← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 17

Sashe 11

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tun da mujahid ya fita yabar gidan su Bai Kara tsayawa inda oga atiku zai Ganda ba ,Dan yariga da ya tsorata da lamarin oga ,tabbas yasan idan ya kamasa ba karamin illa zai Masa ba, gashi yanzu baisan inda zai nufaba, Bai San ta Ina zai Soma neman Zaid ba ,"innalillahi wa'inna ilaihirraju un" ya furta cike da damuwa ya dafe cikinsa Sabi da tsananin yunwa da yakeji ga kudaden jikinsa sun kare ,balle Har yasamu yaci abin ci, yau sama da kwana uku kenan Yana fama gudu sabi da oga amma yarasa mafaka yarasa inda zaije ya buya, ga yunwa tana kokarin kasheshi, duk fari da haske irin na mujahid sai da ya Soma dishashewa Sabi da wahala, ganin yunwa tana son ta illatashi yasa ya Mike daker Yana dafa bango ya nufi gurin wata Mai abinci, Tun kan ya karasa ta Soma wurga Masa harara Tace "dakata anan karma ka karaso aikin banza, Kai kullum saï an baka na sada ka baka da kudin da zakasaya ,Ni naji katon banza da son banza ,kwai Kato da Kai baza ka fita ka nemo kudi ka saya ba saï dai nayi ta ciyar dakai,to walalhi ko ka karaso bazan baka ba" mai abin cin ta fada tana hararar mujahid, shikuwa mujahid duk da Haka Bai fasa karasawa gurin ba Sabi da ciki ba wasaba bashi da zabi da ya wuce ya karasa gurin Mai abincin ya roketa ko lauma biyu ne tabashi yaci, yana karasawa jiri ya daibeshi ya Fadi ,da sauri wani kekkewan sauriyi dayake jingine a jikin motarsa ya tawo gurin, kafin yazo mutane sun kewayesa suna wa mujahid sannu, Yana zuwa ya durkusa Hadi da d'ago kan mujahid yace "sannu bawan allah ,mai ta sameka Haka? Daker mujahid ya iya bude Baki yamasa magana yace "yunwa nake ji ka taimakeni dan Allah" cike da tausayinsa Abjeed ya kalli Mai abin cin yace ,baiwar Allah bashi abinci yaci yadda yakeso ki fadamin ko nawane Zan biyaki" sanan ya dawo da kallonsa Kan mujahid yace "idan ka gama cin abincin kasame ni a mota" daga Haka Bai Kara cewa komai ba ya koma cikin mota ta zauna.

Mai abinci kuwa ganin mai kudine Abjeed gashi Har da mota, tasan komawa Tace zai biyata, Dan Haka ta Debi abinci da yawa ta zubawa mujahid sanan ta hadamasa da kaza da lemo da ruwa, sai da taci yakoshi ya Soma dawowa hayyacinsa sanan Mai abincin ta ce " alhaji ya isheka ko adadomaka idan fa baka ko shiba ka fadamin " "uhm keyanzu baky Abu dan Allah saidan kudi, harda wani kirana da alhaji sabi da munafurci, da Ina kwance Zan mutu Sabi da yunwa kin kasa taimaka min sai yanzu da Allah ya kawo Mai taimako na, bazan Miki Baki ba Amma dai ki kiyaye ko Dan watarana kema wataran Zaki iya tsintar kanki a irin halin da na tsinci nawa yanzu" daga Haka mujahid Bai Kara cemata komai ba ya Mike ya nufi bakin motar Abjeed, kwankwasawa yayi Abjeed ya bude Masa, yashiga ,bayan mujahid ya zauna, godiya ya somayi sa Abjeed sosai sanan yace "bawan allah daga ina kake? Naga kamar kana cikin mawuyacin Hali Ina iyayen ka suke?" Murmushin karfin hali mujahid yayi yace "uhm ninan da kaganni bani da kowa sai Allah ,hatta iyayena bansan inda sukeba ,dafarko Ni almajiri ne Aka kawoni karatu, uwar dakina ta rikeni wanan shine kadai abin da na sani game Dani" "to Amma Mai ya sa naganka a cikin wanan halin ina ita uwar dakin naka?' uhm mujahid yayi murmushi ya bashi labari tun daga farkon abinda ya hadashi da zaidu har zuwa lokacin da oga atiku ya hallakar da rayuwarsa, shima yanzu suke farautar ransa, bakaramin tausaya Masa Abjeed yayi ba , kawai yanayin labarin sa da yaji ta tabbatar da mujahid mutumin kirkine kuma Yana da halaye masu kyau dan Haka Abjeed ya ce "kanason zama tare dani? Zaka bini gidanmu?"

"Uhm wanene bazai so zama tare da mutumin kirki kamar ka ba,idan hakan zata samu zanso n'a zauna da kai" murmushi Abjeed yayi yace "uhm shikkenan Bari n'a Bata kudin abincin nata saï mutafi, naji dadin hakan sosai allah yasa zamanmu tare da Kai yazamar mana alkairi agaremu baki daya" ameen thumma Ameen"mujahid ya fada.

💔 _____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 26*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK TWO✌️*

*Chapter 26*

*Faransa*

Asbitin doctor imam abbanmu ya huce da su Fu,ad tun kafin su karasa jikin Fu ad ya shuka komai nasa yayi sanyi ,motsin da yake da yanzu yadaina Yi ,hatta numfashin da yadaina fita, zuciyar sa kuwa bugawar da Abeed yake ganin tanayi yake Saran zai tashi yanzu yaga tadaina bugawa, Nan take hawayen Abeed ya kasa tsaiwa zuciyarsa da gangar jikinsa suka kasa daukansa, komai nasa rawa yake kamar mazari ,har Abba yayi parking a parking space na asbitin.

Tun kafin su karaso Abba yayi waya da doctor imam ,Dan Haka suna Kara sowa ,da sauri likitocin suka fito, cikin hanzari suka bude motar tare da daukar Fu ad,suka dorashi a gadon majinya ta, Kai tsaye cikin asbitin suka shiga, dashi, kowanne acikin su sai gumi yake, gani suke kamar fa Fu ad ya mutu gawa kawai aka kawo musu, Amma tun da ance a dubashi Babu musu suka shiga dashi cikin d'akin, Abeed kuwa sai bin su yake abaya hankali a tashe , saï leka fu ad yake tacikin window ndakin Yana kuka, Yana addu,a ,to batare da wani Bata lokacin ba likitocin suka rufu a kan fuad dai dai lokacin da doctor imam ya karaso cikin asbitin, tafiya yake cikin Isa da kasaita kamar wan da ba Mara lafiya aka kawo Masa ba, sai wani kekkewan saurayi dayake biye dashi a baya shima sak irin doctor ,Dan Babu abin da ya rasa nadaga halittar doctor imam ,sai dai haske kawai da ya fishi , kekkewan saurayin da akalla bazai wuce shekara 18 a duniya ba. Doctor ne ya juyo ya kalli Dan nasa yace "Amaar ka jirani anan yanzu Zan fito kaji" gyd'a Masa Kai kawai yayi batare da yace Komai ba yasamu guri ya tsaya kusa da Abeed, kurawa Abeed Ido yayi Yana kallon yadda babban mutum kamar mahaifin sai sharbar kuka yake, ganin Haka yasa amaar zuciyarsa ta karye, Allah ya saka Masa tausayin Abeed a ransa, jiki a sanyaye ya tako inda Abeed yake ya dafashi, yace "uncle" d'ago Ido Abeed yayi Yana kallonsa cike da mamaki, da kamar yayi magana sai Kuma zuciyarsa ta Kara karyewa ganin yadda ake dannawa Fu ad kirji Yana numfashi daker" kafafunsa ne suka kasa daukar sa dan Haka ya tafi zai Fadi, amaar ya rukosa Hadi da cewa "haba uncle maiyasa bazaka yarda da Allah shine Mai bayarwa ba Kuma shine Mai dauke abinsa aduk lokacin da yaso, wanan kukan da kakeyi bazai Kara masa komai ba ,da addu a kazauna kana Masa itace wadda zata ceceshi ,kada ka zama rago mana kadinga kwarara zuciyarka, asanina Uncle Kai likitane ,duk wani likita ba a sanshi da rauni ba, ansanku da dauriya to maiyasa wanan ma bazaka daure ba" amaar ya karasa maganar Yana kallon Abeed cike da tausayin sa, "amaar bazaka gane kamai ba, Kai yarone karami, ka kwatanta irin son da mahaifinka yake maka ,sanan ka kwatanta idan Kaine a kwance a irin halinda fu ad ya ke ciki kaine ya mahaifin ka zai ji?" Shiru amaar yayi bai ce komai ba, saï Abeed ya cigaba da cewa "to kamar hakane Nima Ina son Fu ad Ina tunanin ma fiye da yadda doctor yake sonka ,Haka nakeson yaronan ,bana son na rasa shi " ya durkushe a kasa ya fashe da kuka kamar karamin yaro, Abba dake zaune a gefe kuwa zuciyarsa ta ruga ta karye, yasan ayanzu bashi da kalmomin da zai iya fadawa Abeed, sai dai kawai ya kalleshi, Amma shima yanajin ciwan ganin dansa a wanan yanayin.
Chapter 11 · 0% Book details