← Book details Facala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 30

Sashe 9

Facala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yanda ya ke a al'ada barin k'awayen amarya su zauna tare da ita bayan tafiyar y'an kawo amarya.
Yanzu ma ya rage Su'ada kawai da k'awayen ta biyu da y'ar uwarta Jiddah.
Takura mata su kai kan ta tashi tai sallar magriba da Isha,haka ta shanye kukan ta ta je tai sallar,zama tai kan Sallayar bayan idarwar ta ta rafka wani uban tagumi,y'an uwan Angon da ke ta kararaini wajan shiga da fita su su ka k'ara takura ta ta kasa ko d'an yaye mayafin ta fito da fuskarta.

Khairi ce ta hana kowa shigowa cikin d'akin ta ce duk wanda ya shigo ya tsaya falo don ta na son Su'ada ta gyara fuskarta.

Tai tai Su'ada ta tsaya ta d'an k'ara mata kwalliya amma ta k'i yarda, turare ma humra da ta ce ta k'ara gogawa tace ba ta buk'ata,haushi ya kama Khairi ai kuwa ta hau fesa mata turare ta ko ina, duk ta feshe mata jiki.

Su'ada ta d'ago hawaye na d'iga a idonta tace "Ki bari don Allah, wallahi kaina kamar zai fad'o ya fashe don ciwo, k'arfin hali kawai na ke."

Dariya Khairi tai tace "Duk Wannan fa nok'e nok'en da kike a banza wlh,kin dai san yau babbar rana ce don haka dole ta zama ta musamman. "

Hararar ta kawai tai tai k'asa da kanta,don yanda ta ke jin k'irjin ta na bugawa da wani fargaba abun ba magana.

K'arfe tara na dare abokan ango su ka yo mai rakiya.bayan gabatar da addu'o'i da fatan alkairi ga Ango da Amarya a ka tab'a barkwanci tsakanin abokan Ango da k'awayen Amarya.da ga nan dai su ka d'auke su a mota don maida su gida.

Tun fitar su falon ya yi tsit,Ita Su'ada fargaba da bak'unta sun lullub'e ta,shi kuma farin ciki da wani yanayi sun dabaibaye shi,hannu biyu ta sa ya tallafe fuskarsa yana kallon ta,ganin yanda ta duk'unk'une waje guda tana sheshshek'a a hankali ya san kukan bai k'are ba,daman abokansa sun nuna mai vedio d'in da su kai mata tana kuka a gida. A hankali ya mik'e tare da cire babbar rigar da ke jikin sa ya ajiye kan kujera, taku biyu uku ya k'araso ga kujerar da take zaune ya tsugunna,hannayen ta rik'o ya na bin k'unshin hannun da kallon sha'awa don shi kam filawa da jan lalle na matuk'a burfeshi ga mace,jin ta na k'ok'arin janye hannun ya sa ya k'ara rik'ewa da kyau,kusan mintina uku su na a haka can ya saki hannun ya mik'e da fad'in "Ina zuwa ki tashi ki yi alwala kafin in dawo kinji."

Ko eehhmm ba ta ce ba balle ta amsa,fita yai zuwa d'akin Babansu, zaune ya sameshi ya na ta faman murd'a Radio a hankali ya tsugunna gaban sa da fad'in "Baba ba kai bacci ba ?"
Cikin fara'a ya ce "Yanzu dai zan yi Ibrahima,kai me kake ba ka je ga iyalinka ba har yanzu?"

Kansa k'asa cikin jin nauyin wai yau shi a ke kira me iyali yace "Eh daman fitowa nai in ma sai da safe Baba."

"To madalla, Allah ya tashemu lafiya ya yi muku albarka."

"Ameen Amaee Baba."

Da ga haka ya mike ya fito.

Bai same ta a falo ba don haka yai tunanin ko alwala ta ke,d'aki ya shiga don ajiye hular sa da babbar rigar sa.
A kan gado ya isketa ta duk'unk'une cikin lifayar da ke jikin ta,d'an mirmishi ya saki tare da K'arasawa bakin gadon ya rank'wafa kanta sosai,da sauri ta runtse ido ta na k'ara duk'unk'unewa, sanyaya murya ya yi sosai ya sa bakinsa a kan kunnan ta,"Su'ada! meke damunki,nace ki yi alwala mu yi salla. "

Cikin muryar ta da ba ta fita sosai tace"Ba ni da lafiya fa."

"Subhanallah, ne ya same ki?"
Ya fad'a fuskarsa d'auke da mirmishi don ya san neman mafaka kawai ta ke a halin yanzu.

Kanta ta nuna mai da hannu alamar shi ke mata ciwo.

"Sannu kinji,kukan da ki kai ne,yanzu ki k'ok'arta ki tashi ki yi alwala mu yi salla don nuna godiyar mu ga Allah da ya nuna mana wannan ranar wanda dubban matasa da y'an mata ke burin riska,yi hak'uri ki tashi kinji."

Da k'yar ta mik'e ta je tai alwalar shima ya yo.bai tsawaita ba a sallar Raka'a biyu ya yi tare da addu'oin neman alkairai cikin aurensu da neman tsari da ga shed'an.

Bayan sun shafa ya waiwayo da duban sa gareta cikin kulawa da k'ara sanyaya murya ya fara magana "Su'ada ba ni da tantama a kanki,dukkan tambayar da zan miki kan addini na san zan samu amsarta,b'angaren halaye duk ina da kyakyawan sani a kanki,kuma ina kyautata miki zaton d'orewa a haka,fatana Allah ya tabbatar mana da rayuwa me inganci."

Shiru na d'an lokaci ya ratsa tsakanin su,can ya mik'e ya d'auko ledojin da su ka shigo da shi ya fiddo kayan ciye ciyen da ke ciki,takura mata yai kan taci wani abu ciki amma fir tace ta k'oshi ba ta son cin komai, k'arshe da yace ko taci ko ya yi mata d'ura kawai sai ta sa mai kuka,shi kam mamaki ta ke bashi,wani abu ta ke kamar ba ta saba da shi ba,ko ganin farko ta fara mai,rarrashin ta ya yi yace taje ta kwanta.

Ba don zafin da ake ba da bata cire lafayar jikinta ba,don a tsorace sosai take dashi,amma ko kusa ko da wasa ba ta cire atamfar jikin taba,d'an kwalin ma ta kunce ta lullub'e jikin ta da shi.
Shi kam ya na falo ya na cin kazar don sosai ya tara yunwa yau yini guda.
Bayan ya ji ya koshi yai hamdala tare da had'e kayan ya kaisu kitchen.

Kayan jikin sa ya sauya zuwa na bacci,a lokacin har bacci ya fara d'aukan Su'ada ta ji motsinsa a d'akin k'ara matsewa gefe guda tai tana addu'a cikin ranta Allah ya sa karya kwanta a gadon na.
Ya na kula da motsin da take ta yi,amma bai ce mata k'ala ba ya lallab'a can k'arshen gadon ya kwanta tare da addu'o'i ya tofe jikinsa,tun da ga nan ko k'ok'k'waran motsi ya k'i yi don tai tunanin ma bacci ya ke.

Ita kam Su'ada tun ta na zaton jin hannun sa a jikintea, har ta fidda tsammani,don haka ta samu nutsuwa a hankali bacci yai gaba da ita.

Saukar numfashin ta da ya ji ya tabbatar tai bacci, a hankali ya tashi ya kunna haske ya na k'are mata kallo,ta rame tabbas sai dai kuma ta k'ara wani sirrintaccen kyau,musamman da ke ta sha gyaran jiki, gashin kanta ya bi da kallo Wanda d'an kwalin ya zame gefe,k'yalli da bak'in gashin su ka k'awata zuciyarsa,a hankali ya dawo da ganin sa ga hannayenta ya na k'arewa kunshin kallo,kai komai ma na Su'ada abun birgewa ne ga kowane d'a namiji.cikin ransa ya ji ya na sha'awar sa ta a jikinsa
Ya kai hannu da niyar tab'ata tai motsi,da sauri ya janye hannunsa ya koma ya kwanta,don ya san dalilin wannan canjawar ta ta to duk tsoron abunda zai iyq zuwa ya dawo ne,don haka insha Allah shi kuwa ba zai je gareta ba har sai ta samu nutsuwa a gidan.

Kiran Sallar asuba ne ya farkar da shi,da addu'a ya farka,a hankali ya mik'e zuwa falo don d'auro alwala,sai da zai fita masallaci sannan ya tashe ta ya wuce.

Bayan ya dawo a masallaci ya taddata kan sallaya,tana lazimi,bai tanka ta ba ya wuce gado bayan ya cire jallabiyar da ke jikin sa.
Ya kai mintina goma a kwance yaji muryar ta tana cewa "Barka da asuba."

Ta shi yai ya zauna bakin gadon yana y'ar fara'a yace "Amarya kin tashi lafiya?.

Kanta a k'asa tace " lafiya k'alau Alhamdulillah. "

"Masha Allah, ya kan naki ya daina cuwan."

Bata amsa ba sai gyad'a kai da tai.
Shiru na d'an lokaci ya biyo baya,sannan yace "Ki zo ki kwanta mana ko baccin ya k'are."

Tashi tai ta nad'e sallayar ta wuce can gefe ta kwanta.

Dukkan su kowa da abunda ya ke rayawa cikin ransa,shi kam Ibrahim mamakin Kansu ya ke bai zaton zasu riski Kansu cikin d'ari d'ari da juna haka ba,la'akari da soyayyar da su ke gwadawa juna,ya na wannan tunanin bacci me k'arfi ta yi gaba da shi.

Su'ada kam baccin bai k'ara d'aukar ta ba ta gaji da sak'awa da kwancewa ta mik'e a hankali don karta tashe shi tai falo.

Kitchen ta shiga kai tsaye tana k'arewa ko ina kallo,ledojin da ta samu ta bubbud'e, kayan Tea ne a cikin ta farko, ta biyun kuma kaji ne gasassau sai manyan lemukan jarka da fresh milk, k'aramar ledar kuma kayan amfanin gida ne, su man wanke baki, sabulun wanka,omo da dai sauran su,d'aukan lemukan tai ta zo falo ta sasu a firji sannan, sannan sauran kayan kowanne ta sashi inda ya dace,kajin kuwa warming d'insu tai,sannan ta tafasa ruwan zafi ta sa cikin flask d'in tea, Komai tsaf ta shirya a tsakiyar falon ta gyara ko Ina, lokacin ta duba ogogo k'arfe bakawai,ba ta shiga d'aki ba kawai ta shige toilet tai wanka,har tazo ta shirya cikin atamfa d'inkin riga da siket sun amsheta sosai,ta d'auko mayafi mahad'in kayan ta ajiye gefen gado.ta na tsaye gaban madubi ta na fesa turare ya farka,bayanta ya bi da kallo tsawon lokacin da take bakin mudubin,ta juyo da niyar fita a d'akin su ka had'a ido,da sauri ta kauda kanta gefe ta na k'ok'arin d'aukan mayafinta ta yafa,k'afa ya sa ya danne mayafin, ganin haka ya sa ta d'auke hannun ta da sauri ta fice falo,d'an mirmishi yai ya mik'e yana salati, bin bayan ta yai zuwa falon amma sai ya ga ta shige toilet, zama yai kan kujera ya na jiran ta fito,can ta fito kanta a k'asa tace mai "Ga ruwan wanka na had'a."

"To sannu Allah ya saka da alkairi."

Bata ce komai shima bai k'ara magana ba ya wuce toilet d'in.

Da sauri ta shiga d'aki ta gyara gadon ta share shi,sannan ta sa turare ko ina, ta na shirin fita a d'akin shi kuma ya sako kai su kai kicib'us,da sauri tai baya ta na fad'in "Sannu don Allah, ban lura ba ."
Chapter 9 · 0% Book details