← Book details Facala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 30

Sashe 19

Facala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da safe da Su'ada ta fito gaida Baba,ta tsaya su na gaisawa anan take mata godiya.Su'ada tace ai ba komai duk yiwa kai ne.

Kiran number d'in Zakiyya tai tace ya turo Umma Salama ta amsa musu y'an kunnaye,Zakiyya tai ta godiya.

A haka aka cinye watan Ramadan a kai salla cikin k'oshin lafiya,Su'ada ta taka rawar gani sosai,don tai abincin Salla wadatacce duk gidajan danginta dana dangin miji ta aiaika musu.mijinta ma ta fiddashi kunya wajan aboka,domin kuwa taron cin abincin salla a kai a shagon d'inkinsa,wanda Su'ada ta shirya musu abinci iri iri da lemuka.

Daga gajiyar hidimar salla sai ciwo ya rafke Su'ada, ciwon kai yak'i sauka tsawon kwana uku,tun tana shan magani a gida har Khaleelee ya takura mata zuwa asibiti.
Da kansa ya kaita asibitin,gwajin farko su ka tabbatar musu yaron ciki gareta na wata guda,tofa murna farin ciki nishad'i su su ka had'u su ka lullub'e rayuwar Khaleelee a lokaci guda,ya rasa ina zai sanya ransa,godiya yai tayi ga mahaliccinsa,ita kam Su'ada ciwon kai mara misali ya sakota gaba ko ido bata iya bud'ewa, ji take kamar kanta zai tsage,tana dafe da kannata ya kamata ta tashi, su ka fito zuwa bakin titi don daman a a dai daita su ka zo.

Da farin cikinsa ya shiga gidan, tun da ga k'ofar d'akin Baba yake tambayarsu ya jikin nata, cikin fara'a sosai Khaleelee ya amsawa Baba da fad'in "Da sauk'i sosai Baba."

Yanayin da Baba ya ga Khaleelee na farin ciki ko bai tambaya ba ya bashi amsar dalilin ciwon nata.

Tun fa daga wannan ranar sai ciwo ya 'kara sako Su'ada gaba kamar an k'ara hankad'oshi, laulayi sosai ta keyi,amai,ciwon kai,zazzab'i, kwad'ayi ,tsirfa ci wannan k'in wannan, sai ya zamana ko 'kanshi ba ko wanne Su'ada ke so ba,dukka turarukanta taji ta tsanesu,sai na Khaleelee kawai ta ke so,babu abunda ya dami Khaleelee game da tsirfarta,duk abunda tace tana so shi zai mata,duk aikin gidan ya dawo kansa, kama daga girki, wanke wanke,shara da gyaran gado, dukka shi ya ke yi,ko wanka bai barinta tai da kanta, kulawa ta musamman ya ke bata,don tausayi ma take bashi sosai,yanda kullum jikinta bai rabo da zafin zazzab'i,in an samu ya sauka to rana ta take,a nan kuma ciwon kai zai tsananta tai ta tsiyayar hawaye.

Ranar da Mamanta ta zo dubata taga wahalar da take sha ga aiki Khaleelee nata fama dashi,tace Jidda ta zauna ta rink'a musu aikin gida shima Ibrahim ya rink'a fita neman kud'insa, don baya samun zama a shago ko yaushe hankalinsa na gida in ya fitanma.

To zuwan Jidda ya sa Khaleelee samun rangwamin aiki,don yanzu bai aikin komai sai na kula da ita in yana gida, yawon aman da take yi yasa likita ya rubuta musu drip yace a rink'a sa mata,to dake Jidda daman fanninta ne sai take d'aura mata drip d'in kullum d'aya ake k'ara mata,har zuwa lokacin da jikinta zai yi k'wari.

Sakeena kam kullum zata shigo sau d'aya tai mata sannu sai kuma washe gari,don da tai bak'i take basu labarin irin laulayin da Su'ada ke yi take fad'a musu wai tsabagen iskanci da tsirfa ne,da nuna ita wata ce,d'aya cikin k'awayen nata tace "Haba Sakeena kamar biki tab'a haihuwa ba,ai ke mace ce kin san ciki kowa da kalar nasa,sannan ita na fari ne dole zai bata wahla."

Tab'e baki Sakeena tai da fad'in "Ba wani fa,da iskanci ko da laulayin,kullum sai tace ga abunda zata ci kuma sai an dafa tak'i ko kallonsa sai ta canja wani abun,shi yasa take ban haushi, wai ita dole gata me ciki."

Haka taita surutanta na son dole sai ta kushe Su'ada a gun duk wani da ya santa.

To ga wata sabuwa,rana tsaka Su'ada ta tashi da fad'in wai bata son warin gass da an kunna sai tai ta 'ko'karin amai nan da nan kuwa za tai ta kwara shi,abunda duk aka samu taci sai ta fito dashi, Jidda ta d'ora girki haka ta sauke,sai ruwan zafi ta jona musu a kettle su ka sha Tea,da rana kam su ka rasa abunda zasu ci, dole Khaleelee yaje siyo musu abinci,sam Su'ada tak'i ci, tana kallon abincin ta kauda Kai,don ji tai har kanta ya fara juyawa.can tana ta kwance taji yo kamar 'kamshin girkin Sakeena, nan da nan taji shi take son ci,ta kalli Jidda cikin yanayin wahla da ciwo tace "Plss Jiddah ce Maman Abba don Allah ta zuba min girkin ta in ci."

Ba musu Jidda ta sanar da Sakeena sa'kon Su'ada, ba dan taso ba ta amsa da to.

Bayan ta gama girkin ta zubo mata a wani d'an kwano Wanda bai taka kara ya karya ba,ai kuwa Su'ada kamar ta kwana bata ci ba haka ta hau abincin nan da ci, kafin ta gama dashi,Jidda kallonta kawai cikin mamaki tace "Wai Aunty Su'ada dad'in wannan girkin kika ji haka? To in jalop d'in ki ke so a yi miki mana."

Girgiza kai Su'ada tai tana fad'in "Wannan d'in tamin dad'i, da zan sami 'kari ma zan 'kara, girkin yai dad'i sosai."

Shiru Jidda tai tana mamakin lamarin ciki irin haka,a ranta tace "Allah karka had'ani da wannan lalura ni kam ko da lokaci na ya zo."

To da dare ma haka Su'ada tace Sakeena ta sa mata abincinta, Kai tsaye Sakeena tace ita tuwo tai, da Jidda ta fad'a mata tuwo ne tace koma meye ta bata.

Nan ma ba wani me yawa ta zuba mata ba,hannu baka hannu 'kwarya Su'ada ta cinye ta na sud'e hannu.Khaleelee da mamaki shima ya ke kallonta,Jidda tace mai da rana ma haka tasa na amso mata ta cinye kamar ta samu nama.
Y'ar dariya yai yace "Ai Alhamdulillah ma tunda an samu in taci bata aman, bari zansa m Maman Abban magana ta rink'a sa sanwa da ita tunda abuncinta kad'ai take so,mune dai ban san ya zamuyi ba Jidda,Kinga bata son warin gass kuma ba zamu zauna da yunwa ba,meye Shawara?"

Shiru Jidda tai na d'an lokaci kafin tace "Yaya kawai ka siyo mana murhun gawayi,sai ka siyo mana gawayin mu rink'a amfani da shi."

"A'a ko dai risho Jiddah,kin iya amfani da gawayi ne?"

Cikin dariya tace "To ai ni risho d'in ne ban iya amfani dashi ba,sabida ban tab'a kunnawa ba,amma kaga a gida wani sa'in in aiki ya mana yawa ba waje a gass muna kunna kol d'in."

Mik'ewa yai yana fad'in "OK bari na duba naga me gawayin bakin titin nan bai tashi ba."

Daga haka ya fita.

**********
Tsawon sati kullum Su'ada ba ta iya Kai komai bakinta sai girkin Sakeena, ya zama shi kad'ai take jin dad'in sa,safe dare rana.ita dai Jidda zata dafa musu su hud'u ita da Khaleelee da Baba.

Tun Sakeena na yin Kara harta fara turb'unewa,wai a dole ita ta zama wata abar ana nema a wajanta.

Wata ranar litinin Sakeena tak'i d'ora girki har k'arfe d'aya saura ,yara su ka dawo makaranta ba abinci ga Su'ada can ms nata jin yunwa,kawai sai tacewa yaran bata jin dad'i itama,ba zata iya wani shiga rana ta d'ora girki ba,kowa yasha gari da suga da gyad'a. "

Haka yaran su ka jik'a garin su ka sha suna ta murna,don a marmarce suke shan abunsu,Baba kam tuni Jidda ta kai mishi abincin da ta girka,lallashin Su'ada tai tayi akan taci wanda ta girka,ganin yanda Jiddan ta damu ya sa tace ta d'ebo mata,ai kuwa lomarta uku ta fara amai,ita kam ba ta San dalilin da yass yanzu bata iya cin komai ba sai girkin Sakeena.

Ganin yanda ta ke ta amai ga ba komai a cikin yasa Jidda kiran Khaleelee a waya ta shaida mai halin da ake ciki, ba jimawa ya shigo gidan, lokacin ta gama aman tana kwance kan cafet tana ta juyi,Ya d'agota jikinsa ya na tambayarta me take so ya siyo mata.

Cikin muryar rashin lafiya tace "Shinkafa na ke so,amma ta maman Abba ga Jidda tace wai ba tai girki ba yau."
cikin tausayawa ya ke shafa kanta,a hankali yace "Kiyi hak'uri ki canja wani abun na siyo miki yanzu yanzu."

Girgiza kai tai idonta na cika da kwalla tace "Ban son komai wallahi, shinkafar kawai na ke so,kuma tunda babu zan jira in tai na dare sai naci."

"A'a Su'ada ya zaki zauna ba abinci ko kad'an a cikinki,tun safe fa sauran gyad'ar nan kawai ki ka ci,kuma ki zauna har dare."

Baccin da ya fara daukanta ya sa bata k'ara tankashi ba ta gyara kwanciya sosai a jikinsa.

Shi kam gashinta kawai ya shiga shafawa yana matsa jikinta da hannu guda sabida taji dad'in yin baccin. Ai kuwa ta saki jiki tana sakin minshari alamar baccin yayi nisa.

*TAKU CE*
*'YAR MUTAN JA'OJI*🙋
[2/23, 11:58 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

_*page*_ *33 34*

Sai la'asar Khaleelee ya koma shago,ita kam Su'ada har lokacin bacci take,to sanin yawan baccin da take yanzu yasa basu damu ba.
Wajan magriba ta farka,ai kuwa ta farka da mahaukaciyar yunwa,cikinta yai yamutsawa,har jikinta rawa ya ke,tace"Jidda yunwa nake ji sosai wallahi, ji nake kamar hanjina zai tsinke. "

Dafa kai Jidda tai da fad'in "Yanzu ya zamuyi? Kuma naga Maman Abba yanzuma ko girkin bata d'ora ba."

Su'ada ji tai wasu hawaye na zubo mata,dob ta gama sa rai a cin abincin gashi babu,daddafawa tai taje ta d'aura alwala tai salla daga zaune,ta idar tana addu'a Khaleelee ya shigo, Jidda ta mai sannu da zuwa, ya amsa cikin fara'a sannan yace "Yanzu ta tashi ko ta dad'e?"

"A'a bata dad'e ba,yanzu ma ta gama batun yunwa take ji ."

To je ki amso mata wajan Maman Abban mana, Jidda tace "To ai batai fa girkin ba."

Da sauri yace "Yanzun ma? Innalillahi, to me yasa ba tai ba?"

Gyad'a kai Jidda tai da fad'in "Wai tace bata jin dad'i."

Cikin damuwa ya dafe kai,can ya fita zuwa gun Sakeena a bak'in k'ofar d'akin ya tsaya yana sallama. Yaya Muktar ya amsa mai yana d'age labulan yace "Ibrahim ya dai?"
Chapter 19 · 0% Book details