← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 17

Sashe 5

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tashin hankali na rarrafa daga bayan kujerar na koma dakina Ina share gumi , can bayan gado na kule Ina rawar d'ari kamar wan da yake Jin sanyi, cikin damuwa da tashin hankali nake ,zaune a gurin na hada Kai da gywa na rasa mai kemin dadi, inan zaune ina fargaba zuciyata cike da danasani fall nake rike da kaina ,Sabi da sarawar da yake , "yasalam muryar Abbanmu na tsinkayo Yana yiwa zarah magana cikin tsawa da karaji abin da ban taba ji yamata ba ,yau shi naji Yana cewa "fateema ki fadamin wayay Miki ciki? Yanzu Zara abin da zakimin kenan wannan itace sakayyar da Zaki min, innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Abbanmu ya dafe kirji Yana kokarin faduwa a gurin da sauri Yaya yazeed ya taro shi a tsorace , bakin kujerar ya kaishi ya zaunar da shi ,ita kuwa ammi hawayen idonta ya kasa daina tsiyaya Sabi da tsananin tashin hankalin da taji ,sake kallon zarah abbanmu yayi yace "fateema inason ki fadamin uban wa yayi Miki ciki? Shiru Sarah tayi Hadi da sunnar da Kai zuciyar ta na zafi da tukuki , still akaro na biyu Abbanmu ya sake cewa "ki fadamin wa yayi Miki ciki ,Zaki fadamin ko sai na yayyankaki a gidan Nan" abbanmu Bai Gama rufe Baki ba Yaya yazeed ya Dora da tsinkawa zarah Mari hadi da cewa "Zaki fadi Wan da yayi Miki cikine ko saina ci ubanki a gidannan,uhm abbanmu ka gani ko kaga abin da nake fada maka tsiyar kawo bare a gida kenan ,yanzu gashinan taje ta janyo mana masifa ta Bata sunan familyn mu gaba daya ,idan Aka bibiya itama shegiyar ce daga ganin idanun ki" wannan maganar ba karamin zafi tayiwa zarah ba ,tabbas tanason Abeed sannan tanason rayuwa da shi Kuma tana son abbansu Amma hakan bazai Hana tayiwa my boss rashin mutunci Akan cin zarafin da take Mata, budar bakin ta ta kalli Abba Tace "abbanmu kayi hakuri indai wannan cikinne ba kowane yayi min shiba sai Yaya yazeed Kuma wallahi Abbanmu ba karya nayi maka ba" salati my boss ya ja yayi baya hadi da zaro Ido waje bakin sa n'a rawa yace "zarah u nine ma zakiyiwa sharri? Bai Gama rufe bakin Saba yaji Abeed na cewa "abbanmu kada ka dauki maganar ta nasan tayine domin ta yiwa yaya yazeed sharrine domin ta kareni amma maganar ciki nine wan da nayi Mata shi, Dan Allah abbanmu ka yi hakuri kada kayimin mummunaar fahimta wallahi kaddara Tace tazo a Haka Ni kaina ban taba tunanin Haka zata iya faruwa da niba ,Kuma abbanmu kasan halina niba mazinaci bane ,kayar da Dani Dan Allah abbanmu" sauri daga min hannu abbanmu yayi zuciyar sa a sama yace"kull karka saké kirana da abbanku dannu ban haifi mazinaci ba , shashasha kawai Mara tarbiyya a Haka Ina ganinka kamar mai hankali Ashe ba Haka bane jibi Kai yanzu bakaji kunyar hada ido dani ba , wallahi Abeed ban taba jin danasanin haihuwar ka ba saï yau, kuma Bari kaji wallahi wallahi Babu wan da zai zubar da cikinnan sai ta haifeshi Kuma Kaine wan da zaka aureta Amma kusani daga Kai har ita Babu Ni Babu ku"

Arazane zarah ta zube a gaban abbanmu ta fashe da kuka Tace " wallahi Allah abbanmu Yaya Abeed bashi da laifi nice wadda nake da laifi tun da Ni nashiga rayuwarsa, Walla Abba Yaya bashi ne wan da ya tilastani Akan hakaba , soyayyar da nake Masa itace taja Haka kuma Ni atunanina nazata hakan zaisa na mallakeshi ta sauki Ashe ba Haka bane, abbanmu na rokeka kada kace zakayi fishi da shi bashi da laifi kokad'an ,Ni dai da zakayi fishi Dani kayi Amma ban da shi kada ka manta shine Dan da kafi so da kauna acikin yayan ka to meyasa Dan kaddara ta sameshi zaka juya Masa baya, tabbas abbanmu nayar da soyayyar yaya Abeed jarafta ce daga ubangiji n'a kuma nayar da da kaddara kamar yadda kace bazan zubar da cikin ba ,Zan zauna da shi in haifeshi domin yasan irin wahalar da nasha kafin na sameshi ,idan har abin da Zan Haifa yazo duniya lafiya ya rayu inason abbanmu ka kula dashi ka soshi tamkar dan daka Haïfa ,domin inaji ajikina wani bakwan Al amari zai faru a nan gaba ,kafin yaron ko yarinyar ta girma mebi lokacin bana Raye, abbanmu kayafe Mana Dan Allah kada ka kasa daukan wannan kaddarar " kuka Abjeed dake gefe yake Yana kasa cewa komai duk da shi a lokacin yarone Bai Gama sanin komai narayuwa ba Amma ya fahimci maiyake faruwa a lokacin ,

Yaya kuwa kallo na yayi cike da damuwa yace "ka kyauta " abin da yafada kenan ya huce dakinsa ,ita kuwa ammi jikin tane yayi masifar yin sanyi game da kalamen zarah hakama abbanmu ,kunsan wani abu kuwa a lokacin abbanmu ya yiwa zarah magana sannan ya lallasheta ammani ko kadan ,daga ranar ne abbanmu ya Soma danamin tsana ,kafin abin da yafaru a gaba yafaru .

Jikina Babu kwari na Mike na Shiga dakina na barsu a gurin, bayan n'a Shiga daki zama nayi a bakin bed Dina nayi shiru can Kuma sai na fashe da kuka ,uhm kunsan kukan Mai nake ? Ba kukan komai nake ba sai tausayin abin da zai zo duniya batare da aure ba, hakika bana son n'a auri zarah amma yanzu Babu yadda Zan iya tun da taruga da ta danamin tarkon da bazan taba iya kwacewa ba, kamar yadda abbanmu yayi umarni Dole Haka Zan hakura na aure ,saï dai abin da baku sani ba Tun daga wanan ranar nayi bankwana da farinciki da kwanciyar hankali a gidan mu, Daman abbanmu shine farincikina da shi kadai na Saba sai ammi,tun da dama' can Ni mutum ne ba mai son surutu ba ,a kullum n'a saka kafata falon gidan mu saï n'a dawo da bakincikin abbanmu gaba ki daya ta dauki tsanar duniya ta doramin komai yamin zafi kunci yamin yawa, nashiga cikin masifa da tashin hankali , dépression kuwa ba a magana ,wanan dalilin shine yafara Sana diyyar warga tsa zuciyata har na fara kamuwa da ciwan zuciya tun Ina yaro,

Saka makon halin Dana shiga yasa Abjeed ya ke matukar jin tausayina kaf agidanan a yanzu shi kadai take fahimtata sai ammi Yaya yazeed kuwa Daman ba shiri muke ba ,sai tsanar da yake min ta Kara yawa, kullum idan Abjeed ya dawo daga aiki saiya shigo ya ga halin Dana ke ciki sanan ya Dan rarrasheni, ta fita, soyayyar kanwata kuwa ta da tafara Shiga zuciyata saï naji kamar an kwashemin ita saï n'a koma bama nason ganinta ,komai idan tayimin baya taba burgeni ,nigaba daya natsani duniyar , ba daban Abbanmu ya umarceni Dana aureta ba walalhi da sai dai na barta Dan nasan bazan taba iya faranta Mata ba tsakani na da ita yanzu tsanace Mai karfin gaske Koda ace na aureta zatasha wahaalane a hannauna Dan Ina tuannin duk wan Nan masifar da na Shiga itace sila da ace Bata shigo rayuwata ba nasan har yanzu Ina rayuwa cikin farinciki da annushuwa ,sai gashi komai ta dakele.

Kwance atashi a gurin bawa Babu wuya kamar Wasa zarah ciki yayi girma, Dan bama a barinta ta fita ko Ina ,an rufe sirrin a Ina cikin gidan mu sai Kuma kawarta jalila da tasani ,yauma kamar kullum ta tashi da matsanancin ciwan ciki ,Dan mu munyi tunanin bazata rayuba Sabi da wahalar da Tasha tun dare har wayewar garin ranar, washe haihuwa ce tazo bags tatatn "innalillahi wa'inna ilaihirraju un na furta ! Adi da fad'awa tunanin Wai Ni ne Zan samu da batare da aure ba nashiga uku ni Abeed" n'a fashe da kuka adaki lokacin da naji kukan jaririn ya doki kunnena na runtse ido,hannayena na sa na toshe kunnuwana Dan bana kaunar Jin kukan jaririn, kwatsam ammi ta turo kofa Hadi da matsowa gabana dauke da yaron a cikin tsumma tace "alhamdulillah fateema ta sauka lafiya , ga yaron ka" a gigice n'a d'ago ina cewa yarona kuma Ammi?' "eh yaron ka da wanine yayi maka cikin " sunnar da Kai nayi n'ai shiru" Ammi ce tasake cemin "munason kayiwa yaronan hudu ba ,"nashiga uku Ammi dan Allah kifita da yaronan" nan d'anan numfashina ta Soma sama, da sauri Ammi ta tsorata ta fita da yaron zuwa falo , abbanmu ta kaiwa tare da cewa gashin yace kayi masa huduba" "murmushi abbanmu yayi yakalli yaron cike da so da kauna yace "bawan Allah Kai Kuma Haka kaddarka taxo ,sanan ya ce "wane suna kikaga ya Dace dashi?" "Budar bakin ammi Tace "Ina tunanin kusa Masa Fu ad"

_____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 20*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK TWO✌️*

*Chapter 20*

Mikewa zaune Fu ad yayi ya zaro manyan idanunsa waje tare da sakin littafin a kasa ,yace Fu ad, "Mai suke nufi badai ni Fu ad dinba" ya fad'a jikinsa na Bari kamar mazari....
Chapter 5 · 0% Book details