← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 17

Sashe 16

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"To ko Zaki Kira wayar Abban namu kiji" "tab zancen yaushe tun dazu nake Kiran wayarsa a kashe, Ni wallahi hankalina duk ya tashi munira ko Ina tatafi ga wanan yarinyar datake shimfide a dakina ban ganta ba" "uhm umma ko sai guduwa munira tayi da Amnaa wallahi nasan kadan daga cikin aikin munira ne ta gudu" "ta gudu kuma? Tom taje ina idan ta gudu? Kwata kwata nawa munira take yaushe har tayi wayon da zata iya guduwa ta bar gida Kai Anya kuwa" "to umma idan ba Haka bane Mai kike tunani nidai agidanan Banga munira ba to kodai da Abban suka gudu?"

"Abban ku Kuma a,a Amma dai jeki dakinsa kasan drowa kiga akwai wata leda Dana bashi ajiya, inhar Baki ganta ba to wallahi guduwa sukayi Sabi da baisan abin da yake ciki ba ,sai dai daga baya ya duba" "uhm umma kika sani ko munafukar yarinyar Nan ta fadamasa komai ,ai walalhi tsab zata iya, ai Bata da hankali ko kadan " "tab lallai kuwa idan munira tamin Haka Bata kyau taba mun shiga uku! Munyi biyu Babu nasan walalhi sai ta fadamasa fateema ce ta bani akwatinan na bawa su zaid ,nasan duk wani kulli danayi sai ta tonamin asiri".

Acan airport kuwa bayan su munira sun sauka ,dai dai lokacin Amnaa ta tashi daga bacci, har ta keba Baki zatai kuka sai Kuma taga malan, Nan take ta saka dariya ,cikin gwarancin ta na kananan yara wadan da Basu iya magana ba Tace "abba" shima abba dariya yayi ya Mika mata hannu ya dauketa kana suka damu guri suka zauna , BAYAN sun huta sunci sun Sha, sanan suka shiga girgin ,Allah ya taimakesu daidai lokacin jirgin zai tashi zuwa America.

A kujerar baya suka samu suka zauna ita kuwa amnaa saï faman muzurai take tana kallon ko Ina ,malan kuwa ya kura Mata Ido sosai ganin yadda kamannin yarinyar da mahaifiyata suke Kara bayya na, sak copy din fateema ce amnaa, wasu sirarran hawayene suka Soma sauka daga idonsa ,da sauri ya Kau da Kai Hadi da goge hawayen yace "Allah ya jikan ki fateema Allah ya gafar ta Miki daga Haka yayi shiru ya jingina da BAYAN kujerar ya fad'a wani sabon tunanin.

*Faransa*

"Fu ad ka kwantar da hankalin ka ayanzu Tun da dashen order za mu Masa basai mun fita Dashi kasar waje ba ,nan ma zamu iyayi masa ,kazo zamushiga dakin nan dactor ojor zai yi aiki ,nayarda da aikinsa hatta kasashen waje sunaji da shi insha Allahu Kuma zai Mana aiki cikin nasara, Maza ka dauki rigarnan ka saka kaji" geda Kai kawai fu ad yayi ya dau green d'in rigar doguwa iya gywa yasaka ,bayan ya saka ne ya kwanta a saman gadon, Dan madaidai ci, shima doctor imam Haka yayi sannan shima ya kwanta, wata allura doctor ojor yayi musu wadda tasa suka daina motsi inda kasan basa duniyar, Sawa yayi Aka shigo masa da Abeed dakin, nan take kuwa aka shigo dashi a kwance shima baya KO motsi, da ikon allah doctor ya Soma aikin cikin nutsuwa har yayi nisa akai.

Su Abba kuwa dashi da amaar suna tsaye suna faman addu ar allah yasa ayi aikin lafiya, shiru shiru sukaji ba afito dasuba Nan take hankalin su ya Soma tashi Abba ya Soma tunanin kodai anyi rashin nasara ne, saï kuma wata zuciyar Tace "kayi wa iyalenka fatan alkairi sanan kasa yakinnin zasu tashi da yardar allah" runtse ido yayi ya bude ya furzar da iska kana ya cigaba da addu,a can Kuma sai yaji wayarsa ta Soma ruri, dakko wa yayi ya duba ammi ce dai daga lokacin da suka zo asbiti zuwa yanzu Ammi tayi masa misscall yakai do dari Amma ko ta kanta Abba baibi ba, yasan da tasan asbitin da suka zo datuni ta zo ,daga wayar yayi domin itama hankalin ta ya kwanta Dan yasan Gaba daya arikice take musamman yadda taga Abeed ya fita da Fu ad jini na zuba,.

Karawa yayi a kunnen sa yace "hel... Ai Bai karasa ba ammi Tace "abbansu lafiya kuwa kafadamin asbitin nazo naji shiru" "ki kwantar da hankalin ki ammi insha Allahu komai yazo karshe " "ban gane komai yazo karshe ba kar kacemin Fu ad ya mutu?" Ammi ta fashe da kuka, "a,a ba Haka nake nufi ba Ina ñufin Fu ad ya samu lafiya mun kusa dawowa gida ki kwantar da hankalin ki" "dagaske ne abin da kake fadamin, to Ina Abeed Yana lafiya ko Danni wallahi haryanzu inajin wani iri kamar wani abu zai faru" "Kai ammi kenan babu abin da zai faru sai alkairi, da izinin Allah" Yana Gama fad'a Mata Haka baijira abin da zata ce ba ya kashe wayar tasa Gaba daya.

Acan bangaren Abjeed kuwa AK FADAMA suka koma dashi da mujahid, bayan ya kaishi bathroom yayi wanka sannan ya bashi doguwar jallabiya yasaka ,sosai ya Dan Yi kyau abin ka da kekkewa sai ken nasa ya Kara fitowa, Daman gashi babaki ba wahalar rayuwace kawai ta dafar dashi, zama yayi a daya daga cikin gujerun falon ya kwantar da kansa cike da farinciki Yana Mai godiya ga Allah, duk da Jin dadin da yayi na samun rayuwa Mai kyau Yana Jin Babu dadi na rashin ganin Zaid a kusa dashi, Allah yagani har zuciyarsa Yana son Zaid kaddarace kawai ta rabashi dashi,Kuma yanan Yana addu a indai da rabon Zaid Yana Raye Allah ya sake hadashi da shi kodan ya tallafawa rayuwarsa, yanan zaune Yana tunanin Abjeed ya fito da kwanan abinci ya ajiye Masa, zama mujahid yayi ya Soma ci, saï dai baici da yawa ba sabi da akoshe yake, BAYAN ya kammala ci ya Sha ruwa ne ,gurin ya dauki shiru nawasu 'yan mintina kamain daga bisani mujahid ya ce "nazata a duniyar nan mutane masu hali irin naku sun kare ,nayi tunanin masu taimako sun Dade da mutuwa tun azamanin annabawa, Ashe akwai ragowar har yanzu ,agaskiya na gode maka sanan nagodewa ubangijinmu da ya hadani da Kai awanan lokacin, Kai na musamman ne wallahi, allah ta baka abin da kakeso duniya da lahira, duk wata fitina Allah ya kadeta sharrin mutum da aljani Allah ya kare, Allah kada ya hadaka da duk wata matsala tarayuwa bama kaiba har danginku" murmushi kawai Abjeed yayi ya ce "uhm mujahid kenan kayimana addu a allah ya warware Mana matsalar da ta addabi family mu hakan zai fi farantamin rai" "to matsala Kuma Daman Kuma masu kudi Kuna da wata matsala ,Amma Kuma naganka kamar baka da wata damuwa ko?" "Hmm nikuwa nake dadamuwa waya fadamaka masu kudi basa da matsala ,kowa dakagani Allah ne ya haliccesa daga masu kudin har talakawa Kuma ubangiji Yana da ikon saka matsala akowanne daga cikinsu, Mai bima matsalata tafi taka mujahid, Ina cikin damuwa da tashin hankali akan ahalinmu nagane kudi baya Sayan farin ciki, kudi bashine rayuwa ba, saï kaga wasu basa da kudin amma suna rayuwar su cikin farinciki da annu shuwa, kalleni fa kamar ban da damuwa, amma taciki n'a ciki ,baka tambayeni Ina iyaye na ba, kasan dai Ni kadai gidannan yamin yawa ,to Sabi da matsala na tattaro kayana na dawo Nan Danna samu sauki da Salama, amma Ina ,Ina zaune a cikin gidannan abubuwan da suka faru abaya saï suna dawomin kamar yanzu abin ya faru ,matsala akwai ta a gidan kowa sai dai tawani tafi tawani Allah ya iyama yakuma sassauta Mana Baki daya, bansani bama yanzu ko Yaya Abeed ya mutu allahu a,alamu" Abjeed ya tsaya da maganarsa Yana share hawaye.

"To innalillahi damab Haka abin yake, ganinka kana kuka Yana tabbatar min da babbar matsalace Dan Allah idan Babu damuwa inason ka sanar min da abin da ya faru a danginku ,duk da cewa Ni yarone Mai kananun shekaru kada kace na rainaka Amma dai Ina son sanin Maine yafaru arayuwarku, Ni kaina Ina cikin damuwa tun Ina shekara 11 aka rabani da kowa nawa dangina iyayena Ina iya tuno kamannin mahaifina a idona ban sani ba dai shi idan yaganni zai iya ganeni ,banajin ajikina iyayena sun mutu sai dai inajin basa kusa da inda nake sun min NISAN da Har aba da ba lallai na iya ganin suba har na mutu" "a,a mujahid bakasan ikon Allah ba sai kaga ka fiddarai kuma allah ya nuna maka su Nan Gaba, kuma maganar mahaifinka ya manta da kamanninka zaiyi wuya, Tun da Kai kakasa manta kamannin abbanka shima bazai manta ba kacigaba da addu,ar allah ya bayyana maka su inhar suna Raye" "uhm shikkenan insha Allahu Zan cigaba da yin addu a kamar yadda nasaba ,yanzu kabani labarin naka" "uhm kamatsu kaji kenan shikkenan Zan baka kabari sai munzo kwanciya Zan baka labarin insha Allahu" "yauwa hakanma yayi Babu damuwa to Amma Ina Ina jin nauyin kiranka da Abjeed idan Babu damuwa Zan iya cewa Yaya?" "Uhm mujahid kenan kakirani da uncle Abjeed ko Uncle kawai kamar yadda 'yayan yayana suke kirana dashi" "tom shikkenan insha Allahu uncle.
Chapter 16 · 0% Book details