← Book details Facala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 30

Sashe 3

Facala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kicib'us su kai da Jameel yana k'ok'arin shigowa,D'an jenyewa tai gefe tana fad'in "Oh soja kana gari Ashe? Zaka bigeni da k'arfin allurarka."

Dariya yai a taka'ice yace "ina zuwa haka na kawo muku ziyarar bazata.hajiya Jidda har dake za'ai tafiya ma?"

Cikin dariya Jiddah tace "Yaya Jameel ai bamu San kana tafe ba wallahi,zamu je zoo road ne mu amso d'inki."

"Ok to bari in shiga mu gaisa da Mama sai in fito in kaiku ko."

Da sauri Su'ada tace " A'a ba zamu wahalar da kai ba ka barshi kawai wlh zamu hau Napep ma."

D'ora hannunsa yai a baki alamar tai shiru daga haka ya wuce cikin gidan.

Cikin k'unk'uni Su'ada ta je ta tsaya jikin motar tasa tana fad'in "Wai ayi ta takurawa mutum haka kawai,ni nace ban son hawa motar amma ya wani zaro min ido kamar ubana,mutttsss."

Y'ar dariya Jidda tai tace "Kai Aunty Su'ada meye laifin yaya Jameel wai don Allah yanzu shima duk k'ok'arin sa kanki baki gani,duk sanda yazo garin nan yata nacin zuwa wajanki kina yarfa shi,ni kam wlh ban ga aibunsa ba Sam."

"Dallah malama rufemin baki ke me yasa bazaki soshi ba?"

"A'a ai ke yace yana so ba niba amma dai gaskiya Aunty Su'ada a shawarce karki wuce yaya Jameel a cikin zab'enki wlh don mutumin yayi fa."

Ta bud'e baki zata bata amsa ya fito don haka ta gintse kawai amma ta watsa mata harara."

Cikin fara'arsa ya k'araso yana fad'in " kuyi hak'uri na tsaida Ku ko? Ku shiga mu tafi."

Ya bud'ewa Su'ada gaba sannan ya zagaya ya zauna mazauninsa.

*Taku ce*
*y'ar mutan Ja'oji*🙋

[2/23, 11:51 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

_*page*_ *7-8*

*19/10/2019*

Tunda su ka d'au hanya Jameel da Jidda ke hirarsu amma Su'ada tai tsit ta tafi duniyar tunani bama ta jin me su ke fad'i.

Lokacin da su ka tsaya k'ofar Shagon su Khaleelee Su'ada ta kalli Jameel da fad'in "Soja muna godiya fa."

D'an hararar ta yai cikin wasa da fad'in " zan bige wannan bakin in ya k'ara min godiya,sannan zan juya da ku ai,ba sai kun shiga ba d'aga musu hannu su mik'o muku kayan."

Cikin k'osawa Su'ada tace" A'a wane kalan su mik'o mana kuma? Wannan shagon fa da amana tsakaninmu da su,zamu shiga Jidda ma zata bada d'inki."

"Ok to Jiddah in kin bada d'inki naki sai ki amso mata natan."

Kallon sa Su'ada ta tsaya yi zuciyarta na mata zafi da Wannan k'arfa k'arfa haka,tace" Wai ne yasa zan zauna ni d'in a nan?na fad'a ma ga abunda daman ya fito damu kuma sai in coge cikin mota? In ka ga da takura Allah ba damuwa kaje zamu hau Napep mu koma."

D'an mirmishi yai da fad'in "Su'ada dai so kike in tafi ni kam k'afata k'afar ki, kishi nake ji ki shiga tsakiyar mazan nan wallahi."

Kafin ya k'ara d'ora wata maganar Su'ada ta bud'e mirfin motar ta fito ranta bace.

Jidda ma ta rufa mata baya. Ganin haka shima sai ya fito ya bi bayansu.

Da sallama suka shiga shagon amma fuskar nan ta Su'ada ba walwala sam, bayan sun gama gaisawa da yaran shagon ta juya ga Ibrahim tana d'an k'ok'arin sassauta fuskata "Khaleelee ina fatan komai ya zama Ready?"

Da fara'arsa yace "Insha Allah kuwa."

A dai dai nan Jameel ya shigo hannayensa hard'e cikin wando, d'aga musu hannu yai tare da Sallama suka amsa banda Ibrahim da yai kamar ma baiga shigiwarsa ba.

Babbar leda me d'auke da kayan su ciki aka d'auko musu,Jidda ta amsa,tana fad'in "Khaleelee wannan d'in kin Jabir mutumina ne zai min don naga tuni yake k'ok'arin finka zafi yanzu."

Dariya suka sa,Su'ada ta d'an harareta "karyar mutum yafi Khaleelee iya d'inka,ke dai kawai kina son kiyiwa Jabir dad'in baki ya tsatsuboki."

Nan ma dariya suka sa, yayin kuma da tsakin Jameel ya sa suka maida hankalin su gareshi amma sai suka ga ya juya ya fita yana cewa "Jiddah tunda kun gama mu wuce mana."

D'aukan ledar tai ta bi bayan sa, ita kam Su'ada wani tsaki taja na takaicin wannan milkin na Jameel.

"Hajiya ki wuce oga na jira."

Wani da suke wasa da Su'ada ya fad'a. Shima harara
Ta watsa mai tace "kai kaga Oga ni ban ganshi ba wallahi."

Had'e rai sosai Ibrahim yai kawai sai ya fara duba wayar sa.

Ita kam cikin jin haushi ta juya ta fita tana musu sai anjima.

Tunda ta shiga motar ta cona baki gaba tana kallon gefe,shima bai tanka mata ba balle Jidda dake baya.

Suna zuwa k'ofar gate d'in su yaja ya tsaya Jidda dai ta fita tana fad'in "Yaya Jameel sai anjima."

Itama tana k'ok'arin bud'e motar ya dakatar da ita da fad'in "Su'ada ban son kina zuwa wannan shagon,kin zauna kina ta wani hira da dariya."

Cikin mamaki da takaici take kallon sa,ta ma rasa me zatace don haushi kawai sai ta juyar da kanta gefe.

Ya d'ora da fad'in "Su'ada kin san dai yanda nake sonki da kishinki, ban San naga wani namiji na kulaki wallahi, Su'ada yaushe ne zaki ban dama na fito? Ko yaushe na miki magana sai kice karna turo in jiraki, in dai don karatu ne ne ya k'are kuma saura me?"

Yamutsa fuska tai cikin k'osawa tace " Ka bari zamuyi magana don Allah yanzu akwai uzirin da zanyi a ciki."

Zuba mata ido yai cikin nazartarta can zuwa y'an dak'ik'u yace
"Alright, ki je zamuyi waya."

Tana sa k'afarta waje tace "Tnx."

**********
Da dare tana kwance bayan ta gama k'ara dudduba takardunta,tunani take a kan maganarsu da Jameel ta d'azu, wato shi yanzu tana cewa ya fito sai aure a shirye ya ke, gashi Mama ma abunda take jira kenan,in har fa ta bawa Jameel dama ya fito shikenan Ta rabu da Khaleelee,ita fa wallahi bata da wani buri bayan nashi. Wata zuciyar ta tunasar da ita wai ke ma Ibrahim ca yai yana sonki harda kike lissafinsa cikin masoya, ki kama kanki fa ki san me kike yi. Wannan tunanin yasa taji gabanta ya fad'i, tai ta juyi tana jin kanta na wani sara mata don rashin madafa.

______________
Kwanaki biyar da suka biyo baya su Su'ada suka kammala final exam kuma a ranar sukai waleeman su wanda ta k'ayatar su kai abubuwa cikikn tsari,har yamma lis sannan aka tashi kowa da tarin y'an uwansa da abokan arziki da suka zo taya su murna.

Suna cikin motar komawa gida wayar Su'ada tai ringing tana dubawa taga sunan Khaleelee ya bayyana kan wayar" mirmishi ne ya bayyana kan fuskarta ta d'aga tare da sallama" Ranki ya dad'e barka da yamma ya hidima?"

"Me zakace min Khaleelee ina ta zuba ido in ga ta inda zaka b'ullo amma tsit har aka tashi ba komai."

"Kiyi hak'uri d'inkuna ne suka rik'e ni sosai amma naso zuwa,duk da haka zanzo har gida in yi tawa murnar."

"Tom shi kenan ka wanke kanka,kuma ina nan ina zuba ido daga yau har gobe har jibi ."

Dariya yai yace "To shi kenan,Allah ya kaimu zaki ganni kuwa."

Bayan sun kashe wayar kawai sai take ta jinta cikin nishad'i da walwala fiye da wadda take ciki yau d'in.

*******
Tana Sallar Magriba ta d'auko wayarta tana duba pic's d'in da sukai yau har ba adadi,kunna Data tai ta shiga WathApp abunda ta dad'e batai ba,jimawa da yawa network ya wadata nan fa ta shiga d'ora Status ba kama hannun yaro.
Sak'onnin taya murna tai ta samu daga contacts d'in ta,replay ta shiga maida da godiya har lokacin sallar isha'i yai ta tashi tayi,cikin d'oki ta k'ara d'ukan wayarta tana bin duk sakkonin. can sak'on Ibrahim ya shigo,da azama ta bud'e
" _Hhmmm gimbiya sarkin kyau da kwalliya ki babu, ko ina kika shiga sai kin haska mata,gashi dai komai naki da nasu iri d'aya Amma duk da haka kin k'eresu nesa ba kusa ba_."

Y'ar dariyar jin dad'i tai sannan ta maida masa amsa

" _Hhmmm Khaleelee baka gajiya dai da tsokanta fa_"

" _kullum gani kike kamar wai tsokanar ki nake,ni kuma gaskiya na fad'i, Tabbas wannan bawan Allah ya dace kuma yayi zab'e me kyau,duk da naga shi D'an zafin kai ne_."

" _Hhhhhmmm Khaleelee kenan,ai ni ba wanda zai ce ya sameni ya dace da matar aure,don banma fidda mijin ba balle shi yace ya samu_ ."

" _b'oye min dai kike yi,amma da ganin yanda ya ke had'e fuska yana wani d'aukan zafi ai yasan ya kama waje a zucuyarki_."

" _hhhhhmmm Khaleelee kenan,kasan me? Wlh Jameel bai cikin kalar mazan da na ke so,kawai dai shi ke hidimar sa amma ni bai da waje a zuciyata_."

" 😳 _wannan hadaddan gayen ne bai cikin mazan da kike so? Ai kuwa naga matan yanzu irinsa su ke so_."

" _hhhmmmm matan yanzu ai kace,ni dai bai cikin tsarina Sam_"

" _To me yasa bai cikin tsarin naki?kuma wannan kala ne ya ke cikin tsarinki_."

Y'ar dariya tai tana gyara kwanciyar ta don hirara tasu ta fara mata dad'i. duk da tasan in batai taka tsantsan ba zai rafkota.

*Taku ce*
*Y'ar mutan Ja'oji* 🙋
[2/23, 11:51 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

*Na sadaukar ga wannan page d'in gareku dukkan k'awayena na media, bazan manta da Ku ba har abada*🤝🤝🤝

_*page*_*9-10*

Typing ta fara yi tana bashi amsa.

" _Da farko dai kaga Jameel soja ne,ni kuma banda ra'ayin auran soja,sannan kaga kalarsa fari ne sosai,ni kuma namiji fari baya min kwarjini ko kad'an wlh,sannan dai cikin halayensa da yawa basu min ba,don yana da zafin rai da nuna gadara duka banson namiji irin haka,wannan dalilin ne yasa sam bazan iya auran saba_."

Kallon rubutun Ibrahim yai tayi yana k'ara maimaitawa mamaki yake ganin yanda tace farin namiji bai mata kwarjini,sannan shi dai kallo d'aya yaiwa Jameel yasan ya ajiye yayan bankin, yanzu ko dan kud'in sa Su'ada bazata soshi ba kenan.ya dad'e kafin ya bata amsa yana nazarin maganganunta.

" _To wane Namiji ne kalar zabinki_?"
Chapter 3 · 0% Book details