← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 12 OF 18

PART 23 AND TWENTY FOUR

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Laptop din ta ta janyo tana duba cameras din gidan Alhaji mahboob domin kwana 2 bata duba su ba,ganin kamar akwai wani lamari ne yasata saurin shiga camera dazata sadaka da dakin Alhaji mahboob,anan ne fa ta gansa zaune da farin takardu a gaba,kallo take kallon tsanaki kamar daga sama taji ring din wayar ta,dagawa tayi ga number ba suna,daga dayan Bangaren ne aka sa dariya nainah dubunki ta cika,domin na kamaki kamar yadda nai alkawari yanzu haka Ina cikin gidanki,shawarar da zan baki shi ne salin alin ki fito ki kawo kanki idan ba haka ba wallahi kin sanni,take gabanta yayi mummunar faduwa ko me yasa haka waya sani,da mugun sauri ta tattara komai na dakin nata,sannan ta leko ta window ganin mutane tayi zasuyi 20 ga gate man din nata na a wajensu,da Dan sauri ta fara kokarin fita ta kofar baya,amma kuma mutane ta gani da saurinta ta shige kitchen tare da ficewa,katanga ta dare ta Fi ce da gudu,a wannan lokacin ne yasa su ganin ta a take suka rufa mata baya,gudu take suna binta,wani daji ta yanka da bata san Ina zai bulla da ita ba,ganin tana kokarin yi musu fintinkau,yasa shi Dana kunamar bindigarsa cikin sa'a ya harbeta sai dai a hannun hagunta yayi nasarar samunta,cikin jin zafi yasata kwada ihu ta tsaya amma ganin da gaske sun biyota ne yasata kara kaimin gudu take suka nemeta suka rasa,cike da matukar jin haushi yasa shi fadin Nooo,dole haka sukaci gaba da duba wa amma ba nainah ba kurarta,dole suka jiyo suka dawo inda sukai parking motocinsu.
Hammad ne ya shigo gidan hankalinsa kwance yanayi yana danna wayarsa,cike da rashin kulawa wata yar matashiyar budurwa ce ta nufi wajen sa kai tsaye,cike da rashin tsammani ta kwace wayar hannunsa,cikin hanzari ya daga kai yana kallonta yana murmushi,Muniba yaushe kika dawo ne,wadda aka kira da muniba ba ce Tai murmushi ita ma tana kallon sa kamar yau ta fara ganinsa,ummu ce ta fito tana fadin ai ni na manta Hammad amma ta riga da ta sanar min da dawowarta saboda taga Yan uwan,karasawa yayi yana mai zama dama ai ummu hakan yana da kyau ba taje ta tare a kasar turawa ba,muniba Ina su mom fatan suna lafiya,da murmushi tace lafiya Lou ya hammad,wayarsa ta Mika masa ita kuma ta zauna tana kallonsa cike da son ganinsa a wannan yanayin,cikin rashin tsammani yaji yana fadin kwana nawa zaki mana,a zuci ta furta lalle ya Hammad dik wannan dakon son naka da nake amma kake min wannan tambayar,a Fili kuwa furta wa tayi ai zan Dan kwana 2,tashi yayi yace ummu bara naje sama,to Hammad abincin fa ko muniba ta kawo maka,murmushi ya kara yi Wanda ya kara masa kyau yace aa ummu kar na wahalar miki da 'ya kawai na fito na ci,muniba ce ta kallesa tace aa ba wata wahala ya Hammad zan kawo maka,daga haka ya fice ya barta anan tana kallonsa cike da soyayyarsa a ranta.
Shigowa tayi dauke da katon tray tana mai yin sallama,da Assalamu alaika kallonta yayi yace muniba shigo mana,shigowa tayi sai a lokacin naganta na Kare mata kallo fara ce tarr,amma tana da digon tawadar Allah a saman girarta Wanda hakan yayi matukar fito da kyawunta,t ana da Zara zaran gashin Ido sannan idanu masu matukar kyau,sanye take da Riga da wando,wando ya karasance crazy ya kamata sosai,sannan yar tops din Riga pink,kanta taci kitson rubber attached ta nazo da shi zuwa gadan bayan ta,durkusawa tayi ta ajiye tray din hannunta tana mai sakar masa murmushi,shima murmushin yayi mata yana mai kallinta,serving nashi zata yi yasa shi fadin barshi muniba nagode,badan ta so ta mike ta dawo ta zauna akan kujerar,kamar kallonsa take ya sanja kaya daga dark blue na shadda zuwa kana nan kaya,ganin kamar a shirye yake yasa ta fadin ya Hammad Ina zakaje,ba tare da ya dagoba yace zanje wani waje ne ana Jira na ne,cike da zolaya tace ko gurin budurwa ne,ai ni kafff matan garin nan basuyi min,ko ma dai nace miki har yanzu ban samu wadda tayi min ba,murmushi tayi ta Mike to ya hammad zan fita,ok sai na fito,ko 5minute bai kara ba ya fito,ummu ce ta kallesa wai kai Hammad yaushe zaka na samun lokacin Hutu daga aiki sai aiki,yanzu kuma Ina zakaje,da murmushi ya kalleta yace ummu wani waje daga haka ya fice,wata blue din mota naga ya dauka,tare da barin gidan.
Nainah gudu take yayin da jini ke zuba a hannunta na hagu ya mamaye hannun rigar jikinta,cike da daurayi take tafiya dik da batasan Ina take tunkarar zuwa ba,kwatsam ta ganta a bakin titi wani Dan karamin waje ta samu ta tsugunna tana duba hannunta,domin yayi mata nauyi idanunta sun kada sunyi jawur,hammad tafiya yake gradually,ganin mutumi gefe hanya yasa shi parking mota,fitowa yayi sai a wannan lokacin ya gane ko wacece wannan,cike da mazari ya matsa yace baiwar Allah ko zan iya taimaka miki,nainah bata gane sa ba Dan haka ta ce muje,haka ta shiga motar tare da sakin numfashi,domi wani daddadan kamshi ne ya Doki hancinta,tafiya suke kallonta yayi yace ina zan kaiki,idan kaga hospital ka tsaya.
Hammad hankalinsa na kanta,kallonta yake cike da mamakin ganin jini a hannunta,yayinda nainah ke lumshe idanu cikin tsananin azaba,karasawar su asibiti ne ya gane cewa ai ta suma,shiga yayi yasa aka dakko gado sannan aka shiga da ita zuwa dakin theater room,doctor ne ya fito yace wannan harbine sannan munaso ka Nemo mana police domin,kafin doctor ya karasa Hammad ya tare da da fadin doctor dik wani abu kawai kayi,zan biyaka dik adadin kudin da kakeso,kawai so nake ta rayu,juyawa doctor yayi ya koma dakin,daga nan aka fara kokarin aikin.Hammad ne ya juya ya koma zuwa motarsa,shiga yayi zai dakko ATM a wannan lokacin ne yaga jakar nainah,dakkowa yayi yana budewa ba komai a ciki daga laptop sai wayarta,wayar yayi kokarin budewa amma da key Dan haka dole ya hakura,ci gaba yayi da bincika jakar take yaga wasu hotuna,bai damu daya duba ba ya maida komai sannan ya wuce zuwa cikin hospital din,office din doctor ya huce ya zauna sannan ya Mika masa ATM card,doctor ne ya kallesa kallon tsanaki yace ka sai wadan nan magungunan and ka min transfer kudin aikina,nawa Hammad ya tambaya a takai ce,500000 OK take yayi masa transfer sannan ya tashi zai tafi,doctor ne yace sunan mara lafiyar fa,hammad ne ya jiyo tare da fadin Juwairiiyya Shaaban daga haka ya fice,dakin da aka maida ta ya nufa,bayan ya sayi magungunan a kan drawer ya ajiye sannan ya kara kallonta,oh my god tabbas wannan Juwairiiyya ce,amma ai ance min ta mutu,ko ba Juwairiiyya ba ce nasan dai tana matukar kama da Juwairiiyya,jin ring na wayarsa ne ya tina da jiransa ake a gaggauce ya fito daga room din,ok gani nan bani 10minute zan karaso.
Ga shi ance Juwairiiyya
Aunty anam
Nainah
Shin wai wannene sunan ta na zahiri anan
Kubiyo ni tare da ruwan comments and likes
Ashu (SECRET WRITER)
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABON LITTAFI
.....Based on Creative Story....
Chapter 12 · 0% Book details