← Book details Facala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 30

Sashe 12

Facala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta sa hannunta ta rufe mai baki ,wani kiss ya sakarwa tafin hannun,tai saurin janyewa don shock d'in da taji ya harbeta.
D'an mirmishi yai yace "Su'ada bud'e ido ki kalleni din Allah."

Cikin cool voice tace"Bazan iya ba fa."
" Me yasa ba zaki iya ba"

"Kunya na ke ji wlh."

"Kunyar me?komai fa ya riga ya faru,ai batun kunya tsakaninmu ya k'are, tun ranar d'aurin aure ki ka tsiri wata jin kunyata, duk wannan tsumamman kallon an daina aiko min shi,kuma na san dalilin to tunda an kauda dalilin ba sai a barni haka ba in kalli sarauniyar kyau da ga cikin ido har k'asa."

Kanta na kwance a k'irjin sa tace" To duk kallon da kai bai isheka ba,ka kalli duk abunda ka so ai jiya."

Dariya sosai maganar ta bashi,yace "A'a ni jiya ban kalli komai ba,aikin gabana kawai nai,amma yanzu zan kalla in more da ga sama har k'asa."

K'ok'arin fara zuge mata zif ya ke,tai saurin rik'o hannayensa, shi kam dariyar da ke cinsa ya ke k'ok'arin dannewa,ya na k'ara janye mata rigar,
Ba ta san lokacin da ta bud'e idon ba da sauri ta na mai magiyar ya bari ya bari,a lokacin k'wayar idon nasu ta sark'e, wani shagalallan kallo su ka shiga aikawa juna,dukkan su idanuwan su tamkar masu jin bacci haka ya koma,sai da su ka kalli juna su ka more sannan ta maida idon ta k'ara wani lumshe su,cikin jin wani mayen feelings ya bi saman idon nata da lafiyayyen kiss,a hankali tai ajiyar zuciya, mik'ar da ita tsaye yace su je kitchen su yi wanke wanken.

Komai tare su kai har girki ya na tsaye ya kafa ya tsare a dole sai ya koyi girkin,duk nauyin da take ji sai da ya bi hanyar da ta saki jiki su ta daina kakkauda kai.

A ranar wanka ma dagewa ya yi sai da su kai tare,karon farko da yace su yi a taran,don ca yai komai ya riga ya kau a tsakanin su,batun kunya babu ita tunda an k'etare boda🙈

*Ta kuce*
*Y'ar mutan Ja'oji*🙋
[2/23, 11:55 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

_*page*_*21-22*

Yau satin Su'ada guda gidan Ibrahim,zuwa lokacin wata shak'uwa da tsantsar k'auna ce ta lullub'e rayuwar su,ko yaushe su na manne da juna,kulawar da su ke bawa juna dole ta birgeka, don ko motsi d'aya ya yi to a kan idon d'ayan ne.

Kullum da safe Su'ada in ta gama aikin ta za fito su gaisa da maman Abba,sannan ta je d'akin Baba ta gaida shi,to wani sa'in ta kan tsaya su d'an yi hira sama sama,ta koma wajanta,musamma da ke ko yaushe da rana cikin yin bak'i ta ke da dare kuma ta na tare da Oga.

B'angaran abinci kullum in ta dafa na rana za ta kaiwa Baba, sannan da dare ma za ta kai mishi,haka na Jabir ta sa mai kwano a wajanta duk da ya na sa kwano a a tukunyar Sakeena.haka ma yaran Sakeena duk wanda ya shigo cikin au hud'un za ta zuba mai ya ci ya k'oshi.

Yau da rana Su'ada tai girki tare da had'a lemon kwakwa, ta d'auko sabon food flask d'in ta da ta warewa Baba shi,ta zuba mai jalof d'in shinkafa da waken da tai,sannan ta d'auko wani juck ta zuba mishi lemon, a tire ta jera ta d'auka don kai mai.

Ya na bacci ma sallamar ta ta tashe shi,bayan ta ajiye abincin ta ke mai barka da rana ,ha amsa cikin fara'a sosai, "Sannu Sa'adatu, sannu da k'ok'ari, ya bak'unta? Ko dake yanzu kin zama y'ar gida ko."

Kanta a k'asa ta na d'an mirmishi,ya fara bud'e abincin, k'amshin kad'ai ne ya cika hancin Baba amma ya ji wani nishad'i ya saukar mai,duk da shekarun da su kaiwa Baba yawa amma harshen sa na son d'and'ano,da ke da an yi arzik'i komai ci ake kamar a banza,to sa karayar arzik'in ta zo sai tazo dai dai da rashin me d'aki, wannan yasa komai ta cakud'e,abinci sai Wanda suruka ta dafa ta bashi, ba shi da ikon fad'in kalar abincin da ya ke so,ba wai don BA za'a mishi ba,a'a kawai yakana kawaici irin na iyayen da,ba su son takura suruki ko kad'an.

Ganin zai fara cin abincin ya sa Su'ada tashi ta fita.

A tsakar gida ta sami Sakeena ta na ta fama da gwawayi yak'i kamawa gaba d'aya, ga shi lokacin tafiyar yaran makarantar Islamiyya ya kusa,sai k'orafi su ke yi.zama tai kan kujera y'ar tsugunne ta na fad'in, " Maman Abba wannan gawayin anya ba ruwa ne ya tab'a shi ba?.

Cikin b'acin rai da gajiya tace "Su'ada wane ruwa,yaushe ma damunar ta zauna kawai dai mara cin ne,tun ranar da aka kawo buhun gawayin nan nace wa Abbansu ba mai kyau bane,nace ya maida amma taurin kai ya sa ya kafe da fad'in me kyau ne,yanzu kinga tun sha d'aya na ke fama na kunna ya mutu na kunna ya mutu gashi har d'aya ta yi."

Cikin mamakin kalmar da Sakeena ta fad'awa mijinta wai tsabar taurin kai,ta jinjina kai da fad'in " Ba mamaki ruwan ne ya tab'a, tunda kinga da ga kudu a ke kawowa kuma su tuni ruwa yai nisa mu ne dai ruwan bai zauna ba, to ki kunna risho ki hak'ura da gawayin."

"Wane risho Su'ada, ai tun tuni yaran nan su ka mirjemin shi ya lalace."

Karaf Abba yace" To Umma ki d'ebo wancan sauran icen da a kai amfani da shi da biki ki kunna mana."

Zaro ido tai tace "Wa? so kake yau a silleni kenan,ka na ganin da bikin ana girki Ibrahim na k'orafin hayak'i na b'ata gida,tun tuni ka san ya tsani yaga an hura ice a gidan nan,balle yanzu da ya sa kud'in sa yai wa gidan fenti."

Haushi da mamaki su ka k'ara cika Su'ada, wato ita dai Sakeena ba ta iya tauna magana, kawai duk abunda ya zo bakinta fad'in shi take yi,cikin basarwa tace " To ai lalura ne,za'a zauna ba'ai girki bane,tunda gawayin ya k'i kamawa kuma akwai icen ki kunna mana."

Tashi Sakeena tai da ga durk'ushen hura gawayin ta na fad'in "To k'ila tunda kinsa baki ba zai k'orafi ba,bari na hura icen."

Su'ada kam binta tai da ido kawai,tun zuwanta gidan ta fahimci Sakeena a kwai raunin tsafta a tare da ita,don da ga zanin da take yawo dashi a tsakar gida ma kawai za ka gane k'azantarta,sannan ga ga yaranta ma,wani lokaci sai su Kai yamma ba wanka,su yi ta yawo cikin datti.
Maganar Islam ce ta dawo da ita nazarin da ta tafi, "Aunty ki bani abinci unwa ike ci."

dariya ta baiwa Su'ada yanda take maganar,cikin tsokanar ta tace "Ni ba zan baki abincina ba,y'an makaranta zan zubawa su ci kar su makara."

Kuka ta tsanyare da shi,ai kuwa yaran su ka sa dariya Su'ada ma tai d'an mirmishi tana mik'ewa tsaye ta rik'e hannunta "zo muje in baki to karki tara mana jama'a."

Kulan da ta cikawa Jabir ta juye musu a wani babban plate ta k'walawa Abba kira, ya zo ya d'aukar musu.

Taliya ta dorawa Jabir don ta san yanzu zai shigo gidan shima,abinka da aikin gas nan da nan ta dahu,ta na tacewa ta jiyo muryar Ibrahim a tsakar gida.

D'an lumshe ido tai ta na fad'in "My Khaleelee."

Ya na shigowa ta na fitowa a kitchen d'in,tsayawa yai harde da hannayensa a bakin k'ofa,ita ma ta hard'e hannu ta tsaya k'ofar kitchen, sun Kai y'an mintuna su na kallon juna a haka,da ga bisani ya tako a hankali gareta,bud'e hannayenta tai ta fad'a jikinsa,bayan ya yi hugging d'in ta na d'an lokaci ya cikata yana fad'in " Na gaji da yawa yau fa."

Cikin sanyin murya da kissa tace " Me ya faru ?"

"Na sha wahala a gurin gyaran keken nan fa."

D'an marairaice murya tai tana shafo sajensa zuwa gemunsa tace "Eyya sannu my Choice, zo muje in had'a ma ruwan wanka ."

Rik'o Hannayenta yai ya na kashe ido yace "Ba wanka kad'ai na ke buk'ata ba fa."

"To da me kake buk'ata ?"

Rank'afowa ya yi yana mata magana cikin kunne,y'ar k'ara ta saki ta na janyewa baya tace "A'a ni dai bari a gama da wannan d'in."

Kai tsaye ta wuce kitchen ta d'auko mai ruwa me sanyi da cup's, Bayan ya sha ya koma ya kwanta kan kujera,ita kuma ta shiga toilet ta had'a mai ruwan wanka, sannan ta fito da towel, mik'a mai hannu tai ya tashi zaune,ta tsugunna ta na balle mai botir d'in gaban rigar,shi kam idonsa na kanta,duk motsinta ta cikin idonsa.
Bayan ta taimaka mai ya cire kayan duka ya d'aura towel d'in, rigima irin tasa ya dage sai dai tazo ta taya shi wankan.k'wayar idonsa ta ke kalla cikin wani salon so tace "Rigima ko?"

D'an b'ata fuska yai da marairaicewa yace "Ni ba rigima ba,ai kin san na gaji da yawa,ba zan iya wanke bayana ba,ba inda ma zan k'ara fita sai gobe."

Y'ar dariya tai tace "Da wa yake wanke ma bayan in ka gaji."

Haka na ke barinsa,amma yanzu ai da a kwai me wankewa ,kuma ma ai nata ne,tafi kowa amfana dashi yanzun."

Da sauri ta juya ta na fad'in "To bance amin tonon silili ba ni,zo muje na tayaka amma fa ni ba zan yi ba."

Gyad'a mata kai ya ke cikin mirmishi su ka shige toilet d'in.
Rashin wayo irin na Su'ada ya hillaceta itama sai da yai mata wankan.
Bayan sun gama k'ailulansu su ka shirya,ita kam k'aramar riga ta sa mara hannu,tsayinta iya gwiwa,shara shara ce,sabida zafin da ake,shi kam ko riga bai sa ba wando kawai three quarter ya sa.
Su na zaune su na cin abincin ta jiyo muryar Jabir ya na wa Islam wasa, mik'ewa tai zuwa kitchen ta d'auko flask din abincin da ta zuba mai,ajiyewa tai gaban Khaleelee tace "Don Allah ko zaka mik'awa Jabir, ka ga Maman Abba ba ta dad'e da d'ora girki ba,abincin sa ma na bawa su Abba au kaci zasu tafi islame,shi taliya na k'ara dafa mai."
Chapter 12 · 0% Book details