iya kamata ba ko,zan kamata kuma zan kawo ta gabanka,ka tambaye ta dalili idan banyi hakaba,to ka tabbata ban cancanci na zama abokinka ba,kuma abeed sai na kamota indai har Ina numfashi a duniya,abeed ya kamo hannunsa Salim kabi a hankali nidai Ina fada maka,war cewa yayi sannan ya huce ya barshi anan,abeed ne ya kallesa yace ai sai kayi tayi tinda kai bakajin magana.
Nainah farkawa tayi take haske ya gauraye mata idanu,gefe kuma inawar mutum ta gani a zaune akan kujera,baya da kamar 20second mutum ya matso a lokacin ta gane a Ina take,wani daki ne Kato kai kace hole ne Dan tsabar girmansa,cike da tinani maganarsa ta katsesa,ke Azwa wa ma kike,me ya shigo Dake cikin gidana,me kike Nema,kodan a ajiye wannan batun Ina flash din da David ya baki,tsaki taja tana kallonsa,kai waye zaka min wannan tambayar ne,kasan me nakeso da kai mahboob nasan ka ciki da bai nasan tarihinka,nasan ta yanda ka tara kudi,nasan iya adadin mutanen da ka kashe amma ka sani ni bazaka taba iya kashe ni ba,wani wawan naushi ya kai mata,take bakinta ya fashe ya fara fitar da jini,yarinya baki sanni ba kenan,dik wanda ya sake ya shigo cikin wannan dakin baya fita da ransa,ko ki fada min inda flash din nan yake ko kuma yanzu na babbakaki da ranki,dariya tayi tace to babbaka ni kaji,amma kafin nan inaso ka fara daga wayar ka da take haske,kallon wayar yayi yaga new number ta kasar york city,tsayawa yayi domin yasan tabbas yana da ajjiya a wannan kasar,da mugun sauri ya daga,hello baya da Kamar 20second ya Mike yana fadin what me kake nufi ne,and banason jin komai kawai gani nan,juyowa yayi ya kalleta yace kijira dawowata yarinya domin tabbas sai na kashe ki,cike da dariyar mugunta tace to daga baya kenan domin na Riga dana gama da kai,jin karar wata wayar ce yasa shi kallon wayar again number kasar Russia,da sauri ya fita yana share gumi,sauran bodyguard din suka bisa yayin da aka bar daya na fadin nainah.
Dariya nainah ta saka tare da kallon bodyguard din fuska dik jini tace,hey Ina wayata,bai bata amsa ba sai tsayawa da yayi yana kallonta,daga bisa ni kuma shi ma ya fita daga dakin,nainah gyara zama tayi tana goge jinin da yake zubowa,haba Alhaji mahboob kai waye ai kasani daga yanzu babin talaucinka ya bude,domin nakwashe komai na cikin account din ka.
FLASH BACK
BAYAN fitar faisal wayata daga tana fadin shigo kawai ba matsala,turo kofar akayi,wani saurayi ne shi dai ba gajere ba,ba lukuti ba tsaka tsaki,sanye yake da facemask sannan ga jaka a bayansa,zama yayi yana mai ajiye jakar tashi tayi tare da shiga kitchen can ta fito da snacks din da lemo da faisal ya kawo mata,ta ajiye masa,k kallonsa tayi tace ai kasan me zakayi ko,tinda mun gama magana da kai,eaa madam amma ai akwai wasu bayani da zakiyi,wani file ta janyo ta mika masa ka duba dik wani bayanai suna ciki,dauka yayi ya bude sannan ya dago ya kalleta,madam dika fa kuma har account 5,dariya tayi tace eaa naga aiki zaka min ba ruwanka da bincike,tsitt yayi da bakinsa ya kama aiki gadan gadan.
By The Secret Writer
ASHU
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABON LITTAFI
.....Based on Creative Story....
Chapter 14 · 0% Book details