← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 18

PART 9 AND TEN

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Salim ne zaune a dakin Abeed,kallon sa yayi yace kasan yanzu Mene abinci l,nasan dai zancen ba zai huce kudi ba,zamu bata abinda take amma kuma Abeed dole musaka naurar bibiya a jikin jakarki kudin,domin mu samu mu kamata,abeed ne ya kallesa yace Salim kana ganin abinda ka fada zaiyu kuwa,kiran waya ne ya katsesa,kallon wayar yayi ya ga private number ce dagawa yayi yana mai fadin hello daga dayan bangaren ne akace kasa wayar a handsfree,saka ta yayi yace inajinka kasance war muryar namiji ne,kasani Abeed na nuna maka babe amma ka tsaya biyewa Yan sanda ko,wallahi thumma tallahi abeed kasani police bazasu iya kamani ba saboda naci dubu sai ceto,sannan Ina mai tabbatar maka da cewa idan har zuwa wani week din baka kawo min abinda zan fada maka ba to ka sani sai dai na aiko maka da gawar kanwarka,abeed baiyi magana ba yayin da Salim ke kallonsa ganin yaki magana ne yasa shi yi masa alama da fadin ta fadi me yake so,murmushi akayi mai kake ci na baka na zuba malam Salim zakakurin Dan sanda kenan mai aiki da gaskia sunanka Muhammad Salim Auwal inkiya Salim zakakurin Dan sanda Wanda ke aiki a garin Abuja,sunan mahaifiyarka Hajiya Zulaihat sannan kuma kana da Kane guda 1 Wanda ya kasance shi din ya tafi aikin soja,sai kuma akai shiru mudawo kan maganar mu inaso ka tanadar mun naira billion 10 sannan kuma kasaka a kawo mun su inda zan fada maka,and idan ka kawo mun ni kuma zan dawo da baby inda na dauketa sai anjima ka huta lafiya malam Abeed and ACP Salim Muhammad kit aka kashe wayar ba abinda suke sai kallon kallo a tsakanin su.
Alhaji mahboob ne a zaune sai diyarsa safeenah wadda suke breakfast cike da farin ciki,bayan gamawarsu ne ya kalleta yace to safeenah Maza kije ku tafi karki late and ki dawo da wuri ko,dan zumburo baki tayi kai daddy zan tsaya fa aimin saloon sannan kuma zan karar wayar ta ce yasata kallon wayar grandy aka saka,take ta saki murmushi ta tashi ta dauki wayar ta fice tana fadin sai na dawo daddy ka kula da kanka,murmushi yayi yana kallon ta,babban yaronsa ne ya shigo wajen yallabai sir mun bincike gaba dayan gidan David amma ba wata cameras dai dai da laptop dinsa mun duba amma babu komai,tsaki Alhaji mahboob yaja to me kike Jira ku aika min shi inda ba'a dawowa,murmushi babban yaron yayi yace ai da dadewa ma yallabai,good shisa nake Sonka domin Kai aikin ka ba wasa take kake yinsa,tashi yayi yace masa muje yau inada meeting da wani babban Dan kasuwa fitowa yayi yayin da shi kuma yake take masa baya.
Salim na fada maka Wanda ya sace babe hatsabibi ne,da kuma kace min macece ta sace ta,ea da farko na dauka nainarh Sharwaz ce ASHE ma ba ita bace,amma Salim nayi mamaki taya ya sanka haka,murmushi Salim yayi yace kada ka damu da wannan ta turo address din da za a kai mata kudi ka kawo ni zan kai kudin and daganan sai na kamata,sannan inaso ka sani cewa wannan muryar ta macece domin da gaji kasan change voice akayi,shiru Abeed yayi yana saurarensa,daga karshe to ya furta sannan ya tashi yana zagaye dakin abin duniya ya ishesa,gashi bata barsa yaji da rasuwar mahaifinsa ba.
Hajiya areefah ce ke danna waya a dakin ta ita kadai kai da gani kasan akwai kullalliya dagawa akai yawwa abinda nakeso da kai shi ne dik yadda za ayi dik rintsi inaso ka nemomin nainarh Sharwaz domin tabbas nasan tana cikin NIGERIA amma hajiya ki turo min hotanta,kai dallah daka ta min ace kai bazaka iya nemota a haka ba,to nima kaina bansan ta ba wannan aikin shi nabaka,wane aiki kuma mommy fadin Abeed da yanzu ya shigo shi da Salim,saurin katsewa tayi tana fadin ba wani abu bane dama aiki ne na bawa sule driver,ouhh shikenan dama magana zamuyi shikenan to ku zauna ta fada,abeed ya fara yi mata Bayani tana ji,a lokacin data ji zancen naira billion 10 take hankalinta ya tashi ta fara sake
ita ba abin tace kar a tura ba ta bata aiki,shikenan abeed dik yadda kayi ni burina dai babe ta dawo cikin kwanciyar hankali da lafiya,to ya amsa sannan ya kalli Salim yace to yanzu dik wani shirye shirye suna hannunka ni dai zan je na dauko maka su kai kasan kuma yadda za kayi amma Dan Allah a kamamin ita domin so nake na hukunta ta kafin doka ta hukuntata,baka da matsala abeed fadin Salim yayin da yake kallon mood hajiya areefah ya chanja kawai sai ya barshi a mutuwar Alhaji Hassan mijinta.
Nainarh Sharwaz ce ta fara horn kofar gidan Alhaji mahboob gate man ne ya bude ya kalleta sai kuma ya kara so yace hajiya sai dai bangane ki ba,wani murmushi ta saki tace dama nasan za ai haka,wannan shi ne I'd di na sunan Azwa Mujahid sannan kuma Alhaji mahboob shi ne ya turo ni domin nazo na jirasa and ni yar jari da ce,to hajiya take ya koma ya wangale mata gate kamar yadda ya saba,fitowa tayi tana taku dai dai doguwar Riga ce a jikin ta sai wani Dan mitsitsin mayafi Wanda da shi kara babu,kallon gate man din tayi tace zan iya shiga,eaa hajiya ki shiga mana,murmushi tayi Wanda ta tabbatar da cewa lalle tarkonta yayi Kamu,shiga tayi ta fara zagaye falon tana wasa cameras wasu kananu,zaka rantse da Allah haka ba camera bane,sai da ta gama aikin ta tsaff sannan ta kalli time,sai kuma tai hanyar kitchen anan ma ba kowa wata camera ta saka saman ta fito,gateman na hango ta ya taso yana washe baki,ya naji gidan shiru murmushi yayi yace ai dama masui aikin suna wancan dakin ko na kira miki su,da aa ta bishi,sai kuma ta kalli watch din hannunta,kaga Naga alamun Alhaji mahboob ba yanzu zai dawo ba amma Ina tinanin kawai zan tafi na dawo anjima,hannu ta saka a jaka ta dumbuzo kudi ta Mika masa Wanda itama bata san ko nawa bane,mota ta shige ya bude mata gate yana fadin Allah ya kiyaye hanya hajiya Azwa ficewa tayi,tayi Dan tafiya mai nisa sannan tai parking motar laptop din bayan kujerar ta janyo take tai connected sai ga komai na gidan ya bayyana,murmushi ta sak
i tana fadin gani nan zuwa kanka Alhaji mahboob sai kayi Dana sanin sanin mahaifina a duniya.
BY THE SECRET WRITER
Ashu
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABON LITTAFI
.....Based on Creative Story....
Chapter 5 · 0% Book details