← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 7 OF 18

PART 13 AND FOURTEEN

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washe gari tinda safe nainarh ke Shirin fita daga gidan sai da ta hada komai tsaff sannan ta mike tsaye can kuma ta zauna tana mai fadin to yanzu ya zanyi da wannan yarinyar gashi kuma nayi musu alkawarin kai ta gobe,amma bazan saba alkawarin ba zan kai musu ita a goben,falo ya fito a lokacin babe bacci takeyi,kallon agogon bangon dakin tayi taga har 7 ta kusa,rike kai tayi gashi banyi booking flight ba dole sai dai nai driving,kokarin tashin babe tayi ai kwa cikin Za'a ta tashi daganan ta fice kitchen tana hada abin da zata ci domin daukar hanya zuwa Sokoto birnin shehu,a farfajiyar gidan na ganta sanye take da Atamfa Riga da skirt sai Dan karamin mayafi yayin da babe ke sanye da Riga da wando sai p-cap din data dora mata take ta zama kamar namiji wayar ta ta kalla OK taja hannunta suka fice daga gidan a bakin gate ta gansa da motar baka ce sai kyalli take,rufe gidan tayi sannan ta kalli Wanda ya kawo motar tayi murmushi,ni na huce na tafi zuwa Sokoto amma nan da kwana 3 zan dawo kano,inaso ka sakamin Ido akan alhaji mahboob,take tai key din motar ta dau hanyar sokoto,ko me ya faru ohoo amma ku biyoni.
Abeed zaune ya rafka tagumi da gani kasan tinani yake,ifty ta shigo dauke da sallama amma Bai san ma tana yi ba saboda shi hankalinsa kwata
baya wannan duniyar,ifty ta taba sa take ya juyo yana kallonta Dan murmushi ya kakalo da gani kasan iya kan lebbansa ya tsaya,kayi hakuri abeed insha Allah babe zata dawo and kuma kayi baki wasu ne su 5,murmushi yayi yace to aunty ifty bara naje Ina Kika kaisu,na kaisu private room domin kar su takura muku,to ya furta ya tashi ita kuma ta fara kokarin gyara masa dakin nasa.Shiga yayi bakinsa dauke da sallama ganin mutanen da baiyi zato bane yasa ka shi sakin wani kasaitaccen murmushi,ya shigo da sauri suna ganinsa suka mike suna kokarin Isa wajensa,gaisawa suke cike da farin ciki suna kuma yi masa ta'aziyyar rashin mahaifinsa da yayi,amsawa yayi yana mai fadin wai yaushe kuka dawo ba na barku a UK ba amma nayi mamakin dawo war ku,daya ne ya kallesa haba abeed dole mudawo saboda munji mutuwar mahaifin ka kaga dole mu dawo muyi maka ta'aziyya Ina mommy ne,murmushi yayi tana lafiya bara na kira maka ita ko,har zai fita daya daga cikin su ya kallesa yace ka taho mini da babe,take kirjinsa ya bugu bummmm domin baya san ana ambatar babe din nan da haka dai ya fice daga gidan.
SOKOTO
A lokacin da nainarh ta shigo garin Sokoto a lokacin babe tayi bacci tafiya tayi dik da ba wata mai yawa bace,a dai dai wani katon gida ta sauka tin daga bakin gate aka wangale mata kofofin gidan shiga tayi tin daga farfajiyar gidan take hango yara,parking tayi sannan ta fita tare da kulle motar ta bar babe anan da take sharar bacci,shiga take lungu da sako na gidan dik inda ta shige indai babba ne zakaji yana mata sannu da zuwa,amsawa take,babban falon ta shiga anan ta tarar da wata dattijuwar mata zaune ta rafka tagumi,zuwa tayi ta zauna a gaban ta yayin da wasu yammata ke mata sannu da zuwa aunty anam yawwa sannunku ta basu amsa,tsohuwar ta gaida sannan ta mike ta shiga wani daki kuma daban,wata matar ce amma ba ta kai tsohuwar ba tsufa,yawwa anam dama ke nake jira,zauna zama tayi tana kallonta,anam kin ji Na fara fada miki abinda ya faru anam tabbas hakan ita ce ta faru mun Sami lavarin mutuwarta amma mun kasa samun hujja da zata nuna cewa shi ne ya kashe ta,inalillahi wa inna ilaihi rajiun aunty yanzu kina nufin Azwa ta rasu,kuma har kun binneta maimakon ku barin nazo na ganta wani kuka ne ya kwace mata lokaci guda ta fara yinsa,matar bata yi kokarin hana ta ba,sai taba ta da tayi tana mai fadin anam kiyi hakuri kinji amma kuma ta bar miki wani envelope da tace a baki kafin tafiyarta,wata locker ta bude ta janyo envelope sannan ta rufe ta mikawa nainarh (anam) karba tayi ta Mike ta bar dakin tana kuka.
Wani Daki ta nufa tana budewa ta gansa tsaff zama tayi akan kujerar sai da tayi kuka mai isarta sannan ta goge hawayen fuskarta ta janyo envelope din ta fara kokarin budewa,knockimg din da akeyi ne yasata fadin shigo,wasu yammata ne suka shigo dauke da plate a hannu suka ajiye mata sannan suka kalleta aunty anam dama wannan yarinyar ta motar ki ce take kuka mun taho zamu shigo muka ga tana dukan glass sai a lokacin ta tina da babe,dafe kai tayi tana fadin ohh my god wallahi na manta da ita amma bara na mike na taho da ita,fita yammatan sukayi ta bisu har bakin motar ta dakko ta ganin zata yi mata kuka ne yasa ta daka mata tsawa ya isheki malama idan ba haka ba yanzu na kasheki kuma kinsan zan iya ko,take ta hadiye kukanta tana ta raba Ido kamar tsohuwar munafuka,dakin suka shiga ta sa masa key sannan ta ajiye ta ta bata abincin ita kuma ta fara kokarin bude envelope din,wani photo ne a farko na wani saurayi sai wani dattijo a gefensa,sai wata takarda da take a linke,takardar ta dauka ta bude ta fara karanta kamar haka,AUNTY ANAM NI CE AZWA WANNAN MUTUMIN SHI NE WANDA NA BAKI LABARINSA SUNANSA ALHAJI SALMANU WANNAN KUMA SHI NE DANSA MAI SUNA ZAID,AUNTY ANAM DAN SA SHI YAYI MIN FYADE A HANYATA TA DAWOWA DAGA MAKARANTA DASHI DA ABOKANSA,AUNTY ANAM KIMSAN A TA DALILIN INA NA MUTU TO A TA DALILIN DAUKAR FANSA TA NE AUNTY ANAM BA IYA SHI KADAI BA SU SU 5 NE AUNTY ANAM KE KADAI CE ZAKI IYA DAUKAR MIN FANSA DOMIN KE DIN KIN KASANCE YAYATA CE A YADDA KIKE FADI KO DA YAUSHE,IDAN KINASON KARIN BAYANI KI DUBA DAKINMU CIKIN AKWATI NA AKWAI WANI VIDEO DANA YI NA AJIYE SABODA NASAN ZAI MIKI AMFANI A BANGARENKI AMMA AUNTY ANAM KI TAIMAKA KI DAUKAR MIN FANSA NIMA DOMIN BAZAN HAKURA BA,Aunty anam ya kasan ce Dan asalin jigawa state aunty anam na barki lafiya daga taki har kullun mai kaunarki Azwa Mujahid.wani kuka ne ya kwace mata harda shassheka kallon ta babe take ita ma tana kukan.
Wayar ta ce take ruri kallon ta tayi ganin bakuwar number ne yasata daga wa da sauri,an samu damar da zan sace yar gidan Alhaji mahboob,da sauri ta furta no karka fara domin ni Alhaji mahboob din nakeso amma ance ai baya kasar nan,nainah ce tace eaa nasani yanzu haka yana Russia kuma nan da kwana 4 zai dawo dik wani motsinsa Ina sani kawai ka bari na dawo daga zarar na dawo shikenan kuma ta Kare masa dik da anan din ma ba zama zanyi ba domin akwai wani aikin da nakeso nayi amma kuma dai kawai sai na dawo,saurin katse wayar tayi tana goge hawayen fuskarta.kallon babe tayi tai mata alama da tazo wayar ta ta dauka ta kira abeed dagawa da yayi yaji muryar babe tana fadin Yaya wani sanyi ne ya ratsa zuciyarsa take suka fara hira,jin hayaniya yasa nainarh fadin idan ka gama da mutanen kadawo ka kira,zata katse kenan ya roke ta take ta Mika wa babe waya,can kuma ta karba gobe zan kawo maka ita har cikin gida Kamar yadda nayi alkawari,take ta katse ta kwanta ta lumshe idanu.
SECRET WRITER
(ASHU)
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABON LITTAFI
.....Based on Creative Story....
Chapter 7 · 0% Book details