← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 17

Sashe 8

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau da misalin karfe 3 na asbar ranar juma a, zarah ta tashi da nakuda ,duk da cewar ba son Zara nake ba Amma hankalina ya tashi sosai Dan Haka nashiga zarya afalo, in zo in koma Haka na dingayi duk na hada gumi, sabida rashin hankali,ammi ce ta fito daga dakin da zarah take dauke da jariri a cikin zani, cikin farinciki n'a isa gurin ina murna nace "Ammi ya jikin nata dagaske zarah ta haihu?" "Da sauki Abeeddeen zarah ta haihu lafiya Kuma tasamu yarinya mace ,gatanan Mai Kama da ita sak" take nazube a kasa nayi sujjada tsabar farinciki da jindadi nake godewa Allah da kyautar da ya bani, dai dai lokacin da Abban mu ya sakko daga sama Yana farinciki, ya amshi yarinyar Yana 'yar dariya budar bakin abbanmu yace "amaryata kenan daga kallon yarinyar Nan har naji Ina masifar sonta Zan so ace ta zauna a hannuna, " Ammi ce tai murmushi Tace "uhm Wai Adeena ai daga ganin yarinyar akwai Shiga rai" "au Har an saka mata suna" "uhm wallahi tana zuwa duniya Zara,u ta tambayeni Mai ta Haifa ,sai nace Mata mace shine Tace alhamdulillah tanason Asawa yarinyar Adeena Dan tun ba yanzuba tana masifar son sunan" murmushi Abba yayi yace "shikkenan ai duk abin da takeso shinake so... Abbanmu Bai Gama rufe bakinsa ba bala'i da masifa ya turo Kai,sallama mukaji kamar daga sama daidai lokacin da wani tsoho ya shigo tare da wata Mata a bayansa , abbanmu nagani ya dafa kirji ganin wanan matar Haka ma Ammi bakinta n'a rawa Tace" momy! Idonane yakai kan fuskar wadda Aka Kira da momy nan take na Soma tunanin ainda na santa, sai kuwa naji ammi Tace "Abeed ga momyn ka ,Kai alhamdulillah Ashe dama' Zan sake ganin ki zaliha?" Wadda aka Kira da momy ce ta karaso gaban Ammi tana murmushi Tace "nayi kewarku yanzu Abeed dinane ya girma haka?" "Uhm shine gashi har da yara biyu yanzu matarsa ta haihu Kinga jaririyar ma" ammi ta fad'a Hadi da Mika Mata jaririyar, abin da momy ta ganine yasa zuciyarta tayi wani irin bugu ,ganin kamannin yarinyar ta sak a fuskar jaririyar addu a ta Soma Yi a zuciyar ta tana rokon Allah kaddai abin da take tunani hakane" Bata Gama tunanin ba taji wanan tsohon da suka shigo tare wan da ya kasance shine Shugaban gidan marayu ada, yace "malama zaliha wanan shine alhaji Ak FADAMA lokacin da Ina aiki a gidan marayu shine yazo neman yarinya mace ,kasancewar Bai taba haihuwar yarinyar mace ba sai maza ,shine na Dan kamasa zara,u a hannunsa, Ni zanzu Zan koma tun da na rakoki" zaro Ido momy tayi Tace "abbansu Ina zarau take?" Bakin Abba na rawa yace "Kar dai kicemin zarau 'yarki ce?" "Ban gane ba Zara,u 'yatace ta cikina Kuma bakowa bane mahaifiyata face Kai, Zara,u kanwar abeed ce uwa daya uba daya ,dan Allah ku fadamin kardai kuce itace matar Abeed " "innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! Abbanmu ya furta tare da dafe kirji ya sulale a gurin ,Haka itama momy faduwa tayi a gurin sumammiya ,itakuwa ammi jirine ya Soma dibanta Dan Haka tasamu gefan kujera ta zauna jikinta na rawa kamar mazari hawaye sun kasa zuba a idonta sai dai kukan zuci.

Nikuwa Ina tsaye kafata ta kasa daukar gangar jikina Sabi da tashin hankali,a daidai lokacin cin da nake kallon mahaifiyata a kasa da mahaifina Babu ko numfashi a jikinsa, sai dai Kash nakasa tabuka komai a Kai, domin Nima idan ban da innalillahi wa'inna ilaihirraju un BABU abin da nake furtawa, Gaba kidaya zuciyata ta daskare hawayen idona sun kasa zuba sai dai kukan zuci, ba Zan iya musaltamuku yadda nakeji a wannan lokacin ba Amma Ni dai nass Allah shine yabarwa kansa sani, da ace bani da tsawan kwana a wannan lokacin tuni na Dade da mutuwa Sabi da tashin hankali, saikuma wata dangana Mai karfi tazomin lokaci daya na kasa aikata abin da nake sakawa a zuciyata ,ma ana na kashe kaina kawai na huta, ammi Bata Ankara ba taga na Fado a kasan tayil din sai jikukai timmm , lokaci daya kaina ya fashe, ammi ta sake gigicewa ,zarah dake cikin daki kuwa ihun ammi ta jiyo ta fito da gudu, abin da taganine ya razanata ,yadda motar asbiti takawo wa gidanmu dauki ,anata zubamu a mota, itama zarah Shiga motar tayi cike da tashin hankali da damuwa, Haka itama ammi tama manta da Adeena dake kwance a kan kujera Sabi da tashin hankali.

Abjeed da yazeed kuwa bayan tafiyar my asbiti ne suka shigo gidan nan d'anan suka Shiga Kiran mutanen gidan amma shiru hakama dubawa Babu inda Basu dubaba Amma Babu kowa, Abjeed ne yaji ihun jaririya saï lokacin ya Ankara da Adeena wadda take kwance a kan kujera tanata tsala ihu baiwar Allah kenan, cike da mamaki Abjeed ya kalli yazeed yace "Yaya kaga wannan Kuma daga Ina?" Basu Gama karasa maganar ba sai ga Kiran ammi ya shigo wayar yazeed da sauri ya daga ya Kara a kunnen sa yace "ASSALAMUALAIKUM" yanayin muryarta dayajine ya hanasa karasa fad'ar abin da zaice yayi shiru , Ammi ce Tace "yazeed Maza ka koma gida yanzu ka dakkomin yarinya a kan kujera n'a barta kayi sauri dan Allah mun nan asbitin doctor imam" "asbiti Kuma ammi? Mai kukaje Yi?" "Uhm nidai kawai Haka nace maka kayi sauri Dan Allah idan kazo zakaji komai" daga Haka Bata sake cewa komai ba ta k'atse wayar, yazeed ne ya kalli Abjeed yace "Maza ka dakkomin yarinyar nan yanzu muje asbiti " "asbiti kuma yaya waini ban gane ba maiyake faruwa ne da fari mun dawo bamu ga kowaba sannan kuma munga yarinya ita kadai tana kuka a falo, yanzu Kuma Kai kace asbiti Anya lafiya kuwa ?" ",Nima dai ban saniba ya isheni Haka tambayoyin Nan naka nikaina amsa nake bukata muje asbitin maji koma Maine, daga Haka suka fita Adeena na hannun Abjeed ,mota kawai suka shiga Mai gadi ya bude musu gate suka fita daga gidan, Kai tsaye asbitin doctor imam suka nufa.

Tun da su Yaya yazeed suka iho asbitin suke fuskantar tashin hankali da masifu iri da ban da ban, har zuwa lokacin da dukkan mu muka farfado, har ga Allah banso na tashi ba Dan Ni nagama saddakar wa mutuwa zanyi, ashe da sauran kwanan agaba, ubangiji yaruga da ya tsara dole sai na rayu na tadda wannan masifar, lokacin da na Soma bude Ido addu a na runkayi Allah yasa mafarki nake wannan abin ba gaskiya bane, domin ko a tarihi ban taba Jin irin wannan kazantar ba,ko a film da suke makaryata ban taba ganin ance ya da kanwa sun auri junansu ba, sai akan mu Dani da kanwata, inama ace baya zata dawo yanzu, inama Ace Allah ya dauki rayuwata kafin Naga wannan kaddarar ,inama ace kunci zai yaye daga bakin ciki zuwa farinciki, inama ace ba a familyn ak fadama da zo ba ,da irin wannan tashin hankalin gwara ace an haifeni a gidan talakawa na wuni a titi ina bara neman abin cin da zanci, wannan masifar dame tai Kama ga dukiya iya dukiya abbanmu ya taramana sai dai farinciki yayi Mana Katanga a gidanmu amemakon kudi su yaye damuwa ,saï yakasance kudi ba komai bane face masifa, har gwara a halicceni a talaka nasamu farinciki da kekkewar rayuwa, da a halicceni a gidan masu kudi Babu kwanciyar hankali, yanzu Mai yayi saura a duniyar Nan ,nasan nidai tawa ta kare domin bana da bakin magana, bani da abin da Zan iya cewa su Fu ad idan sun girma, lokaci daya Abeed ya daga hannunsa sama yace "ya ubangiji ,ya Wanda yafi kowa sanin duniya da abin da yake cikinta ,ya zaljalalu Wal,ikram ,ya ahadussamad , ya ubangijin halittafir farko Mai rayawa da kashewa, Ina rokon ka da hannayena tsarkaka, da zuciyar da takasance mai rauni ,allah Kana ganina allah karka doramin abin da bazan iya ba, ya Allah kada ka doramin abin da zuciyata zata kasa dauka, ina rokonka da duk zuciyata ,allah kasa lokacin da fu ad da Adeena zasu girma su mallaki hankalin kansu bana Raye, Allah kasa kafin lokacin nadade a karkashin kasa" Abeeddeen ya karasa addu,ar Yana fashewa da wani sabon kukan lokacin da Abjeed ya shigo d'akin dauke da Adeena a hannunsa, karbar yarinyar Abeed yayi ya kare Mata kallo ,sai Kuma ya saki murmushin takaici yace "allah sarki kekuma Haka Taki kaddarar tazo ya da kanwa sune iyayen ki , innalillahi wa'inna ilaihirraju un wallahi ko dadin fad'a Babu" Abjeed ne ya zaro Ido gami da zama a gefan gadon cie da rashin fahimtar mai yayan nasa yake nufi yace

"Yaya Abeed ban fahimci Mai kake nufi da Yaya da kanwa ba, Mai kake nufi Yaya?"

"Uhm Abjeed"

"Yaya Abeed"

Lumshe Ido nayi na bude Hadi da ware su Gaba daya Akan Abjeed dake zaune nace "shin idan na ce maka zarah kanwa Tace uwa daya uba daya zaka yarda?"

Wani wawan furgita Abjeed yayi yafada baya Nan take kansa ya bugu a bango, zuciyarsa cike da fargaba yace "what? No wallahi karya ake koma wane yafada ,haba Yaya meyasa zaka yarda karyane wallahi Wai maiyasa abbanmu bazai barka Haka bane ko so yake bakinciki ya kasheka eh, kawai Sabi da a rashin sani ansamu cikin Fu ad shine daga wannan sai ace wannan, mu shikkenan baza abar family dinmu ya huta ba ,why akan me?

"Uhm Abjeed kenan yau Abban da kake tunanin shi yafada ba shine ba, mahaifiyata da kanta itace wadda ta Fadi haka"

"Mai mahaifiyar ka fa wai wai momy kake nufi yaushe Har momyn tazo ?

"Abjeed yanzu Haka momy tana asbitin Nan Rai a hannun Allah ,zuciyarta takasa daukar wannan abin ,Ni kaina Banda na dogara da Allah Kuma nasaba Shiga irin wannan yanayin inaga da sai an daibi gawawwaki a gidan mu, wallahi Abjeed Ina Mai danasanin ganin wannan bakar ranar ,da ace nasan Haka zata faru tuni na manta da kashe kaina tunkafin nasan wannan labarin, amma yanzu gashi nasan wannan abin kadai bazai barni nasamu Salama ba, shin Abjeed anan wane Mai laifi abbanmu ne ko momy ko Kuma Ni ko zarah?"
Chapter 8 · 0% Book details