← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 3 OF 18

PART 5 AND SIX

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Gudu take shararawa a saman titi kamar zata tashi sama tsabar sauri lokaci guda ta fita daga garin Abuja,gudu take bata dade ba ta iso garin kano ta dabo tumbin giwa,nasarawa G.R.A anan ta fara horn budewa akayi ta shiga gidan kallon gidan tayi daga motarta sai kuma ta tabe baki ta fito a lokacin babe ta farka ganin ta a wani gida na daban ne yasa ta kwala kara da kuka wani kallo ta bita da shi take ta hadiye kukan,tafiya take yayin da wani saurayi na binta,ka tabbata komai dai dai ko ba Wanda zaiga komai,murmushi yayi yace ba tabbatar miki madam,shikenan danna waya tayi ka duba nasa maka kudinka,take yaji kudin shikenan to madam sai anjima ka tafi da wannan motar Dan ta gama amfani,tafiya yayi ita kuma ta ja hannun babe suka shiga parlorn gidan tana shiga ta wulla ta kan kujera sannan ta lock din kofar ta shige dakin da yake kallon ta.
ABUJA
Abeed ne ya shiga dakin mahaifinsa ganin dakin kaca
ne yasa ka shi dube dube da sauri ya sauki wayarsa yayi dialing number areefah,bata dade ba ta iso yana ganin ta ya kalleta mommy ya haka kuma kalli yadda akayi wa dakin dik wasu takardu masu muhimmanci an dauke su mommy kenan wa ya shigo,dube dube take amma ba wata alama da sauri ta ce kiramin Audi mai gadi,waya ya daga ya fara dialling number sa a bayan gidan suka hadu Audi rantse
yakeyi akan shi fa ba Wanda ya shigo gidan nan domin sai da ya rufe ko Ina sannan ya kwanta,hajiya ce ta furta inalillahi wa inna ilaihi rajiun shikenan Abeed wallahi mun mutu,tsaki Abeed ya ja ya koma yayin da hajiya ta wuce ta falo wata yar uwarta ce tana tambayar ta me ya faru amma ta kasa bata amsa kawai bakomai ta furta ta juya taci gaba da tafiya.
Fitowa tayi tana mai kallon inda ta bar babe tsaki ta ja tana furta aikin banza kawai,jin karar waya ne yasata kallon wayar private number ce ko kallo bata yi ba bare a saka ran zata dauka,zama tayi tana kallon yarinyar take kuma ta dauki wayar tana dannawa sai kuma ta fara yiwa wannan kyakkyawar babe video yayin da ita kuma take kuka tana kiran mommy da Yaya Abeed tsaki taja take ta shiga WhatsApp ta fara lalube wata number ce da akayi save da A ta tura videon sannan ta kashe wayar tare da tafiya Dan jin ana knocking ta Riga da tasan ko waye.
Abeed na kwance abun duniya ya isheshi ya rasa ta inda zai fara tabbas wannan yarinya akwai shegiya,gashi shi yanzu ba zai iya cewa gata ba domin daddy ne ya santa,jin karar Sako ne yasa ka shi sakin tsaki aikin banza ya furta tare da tashi ya shige bandakin dakin domin watsa ruwa tare da dauro alwalar sallar azahar,fita yayi aka ja jam'i da shi daga haka kuma ya nufi dakinsa ya kwanta yana kwanciya bacci ne yayi awon gaba da shi.Hajiya areefah ce zaune a private room din su wani mai kama da Hassan ne yace areefah tayaya za ace Hassan ya mutu kuma ace farat daya ki fada mana tayaya ace mutum cuta,murmushi areefah tayi tace ai dama dole ne a mutu ko da ciwo ko babu ciwo domin dik mai rai sai ya dandani dacin mutuwa,sannan kuma da kake wannan abin Hassan a Germany ya rasu kuma nayi bincike ya nuna cewa eaa lafiyarsa kalau kawai cuta ce ta lokaci daya,dan haka ba sai mun tsaya Muna wani bincike Hussain da haka ta tashi tana mai goge hawayen fuskarta.
Fitowa tayi ta kalli babe sai kuma ta ja tsaki sanye take da Riga da wando hade da belt a saman wandon,kalar ja sai wani bakin mayafi datai rolling din sa,ke idan bazaki ci abincin ba zaki iya zubarwa Dan ubanki,ficewarta tayi ta barta anan tare da saka lock a kofar,dai dai bakin kofar ta tsaya tana jiran ta samu abin hawa,wata mota ce kofar Jeep tai parking a gabanta,tare da zuge glass din motar tsaki ta ja tana mai fadin aikin banza kawai dik kyanka ba ta kai nake ba yanzu a Fili kuwa hade rai tayi Kamar bata tana dariya ba,mutumin ne ya kalleta yammata barka,tsaki ta ja a lokacin wani mai nafef yazo wucewa tsayar da shi tayi ta shige tabarsa anan yana mai murmushi a bakinsa,karki damu domin tabbas na samu mata Dan sai na aureki,da haka yaja motarsa ya wuce yana mai tina kyawun da Allah yayi ma wannan yarinya.
Sai can wajen la'asar areefah ta fara Neman babe gaba daya Neman ta akeyi a lokacin mutane sun fara tafiya kuma domin dik sun watse sai kanwar areefah kawai mai suna iftinan budurwa ce,nemanta suke kofar dakin Abeed ta tsaya ta fara knocking tashi yayi yana kallon kofar budewa yayi iftinan ya gani hankali tashe,abeed kaga babe kuwa zaro Ido yayi yace aunty ifty me ya faru ne wai,meye ma bai faru ba Abeed babe muke Nema hajiya tace tin safe rabon da ta ganta,kuma mun tambayi masu aiki dikansu sunce basu ganta ba,ba abinda ya furta sai inalillahi wa inna ilaihi rajiun babe da sauri ya fito yana dubata amma Ina ko sama ko kasa bai ganta ba,mota ya fito da ita direct ya bar gidan yana zagayawa unguwar,yayin da areefah ta fara dialling number dik Wanda tasan babe zata bi amma Ina ba labarinta,haka Abeed ya gaji ya dawo gida yana mai nuna bacin rai,dakinsa ya shiga ya dakko wayarsa dialling number wani abokinsa police yayi amma taki shiga,hakura yayi ya ajiye wayar,wata dabara ce ta fado masa tare da shiga WhatsApp ganin wata number yayi amma ba suna,bai ko duba ta ba ya fara yiwa abokinsa magana,har zai sauka sai yaga video ne,ya san akwai matsalar da yake fuskanta shi sa ya shiga ya kunna video babe ce ke kuka da kayan da suke jikinta,take ya fara kwala kira babe babe mommy aunty ifty kuzo ga babe,areefah da iftinan har hada kai suke wajen gudu.
??ASHU??

Secret Writer
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABUWAR MARUCIYA
SABON LITTAFI
.....Based on Creative Story....
Chapter 3 · 0% Book details