← Book details Facala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 30

Sashe 7

Facala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin shauki ya ke kallonta, gaba d'aya sai ya ga ta canja mai,yanda ta rufe fuska ma sai ta bashi sha'awa, k'asa sosai ya yi da murya yana fad'in " To tunda ni ba'a min barka da zuwa ba ni bari in miki barka da gida, Allah ya taimaki Gimbiyar mata zak'in zuciyar Ibrahimal Khaleel, ina fatan na same ki cikin koshin lafiya."

A hankali ta zame hannayen ta amma idonta a k'asa tace "Sannu da zuwa ya Ibada ya aiki?"

Y'ar dariya yai yace "Ni ba'a amsa gaisuwar da nai ba an min wata,to Sannunki, Ibada Alhamdulillah, aiki kuma gashi muna fama kullum ba sauk'i. Ya Mama da sauran y'an gidan?"

"Duk su na lafiya qlau,Ya jikin Baba?"

"Baba jiki da sauk'i Alhamdulillah."

Shiru ne ya d'an biyo baya,shi ya k'ara kauda shurun da fad'in "Kin rame Su'ada ko azumin ne?"

d'agowa tai karo na biyu su ka had'a ido,ya k'ara narkar da idanuwansa cikin nata, kauda kai ta d'an yi cikin kaucewa kallon tace"Kowa haka ya ke fad'a, amma ni banga ramar da nai ba."

"Hhhmmmm ko kowa ma bai gani ba ni zan gani ai,kinga alamun ci gareki yanzu ba'a samun yanda ake so shine aka rame haka."

Da sauri ta kalleshi da fad'in "A'a fa, Allah ni banda ci,kawai ulcer ta tayar min ne jiya da yau,amma ba azumi bane."

Mirmishi yai yana kallonta sosai,don ta mishi kyau k'warai da gaske.ganin kallon ya yi yawa yasa cikin Shagwab'a tace "Oh Khaleelee kallo haka."

Kwaikwayon muryar ta shima yai yace "Oh Su'ada kyau iya kyau haka."

A tare suka saki dariya, daga nan kuma suka shiga hira me gardi irin ta Masoya.

Awa guda cif ya yi ya ga goma ta yi,kallonta yai tare da kallon agogo yace "Hajjaju dare ya yi ko?"

D'an turo baki tai kalar na shagwab'a tana girgiza kai tare da marairaicewa.

"Wasssh Allah wannan salon fa zai iya hanani tafiya don Allah a barni in tafi kinji."

Juyar da kai gefe tai tana buga k'afa alamar tak'i yarda d'in.

Gaba d'aya abunda take k'ara narka Ibrahim take,yama rasa me zaice don ta wullashi duniyar shauk'i sosai,daurewa ya yi ya sauko da ga kujerar sa ya tsugunna gaban ta yana had'a hannaye alamar ban hak'uri, "Zan tafi ne badan na so ko na gaji ba,sai don lokaci ya nuna kamatar in tafi,sannan kin ga akwai tarin ayyuka agaba na, zan je in d'ora inda na tsaya,in harhad'a musu d'unkunan su su harhad'a min kud'ad'e na in samu in yi aure, kullum in ta zama tare da shagwab'ab'b'iyar mata ta."

Bata San sanda ta sa dariya ba har duka hak'oran ta su ka bayyana.
Ya na ganin haka ya mik'e shi ma ya na dariyar, ita ma mik'ewar tai tare da hard'e hannayen ta a k'irji ta tsare shi da lumsassun idanuwan ta,sosai shima ta narkar da nasa su ka sark'e idanuwan junan su cikin mayen so.

Ita ta fara janye nata a kasalance tace "Sai kuma yaushe Khaleelee?"

Sauke ajiyar zuciya yai Sannan yace " Sai zuwan Salla kuma,in na samu kaina zanzo in miki awa uku cikakku kinji."

D'aga mai kai tai cikin gamsuwa. Shi kuma ya saki mirmishi ya na nuna mata ledojin da su ke gefe, "Su'ada ga wannan ba yawa kin san mijin naki me k'aramin k'arfi ne."

" Don Allah me yasa ka wahalar min da kanka wajan siyayya,Allah da ka barshi amma har wannan uban kayan."

Zare ido ya yi ya na d'ora hannunshi kan lips d'in sa kamar ya na tsoratar da yaro.

"Kin san me ye a ciki kike cewa da yawa? Kuma ban wahalar miki da kaina ba wajan siyayya ba wani abu ne me yawa ba fatana kawai su yi miki."

Annuri ne ya k'ara k'aruwa a kan fuskarta tace "To na gode Khaleelee, Allah ya k'ara bud'i da arzik'i me amfani,Allah ya tsare min kai."

Sosai ya ji dad'in addu'ar ta cikin fara'a matuk'a yace"Ameen Ameen Sweet Su'ada. in kin shiga ki gaida min Mama ki yi mata barka da shan ruwa, ki gaida Takwara me baccin wuri."

"Ok duk za su ji insha Allah."

Rakiya tai mai gate ya fidda mashin d'in sa da ya zo da shi, cikin kewar juna su kai sallama ya tafi.

Da ta dawo ta d'auki ledojin manya guda biyu ta shiga dasu gida,a falo ta samu kowa duk su na kallo,ajiye ledojin tai gaban Mama tana fad'a mata sak'on gaisuwar sa,Mama ta amsa cikin jin dad'i.

Ita dai wucewa tai d'aki don cire kayan jikin ta.Jidda ce ta bud'e ledojin, ta farko Atamfa ce me kyan gaske, d'inkin riga da siket abunka da masu abu,an tsantsara d'inki, sai material royal blue me laushi an mai d'inkin doguwar riga, yaji stone work, sannan takalmi kamfanin Vinci, da mayafi kalar takalmin.
D'aya ledar kuma kayan ciye ciye ne fal su cake da su ice cream da lemuka.

K'alawa Su'ada kira Mama tai, ta fito da ga d'aki, kallon tuhuma ta kafe ta dashi,a sanyaye ta k'araso ta zauna kusa da ita.

"Su'ada wannan kayan fa?"

"Mama shi ne ya kawo min." Ta amsa mata.

"Na San shi ya kawo miki ai,ina miki maganar sun yi yawa ne,ban son kina takurawa bawan Allah fa,Su'ada a rayuwa kin san kowa da yanayin k'arfin sa, Ibrahim akwai hidima a gaban sa, bai kamata ya sawa kansa damuwa a ire iren wannan hidimar da samari ke yiwa y'an mata ba, aure ne a gaban sa,fata na ki samu kwanciyar hankali a gidan auran ki ba wani k'yale k'yale ba. Su'ada karki rink'a nuna mai ki na son ya miki wata hidima kinji ko,duk da na san ba halinku bane son abun wani,amma ki k'ara kiyayewa kinji."

Jiki a mace ta gyad'a kai da fad'in "To Mama insha Allah zan k'ara kiyayewa."

Bayan Jidda ta shigo mata da kayan sawar dak'i ta bubbud'e su tana dubawa,mirmishi kawai ta ke, a ranta ta ke cewa 'Allah sarki Khaleelee na,Allah ka k'ara bud'a mishi ka dafa mishi cikin sana'ar sa."

*28/10/2019*

*Taku ce*
*Y'ar mutan Ja'oji*🙋
[2/23, 11:53 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

*Dedicated 2*

*Aunty Maimuna OG* *malamata ta adabi . . .*
*Maryam Obama*🤭🤣🤣🤣

*Hassan and Hussain 80k*

*Alherin Allah ya kai muku har gadon barcinku*💃

*page 15-16*

An kasafta gidan su Ibrahim an fidda mai b'angaran sa, d'akuna takwas da ke cikin gidan ya zama guda hud'u nashi guda hud'u na Muktar amma kasancewar Baba na zaune a d'aya, Jabir d'aya, kuma cikin rabon Muktar na sun ya ke ya sa ya zama biyu ya ragewa Muktar duk su ka kwashe kayansu su ka had'e a d'akuna biyu,Wannan dalilin ya sa Sakeena ta fara magantuwa da k'unci ta ke k'orafin tunda dai Amarya za'a kawo ai ita d'aki biyu ma ko uki sun ishe ta,ita dai gaskiya an shiga hakkinta,duk surutun da ta ke yaya Muktar bai kulata ba.

Kud'in da ke hannun Ibrahim da kud'in filinsa da ya siyar ya bashi damar sauke duk d'akunan na sa da yankin tsakar gidan da aka fitar masa ya shaci gini lafiyayye, a kai mai tsarin gini na zamani,falo babba da d'akuna biyu sai kitchen da band'aki duk cikin falon sannan d'an k'aramin tsakar gida a ka fitar da k'ofa zuwa tsakar gidansu yaya Muktar. Wata biyu a ka d'auka wajan ginin don a sannu ake yin komai,kafin me lafiyayyan waje ya fito ya yi fes da shi, har tsakar gidan su Sakeena a ka gyara zuwa k'ofar gida.

A b'angare guda kuwa Hajiya Uwa wata uwar d'akin Ibrahim ce kuma y'ar uwar mahaifiyarsa ce,harkar saida kayan sawa ta ke,su na shiri sosai da shi don shi ke d'inka ma ta kayan saidawar ta,Ita ya d'ora kan had'a lefe,komai ita ya ke bawa ta na siyo mai,kasancewar ta wayayyiyar mace kuma tsohuwar y'ar kasuwa ya sa ta ke siyo mai kaya na d'aukan magana.

**************
Wata k'awar Maman su Su'ada principal a makarantar emmata ta karb'i takardun Su'ada ta samo mata teaching,kai tsaye Ibrahim ya amince mata a lokacin da ta sanar dashi,kuma ya bita da addu'ar alkairi, cikin d'an lokaci ta fara koyarwa a secondary d'in.

A bangare guda kuwa lokacin bikin su sai k'ara k'aratowa ya ke an cinye watanni yanzu har ya rage sati biyar.

Dukkan abunda a ke buk'ata a lefe an gama had'awa, Hajiya Uwa tai wa Ibrahim namijin k'ok'ari don ta had'a mishi komai ba raini.Yaya Muktar shi ya siya mai akwatina set guda 6 peaces kamar yanda yai alk'awari.

Ranar a ka kawo kayan gidan su Ibrahim don y'an uwa su gani kafin a kai.
Ranar Hassada ta biyu ta fara kama Sakeena a kan Su'ada, ta gama hassadar ginin da a kai mata sannan ta zo hassadar ganin irin kayan da a ka had'a mata. Cikin mutane ta na ta murna kamar me,amma da ta shiga d'aki ji tai kamar ta zubda hawaye don takaici.
Da dare bayan Ibrahim ya dawo ta ke tsokanar sa cikin barkwanci da ga nan ta soko mai a bunda ke ranta "Ibrahim wannan kaya haka na ce anya kuwa ba a yi k'arya ba wajan had'a su,ina ganin kamar ka k'are k'arfin ka a lefan nan,Allah ya sa ma dai Hajiya Uwa ba ta had'a ma harda bashi ba duk da na ji Zakiyya ta na cewa komai kud'i ka ke badawa a siyo ma."

Cikin mamaki ya ke kallon ta,can ya ce" Maman Abba me ye abun k'arya cikin wannan kayan? Akwati shida shi ne k'aryar?lalle don bi ki san wace Su'ada ba shi yasa har ki ke zaton an yi k'arya wajan had'a mata wannan kayan. To kin san me?cikin kayan nan babu a bunda ya ke bak'on ta,duk ta saba amfani da irin su har ma na sama da su.wannan kayan ba komai bane wlh don da ina da kud'i Su'ada ta fi k'arfin wannan kayan zan ninninka mata su."
Chapter 7 · 0% Book details