← Book details Facala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 30

Sashe 15

Facala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shafo gefen fuskarta ya yi yana cewa "Ok ba damuwa.amma fa kayan sun miki kyau sosai."

Mirmishin jin dad'i tai,don a kullum burin Su'ada tai abu Khaleelee ya yaba to ta gama jin dad'i. "

Bata k'ara cewa komai ba ta mik'e daga jikinsa tana fad'in "Taso ka watsa ruwa muci abinci."

Hannunta ya kama ya mik'e tare da bin bayanta.

************
Sakeena tun da ta fita a gun nasu take ta mita, wai ana kallon yara baza'a kula dasu ba,don rashin sanin darajar haihuwa,ba komai ai a sannu mutum zai haihu ne zai san meye d'a da dad'in sa.
Bayan ta gama wannan mitar kuma ta d'ora wai Su'ada ta na sa kayan da basu dace ba gaban yara zata b'ata mata tarbiyar y'ay'anta.
Yaya Muktar na jinta yai mata banza, don sabbin d'abiun da Sakeena ta samo abun na b'ata ransa matuk'a.

*************
Wajan k'arfe goma na dare su na kwance kan gado tai matashi da k'irjinsa, shi kuma yana wasa gashinta,a hankali tace "My choice!"

"Um Zuciyata."

K'ara shigewa jikinsa tai sosai tace "D'azu fa naga kamar Maman Abba tai fishi kam fad'uwar da Islam tai,kuma ka k'ara laifi bayan wanda nima nai,ka kori sauran yaran."

D'an tsaki ya yi yana tab'e baki yace "Au ke abun ya dameki kenan,har kin kasa cireshi a ranki tun d'azu."

Gyara kwanciya tai a jikin nasa tana magana cikin nutsuwa tace "Ba haka bane, ka gane My Choice, duk uwa bata k'aunar jin kukan d'anta,kuma kaga ita za tai tunanin ko ina falon yarinyar ta fad'i, sannan da tace Islam tazo su tafi bai kamata kace sauran ma su tashi ba,za tai tunanin wani abu a ranta."

Cikin rashin damuwa yace "Rabu da ita,ina sane nace su je,kina ganin yanda tazo ta tsaya kan mutane ba wata gamsashshiyar sallama fa ta fad'o mana falo,kuma tazo tana ta wani ciccin magani,da gangan za'a bar yarinya ya fad'i ne,kuma ita fad'uwa in tazowa yaro ko a cinya yake ai zai fad'i har tana wani fad'in wai kamar ba babba a wajan,wallahi wannan abun da Sakeena na yi sam ta fara fice min a rai."

Jin da tai muryarsa ta fara canjawa alamar fishi yasa ta shiga shafa k'irjinsa a hankali take fad'in "Kayi hak'uri kaji,wata rana sai labari, amma don Allah karka k'ara cewa yaran su fita daga wajan nan kaji."

Gyad'a kai kawai yai yana juyar da ita,cikin tsokana yace "Kin daddaneni kin d'ora min nauyi,nima bari in rama gaskiya."

Bubbuga k'afa ta farayi a gadon tana fad'in "A'a ban yarda ba,kullum cikin danneni ka ke,don na d'an d'ana shine zaka min wayo."

Bai bari ta k'ara cewa komai ba yasa bakinsa cikin nata. 🤐

*Taku ce*
*y'ar mutan Ja'oji*🙋
[2/24, 12:05 AM] LAYUZA KABIR: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

_*Congrat Xeryisher, ina tayaki murnar kammala littafinki na KUCAKAR KISHIYA,Abunda ki kai dai dai Allah ya baki ladan,abunda ki ka kuskure Allah ya yafe miki*_🙏

_*page*_*25-26*

Rayuwa taci gaba da garawa Su'ada a gidan Khaleelee, bayan matsalar matar wan miji (FACALA) Su'ada bata da wata damuwa,mijinta yana bata kulawa d'ari bisa d'ari, uban mijinta yana mu'amulantarta tamkar y'ar cikinsa,haka y'an uwan mijinta su ke zaune da ita lafiya lafiya,kowa Son barka,don haka mafi yawan lokaci in tasa damuwar halin Sakeena aranta kuma ta tuna alkairan sauran mazauna gidan sai ta gode Allah taji komai ya fice a ranta.

Yanzu kuma wani sabon balli da Sakeena ta sako a gidan shine, wai dole Jabir ya koma d'akin Baba da kwana don tun bayan bikin su Su'ada tare su ke kwana da Abba a d'akin sa, to Jabeer baya shigowa gida da wuri sai sha d'aya, shi kuma Abba ga baccin wuri, ko yaushe sai dai ya kwanta a falo don Jabir baya barin key tun randa ya lalata mishi wayarsa da ya barta jikin charge yaje bacci yai danne danne ya lalata mishi,shi kuwa yace ya daina barin key d'insa,sai dai in ya shigo a tashe shi yaje ya kwanta, yanzu kam ta mirje idanuwanta tace sam bazai yuyu ba,d'aki dai cikin kason mijinta yake, don haka ita me 'Ya'ya hud'u an had'ata da d'aki biyu,sauran dakunanta biyu kuma uban miji da k'anin miji sun gaje, ga amarya ma da bata da kowa an shatar mata waje ita guda ko don ita an san y'ar masu dashi ce.

Tun safe yau take mita,kasancewar week end ne,Su'ada na gida, tana ta y'an gyare gyaran ta, haka ma Jabir Yau ya tashi da wanki kuma yana ta kwalemar d'akinsa.

Duk yarda maganar da take Jabeer yana jinta sarai amma sai ya kauda kai,uzirin da su kewa Sakeena ko yaushe shine, da can ba haka take musu ba,in ka d'auke k'azanta da rashin son gyara gida bata da wata matsala,amma tun auro Su'ada gaba d'aya ta firgice ta zama wata fitinanniya,ko hira ka fiye yi da Su'ada sai ta fara had'ema rai.

Bayan ya gama wankinsa ya fito da kayan gadon ya ke ta gogesu,da sauran tarkacen d'akin, can ya jiyo muryarta tana magana.

"Wallahi Allah cutar da ake min a gidannan ta isheni, gashi yanzu ina ji a radio wani malami yana fad'i cewa da yaro namiji ya tasa a raba shi da 'Ya'ya mata,to sabida ni bani da gata cikin gidan nan,yaro d'an shekara goma sha an barshi yana raba dare cikin mata,yo kullum yaro sai yayi barcin farko cikin mata sannan a tashe shi,kuma yanzu ga faruk ma ya fara girma shekara shida ai shima ya dace ace na cireshi a d'akin nan,ya dace ace Baby kad'ai ke kwana a falo ita da Islam amma da nai magana sai ace na fiye k'orafi da rashin son zaman lafiya,wallahi dole asan abun yi,tunda dai duk d'akunan nan sun zama mallakin ubansu,ya dace a barsu su wayata kuma,yo in banda ma lalura ace mutum ya zauna gida tun da k'uruciyarsa cikin garadan maza kuma har yanzu ba canji, tunda dai shima mutum an bashi matsugunni sai ya koma can da zama in an taki gaskiya fa."

Iya k'uluwa Jabir ya gama k'uluwa, duk sanyi irin na y'an gidan shi kam babu shi ciki,don sam baida hak'uri don haka bai son shiga sabgar mutane.
Yanzu d'in ma wani k'ululun bak'in ciki ne ya turnik'eshi,sam Sakeena bata gane dalilin da yasa yake mata kara,ta d'auka isarta ne ko wani abu,amma bari yau ya nuna mata shima d'an zamani ne.

Fitowa tsakar gidan yai ya tsaya cikin b'acin rai ya ke fad'in "Ke malama wai me ki ke son cewa? Fad'i abunda ke bakinki kai tsaye ki daina kwana kwana hakan zai sa nafi saurin d'aukan haske."

To daman me neman abokin tayi,nan da nan Sakeena ta shiga ruwan bala'i.

"Kar kai min rashin kunya kaji ko,kuma duk maganar da nake ai kaji kuma kasan Inda ta dosa,don haka d'aki nake son a bani guda zan had'a 'ya'ya na maza a can,kuma ba zan yarda da wani cewa ku rink'a had'uwa tare ba,yaro yayi barci tun sallar isha'i sannan sai bayan shad'aya a tashe shi, don haka naje karshe,hak'urina ya k'are wallahi dole a san abun yi."

Cikin fishi ya fara maida mata martani yace "Fad'a min cikin gidannan bulo nawa kika kawo da za'a gina?har kike ikirarin dole sai an baki d'aki kinsa 'yay'anki maza,to baza'a bayar ba k'arfinki ya k'watar miki, don tsabagen rashin mutunci har kina fad'ar wai sauran d'akunanku guda biyu uban miji da k'anin miji sun gaje, wallahi Allah Maman Abba ki gyara halinki sam wannan halin da kika samo ba d'abiar arzik'i bace,kuma ki shiga taitayinki kan yin duk furucin da ya fito a bakinki don wata rana zakiyi furucin da zai zame miki danasani."

Bambami fa Sakeena tai tayi kamar ta ari baki,ganin abun yak'i k'arewa ya sa Su'ada fitowa daga b'angarenta,hak'uri take ta bata,sannan taiwa Jabeer magana kan yayi shiru haka nan.amma me sai abun yake neman komawa kanta,ganin haka yasa ta koma b'angarenta taci gaba da ayyukanta.

Cikin ikon Allah sai ga Ibrahim, yana shigowa yaji yanda Jabeer ya ya ke caccakawa Sakeena magana,cikin tsawa yace "Kai Jabeer meye haka? baka da hankali ne? rufewa mutane baki dalla."

Cikin bala'i da masifa Sakeena tace "A'a ka barshi dai ai d'aurin gindi ya samu,in ba rashin mutunci ba yaron da na raina a hannuna cikin gidan nan amma shine yake k'ok'arin zagina."

Hak'uri Ibrahim ya fara bata yana fad'in "Meya faru ne haka? Me yai miki don Allah?"

"Ka tambayeshi mana,ka tambayeshi wace rashin kunya yake min."

Ibrahim ya juya ga Jabeer yana Tambayar sa meya had'a su.

Bai rage komai ba,ya fad'a mai duk maganganun da tai mai da Wanda shima ya maida mata.

Fad'a Ibrahim ya shiga mai yana fad'in "Kai zafin kanka har a cikin gida,Sa'arka ce,duk abunda tai maka bazaka iya kai k'ararta ba sai ka zauna kana cacar baki da ita.karka bari na k'ara jiyo muryarka wallahi."

Daga haka ya juya ya shige b'angaransa.ita kuwa Sakeena an samu yanda ake so nan ta k'ara bud'e wuta da yara maganganu.

Shi kam Jabeer kamar zuciyarsa zata fito haka yake ji,yanzu duk abunda Sakeena ta fad'a bai zama laifi ba sai nashi ne laifi,cikin fishi ya fice cikin gidan.

Ibrahim kam yana shiga ya zauna falo dafe da kansa,Sam shi bai son hayaniya a rayuwarsa, matsalolin gidan nam sun fara mai yawa.

Hannun Su'ada yaji a cikin nashi ta zauna jikinsa tana magana "My Choice sannu da zuwa,daina tagumi kaji don Allah."

Ta janye mai hannayensa daya dafe Kai.

Zuba mata ido yai ransa a b'ace yace " kina ji Suna rigima amma kika kasa kirana a waya ki sanar min."
Chapter 15 · 0% Book details