Sashe 10
Facala Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mirmishi mai sauti ya saki ya na matsowa gareta,ja da baya ta fara ta na d'ora hannayenta a saman fuskarta don d'an towel ni kawai a jikin sa, sai da ta Kai ga bango ta tsaya shi kam yai mata k'awanya ya sa duk hannayensa ya tokare ta yanda ba za ta iya samun wajan fita ba.
Duk jikinta rawa ya ke zuciyarta na bugawa,a hankali ya fara magana " Su'ada wai tsoron na mene ne duk kin takura kamar ba tare ki ke da Khaleeleenki ba? don Allah ki saki jikin ki kinji,ba abunda zan miki fa."
Yanda ya ke maganar cikin cool voice ga shi ya matseta sosai kuma cikin kunnanta ya ke aje numfashi duk sai tsigan jikinta ta fara tashi.
Cikin tsoro da shagwab'a ta fara magana "To ni dai don Allah ka matsa kuma ka sa kayanka."
"Hhhhhmmm wai tun kafin me afkuwar ta afku ki ke jin kunya haka?"
Yarfe hannu ta farayi idanuwanta a runtse ta ce"Wayyo ka bari don Allah, ban hanya in wuce falo na jira ka."
A hankali ya saki dariya ya na matsawa ya ce "To wuce na matsa."
Da sauri ta fice zuwa falo,wata ajiyar zuciya ta sauke bayan ta zauna kan kujera.
Ta na zaune wajan mintina ashirin ya fito sanye da wani lafiyayyan yadi me laushi, fari k'al ne me layi layi sannan shara shara ne ana hango farar singlet d'in da ke ciki,ba hula a kansa sai gashin sa da ya gyara, daman ga gyaran fuskar da ya sha na angonci hakan ya k'ara fito da kyan sumar ta sa.
Kallo d'aya tai mai tai k'asa da idonta,k'arasowa ya yi gabanta ya tsugunna tare da rik'o hannayenta biyuYace " Amarya na gama shiryawa,d'ago ki gani nai kyau?"
A sace ta kalleshi sannan ta gyad'a mai kai alamar ya yi kyau.
"Ok me ki ka girka na ga flask?"
"Ruwan Tea ne kawai sai wancan naman da na d'umama."
"Sannu da aiki kin yi k'ok'ari, raso mu ci to."
A kunyace dai ta daure su ka karya, sannan ya taya ta su ka wanke cups da plate d'in da su ka b'ata.
Lokacin k'arfe tara ta yi, yace mata zai fita ya gaida Baba da sauran mutan gidan,mak'alewa tai za ta je,ba ja yace ta sa mayafi su je.
A tsakar gida ya sami su Zakiyya da sauran y'an biki da basu tafi ba su na ta aikin had'a abun karyawa.kowa ca ya yo kan Amarya da gaisheta,ita kam kunya ta lullub'eta sai tadabarbarce,ganin haka ya sa yace su k'arasa wajan Babah.a d'akin sa ya na zaune ya na jin Radio su kai sallama shi a gaba ita a baya ,cikin dattako ya amsa gaisuwar da Su'ada ke mai, sannan ya amsawa Ibrahim,nan ya k'ara musu nasiha sosai kan hak'uri da juna,sun jima a d'akin duk jikin su ya mutu.
bayan sun fito d'akin Sakeena su ka shiga,Su'ada ta gaisa da jama'ar d'akin da bata san su waye ba,nan ma ta dad'e zaune don shi fita yai ya barta.
Zakiyya ce ta kawo mata k'osai da kunun tsamiyar da su kai na karyawa, ita dai ba ta ce ta k'oshi ba kuma ba ta ci ba,har Khaleelee ya k'ara shigowa ya samu duk an fita an barta wai ta karya, dariya yai ya na kallonta ya ce"To ke ki sha kunun mana ki ka sashi a gaba."
A hankali tace mai "Allah na k'oshi kuma kunya na ke ji nace ba zanci ba."
"To taso mu koma wajanmu sai nace musu a can zamu ci ko."
D'aukan abincin yai ta biyo bayan shi, a tsakar gida yace wa su Zakiyya wai kunya ta ke ji zata ci a can.
******
Janta yai ta yi da hira don ta saki jikinta, a hankali ya jawota jikinsa ta na k'ok'arin matsawa ya k'i bata dama,a hankali ya kai hannunsa wuyan rigarta yace "Ban San ya a kai d'inkin nan ya miki yawa ba,zan ragesu in kin cire don ban san ki na yawo cikin d'inki."
Nok'e kafad'a tai da fad'in "um um karka rage,ramar da nai ce ta sa haka."
"Oh da jikin ba haka ya ke ba ashe,ni ramar fuskar kawai na gani ai,ashe jikin ma ya rame,to wai me ya sa ki ramar ne ."
K'ok'ari ta ke dole sai ta tashi a jikin sa shi kuma ya k'i yarda,kamar za tai kuka tace "Don Allah ka barni,ni bacci na ke ji fa."
Y'ar dariya yai ya na k'ara gyara mata kwanciya a k'irjinsa yace" ki yi baccin ki a nan,nan shine makwancin ki."
Shiru tai ba ta k'ara ko k'wak'k'waran motsi ba,ta lumshe ido a ranta ta ke tunanin, yau ita ce kwance jikin Khaleelee matsayin matarsa, Allah abun godiya ne,don haka ba zata gaji da gode mai ba,da ya mallaka mata muradinta abun alfaharita ba.
Ga Khaleelee shi ma wannan tunanin ya ke, yana ta hamdala cikin ransa.
**********
K'arfe d'aya na rana y'an uwan Su'ada su ka zo da gara nik'i nik'i.
Kayan abunci masha Allah, shinkafa manyan buhu biyu,ta tuwo babba d'aya,taliya kwali uku macaroni uku indomi uku ga buhun semo biyu,manyan jarkar man k'uli da manja,ga magi kwali biyu, sauran kayan yaji su duk cikin robobi,dangi su citta,kanumfari,yaji,kub'ewa kuka,kanwa da dai sauran su, b'angare guda kuwa kayan alkali da dubulan da su nakiya su cin cin ne ciki manyan Mazubi.
Sai da aka fitarwa dangin miji kayan ciye ciyen na su tsaf,sannan a ka warewa Baba na shi daban.
Wannan gara ta k'arawa Su'ada k'ima a idon y'an uwan mijinta balle shi ma uban gayyara don aka mishi gata matuk'a, a Wannan zamanin duk namijin da a ka had'awa wannan gara ai an mai gata.
Sai yamma y'an uwan Su'ada su ka tafi, zuwa lokacin duk sauran y'an su Ibrahim na da ke gidan su ka tafi,ya rage sai ya su ya su.
Ibrahim na shigowa gidan ya ji tsit, k'ofar d'akin Sakeena ya tsaya ya na magana "Maman Abba bak'i sun tafi sun barmu mu kad'ai ko?".
A wani ya mutse ta amsa mai " Wlh kam kowa ya koma inda ya fito."
Bai damu da yanayin da ta amsa bai ba ya d'ora "To Allah ya saka da alkairi, ai ansha hidima sannunku da fama da jama'a."
Gidan ya bi da kallo ko ina ba kintsi,ya gyad'a kai kawai ya wuce b'angaransa.
Su'ada ba ta k'ok'arin had'a girkin dare,kitchen d'in ya lek'a ya na mata sannu da aiki,ta amsa itama ta na mai sannu da shigowa.
D'aki ya wuce ya cire kayan jikinsa ya sa wando 3 quarter da riga k'arama.
Fitowa yai tsakar gidan Sakeena ya kira Abba ya na tara mai ruwa a famfo ya zage ya wanke gidan tsaf har band'aki sannan ya wuce k'ofar gida ya share tas.
Ya na shigowa ciki ya wuce toilet yai wanka tare da d'auro alwalar sallar magriba.
Ita kam Khadeejah bayan ta gama girkin ta tsaka wanka cikin wata doguwar riga y'ar saudiya me duwatsu ta yafa mayafin rigar,
Sai bayan magriba ya shigo gidan,a nan su ka ci abunci dare,bayan sun gama ya had'a musu kayan kallo, a nan ma janta yai ta yi da hira ba laifi ta sake sosai yanzu har tai ta bashi labarin biki.
*TAKU CE*
*Y'AR MUTAN JA'OJI*🙋
[2/23, 11:54 PM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭
*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*
👩🏻💻👨🏻💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_
__*Sadaukarwa ce gareku Y'an Zamani Writers Association, y'an uwa abokan aiki.*
*Nasmat Muhd Ark'illa*
*Amah Alh.Kabir*
*Zainab Shazee*
*Zeesa*
*Fatima Zara Eyman*
*Meenauwal*
*Hafsah Usman waziri*
*Hafsah I Umar*
*Aysha xeryeesher*
*Princess Deejah*
*Bilkisu M33RAH*
*Umaima Muneer*
*Baby Fara*
*Haseena Baby*
*Deebersh*
*Bilkisu Abdallah*
*Na gaisheku kyauta wlh*👌😂
*page 19-20*
Kwanan Su'ada uku a gidan amma Ibrahim ya sa mata ido,so ya ke duk fargabar da ke tare da ita ta kau, a cikin y'an kwanakin ta sake da shi,za su ci abinci tare ba tare da tai nok'e nok'e ba,har zai sa ta a jikinsa ma ba ta ture shi ba,da wannan damar yau yai amfani,su na kwance a gado bayan sun yi shirin bacci ya kunna game a wayarsa yace mata su yi tare,ai kuwa kasancewar wayar na hannunsa ya sa ta shiga jikinsa sosai su na game d'in, lokacin da hankakinta ya koma duk ga game d'in shi kuma a lokacin idanuwansa su ka koma ga k'irjinta da rigarta ta yo k'asa ta ba su damar bayyana.
duk jikinsa ya mutu,tunaninsa ya fara nisa,ya ji ya d'okantu da kasancewa da ita,a hankali ya janyo ta jikinsa ya na karb'e wayar da ga hannunta ya kashe,tirjewa ta fara yi cikin y'ar shagwab'a ta ke cewa "Ni dai Allah ban yarda ba,ni dai ka bani in ci gaba,don ka ga zan cinyeka shi ne ka k'wace ko."
Rik'e hannayenta duka biyu ya yi da ta ke k'ok'arin k'wace wayar a hannunsa,ta fara birburwa a jikinsa ta na goga kanta a k'irjinsa,cikin dashashshiyar murya yace "Su'ada ki na yin barna fa wannan abun da ki ke yi."