PART 7 AND EIGHT
Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Inalillahi wa inna ilaihi rajiun aunty areefah babe ce wannan,gaba daya dakin kowa ya shiga taitaiyinsa ba mai magana,areefah kuwa kuka ta saka tana mai Dana sanin barin babe ita kadai a wajen a lokacin da mutane suke shiga da fita,ifty ce ta kalli Abeed ta ce kira number nan muji,kira ya fara kokarin yi amma Ina anki dagawa daganan kuma sai ga kiran Salim wato police man abokin abeed,dagawa yayi yana mai furta hello gaisawa sukayi har yayi masa gaisuwa,abeed naji abinda ka ce amma ka bari gobe zanzo gidan dik yadda ake ciki ZAMU samota insha Allah kaji,abeed ne ya ce Salim sun tura min videon babe,ta ina Salim ya tambaya ta WhatsApp amma bari na tura maka ka gani,ok ya furta tare da katse wayar yana mai kokarin komawa WhatsApp din da tura masa.
Katafaren gida mai cike da kyau,kudi da kayan more rayuwa,na shiga domin dauko muku rahoto,wani katon gate black aka wangame take manyan motoci ke shigowa kirar Jeep sai kuma wata a tsakiya fara sol,tin kafin ayi parking manyan sojojin ke dirowa tare da tattarewa a gaba motar nan mai launin fara,sai da komai ya kammala sannan aka bude motar,wani dattijo ne amma kai da gani ai bazaka kira shi da dattijo ba,saboda kudi sun zauna a gurin wannan dattijo,fitowa yayi yana mai kallon gidan kamar wani Wanda ba a gidan yake ba,tafiya yake yayin da sojojin ke take masa baya,dai dai lokacin da zai shiga falo ne ya kallesu yace ok,gaba dayansu juyawa sukayi suka barbazu kowa ya kame yana muzurai kamar wasu karnukan farauta.Alhaji mahboob kenan cikakken Dan gwagwarmaya kuma babban Dan siyasa,a dik fadin nigeria ba Wanda bai sanshi ba,mutun ne shi mai fuska biyu,fuskaar farko ya kasance mutum mai kyauta amma fa idan yaso fuska ta biyu kuma ku biyoni don ji.A falo na tsinto shi ya zauna yana kallon yarinyar sa da take takowa da sauri Masha Allah kana ganin ta kaga kamaninta Dana ubanta Alhaji mahboob dik duniya wannan yar tasa ita kadai ya mallaka,Safeenah ta kasan ce kyakkyawa,a kasar Poland take karatun ta tin daga matakin Primary har zuwa yanzu data kammala Secondary ta dawo NIGERIA ne saboda tana son ziyarar kakaninta kasance war mahaifiyarta ta rasu wajen haihuwarta,alhaji mahboob ne ya kalleta yana fadin safeenah ya makarantar turo baki tayi haba daddy sai kuma tayi shiru,shikenan safeenah am so sorry,dariya ta saka daga nan suka juya alamar hirar zuwa wata daban kai da gani kasan suna cikin farin ciki.
Ba ita ta dawo ba sai wajen karfe 10 na dare shiga gidan tayi kai tsaye parlorn ta bude ta shiga kallon inda ta bar babe tayi gani tayi tana bacci,tsaki taja ta huce zuwa dakinta,jakar da tazo da ita ta ajiye akan gado tare da shigewa bandaki,wanka tayi sannan ta dawo ta zauna,jakar ta dauka ta fara zazzage abinda yake ciki hotuna ne barkatai,sauri tattare su tayi ta dakko wata jaka ta durasu tare da mikewa tsaye,a gaban babe na ganta a tsaye tana kallon ta kama ta tayi tana murmushi ta kwantar da ita kan kujerar dakin sannan ita kuma ta shige dakin ta bayan ta tabbatar da ta kashe fitilar dakin.
Safeenah look dole ne ki bisu ku fita tare saboda me na tara kudin ai saboda ke ne,saboda na kyauta ta miki,jin wayar sa na kara ne yasa shi kalla,dagawa yayi tare da karawa banji mai aka ce ba,sai cewa yayi ku ajiye min shi a gidan gonata zuwa gobe ZAMU hadu dashi,safeenah ce ta kalleta ta ce daddy dawa kake waya,karki damu my safeenah abokin kasuwanci ne ya kawo min kaya kinji,ok daddy amma kasan da cewa dai gobe zanje siyayya saboda kasance war ZAMU kauye ko,murmushi yayi na sani amma safeenah tayaya Kika iya Hausa haka,murmushi tayi koya nayi mana daddy da YouTube,kallonta yayi yana mai kara jin kaunar yarsa a cikin zuciyarsa,sai wajen 11 sannan sukai sallama ya Rakata dakin ta ta kwanta,sai da ya tabbatar datayi bacci sannan ya zame jiki ya fice daga gidan zuwa gidan gonarsa.
A katon filin Dake gidan gonar na hango yayi parking motarsa,yana mai takowa ya kara sa cikin katon hall din Dake cikin gidan gonar tasa,shiga yayi yana mai kallon wani mutum a daure tamau da igiya akan kujera ga bakinsa nan dik a fashe,a takaice dai kallo daya zakai masa kasan cewa tabbas yaci duka,duka bana wasa ba kuwa,karasawa Alhaji mahboob yayi ya daga kansa yana mai kallonsa,ina cameras din nan,murmushin karfin hali mutumin yayi yace na boyesa,wani kallo ya bisa da shi wato kenan kana nufin bazaka bani ba,eaa ya amsa masa,alama yayi wa wani daga cikin mutanen sa take yazo ya fara jibgarsa,shi kuma ya harde ya zauna akan kujera yana kallonsa,ya Isa Alhaji mahboob ya furta kasani David idan ka bani videon nan zan sake ka kuma zan maka Sha tara ta arziki,wanda aka kira da David ne ya kallesa fuska jawur karya kake Alhaji mahboob wallahi karya kake domin nasan ko da nabaka ko ban baka ba kashe ni zakayi,dan haka na bada shi inda za'a nuna kowa ma ya gani,wanin wawan naushi aka kai masa Wanda ya katse maganar ta sa,dagowa yayi ya kallesa sai yayi murmushi Alhaji mahboob kayi kuka da kanka domin nan gaba kadan zaka rasa wani babban abu naka da kake matukar ji da shi Ina mai baka shawarar tin wuri ka adanasu,mikewa tsaye yayi sai kuma ya kalli mutumin nasa yay murmushi,mutumin ne ya kallesa yace yes sir da haka ya fice ya tafi zuwa gidan sa.
Abeed,areefah,ifty gaba dayansu ga sunan a zaune ba Wanda ya kara magana kowa na sake
a zuciyarsa,abeed ne ke sakawa dama naga wadda ta kashe min mahaifi,ina ma zanga wadda ta sace babe da yau na tabbatar mata da cewa ni ma da ne domin tabbas nasan Wanda ya kashe daddy shi ne ya dauke babe,tsaki yaja yayin da hajiya areefah ke fadin wai shin Dame zanji yarinya ta hanani rawar gaban hantsi,shikenan ni dik wani kulli Dana kulla sai ta since shi amma ya kamata na dauki mataki akanki domin Naga kinaso ki hanani nasake,ifty kam sai raba Ido take ta rasa ma tinanin me zatayi,kawai saita kwanta akan sofa tana mai zare idanu kamar wata munafuka.
By the secret Writer
Alkalamin ASHU
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABON LITTAFI
.....Based on Creative Story....