← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 17

Sashe 14

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Amaar ne ta dawo bakin gadon da fu ad yake ya zauna cike da tausayin su yace "abokina!! Dagowa fu ad yayi idanunsa cike fall da hawaye ya zubawa amaar su , "meyasa bazaka yafewa Abban ka ba, wallahi Fu ad uncle Abeed Yana masifar sonka wallahi Yana kaunarka ,kada kace zaka zuba Ido rayuwarsa ta salwanta, kasan halin da yake ciki kuwa ? Zan iya rantse maka kaf duniyar Nan yafi kowa sonka ,Fu ad shifa ubane a gareka kowane irin laifi yayi maka baikamata ace kayi Masa hakaba ,yakamata kazama Mai yafiya ga mahaifinka, ayanzu uncle abin tausayi ne, mutuwar sa takusa fu ad abbanka kwanan sa yazo karshe, wallahi summa tallahi muddu uncle ya mutu baka je ka sasanta da mahaifinka ba saï ka hadu da fishin ubangiji, ayanzu ma banjin Uncle Abeed zai tashi ba, Dan dazu abbanmu ya tabbatar min da cewa saura kiriss Abu kadan zai iya sa zuciyarsa ta buga, kuma kaga Haka tafaru agabanka ya dafe zuciya ya fad'a kasa ko motsi bayayi, wallahi mutuwar Yaya Abeed ayanzu tarataya ne a wuyanka da Kai da abbanmu, allah sarki bawan allah Tun daga lokacin da yake saurayi yayi bawankwana da farinciki ,harna manta lokacin da Naga uncle yayi dariya ,kullum cikin damuwa yake ,wataran idan Ina tuna yadda yake mun dariya da murmushi da fararan hakoransa masu kyau sai naji dama' da ta dawo ,Amma yanzu duk kun dushashe komai ,idan kun kasheshi kun huta kaddarace Kuma Babu wan da ya Isa ya canza ta, Haka zalika kaima bazaka taba canza sunan ka daga shege ka koma dan sunna ba, ku kasheshi kunji" amaar ya fad'a zuciyarsa na tukuki cikin masifa ya Mike ya fita, shikuwa Fu ad jiyayi kamar an watsamasa gawrashi a zuciyarsa ,kansa na Masa nauyi kamar wan da dutse Mai nauyi ya Fado kansa, Nan take yarasa inda zai saka kansa yaji dadi komai na duniya ya tsaneshi baya son jin komai, ayanzu jiyake zuciyarsa tayi rauni ,bayason ya rasa mahaifinsa, yanzu kenan yazaiyi , ya tabbatar da maganar da amaar yake fad'a Masa gaskiya ce ubangiji zai iya kamashi Akan Haka, kuma shima shiada ne, Tun da yataso ahaka yasan yaya Abeed badan karyayi karya ba da saï yace Tun da yake Bai taba ganin dariyar sa ba, amma yanzu lokaci yayi da yakamata ya nunawa mahaifinsa kulawar da yarasa abaya, ya tallafeshi su rungumi kaddara su maida komai ba komai ba, Yana tsaka da tuannin da yake yaga doctor imam yashigo, bakinsa na rawa yace "doctor ya jikin abbana?" Kallon sa imam yayi cike da mamaki Wai yau shi yakira Abeed da abbansa, cike da damuwa yace "abbanka yanacan mungaza ,munrasa yadda zamuyi ba irin kokarin da bamuyi akai ba Amma munkasa ceton rayuwar mahaifinka, uhm Allah sarki bawan Allah Yana kaunarku sosai, ana neman jinin da za a samaka ,kasan Mai yace ? Adebi nasa Gaba daya idan zai maka asa Kama shi ya mutu Kai Kuma karayu uhm uba nagari kenan gashi munaji muna gani zamuyi asarar irinsu a family dinmu" kuka Fu ad ya fashe dashi lokaci guda ya funcike jinin da ake Kara Masa tare da Dora hannu aka yace "Innalillahi wa'inna ilaihirraju un!! Nashiga uku! Ina abbana yake ? Dan Allah uncle kaceci rayuwar abbana kada kabari narasa shi ,Dan Allah uncle, wallahi Ina son mahaifina Ina kaunarsa fiye da komai aduniya ,Ada zuciyata ce takasa daukan abin da n'a karanta acikin littafinnan amma yanzu n'a gane kuskuren danayi , hakika yaya Abeed ya Dade Yana boyemin kansa a matsayin mahaifina kawai Dan nasamu rayuwa Mai kyau narayu cikin farinkici ki kada na San wannan maganar ,bawan Allah kenan shi kullum Yana zaune cikin depression wallahi ayanzu natsani kaina banason ya mutu, muddum Yaya Abeed ya mutu bazan taba yafewa kaina ba Nima saina kashe kaina, tarihin ya kare daga kanmu saidai komai yazama tarihi" "uhm Fu ad kenan Ina fadamaka uncle ya nacan munkasa cetar rayuwarsa kana gayamin wasu maganganun banza da bazasu amfane mu ba, ada maganganun ka suna da amfani lokacin da yake Raye ,nasan ko Babu komai zasu faranta Masa Rai , Amma ban da yanzu ,maiyasa Haka? Why? Kun kasa daukar kaddarar ku kun cutar da bawan Allah ,shi kansa da ce an bashi zabi Akan kaddarar da Allah ya Dora Masa wallahi nasan bazai zabi wannan kaddarar ba, maiyasa ku mutane bakwa ganewa Kuna komai kanku kuka sani, yanzu gashinan yamutu sai Kuma kuci kanku ,idan kun gadama kuyi Masa addu,a idan Baku ga damaba ku tsine Masa, shidai tashi ta kare.... Bai karasa magana ba yaga shigowar Amaar da gudu har Yana haki ,cikin tashin hankali ya shiga cewa "daddy zoka gani ,kazo kaga Ni" "Mai zangani?" Doctor ya fad'a cikin furgici "uncle Abeed ne...." Ga ba dayansu Har da Fu ad wajen futa daga dakin domin suje suga maiyake faruwa.

*Adamawa*

Umma! Wai da gaske kin fasa zuba wanan maganin? "Uhm kedai Bari sumayya wallahi munira tabani mamaki gani nake kamar dagaske zata iya kasheni idan har na taba lafiyar malan" "hmm umma Wai ita yarinyar Nan Mai ta takane sai me idan kin kashe Abban muma ai Haka muka hakura bawai Dan bama sanshi bane, Allah kada ki biye ta muyi abin da ya kamata kawai, "ah ah sumayya walalhi daga gani yarinyar Nan dagaske take kamar yadda Tace zata min yankan rago tsab zata iya" "to yanzu Mai yakama muyi kenan umma tawace hanya zamubi domin muga komai ya kammala?"

Tsulum sukaga munira a tsaye a gabansu ta ruke kugu tana hararar su , sumayya ce ta had'e rai Tace "kutumar uba ke harni Zaki tsayawa Aka ?,ni sa ar kice"? "Bansani ba nidai nafada muku wallahi idan Har kuka kashe Abba saina kashe umma" "laaaa ha ila ga,illahu yau Naga futsa rarriyar yarinya Ni Zaki na fadawa Haka Ni mahaifiyar ki?" "Harara ta watsawa umma Hadi da cewa "bakija girmanki ba rudin duniya ya sa kin manta da cewar ke uwace,komai n'a duniya ya rufemiki Ido kin kasa tantance fari da Baki,walalhi umma kikiyayi duniya duniya itace wadda zata rudeki kikoma kurma kizama makauniya duk akan kudi, wallahi ubangijin da ya halicci duniya ma Bai bamu damar yin hakaba Kuma baice mu aikata zunubi ba, Kuma karda ki Yi Abu kizo kina kaddarace wallahi wanan ba kaddara bace ganganci ne umma, walalhi ganganci kikeso kiyi, nidai Ina rokonki a matsayinki n'a mahaifiyata ki bi duniya a sannu ,kitina Zaki koma ga allah duk abin da kika aikata akwai ranar sakamako ,hatta AMNAA dakike yiwa mugunta akwai ranar da zatazo baki da bakin kare kanki agaban allah rayuwa ce komai kikagani daga allah ne ita kanta yarinyar da za a Bata zabi bazata so ta zauna da mace irinki ba ,ki gadai ikon allah mahaifiyar ta mai imani mai hankali mai tausayi Amma Kuma ta rayu agurin gurbatacciyar uwa wallahi umma ina danasanin saninki a matsayin mahaifiyata" tana Gama fadar Haka tafice hawaye nabin kuncinta,

Umma dai Baki da hanci suka saka suna kallon ikon ALLAH.

💔 _____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 29*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK TWO✌️*

*Chapter 29*
Chapter 14 · 0% Book details