← Book details Facala Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 30

Sashe 27

Facala Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadda kai yai kafin ya d'ago yace "Su'ada ni kam a wannan rayuwar akwai namijin da ya kaini Sa'ar surukai? Ina tabbatar miki ni d'in na daban ne a Wannan rayuwar,ana dad'ewa ba'a sami surukai irin nawa ba.bazan gajiya dayi musu addu'a ba,Allah ya bani ikon k'ara rik'e musu ke da amana."

"Ameen Ameen" Su'ada ke amsawa a lokacin da yake ta yiwa su Abba da mama addu'a.

Tashi yai zuwa gun Abba yayi godiya sosai.

*****Sakeena dai tun Randa Khaleelee yaje sukai magana da Su'ada kan cewa ba taron suna daya dawo gida yake fad'a mata ba suna,to tana kan hakan cewa ba suna,amma kwana hud'u da haihuwa da haihuwa Su'ada ta kitara a waya tace don Allah ta fad'awa mak'otansu zancen suna, bata ce mata Khaleelee yace ba suna ba ta bita da to.bayan ta kashe wayar ta jijjiga kai da fad'in "Wato mijinki yace ba suna,shine ke don son iyawa zaki ce in fad'awa mak'ota ko,to wannan karon zaki sha kunya, don zan miki gayyar da zaki rasa abun basu,tunda ke kin iya k'i fad'i."

Tun a lokacin ta tashi yara ta rink'a aikasu gida gida wai suce Su'ada tace a fad'a musu zancen suna a can gidan iyayenta medile,har bayan layinsu da kewaye ta ai aika. Ai kuwa mutane da son abun duniya sunga wancan karon yanda akai wadak'a da abinci da nama,ga take away in mutum zai tafi, wannan yasa kowa d'ora aniyar zuwa suna medile,ca suke don dai kud'in mota naita d'ari ta kaika ta dawo da Kai. Hhhhhhhhh kaji son banza fa.

*********Mama ta shiga kasuwa ta siyowa Su'ada tsadaddan less da dank'ararriyar shadda, ga takalma da mayafai,sannan yaro ma aka siyo mai kayansa rankacakaf.

Abunka da matar tela, tuni ya kawo mata wancan kala biyar din data bashi sannan ya k'arb'i less da shaddar suma yace zuwa fan suna da safe zai gama.

********
Ranar suna yaro ya amsa sunan Muhammad Mustapha,za'a rink'a kiransa da Fudail.

Hidimar suna sosai ake a gidan,dangin Khaleelee da suka zo Waje daban aka saukesu tare da kayan abunci ci iya cinka, ga lemukan jarka kala kala.

Da azahar kam sai ga gayyar y'an unguwar su Su'ada inda kasan an kunna famfo haka suka rink'a shigowa.sosai Su'ada tai mamakin yawonsu,amma taji dad'i sosai,suma tarya akai musu ta girma.
Aka wadatasu da abinci kala kala da lemuka,ai kuwa nan suka shiga zance da watsa shinkafa,wata cikinsu da bakinta bai iya shiru tace "Kai masha Allah, Ashe dai da gaske da ake fad'a yarinyar man y'ar masu dashi ce, ji gida don Allah, dasss ko ina fees. gashi dad'i na da hidimarau abunci ba k'auro,kinga wannan haihuwar ma da take ta biyu komai rabajau."

Wani kululu ne ya tasowa Sakeena, a duniya in kana son ganin bak'in cikinta to ka rink'a fad'ar arzikin su Su'ada a gaban ta.tabbas da tasan wannan hidimar aka shirya da bata gayyaci kowa ba,ita da tai gayya don aji kunya amma sai akasin hakan.

Dangin Khaleelee sun San wannan hidimar bashi yayi ba,tunda sun san yanzu halin da yake ciki,don haka su kaita sawa iyayen Su'ada albarka.

Khaleelee ma lokacin da yake shago yaga almajirun au Su'ada da kayan abinci nik'i nik'i, yayi mirmishi yayi cikin ransa yana fad'in "Allah ka sakawa iyayen matata da gidan aljanna, itama kai mata sakayya da alkairi ya bani ikon kula da ita.

Bayan sun yi walimarsu a shago, da la'asar ya d'and'asa wankansa cikin sabuwar shadda ya nufi gidan suna don Su'ada nata kiransa da wai yazo me hoto yazo,shi da Jabeer suka je,suma aka k'arasa hidimar Sunan dasu.

***Tunda Sakeena ta dawo gida take bak'in cikin hidimar da akai a gidansu Su'ada da yanda taga an k'ara gyara musu gidan,wani kishin data kwana biyu ba tai akan Su'ada yau taje ji,haka ta kwana rai ba dad'i.
(Ya Allah! Wai don Allah me had'a facala kishi da facalarta,ke baku had'a miji ba baku,had'a tukunya ba,Baku had'a komai ba Sai y'an uwar takar mazaje amma Ku zauna kishin juna."

*Taku ce*
*Y'ar mutan Ja'oji*🙋

[2/24, 9:17 AM] LAYUZA KABIR: 👭 *FACALA* 👭

*NA*
*LAYUZA KABIR* *ADAM*

👩🏻‍💻👨🏻‍💻
*ZAMANI* *WRITERS* *ASSOCIATION*
📝
_We_ _are_ _here_ _to_ _educate_ , _motivate_ ,and _entertain_ _our_ _Readers_

_*page*_ *47-48*

Kula sosai Mama take bawa Su'ada a zaman jegonta,sati guda da suna Abbansu ya tafi legos, kwana uku da tafiyarsa ya turowa Khaleelee dubu d'ari wai ya k'arasa shirya shagonsa.lokacin da wannan sak'on yazo ga Khaleelee ji yai ya rasa ma da wane baki zai yi godiya, sabida alkairan Su'ada da iyayenta gareshi sun yi yawa,shi ya kamata yayi dawainiya da iyayen matarsa,amma gashi sune suka bashi ya kuma suke dawainiya dashi, lalle samun surukai irin wannan sai an tona.

Kiran Abban yayi a waya yana mai godiya, Abba kam ya kamashi da fad'a kan cewa shi uba ne a gareshi, duk abunda yai masa bai buk'atar godiyarsa,don haka ya daina godiya a tsakaninsu.

Da Khaleelee ya fad'awa Baba shima godiyar yai tayi,yanawa iyayen Su'ada addu'ar alkairi.

Da sallar isha ma da suka had'u da yaya Muktar a masallaci yakw fad'a mishi bayan keke ga dubu D'ari Abban Su'ada ya k'ara mai,godiya shima yayi,har suka shigo gida suna maganar, Sakeena dake tsakar gida tana d'aura alwala tana jin me suke tattaunawa,jin abunda Abban Su'ada ya yiwa Khaleelee ya sa jikinta mutuwa murus,,ta san ita kam in mijinta ne ya samu wannan jarabtar Babanta bashi da ko dubu goman da zai iya tallafa mai,tunda gobarar nan ta afku ko yaushe cikin hidima yake da su, ga keken daya siya mishi industrer iyayen dubunnai ya fidda ya siya,ga hidimar suna da yai musu, sannan ga wannan kud'i ya bashi,eh Lalle Khaleelee auran jari kawai yayi.

Abunda tai ta maimaitawa a zuciyarta kenan jin wani d'acin Bak'in ciki na tasowa daga mak'ogaranta zuwa harshenta.

________Cikin ikon Allah Khaleelee ya shirya shagon sa kamar da,sai dai har zuwa yanzu kekuna basu k'aru ba,daga Wanda Su'ada ta bashi ya siya,sai Wanda Abbanta ya siya mai,sai kuma wata uwar d'akin sa ta bashi bashin keken surfani guda d'aya duk wata zai rink'a biya. Ai kuwa sai ga shago yayi ras.

************
Lokacin da Su'ada tai ar'bain ta rok'i Khaleelee ya barta taje garin Abban su wato Darki,da farko yaso yak'i yarda Amma tai tai mishi magiya, ba dan yaso ba ya barta.

Tare suka tafi da dukkan k'annanta,kwana biyu su kai suka dawo.
Washe garin dawowarta Ta koma gidan mijinta.

___________
Haka rayuwa taci gaba da garawa yau da dad'i gobe babu,fannin miji kam sai godiyar Allah,don Su'ada kullum cikin godewa Allah take,bata da wata damuwa tsakaninta da mijinta,ko yaushe cikin kyautatawa juna suke.
Fannin FACALA kuwa me hali bai fasa halinsa sai dai a samu sassauci wata rana,to haka Su'ada ke k'ara hak'uri kullum ga Sakeena,don bata fasa halinta na kishi da hassada.

*BAYAN Y'AN WATANNI*

*********
Wata ranar jumma'a Khairiyya tazo gidan Su'ada ta taho da Nusrat don har yanzu ba'a dawo da ita ba.

Kwalliyar kawai da akaiwa yarinyar abun kallo ce,ga tsananin kyawu da kullum take k'arawa, harma wasu na cewa duk kamarta da mamanta tafi maman nata kyau.
Masha Allah, dake kuma ta d'auko tsayin mahaifinta sai ake ganin saurin girmanta,duka lokacin shekarunta biyu,amma zaka ce tayi uku ko ma tafi haka,sanyin halinta sak na mahaifinta,duk da Su'ada ma akwai hak'uri to gado biyu tayi, zaka dad'e baka ji hayaniyar yarinyar ba,balle kaji kukanta,sam bata da rikici irin na yara da rigima,sosai zaka tabbatar da hak'urinta.

An mata kwalliya cikin riga da wando y'an kanti,wandon Jean's bak'i,sai wata riga me jikin santsi kalar ruwan madara me haske sosai,duka gaban rigar an sa stones me d'aukan ido,k'afar ta sanye da wani bak'in d'an ubansu takalmi sau ciki,kallo d'aya za kaiwa takalmin kasan da iyayen kud'i aka siye shi,kanta kuwa wani k'ananun kitso ne da aka sawa bit tako ina, ga wasu k'ananun ribbons an jera, dake Allah ya mata baiwar gashi me cika da tsayi tamkar mamanta,kai da kaga yarinyar kaga jinin fulanin asali.kuma dake akwai kula sosai da gata tare da ita sai kaganta tamkar d'iyar turawa.

A tsakar gida Kairiyya ta iske Sakeena na girki, bayan ta dire Nusrat da ga hannun ta zuwa k'asa ta gaida Sakeena cikin girmamawa, itama cikin fara'a ta amsa amma duk hankalinta na ga Nusrat,kallon yarinyar take tamkar bata santa ba,cikin d'an yak'e tace "A'a Nusrat y'an mata,yau an kawo mana ziyara kenan, zo in ga kwalliyar taki."

Tsayawa yarinyar tai tana mata kallon rashin sani,amma dake bata da k'iwa sai ta k'arasa gareta,Sakeena ba tai la'akari da bak'in gawayi da maikon dake hannunta ba ta Kai mata cacima tana d'orata a cinya,d'an wasa tai mata sannan ta sauketa ganin kairiyya ta ja ta tsaya tana jiran ta direta su k'arasa.

Su'ada da ta jiyo muryar khairiyya tun shigowarta amma taji shiru bata shigo ba,a ranta take fad'in'To Khairiyya da bata shiri da Maman Abba me ya tsaida ta a gunta'
Bata gama zancen zucin ba taji sallamarta ta shigo,da fara'a ta tare ta amma sai ta ga khairiyan ta turo baki gaba,alamar ranta a b'ace yake,dubanta tai tana fad'in "A'a ke kuma ke da wa naga kina kunkuni."

Wulla jakarta tai kan kujera gami da zama tana yatsina fuska tace "Kai Aunty Su'ada Wallahi matar nan ba ta da nutsuwa,fisabililla kallin abunda tai min." Ta k'arasa maganar tana nunawa mata gefe gefen rigar Nusrat.cikin rashin fahimta Su'ada tace "Meya faru ne ban gane ba,ke da waye?"

K'ara yatsina fuska tai cikin b'acin rai tace "Wannan Maman Abban mana,dubi yanda ta d'aukar min yarinya hannunta duk bak'i da maik'o, sabida k'azanta,in tasan hannunta bai da kyau ai sai ta hak'ura da d'aukan ta ba dole a Kai mata ba."

Dariya Su'ada tai tana rik'e baki tace"Kai!lalle ma,to don ta miki kara ta d'auke ta sai ya zama abun haushi. "

"To ni nace ta d'auke ta ne,jifa yanda ta b'ata mata riga,mutttttssss."
Ta k'arasa maganar d'auke da tsakin takaici.
Ita dai Su'ada dariya abun ya bata sosai,ko dake daman tasan Khairiyya sam ba hak'uri gareta ba,amma anan kam bata ga abun mita ba,kuma tasan sarai da Sakeena bata d'auki yarinyar ba hakan ma sai tai k'orafi tace ko kula Y'ar ba tai ba.
Chapter 27 · 0% Book details