← Book details Fansata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 1 OF 18

PART 1 AND TWO

Fansata Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Germany????
12-May-2022
04:00
THE MANDALA HOTEL
Daki mai number 200 a cikin hotel din mandala dake cikin kasar Germany,police ne ke zarya a dakin yayin da jini ne tin daga bakin kofar dakin dake cikin hotel din,daya ne a cikin police din da gani babba ne a cikin police din Sara masa sukai,direct ya cusa kai cikin dakin,jini ya fara gani,jini yabi har ya zuwa dakin dai dai bakin gawar dake cikin toilet din ya dakata,yana kallon jini a wajen,toilet din yabi da kallo yana mamakin wannan kisa,wani Dan sanda ne ya shigo,kallonsa yayi cikin harshen turanchi yace masa a dauki gawar zuwa dakin bincike,sannan a tabbata an gwada komai a dakin nan domin tabbas,wannan maka shin nasan sai ya bar wata sheda,oK sir ya furta sannan suka fara kokarin har hada kayan da kuma gawar.
Dan sandan ne ya fito kallon manager hotel din yayi inaso ganin CCtv cameras din Dake wannan hotel din da na wannan dakin ma gaba daya,oK ya furta tare da nufar lifter dan fita daga wannan hawan na dakunan.Dai dai wani bakin daki suka tsaya kallon officern yayi yace sir wannan ne dakin da CCTVs din kowanne waje yake aiki,shiga yayi yana fadin OK to muje mana,zama yayi a kujerar da aka tanadarwa Wanda zai iya zama daga baya,sannan ya fara basu umarni abu masa yadda cameras din suka kasance,a jiya kawai,dubawa ake kallon cameras din yake dik cameras din da aka huce sai ya ga wata yarinya zaune ko kuma a tsaye alamun ta sun nuna bata da gaskia,kallon ta yayi yace binciko min wannan yarinyar OK ya fada,tashi managern yayi ya nufi wajen reception yayin da officern ke binsa a baya yana kallon wajen daya bayan daya,can kuma ya kalli officern sir Dan karaso,matsowa yayi yana dubansa da kyau,Managern ne ya kallesa sunanta naiiinah Sharwaz,shekarunta 20 ta sauka a daki mai number 309 sannan kuma ta sauka ranar 10-may kaga kenan yau kwananta 2,ok ZAMU iya zuwa dakin nata,tambayar da officern yayi wa manager,sosai yallabai muje ko.
Dai dai bakin dakin suka tsaya suna knocking amma shiru sukaji kamar ba kowa,managern ne yasa ka I'd din sa take dakin ya bude,dakin yana nan tsaff dashi,komai a wajen da yake ba abinda yake fitarwa sai kamshi,wayar jikin bed din ya kalla take ya kira reception,Seena kwana nawa tace zatayi,ok sir bara na duba ta fadi hakan cikin yarensu,can kuma ta nisa yallabai yau ta tafi da karfe 04:15,ok seena nagode,ajiye wayar yayi yana kallon officern tare da Basa dik wani bayanai,kallon sa yayi yace ka turo mini da daukarsa videon nan da muka gani sannan ka tabbatar ka turo min hotunan yarinyar Kamar yadda nace maka,ficewa yayi sai kuma ya dawo da baya a Ina zan samu mai wannan hotel din,manager ne ya kallesa yace yallabai yanzu haka yana Morocco sai dai idan ya dawo zuwa jibi,ok yayi wucewa yayi yana kallon dik wani lungu da saki na cikin hotels din.
Direct babban office din su ya nufa,a bakin dakin binciken su ya tsaya yana saka wasu numbers,sai kuma ya bude shiga yayi yana kallon gawar da take gefe na dattijon mutumin,sara masa sukai tare da tattaruwa gabansa,shin an samu wata maka ma ne,eaa suka bashi amsa,wani ne ya fito yallabai sunan sa Hassan Daheer Dan asalin kasar Nigeria ya kasance kuma Dan kasuwa ne sannan shekarun sa 50-55,sannan anyi amfani da da pillow ne wajen kashe shi bayan da sai da aka bashi guba a lemo yasha,sai dai gubar taki bin jikinsa shine akai amfani da pillow bayan ya galabaita,wata mace ce ta matso sannan sir akwai wani abu ma munga wani jini a jikin hannunsa da muka aunasa mun tabbatar da jinin mace ne yallabai yar shekaru 25,girgixa kai yayi alamun ya gamsu da jawabinta,karar waya yaji take ya zaro ta yana mai ba kowa umarnin su hadu a dakin tattaunawa.
A zazzaune suke yayin da aka kunna dik wani video na yarinyar daga karshe kuma aka nuno hotunan ta,fara ce tarrr fuskarta dauke da glass,sannan tana da dogon gashi baki kirin kyakkyawar mace dai kawai,wannan ita ce abin zargin mu suna naiiinah Sharwaz yar asalin kasar India kuma a yau din nan zata bar kasar nan da karfe 6:00pm a yanda na samu masaniya Dan haka na tura hotanta ta group na WhatsApp dik wani filin jirgi dayake birnin Germany a dubata daga nan zuwa lokacin tashi Dan haka ku tashi kuje,mikewa sukayi tare da sara masa suka bar dakin kowa yana mai dannan wayarsa.
Gaba daya sun zagaye airport din saboda a yanda suka Sami masaniya wannan jirgin shi kadai ne zai tashi a wannan lokacin a dik fadin Germany,sai shige da fice suke ko zasuyi samu mai kama da wannan mata amma Ina ba ita ba alamun ta,da haka har 6:00 jirgi ya tashi zuwa kasa nigeria,ganin jirgin ya tashi ne yasa suka nufi wajen managern tare da tambayar sa Ina wannan jirgin zai sauka,jin ance Nigeria shi ya tabbatar musu da abin zargin saboda,ko ba komai shi ma Wanda aka kashe Dan Nigeria,dole suka tafi zuwa office din su Dan sanar da ogansu wannan maganar.
Gaba daya a cikin jirgin kowa harkar gabansa yake,wata kyakkyawar budurwa na hango kana ganin ta kaga bafulata na domin Kai kace baturiya ce sanye take da English wear sai karamin bakin mayafi da Tai rolling da abinta,murmushi kawai ta saki yayin da tajita a saman gajimare,lumshe idanu tayi tana murmushin mugunta,(THINKING)
Knocking kofar take tashi yayi ya bude yana kallon matar data shigo,take yaji yau yayi sabon Kamu,kallonta yayi sanye take da riga iyakar kwauri,sosai yake kallon ta can kuma yace mata juya naganki,juywa tayi sai ya karemata kallo sannan ya saki murmushi kai yau seaaa ya samo min zazzafa,zama yayi suka fara hira jefi jefi,dashi tashi tayi tsamm ta tafi zuba lemo,fakar idan sa tayi ta saka kwaya a lemon,zama tayi tare da Mika masa,sha ya farayi,ko 20mint ba ayi yaji bacci,kallonsa tayi ganin kwayar bazatayi aiki bane yasa ta saka pillow ta dannesa,dik da tana jin yadda yake karce mata hannu amma bata hakura ba sai da ta kaisa,fitowa tayi ba Wanda yaganta ta wuce zuwa dakinta,bata dade ba ta fito ta fice,bude idanunta tayi tana sakin murmushi da sannu zanzo kanku domin na dauki FANSA ta kuma na kwace dukiya ta,azzaluman banza,daga nan kuma ta kishingida tana mai rufe idanunta take mood din ta ya sauya,lokaci guda kuma sai ga hawaye shaaa akan fuskarta.
FANSA TA
By The Secret Writer (Ashu)
SABUWAR MARUCIYA
SABON LITTAFI??
.....Based on Creative Story....
Chapter 1 · 0% Book details