← Book details Facala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 30

Sashe 25

Facala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka bai k'ara bi takan abincin ba ya kwanta tare dasa yarinyar a k'irjinsa yana d'an shafa bayanta.

___________
To tun daga ranar sai Su'ada ta rage bawa Baby Nusrat, in ta shiga wajanta dai zata bata ita tai ta mata wasa amma bata bari ta fito da ita tsakar gidansu.

Ganin haka yasa duk jikin Sakeena sanyi.duk da Su'ada bata wani canja mata a fuskaba amma tasan sarai abun na ranta,yo in maye yaci ya manta uwar d'a ai bazata manta ba.

**********
Rayuwa na ja,abu da yawa na faruwa, a haka har Nusrat ta sami watanni bakwai, kuma alokacin ne wani cikin ya b'ullo a jikin Su'ada, na watanni biyu,Su'ada bata da zab'i sai zab'in mijinta,don taso tun da wuri ta fara tsarin iyali amma Sam Khaleelee ya zubawa idonsa toka yace bai san batun ba, bata ja cancan ba ta bari,to haka yanzuma da cikin ya bayyana taji fargaba sabida duka Nusrat watanninta bakwai,akwai d'awainiya sosai a kanta.ga aiki ga hidimar gida,amma tasan tunda Allah ya tsara mata hakan to bazai kasa basa hanyar da zata sami sauk'i ba.

A b'angaran Sakeena ma tana nan tana ja,haihuwa yau ko gobe don tsohon ciki gareta.

Su'ada bata da mugunta kk rowa,ita komai nata bai rufe mata ido ba a rayuwa, hakan yasa ake samun sauk'i cikin zamanta da Sakeena, tabbas da yanda d'abiun Sakeena suke haka nata suke to lalle da abun bazai kyau ba. Amma dake ita komai nata cikin nutsuwa da ilimi take sai wani d'abiun shirme na facaloli bata yi,don ita har ko yaushe d'aukan FACALA take matsayin Y'ar uwa.

Wannan karon cikin bai bata wahla sosai,don haka bayan ita da mijinta bama Wanda ya san tana da shi.

************
Cikin ikon Allah Sakeena ta haihu lafiya,y'arta mace.ba kyashi ko hassada Su'ada ta harhada kayan Nusrat na jinjirantaka kaf, ta baiwa Sakeena, duk da tasan anan gaba kad'an duk abunda ta bayar d'in sai ta k'ara siya,amma hakan ba damuwarta bace,tunda tasan Allah ya hore Mata abunda zatai hidima dashi.

Sosai Sakeena taji dad'in wannan tulin kaya da Su'ada ta bata don daman abubuwa da yawa bata dasu sabida ta kwana biyu bata haihunba,duk da taci burin yin hidima sosai a Wannan haihuwar sabida yanda taga Su'ada tai abubuwa tamkar biki abun ya birgeta,kuma ta K'ara jin kishi a ranta na itama sai tayi kwatankwacin haka.Lokacin da tajewa yaya Muktar da abubuwan da take so yai mata,ya kalleta cikin mamaki da fad'in"Sakeena shin kin manta yanda rayuwar nan ta canja ne,kina kallon wannan term d'in duka sati d'aya da komawa na kashewa yara kud'in makaranta da sabon uniform da littattafai,a gabanki na buga lissafi uban kud'in dana kashe,account d'ina gaskiya yanzu ba wani kud'in kirki a ciki,kud'in dana ware zan sai rago ne kawai dana abincin suna,don haka kiyi hakuri yanzu kam gaskiya bazan iya miki way'annan uban abubuwan ba sabida bani da Wallahi. "

Tumzuro baki gaba tai cikin b'acin rai tace"Amma ai haihuwa ba mutuwa bace,tun ciki ba wata guda ake mai tanadi,mutuwa ce ke zuwa bagatatan,don haka gaskiya ba zai yuyu ace duk haihuwa sai dai inyi malejin komai ba,yanzu shekara biyar rabona da haihuwa, ya kamata ace an min komai na bajinta,fisabilillahi fa."

Shi duk mamaki ma ya gama cikashi, bai tab'a zaton rashin lissafin na sakeena ya Kai har haka ba.

"Wai Sakeena yanzu haihuwa ta nawa kikai don Allah?"

Wani kallon rainin wayo tai mai kafin tace " kai za'a tambaya wannan ai,dalili kuwa kai kake yin cikin don haka zakafi gane lissafin yawon haihuwar. "

"To Yanzu Sakeena in kina da lissafi ko a haihuwar fari ne kika ce nai miki Abu nace miki bani dashi kya yimi uziri,balle haihuwa ta biyar, meye ban yi miki ba lokacin da babu hidima sosai a kaina? Kafin kice nake miki, amma yanzu in kika ce nai miki abu nace bani dashi sai abun ya zama tashin hankali? Ki ci gaba in kina kallon wannan hanyar ce me b'ullewa a rayuwar ki.Amma bazan gaji da fad'a miki ba cewa na kusa gajiya da halinki.kuma kin sani randa duk hak'urina ya k'ure a kanki abun ba zai mana kyau ba."

Jin ya hau sama ya sa tai tsit da bakinta sai kumbure kumbure take kamar fanken da ya sha yis.

*********To iya dai abunda Allah ya horewa Yaya Muktar yayi iya yinsa na abincin suna,haka nan kayan barka yayi abunda zai iya.
Khaleelee ma ya bashi gudunmawar dubu biyar sannan ya siyawa Babyn riguna masu kyau guda uku.

Su'ada kam tai mata kunun aya da yawa sabida taji tana fad'awa wata k'anwarta tana son yin kunun aya da alale na suna kuma bata sa kud'i, to daman tana ta tunanin me zata mata na sunan don haka tai mata kunun ayan da alale da yawa.

Y'an gidansu Su'ada sun zo suna harda maman su,da atamfa turmi d'aya da riguna biyu masu tsada maman ta bawa Sakeena.
Sakeena a zahiri taji dad'in abunda Su'ada tai mata da wanda mamanta tai mata,amma kasan ranta take kishin inama itama tana da dama kalar ta Su'ada, ace komai zaka fidda kud'in ka kayi shi yanda kowa zai gane kayi bajinta, Amma ba wannan damar,k'arshe ma wadda kake kishin akanta wai ita zata taimaka maka,kaicon wannan rashin kud'i.

***********
Lokacin da cikin Su'ada ya kai wata bakwai lokacin Nusrat ta cika shekara guda,don haka ta yayeta ta kaita gidansu kamar yanda mama ta buk'ata.

*******
Tashin hankali Wanda ba'a sa masa rana,ranar wata Alhamis ne cikin dare Khaleelee yaji Jabeer na bugun k'ofar su cikin tashin hankali ,jiki na rawa Khaleelee yazo ya bud'e mai daga shi sai gajeran wando. kafin ya tambayeshi meye Jabeer ya fara fad'a mishi"Yaya Khaleelee wuta ta kama a shago,yanzu su hamza ke kirana a waya wai wuta nata ci cikin shagonmu. Kan Khaleelee rik'ewa yayi,hankalinsa yai bala'in tashi, da gudu ya koma d'aki yana neman riga yasa,Su'ada data biyo bayansa jikinta na rawa take fad'in "me ya faru ne Abban Nusrat? Don Allah fad'a min abunda ya faru."

Tana saka jallabiyarsa yake fad'in "Su'ada wuta ce ta kama a shagonmu."

Daga haka ya fito da sauri, a waje yaya Muktar har ya rigashi fita shi da Jabeer.

Lokacin da suka je shagon waje ta turnuk'e fa wuta ce ke ci bilhakki,don kusan shaguna hud'u ne su ke ci a wajan.
Jama'a duk sun fito duba shagunansu.
Lokacin da y'an fire services suka zo wutar taci abunda taci don tai b'arna matuk'a,sabida shagon dake kusa da su na saida katifu ne,na hannun hagun kuma na saida yadika ne.
Sai wajan sallar asuba akayi nasarar kashe wutar,a lokacin ne kowa ya fara duba shagon sa, babu wani abun mora komai ya k'one murus sai k'arafuna,

'Innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun'

Shine kalmar da Khaleelee keta maimaitawa lokacin da yaci karo da sif d'in da yake zuba kayan da bai d'inka ba,ta k'one k'urmus ita da abunda ke cikinta.

*Taku ce*
*Y'ar mutan Ja'oji*🙋
[2/24, 12:04 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

_*page*_*43-44*

To kamar yanda kowa ya sani wuta na da cin rai,amma kuma k'addara ce da jarrabawa,in ka mik'a lamuranka ga Allah sai ja sami nutsuwa kuma ya maida maka mafi alkairi.

Khaleelee yayi ta maimaita kiran 'Innalillahi wa'inna ilaihi ra'jiun' hakan yasa yake samun nutsuwa.
Yau kwana biyu da yin gabarar,duka kostomomin sa da yasan da kayansu gurinshi ya sanar dasu halin da ake ciki.kuma fad'a musu duk wanda yake ganin a biya shi kayansa to yayi mishi magana,wanda ya yafe kuma ya gode.

To dake lokacin kusan azimi ne akwai bala'in kaya a shagon nasu jama'a nata kawo d'inki,kuma mafi yawon kayan shagon masu tsada ne kasancewar yana hurd'a ne da masu hannu da shuni.
To ba'a raba su da sabbin customers ko yaushe, don haka duk wa'yanda basu wani saba ba suka nuna kin amincewarsu,wasu suce a raba asara ya biyasu rabi wasu suce a biyasu duka.

List yayi na wa'yanda suka nemi hakkinsu,da kud'in kayan nasu.

Tofa! Abun da yawa,lissafin da yayi kusan kayan dubu d'ari uku ake nema ya biya,dukda masu Neman basu fi mutum goma ba amma adadin kayan nasu yakai wannan kud'in.

Da farko Jabeer ca yai babu wanda zasu biya komai,don suma asarar da sukai bata misaltuwa,kekunansu babu Wanda zai moru,daga na d'inki har zuwa na surfani.k'arshe ma sa suka had'a karafunan y'an gwangwan ne suka siya.

Damuwar da Khaleelee ke ciki ta bayyana jikinsa, dukda k'ok'arin sa na boyeta.
Sosai Su'ada take kwantar mai da hankali,tana nuna mishi jarrabawa ce, yayi hak'uri, Allah zai maida mishi mafi alkairi.

Da kalamanta yake samun nutsuwa,haka Baba duk da yana cikin rashin lafiya amma zai kirashi d'aki yayi tamai nasiha da kalamai masu dad'i.

*******
Khaleelee ya had'a kud'in da suke cikin account d'insa duka budu d'ari da hamsin ne,kuma dubu saba'in ta mutanan da sukai mai transfer kud'in d'inkinsu ne,to tunda d'inki bai samu ba sun yafe mai kaya ai dole ya maida musu kud'in su. Bayan ya maidawa kowa ya rage dubu tamanin,tanan ya fara ragewa sabbin kostoman nasa.

Ranar litinin da Su'ada taje aiki, ta tsaya banki ta fito da kud'in cikin account d'inta duka,daman ita ba amfani take da kud'in albashinta ba,ko ya shigo barshi take ciki,in kaga ta cire kud'i to biki ko suna ne zatai gudunmawa ko anko,sai kuma alheri da takewa mutane.

A ranar ta bashi kud'in yaje ya bibbiya sauran kud'in su, duk da sunsha fama kafin ya k'arb'a, ca yai ba zai amsar mata kudinta ba,sai dai in rance ta bashi,sai da yaga da gaske tana mai kuka sannan ya amsa.

Bayan ya biya su duk kud'insu,sauran ya dawo Mata dasu,ta ajiye.sabida so take ta bashi ya sai keke ko guda biyu ne.

**********
Yau wata guda da yin gobarar su Khaleelee gashi har an shiga azumi.

Sun yi tsammanin hukumar dake kula da shagunan kasancewar shagunan gwamnati ne zata gyara musu shagunan da wuri amma har azumin ya kama ba'a gyara ba.
Kud'in da Su'ada ta bashi ya sai keke,guda daya siya ya ajiye a gida, wa'yanda suka sami labarin yana d'inki a gida ne suka d'an kawo mai ba wani me yawa ba.
Chapter 25 · 0% Book details