← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 18

PART 11 AND TWELVE

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tin da sassafe Salim and abeed sai wasu Yan sanda da sukayi shiga kamar ba police ba su biyu a cikin mota kirar Jaguar,hussaine ya leko motar yace wai abeed Ina zakuje bayan kasan da cewa Muna karbar gaisuwa,shine zaka tafi kallonsa yayi bayan ya kalli Salim yace aa ai uncle wani waje zamuje ne ni da abokin amma yanzu ZAMU dawo ba dadewa zamuyi ba,yayin da hajiya areefah ke hangesu ta saman bene,da sauri ta juya zuwa dakinta su kuma su Salim suka fice daga gidan.Hajiya areefah ce ke waya ka tabbatar ka kwace wannan motar kai bama motar ba ka bude Boot din bayan zakaga wata jaka mai launin ja ka dakko mini ita zanzo muhadu idan ka gama aikin da nasaka ka,kitt ta kashe tana mai zauna wa Allah yasa wannan aikin nawa nayi nasara a kansa.
Abuja airport ta sauka tana tafe tana waige daga ita sai lace black da ratsin pink a jiki,tafiya take dai dai fitowar ta ne ta kake mota a waje,da murmushi ta shiga motar tai mata key take ta bar wajen,wayar ta ce take kara,saurin dubata tayi ta dauka hello,eaa komai yayi amma ka tabbatar mini da cewa kayi mata full tank ko,ok take ta kashe ta fara kokarin kiran abeed,bugu 1 ya dauka yana mai fadin yanzu Ina kake so na kai maka kudin,murmushi nainarh tayi tace kwantar da hankalinka mana da samari ka duba WhatsApp na tura maka location din,sai a lokacin ta kashe tafiya take a saman titi cike da kwarewa ta masu tuki,dai dai wani restaurant ta tsaya ta ci abinci sannan ta cigaba da tafiya.
BAYAN WASU LOKUTA
Abeed ne ke fadin nariga da na dakko miki kudin amma wannan uban mutanen da Kika turo min na meye,nainarh ce ta furta whaaaat no ni ban turo kowa ba Dan haka dik yadda za ayi ka kasance ka kubuce musu domin indai ka bari wannan kudin suka salwanta to wallahi ka salwanta rayuwar kanwarka,salim ne ya warce wayar wai ke wace irin dakikiya ce kuma jahila mara imani,murmushi mai sauti ta saki tace wait Salim ka dai na zagina domin Kai din ma ba fin karfi na kayi ba amma Ina baka girma ne saboda ka kasance police kuma bani da wata alaka da ku,amma Ina da alaka da Abeed ka sani wallahi ko Kaine aka maka abinda aka min abinda za kayi kenan,sannan ka kula min da jakar kudina na fada maka,katsewar wayar ne yasa abeed karawa motar gudu sukayi nisa sosai inda ta nuna musu location din nan din suka nufo amma me abin ya basu mamaki ganin daji ne,dik wannan abin da ake nainarh Sharwaz na kallonsu tana murmushi dakyau ta furta,sun Dan ja baya kadan sannan da guns a hannun su,wayar ta dakko ta kirasu meye na wani tahowa da bindiga kamar zaku kama yar ta'adda,murmushi Salim yayi yace ai ke har kinfi yar ta'adda Ina mai tabbatar miki da cewa yau sai na kamaki,dariya tayi tace Allah to Ina maka fatan nasara malam ACP Salim Muhammad.
Da gudu suka shigo kan titin yayin da suke bin location din da jakar ta nuna anyi da su gudu suke dai dai wani bakin gida karami suka tsaya suna kallon gidan,take Salim ya bada umarnin a zagaye gidan shi kuma shi da Abeed zasu shiga,shiga sukayi tin daga bakin kofar falon suke jiyo warin cigarette,shisa and tobacco,take suka shige dakin abinda ya basu mamaki shi ne wasu dabar Maza ne a zaune sai shaye
suke,take Salim ya Dana bindiga sa ya kallesu yace Ina shigabarku gaba daya dariya suka sa,wane irin shugabar mu,kai mu shugabanmu yana ciki shiga mana zaka gansa,dik wannan maganar cikin maye suke yin ta da gaji kasan ba hankali,dakin da ya nuna musu suka shiga jaka suka gani a ajiye ba komai sai tilin ganyayyaki da takardu,salim ne ya furta ohh shitt amma wannan yarinyar anyi hatsabibiya,kiran wayar abeed ne ya katse sa,dariya ce ta fita daga cikin wayar tace wai ku tinaninku karami ne an gaya muku Ina yadda da mutane,bana taba yadda da mutane shisa a lokacin da kuka bani kudin na chanja jaka sannan na bar wannan anan,ta yiyu yanzu wani ya dauka ne sai dai ku kama shi sannan kuma kudi ne nariga da na samu yanzu ku Jira zuwa nan da kwana 2 masu zuwa ranar sadakar 7 kenan zan dawo muku da babe byeee.Salim ne ya rike kugu yana mai wani irin jin bakin ciki da yasa bai kama ta ba,fita yayi kawai abeed kuwa bin bayansa yayi yana mai Dana sanin abinda ya faru,salim ne ya kalli Abeed yace tabbas abeed sai na kamata a ranar da zata kawo kanta nan da kwana 2 zan shirya mata Shirin fa sai tayi matukar Dana sanin zuwan ta Abuja dawo da babe,abeed girgiza kai yayi yana mai tinanin wani abun daban,domin yasan da cewa ba Wanda yasan sun dakko wani abu a jaka daga mommy sai shi sai Salim sai wannan police sin biyu.
Hajiya munyi rashin nasara kafin muje an Riga da an kwashe komai a cikin jakar ba abinda muka samu sai wasu takardu da yayi,whatt kana da hankali guy kasan na wane a jakar,oh my god take ta katse wayar tana mai tinanin abinci daga baya kuma ta fashe da kuka,wannan yarinyar anyi hatsabibiya kin rabani da komai saboda haka sai kuma tai shiru kasancewar ifty ce ta shigo,da sauri ta kara so aunty kuyi hakuri babe zata dawo,wani kallo ta mata Wanda in Banda ita ba Wanda yasan me yake nufi,sai ni da nake zaune Ina Baku labarin,can kuma ta saki murmushi da fadin ba komai iftinan,dama aunty kinyi baki ne daga Katsina,take ta mike tana fadin to muje mana ifty ko,to ta amsa ta wuce gaba iftinan na binta a baya.
Dare yayi sosai a zaune na ganta a gaban laptop tana kallon yanayin gidan Alhaji mahboob da abinda yake faruwa murmushi ta saki inan tafe,na baka kwanaki 2 ne ka huta saboda nima inaso na gama wannan aikin ne amma Dana dawo kareka wallahi sai ka rasa inda zaka saka kanka,hhh ba takamarka safeenah ba,ni kai zan farwa ba 'yarka ba,tashi tayi ta kalli babe Dake zaune tana cin abinci murmushi tayi mata babe ki gode Allah domin nan da jibi zaki koma wajen mahaifiyarki,tashi tayi dik da nagama mahaifiyar take ba sonki take ba amma ai ke kina sonta,wucewa tayi har tayi nisa ta tina da wayarta Dake kara komawa tayi ta dakko,daga wa tayi banji me aka ce ba sai zubewa tayi a kan kujera tana fadin inalillahi wa inna ilaihi rajiun take sai ga hawaye sharr karo na 2 da Naga hawaye akan fuskar nainarh Sharwaz,take ta mike ta shige daki ta bar babe anan da take kallon cartoon tana murmushi.
BY the SECRET writer

Ashu
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABON LITTAFI
.....Based on Creative Story....
Chapter 6 · 0% Book details