← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 18

PART 3 AND FOUR

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

NIGERIA????????
Abuja airport anan jirgin ya sauka yayin da dik wani passenger ke fitowa da jakansa,fitowa yarinyar tayi take ta saki murmushi tana kallon yanayin garin da zai iya zubda ruwa ko wane lokacin,daga ita sai karamar jaka a hannunta,tafiya take sannu a hankali,dai dai bakin airport din ta tsaya tare da daga waya Naga banganka ba,take wata mota ta kara so gabanta,da Dan sauri ya fito ya bude mata sannan kuma ya rufe yaja suka bar wajen.Tafiya suke ba wani Wanda yace wa wani uppan,dai dai wani madaidaicin gida ya tsaya fitowa yayi ya bude mata ta fita tare da daukar karamar jakarta,kaje sai na nemeka zan tura maka kudin,ok yace yana mai fadin Allah ya huta gajiya,kallonsa kawai tayi ta tsaya tare da zuwa key ta bude gate din tare da shiga cikin gidan kai tsaye.
Garki Abuja wani shahararren gida ne kai da gani kasan naira ta samu wajen zama,katon parlorn wata mata ce katuwa zaune akan sofa tana shan kayan marmari abinta kai kace ba abinda yake damunta,jin karar waya ne yasata daga kai ta kalli wayar sai kuma ta saki murmushi,dagawa tayi tana fadin hello Zeezee yadai,ok shikenan katsewa tayi ta kuma gyara zama tana kallon television din tashar arewa24,jin karar wayar ne yasata kallon screen din number ce kai da gani kasan bata kasar nan bace dagawa tayi tana mai tashi zaune,eaa yallabai ok yanzun nan zan taho,tashi tayi bayan ta ajiye wayar akan table shigowar wata budurwa ce ta kalleta mommy Ina kuma zakije kallon ta tayi tai murmushi babe Germany zan tafi yanzun nan kuma kira min yayanki a dakinsa kinji,toh mommy zan biki ta kalleta tana jiran abin da zata fada,kinga babe sorry bazani da ke ba fa,take ta zube a kasa ta fara kukan shagwaba tafara jijjiga kafa,kallonta matar tayi tace shikenan tashi Maza kije ki shirya ki kiramin Abeed kin ji to ta amsa ta wuce tana tsalle da murna,gajiya tayi ta tashi zatabi bayan babe shigowar Abeed ne yasata saurarawa tana fadin kaje ka shirya kazo mu wuce Germany Dan an kirani ance min ba lafiya kuma Ina mai tabbatar da cewa wannan hatsabibiyar yarinyar ce Dan nasan dama dole sai ta bayyana,firgigit ya kalleta sai kuma ya tashi da mugunta sauri ya fice Shima,basu dau wani lokaci ba sai gasu sun fito a shirye suna masu yiwa gateman kashe da kuma yiwa ma'aikatan gidan sallama dik da cewa gobe zasu dawo ko zuwa dare.
A zaune take ta dora kafa daya kan daya tana ta aikin Danna waya wata shimi ce a jikinta yayin da ta kulle kanta da ribbon kalar shimin,murmushi tayi tana yi tana shan coffee din data hada,domin gasa cikinta,kallon system din tayi ganin tayi mata alert take ta ajiye wayar da coffee ta maida hankalinta kan systems din shiga Naga tayi taje Naga videon yadda hajiya,babe da Abeed ke fita daga cikin gidan su,take ta kurma ihun samun nasara,amma kuma taje sai launin fuskarta ya chanja ta fara lissafin abubuwa,can kuma ta saki murmushi hakan ma yayi min hajiyah areefah katsewa tayi ta kishingida ta kwanta tana tinanin abinda ya kamata kuma yanzu,can kuma ta tashi na gama da wannan daga zarar na kwashe dukiya ta daga wajen su amma taya zan iya wannan aikin ni kadai,murmushi ta kara yi a karo na biyu zan iya mana ni ce fah take ta saka dariya.
A yanayin garin ruwa ake sosai Kamar da bakin kwarya,fitowa tayi daga dakin sanye da fararen kaya doguwa ce sai kuma rigar ledar da ta dora akai tana tafe tana murmushi,abinda ya bani mamaki shi ne ganin take lokaci guda ta dare Katanga ta haura,cikin gidan su Abeed na ganta amma kuma ta baya,tafiya take cike da sanda kamar barauniya,kofar baya ta murda jin a kulle yasata furta dama nasan za a yi hakan,aljihun rigar Naga ta duba take ta fito da mukulli ta bude,shiga tayi kofar gaban tace ta sakawa lock sannan ta dawo ta cire wannan rigar ledar da farar rigar sai gata kuma ta wata yar karamar Riga iyakarta gwiwa tana da sararren hannu,shiga ta fara yi kai kace tasan gidan dama dai dai wani daki ta tsaya tana murdawa yana budewa murmushi tayi,shiga tayi take hoton Alhaji Hassan tsaki ta ja tare da daukar hotan ta wulla shi gefe sai kuma ta saka dariya kamar wata mahaukaciya,locker ta fara bi tana budewa kamar wata zararriya can kuma ta bude ta karshe take idanunta yakai kan abinda take nema,takardune fito da su tayi ta wuce daga dakin zuwa parlorn shirya su tayi ta zuba a jaka sannan ta saka la ta maida kayanta ta fice kamar ba wani mahaluki daya shiga gidan.Bayan wasu mintuna a parlorn na ganta tana ta murmushi ita daya kai da gani kasan na mugunta ne,abinda ya bani mamaki daki ta shiga ta ajiye takardun tabi lafiyar katifa.
A tsaitsaye suke yayin da hajiya areefah da Abeed suke kallon juna ita kuwa babe ma bata wajen ko Ina suka ajiye ta oho musu,wani babban ma'aikaci ne ya kallesu ya furta come inside ma,shiga sukayi yayin da wasu kuma suka turo wani gado kai da gani kasan Wanda ake dora gawarwaki ne suna tsayawa gaban hajiya suka juya,babban ma'aikaci ne ya matso tare da dage kyallen take idanunsu sukai tozali da Alhaji Hassan kwance a mace wani mahaukacin kuka areefah ta fasa Wanda dik yawancin ma'aikatan sai da suka juyo da kallansu kanta amma ita bata damu ba,da kyar Abeed ya jata waje idanun nan sunyi jawur kamar gauta,zaunar da ita yayi Shima yana mai give hawayen fuskarsa,sai kuma ya tashi ya shiga ciki,yafi awa 1 a ciki sai ga shi ya fito mommy ki tashi mu tafi komai ya kammala muje muyi Shirin komawa gida domin mu samun a binnesa,amma mommy kinsan wannan ya fiddo da wayarsa yana nuna mata videon mommy sunan ta nainarh Sharwaz murmushi ta saki amma da gani kasan na bacin raine,wannan ita ce wadda take bibiyar mahaifin ku dama kawai tayi baddakama ne,tafiya take,dai dai bakin hotel din ta gyara fuskarta suka shiga,a zane suka tarar da babe sai games take a wayar ta,mommy ce ta kalleta to babe tashi mu tafi ko,to ta amsa ta tashi ta dakko jakarta,kafin suje airport komai ya kammala daga nan suka dunguma suka taho Nigeria.
Karfe 6:00 na safe ne Dan haka jerin motoci ne suka zagaye su anan fa suka shiga gaba daya areefah na cikin tashin hankali domin tasan wacece tai wannan kisan amma bata da sheda,kallon Abeed tayi tace taya akai suka baka wannan gawar ma kasansu da shegen tsattsauran ra'ayi,fuskar nan da gani ba mutunci mommy Bayani nai musu kuma sun gamsu Suma sun tabbatar da cewa makashiyar tana nigeria shisa suka bani gawar,abeed areefah ta fada juyowa yayi karna kuskura naji kacewa Yan uwan mahaifinka cewa kashe sa akayi,kallon ta yayi da mamaki amma mommy why take ta bata rai tace umarni nake baka Abeed kawai ka ce mini to ba ka tsaya kana min wannan tambayar ba.jin anyi parking ne yasa su kallon hanyar anan ne suka ga ASHE har sun iso babe kuwa bata ma motar tana motar gaban su ,fitowa sukayi suna kallon yanayin garin da akayi ruwa jiya,shiga gidan sukayi ba ayi wani kwakkwaran minute 50 ba sai ga gida ya cika da mutane kasance war Alhaji Hassan babban mutum ne a fadin garin Abuja,babe kuwa tana can wajen garden tana wasa da wasu yara su biyu,a kusa da su wata mata ce sanye da hijabi tana kallonsu,matsowa matar tayi tace sannu yara wacece babe anan,dagowa babe tayi tace ni ce murmushi tayi tace Zo na aikeki waje ki dakko min teddy a mota na,da sauri ta tashi tana mai kallon ta domin ita a rayuwar ta tana son teddy,mukulli ta Mika mata ita kuma ta fice baya da Kamar second 30 sai ta bi bayan ta a lokacin ana kokarin fita da gawar Alhaji Hassan a waje ta ganta a tsaye,wayo tayi mata har ta shiga motar,shiga ita ma tayi take ta janyo wani tissue ta Shaka mata shi a hanci anan wajen ta zube a kasa,kujerar baya ta kwantar da ita tana mai ta da motarta da barin gidan.
THE SECRET WRITER

ASHU??
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABUWAR MARUCIYA
SABON LITTAFI??
.....Based on Creative Story....
Chapter 2 · 0% Book details