← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 18

PART 19 AND TWENTY

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Hammad ne kwance akan gadonsa mai matukar kyau da daukar hankali,tinani yake sai kawai yayi Murmushi Ina ma zan ganki,domin tabbas naji cewa Ina sonki tin daga kallon farko da nayi miki,amma kin tafi baki tsaya na gabatar miki da kai na ba,shi kadai yake ta wannan tinanin nasa da ba karewa zai yi ba.
Sokoto dira tayi a gidan data sauka,a lokacin safiya ce,kUma ta kama weekend dik akasarin mutanen gidan na daka na bacci,take tai parking ta fito ta wuce zuwa dakinta,tana zuwa ta fada kan bed tana huci kamar wata zakanya,t Sam ta mike tare da shigewa toilet,ta Dan Jima sannan ta fito daga ita sai tawul,sai kuma wani tana goge ruwan kanta,akwatinta ta bude tare da dakko wata yar Karamar Riga ta saka sannan ta bi lafiyar katifa,rintse idanun ta tayi tana tina rayuwar baya daga haka kuma zumbur ta mike,kallon kusuruwar dakin tayi anan ta gane ta manto wayar a mota,dawowa tayi ta kwanta tare da rufe Ido sai dai ta kasa bacci,saurin budewa tayi tana huci,sai kuma ta fashe da kuka,ganin bacci ya gagareta ne yasata mikewa,wata rigar ta sanja ita ma din dai dik yar karama ce,sannan ta nazo da dogon gashinta,tana murmushi ta fice daga gidan,motar dazu data shigo da ita ta kalla taga tayi dauda,dik ta kukkurje,da haka ta fice tare da tare mai napep,wani katon eatery Naga ta shiga take tai ordern abincin tana ci.
Hajiya wallahi sai dai kiyi hakuri domin nainah ta gudu,kai oga mai kake fadi haka mai kake tinanin cewa,kana nufin kace min ta gudu wai kun kasa kamata to kai kana aikin me,hajiya sai da ta jiwa mutanen mu a kalla guda 6 ciwo,anya hajiya nainarh ba aljana bace domin wallahi batt muka nemeta muka rasa,naji shikenan yanzu na Baku nan da 24 hours ku Nemo min ita dik Wanda ya kawo ta zan Basa naira million 1,allah hajiya tsaki taja tana fadin na tana muku karya ne ko na tana muku wasa a kan kudi,aa hajiya ko daya kawai dai Ina so ne na tabbatar da abinda kunnena yake ji minne,amma shikenan zamuyi yadda kikace,da haka ta katse wayar tana mai Jan tsaki,dik AC da take kadawa a dakin amma wani mugun zafi takeji.
Abinci take ci hankalinta kwance,shigowar wasu samari ne yasa ta fara kallonsu tin daga sama har kasa su 5 ne ko wanne yaci wanka wanda ba laifi yayi kyau sosai,a dai dai lokacin data kalli na karshe ne idanunta suka sauka akan na zaid yaro ga Alhaji SALMANU nai ji da naira,da wani kallo ta bisu da shi a wannan lokacin ne ta tai tinanin wannan ai su ne rukunin da suka yi Azwa Fyade,murmushin mugunta taja tana furta ni da ku ne gani nan kanku samari,gyara zamanta tayi ta nazo da gashinta take kyanta ya kara fitowa,table din kusa da ita suka zauna suna hirar abinda ya shafesu,ganin harta gama basu san da zamanta ba ne yasata mikewa cikin salo na tafiya,take suka fara kallonta zaid ne yayi murmushi yace kyakkyawa,kalli kyawunta wannan da zan same ta da tabbas na more ta wallahi,dariya suka sa masa ganin ta samu nasara ne yasata karasawa to me zai hana yallabai,ka bani address yau sai nazo muhadu,muhadu a club din da yake wajan gari yau da misalin karfe 11 sweety,sai na Zo daga haka ta matsa ta sumbace sa sannan ta fice yayin,da zaid ke ganin yau sai ya more ta domin tabbas yau ta kwanta masa yarinyar ta hadu.
Ummu ce ta shigo ta kalli Hammad wai Hammad kwana 2 me ne yake damunka ne,murmushi yayi yace ummu me Kika gani ne,meye ma ban gani ba hammad,ka fada mini me ke damunka,nace kayi aure ka tsaya kana min inda
,kada ka manta dika fa aure 2 kayi kuma dik ka rabu da matan,wai Hammad me ke damunka ne,tashi yayi ya zauna yace ummu kinsani kema,kinsan dalilin ko kuma ni ita nake Jira ta dawo,domin nasan Juwairiiyya bata mutu ba ummu,dafasa tayi tace Hammad Juwairiiyya ta rasu tin Muna kasar france,to amma ummu ai ba a nuna mana gawar ta ba ko,ummu bata mutu ba a cikin zuciyata nakeji bata mutu ba wallahi,hammad ummu ta kira sunansa,dagowa yayi yana kallonta fuskarsa dik kwallah,to a Ina zaka samo Juwairiiyya taka,zan samota ummu zan samota domin Naga mai kama da Juwairiiyya sati 3 da ya huce,amma bata min magana ba,amma tabbas suna kama ummu,shikenan Hammad amma ka sani na baka nan da 2month idan baka Nemo Juwairiiyya ba to tabbas zan aurar da kai ne,sai ace na maka auren dole da murmushi ya kalleta yace haba ummu,da haka ya tashi ya tafi yayin da ummu ke bin bayan Dan nata tana mai matukar jin tausayinsa da ya mamayeta,a dakinsa ya tsaya wani karamin dakinsa tura ya shiga take sai ga wasu photo na yarinya masu matukar daukar hankali,kowane photo dariya take Dan karamin dimple din bakinta ya lotsa,ya dade a wajen daga bisa ni kuma ya dauki wani LITTAFI da alama dai diaries ne,sai kuma ya ajiye sakamakon jin karar wayarsa da sauri ya fito yana mai rufe dakin,sannan ya dauki wayar,hello Muazzam OK to ka shigo mana
ina room dina.
Alhaji barka da hutawa,wani kwakkwaran tsaki yaja yana mai fadin,kai waye har zaka sa na Tako kasar russia,har ni zaka mai da Wanda bai san abin da yake ba,da sauri mutumin ya tsugunna yana fadin wallahi Alhaji aa ba haka bane kawai,kawai me saboda kai kawai,ka Riga da kasan me nake aikatawa mutanen da sukayi kokarin raina min hankali,ba sai na fada maka ba domin kasan da cewa ni dinan ba imani gareni ba,kallon yaronsa yayi yace kuje da shi idan yaki yayi abinda nace ka kashe shi kawai.
Club ne taron Maza da mata kowa na uzurinsa,nainah ce ta dakko daga wata mota,alama tayi masa da ya tafi,sanye take da wata iriyar English wear har kasa take amma kuma ta kasan ce gaba daya da ita kara babu,domin shara
ce,takowa take yayin da dik wata halitta ta jikinta ke motsawa,tin daga nesa kallo ya koma kan nainah daga masu fadin,masha Allah sai masu ihu da tafi,ciki ta shiga yayin da dik mazan wajen sukayi wajenta,kallonsu tayi a zuciyarta ta furta mayun mata kawai,direct barin zaid tayi da abokansa,tin daga nesa da zaid ya hangota take ya yi suman zaune ba shi ba harta abokansa ma haka,dai dai lokacin da ta karaso ne ya kama hannunta yana murzawa,murmushi tayi masa shi kuma ya maida mata,kujera ta samu ta zauna suka fara kallon kallo,lemo aka kawo mata take ta Sha abinta,daga haka kuma suka juya zuwa rawa a tsakiyar club din,nainah rawa take Kamar wadda ba kashi a jikinta,kowa na wajen na ihu ana jin dadi,jin an rikota ne yasa ta kalli wanda ya rikota sai kuma tayi murmushi tana sunbathe kumatunsa,bayan kamar awa 2 ne suka fito tare da nainah sai zaid a mota,kin bani nishadi yammata amma yanzu gidana zamuje ko gidan ki da murmushi tace gidana mana tinda kasan da cewa yau ranata ce,cike da wani salo na magana ta fadi hakan,to madam da haka suka yi hanyar da nainarh take fada masa.
Ashu
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABON LITTAFI
.....Based on Creative Story....
Chapter 10 · 0% Book details