← Book details Facala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 30

Sashe 30

Facala Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Rik'o hannunsa Sakeena tai sannan tace "Ai da kin kawo shi nan kin yi aikinki,ga Nusrat har tai bacci shi ido biyu,barshi ki je ki aikin ."

Juyawa Su'ada tai tana fad'in "Yauwa ai kuwa kin kyauta,bari nai sauri sauri na gama."

Sakeena kuwa d'aukan Muklees d'in tai ta sashi a jikinta tana ta lallab'ashi har yai bacci sannan shima ta kaishi d'aki kusa da Nusrat ta kwantar da shi.

Wajan k'arfe tara Yaya Muktar ya dawo,yana shiga d'aki ya iske su Nusrat a shimfide kan gadon Sakeena, abunda ko y'ay'anta ba ta bari su kwanta mata a gado,abun ya mishi dad'i, shi kanshi yanzu canjin da yake gani tare da ita abun na birgeshi sosai.

D'an mirmishi yai yace "Bak'i ki kai a d'akin?"

Cikin yar dariya tace "Su Nusrat ne fa."

Kamar bai gane ba yace "Au,mamansu bata nan ne?"

"A'a aiki dai za tai ne,ta kawoshi nan,Nusrat kuwa daman ka san sai tai bacci take shiga d'akin su."

Zama yai gefen ta yana rik'o hannunta ya fara magana cikin k'asa da murya, "Sakeena! sosai nake jin dad'in yanda ki ka d'auki Su'ada yanzu tamkar k'anwarki,hakan na faranta raina,musamman da kike k'ara Jan yaran nan a jikin ki, hakan zai sa su k'ara shakuwa da y'an uwansu,na tabbata ko bayan ranmu y'ay'an mu zasu zarce da karfaffan zumunci.na gode sosai Sakeena, ki k'ara had'a mana kan zuri'armu matsayin ki na babba kin ji."

Gyad'a kai tai jikinta a sanyaye tace "Daman can shed'an ne ke sani kin Su'ada, don Su'ada ba ta tab'a yin abunda zai bata raina da gangan ba,tana ban girmana yanda ya kamata,sannan a wannan rashin lafiyar tawa na gasgata cewa FACALA y'ar uwa ce,kuma abokiyar hadin kai ce,yanda Su'ada ta tallafeni da yarana da duk hidimarmu ni na kasa mata hakan a lokacin da take laulayin ciki,na ji kunya matuk'a da yanda tai ta d'awainiya da ni,bata kyankyamina haka za ta zauna ta wanke min wajan ciwon nan tas ta samin magani,sannan ta shirya min yarana, tai musu girki.lalle FACALA ba abokiyar fad'a da gaba bace.kullum ina son bawa Su'ada hak'uri kan abubuwan da nai mata na rashin kyautawa a baya amma ina jin kunya wlh."

Fara'a sosai kan fuskarsa yace "Karki damu,kawai ki bata hak'uri ki cire jin nauyi ko wani abu a ranki,hakan zai sa ku k'ara kusanci da juna."

Gyad'a kai tai kafin tace "Insha Allah da safe zan mata maganar."

*Taku ce*
*Y'ar mutan Jaoji*🙋‍♀

👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

💔💔💔💔💔💔💔
*Na sadaukar da wannan page d'in kacokan ga k'awa kuma Aminyata. Amrah Auwal mashi,Allah ya tsareki a duk inda ki ke,ya sa kece amrya kuma uwar gida a gidan uncle Aliyu sadauki*😍🙏

*page 50*

🔚🔚🔚🔚🔚🔚

****************
Tun da ga wannan lokacin wata shak'uwa da k'arin zumunci ya karfafa tsakanin Sakeena da Su'ada, har ta kai Sakeena ta hana Su'ada bawa me raino rikon Muklees, ko yaushe wajan ta take barinshi,ita zata shiryashi ta bashi abinci, don daman shi ba mai kulafacin nono bane don haka ta yaye shi.

*Bayan wasu shekaru*

Abubuwa da yawa sun faru,na dad'i da akasin hakan,ciki kuwa harda k'arin haihuwa da Su'ada tai,wanda zuwa lokacin take da Yaya bakwai,autanta me sunan Yaya Muktar ma a lokacin shekarsa takwas, sai sakeena da ta k'ara haifar y'an biyu duk mata.
Zuwa lokacin Abba yana da shekaru talatin a duniya,kuma yana can k'asar Niger inda yake safarar waken suya, yayi karatun degree dinsa a fannin kasuwanci,lalurar ciwon suga da ta zaunar da Mahaifinsa waje guda ya sa shi ke d'auke da wani sashi na nauyin gidansu,yayin da Khaleelee ke d'auke da kaso mafi yawa na dawainiyar tasu.

Su'ada da Khaleelee a yanzu ba sa kano, suna zaune a Kaduna, kasancewar tuni Khaleelee ya bar d'inki, ya sami aiki a karkashin hukumar costume.yanayin karatu ya sa basu tafi da Nusrat da Muklees can ba,suna zaune gun Sakeena,sai sauran ne tare da su.

Fannin gida kuwa suna dai wannan gidan,sai dai Khaleelee ya rusheshi duka kowanne ya mai sabon gini sama da k'asa, babu wanda zai ce Wannan gidan na su ne,in sun zo hutu nan su ke yada zango.duk karatun y'ay'an yaya Muktar da na shi shine d'aukan nauyi.

___________________
Hajiya Su'ada zaune tana wayarta don nemo number Hajiya Sakeena,Jim kad'an da shigar kiran ta d'aga, daga b'angaran Hajiya Sakeena tace "Hajjaju yanzu na ke shirin kiranki fa,da gaske yaronki ya matsa number ba ba za'a d'aga mishi biki ba,wai dole ayi kamar ya da aka sa."

Dariyar kamilallun manyan mata Hajiya Su'ada tai kafin tace "To daman ai Kune da son kai,in ba haka ba ansa biki lokaci ya k'arato kawai yarinya ta bullo da wani batu Ku kuma Ku biye mata,tabbas da Nusrat kusa da ni take zata sha bugu,to kin sata a gaba tana yin yanda taso,don haka fatana Allah ya dawo da Abba gida lfy,sati guda da dawoqarsa za'a fara biki."

Cikin mirmishi Hajiya Sakeena tace "To an fi karfinmu dai ni da y'ata, shi kenan Allah ya kaimu lokacin."

"Ameen Ameen."
Hajiya Su'ada ta amsa.
Bayan sun yi sallama ta kashe wayar tana bin labulayen da su kaiwa falon k'awanya,wani tunanin take a ranta na shekaru ashirin da su ka wuce.
Tana tuno rayuwarsu da Sakeena tun farkon aurenta har zuwa yau,wato har kullum tana k'ara tabbatar da cewa FACALA ba abokiyar ga da fad'a bace,FACALA y'ar uwace,zuwa yanzu gashi zumuncin da ke tsakanin ta da Sakeena har za su had'a yayansu na fari aure,wato Abba da Nusrat.

Wani mirmishi ta k'ara saki tana fad'in *ALHAMDULILLAH*

_*Anan na kawo k'arshen Wannan littafi nawa na FACALA, ina godiya ga sarkin da ya bani ikon rubuta shi, abunda nai dai dai Allah ya ban ladan,abunda na kuskure Allah ya gafarta min*_

_Masoya da su kai jimirin bina cikin labarin ina godiya matuk'a da gaske, Allah ya bar zumunci_

*Sharhi ko shawara*👇
*07067270055*
_Layuza kabir Adam_🥰😍🙋‍♀🙋‍♀🙋‍♀
Chapter 30 · 0% Book details