← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 17

Sashe 13

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Leda daya doctor ya saka Masa sannan ya futa, Kai tsaye gurinsu Abba ya koma, Nan ya samesu a tsaye suna jiran dawowarsa, Abeed ne yace "doctor ya jikin nasa da sauki dai ko?" "Uhm jiki da sauki babu abin da zamuce sai dai muce alhamdulillah, yakamata yanzu kaima muje a sake duba lafiyar ka tun da kaima kaga ba cikakkiyar lafiya ce da Kai ba, Tun da yanzu abin ya Dan Soma lafawa, koya kace ?" "Uhm doctor kenan ai Ni basai an dubani ba ajikina nake kin bazan Kara wasu shekaru a duniya ba zan mutu" "hmm wallahi kabani dariya to ai kowa zai iya mutuwa bama kaiba nikai na jiran tsammani nake, ako da yaushe dama amfison mumini kullum ya kasance cikin tunawa da mutuwa, sai kaga Kai da baka da lafiya baka mutu ba nikuma na mutu, shi Allah Haka yake ,sai ya dauke yaro ya bar tsoho ya dauke 'ya ya bar uwa,Dan Haka duba lafiyarka ta zamar min wajibi tun da Ni likitanka ne" "hakane doctor bakai karya ba, mutuwa tana wuyan kowa rigace duk lokacin da tazo zata dauke ka batare da shiriba ko jinkiri, Amma abin da nakeso na nusashshe da Kai shine, Ni wa Adina yakusa, Sabi da zuciyata saura kiriss a yanzuma idan Aka ce maka n'a fadi n'a mutu kada kayi mamaki, ayanzu bani da wani buruka a duniya da ya wuce guda 4 na farko Ina son kafin na koma ga mahaliccina idona yayi tozali da kanwata Zara,u, na biyu Kuma Ina son abbanmu ya yafemin bana son na mutu Yana fishi dashi ,domin fushin mahaifi ba Wasa bane shi kadai zai iya jefani wuta, na uku Kuma Adeena da Fu ad su ji jaina su daukeni kamar yadda kowanne yaro yake daukar mahaifinsa a zuciya, inason su yafemin su tausaya min sannan su yafewa mahaifiyar su domin muma wannan abin da ya faru ba laifin mu bane ,kaddarace Allah kadai shi yabarwa kansa sani, bamu da tabbacin dalilin da yasa ubangiji yayi hakan ,muma ba yin kanmu bane, buri na na hudu Kuma ,inason kafin na mutu yakasance bani da komai a kaina, inason inje gurin ubangiji batare da wannan zunubin ba, inarokon Allah yayafemin kafin na bar duniya, Kuma insha Allahu zanci Gaba da addu,a Ina neman yafiya a wajen ubangijin mu, nasan allah gafurur Rahim ne ,mai yafe wa bawa duk wani zunubi Mai girma ko kankani aduk lokacin da bawa ya tuba, nima Allah ya sanyani daga cikin bayinsa tsarkaka" daga Haka abeed ya sa hannu ya goge idonsa ,Bai kalli ko da inda Abba yake ba ya juya yanufi d'akin gwaji, jiki a sanyaye doctor imam ya bishi a baya ,dan jikin doctor ba karamin mutuwa yayi da irin wannan kalamen da Abeed yayi ba, shikuwa Abba siririyar kwallar da ta kwaranyo Masa ya goge, zuciyarsa na Masa tukuki da zafi yace "Allah yasani Abeeddeen kaf cikin yarana nafi sonka fiye da sauran, Kuma har yanzu har gobe ina sonka ,nasan soyayyar ka a jinin jikina take d'ana, Babu yadda na iyane dolene sai na nuna maka gyranka bazan taba zuba Ido Ina kallonka kana barna ba, sai gashi saurin yanke wukunci danayi Akan ka yajamin masifa da bala,I nasan da ace nayi jinkiri da Haka Bata faruba, yanzu wagari ya waya na daura aurenka da kanwarka wadda kuka fito ciki daya, innalillahi wa'inna ilaihirraju un" abba yasake fashewa da kuka ya cigaba da magana acikin zuciyarsa.

Tom Bayan doctor imam ya yiwa Abeed gwaji sakamakon ya tabbatar Masa da yanayin da Abeed ke ciki, wannan sakamako ba karamin ta dawa imam hankali yayi ba, dan gaba daya ya gigice zuciyarsa tashiga harbawa yashiga kallon Abeed cike da mamaki idanuwan doctor a waje yace "innalillahi wa'inna ilaihirraju un!! ABEED! Abeed! Wai shin dagaske nake ganin takardar Nan ko mafarki nake, dagaske ne abin da sakama kon nan ya bayar? Dubamin kaima likitane ai duba da kanka ko dai Ido nane" yayi maganar idonsa sun cicciko da kwalla kamar zaiyi kuka,

Hannun Abeed na rawa ya amshi ta kardar ya Soma dubawa, memakon imam yaga Abeed ya tada hankalinsa sai kawai yaganshi Yana murmushi Yana jijjiga Kai, sai dai idanun Abeed na zub da hawaye yace "hmm doctor kenan ,Wai da baka yadda da maganar danake fada maka ba uhm ninasan Haka zata faru " "amma Abeed meyasa Naga ranka Bai baci ba,Kuma hankalin ka a kwance? "Uhm Sabi da mutuwar nakeson nayi tun ba yanzu ba, Ni ayanzu damuwata daya na mutu su abbanmu basu yafemin ba" "Kai ammafa abeed ka barni mamaki Wai shin bakaga kwana nawa ne yarage maka ba?" "Uhm s'aime Dan zam mutu nawane suka mutu akayi hakuri Aka manta dasu ,ki da ace namutu imam duk tsoron mutuwar da kake kaima wataran saika biyoni, zaka mutu kaje inda bakason zuwa, me ake tsoro a mutuwa ne, kwanciyar kabari a karkashin kasa, ko Kuma tashin alkiyama, ko Hawa kan zira,I akomai ka kake tunani hmm duk wadanan abubuwan nafi kaunarku da wannan masifar danake cikin ta a yanzu, Wllahi doctor yanzu idan fu ad ya farka bani da abin da Zan iya ce Masa, wallahi bani da bakin magana" yasake fashewa da kuka abin tausayi, hànnun sa yasa a jikin bango Dan karya fadi, sabi da jiri yake bazai iya tafiya awannan lokacin ba,

"Kayi hakuri komai Mai hucewa ne insha Allahu baza ka mutu ba saï ka samu farinciki kafin ka mutu ,yadda bakinciki zai yaye daga gareka" "ameen thumma Ameen doctor yanzu Ina 'dana ya farka ne ? "Eh to mintinan da muka bashi ya ci ace ya farka ,yanzu kuzo mushiga muga" "okay tom muje Amma ka dan taimaka n'a dafaka karma fadi" abeed ya fad'a Yana goge hawaye a lokacin.

Dafa doctor yayi har suka shiga d'akin suka tarar ma Fu ad ya Soma bude Ido, sai dai har yanzu akwai hawaye masu zafi a gefan idonsa, bayan ya kammala bude idonne ya kalli duk abin da ke cikin dakin, sannan ya karewa su Abeed kallo, tabbas mahaifin nasa ya rame sosai kamar ba Abeed d'in da yasani ba, yayi wani irin baki ga uban kamshin wuya kamar a saka sabulu ya zauna, tabbas tausayin sa ya Soma kamashin Sabi da ya Soma rinjayar tsanar da yayi Masa, ganin zai iya fashewa da kuka yasa ya dauke kansa daga garesu ya juya, bakin Abba na rawa yace

"Fu ad ya jikin naka Naga ka juya ,ki bakason ganin mune? Dan allah kàyi hakuri ka saurareni " "uhm abbanmu kenan baku da abin da zaku iya fadamin ,wallahi ko kadan Baku da bakin magani, Wai shin bakwa Jin kunyar hada ido Dani ,wallahi na tsaneku bana son ganinku, natsani duniyar Nan, meyasa za a ceceni ,akan meyasa Baku barni na mutu ba, kunfiso ku sani agaba Kuna muzguna min ,wallahi banyi dacen iyayeba idan da ace anyi shawara Dani kafin nazo duniya wallahi bazan zabeku a matsayin iyayena ba, mugaye kawai azzalumai, kunbi San duniya da rudinta kawai Dan ku cutar Dani......" Da sauri doctor ya rufe Masa Baki yace, haba Fu ad ya Isa Haka, Anya kana da hankali kuwa iyayanka kake fadawa Haka, ka daina Kar ubangiji yayi fushi da...... Ai kafin ya karasa maganar sukaga Abeed ya yanke jiki yafadi ji kake teemmm ,

💔 _____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 28*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK TWO✌️*

*Chapter 28*

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju un!! Abba ya furta Hadi da yin kan Abeed doctor kuwa kallon yanayin da Abeed ya fadine yasashi shiga shock ya tsorata Bai San sanda ya Dora hannu aka ya yafurta "munshiga uku Abeed!!!........ Shikkenan Fu ad ka kyau ta burinku ya cika kun kasheshi ,waye baya laifi aduniya ,mu kanmu muna wa ubanjinmu laifi Kuma ya yafe Mana, to Mai yasa ku BAZAKU yafe Masa ba, Mai yayi muku kukeson kasheshi , shikkenan Daman yadade Yana cewa wa,adinsa yakusa zuwa ashe da gaske ne ga dansa n'a cikinsa Yana neman kasheshi, abbanmu ka mashi muje" kamashi abba yayi suka fita da Abeed jiki a sankame ko motsi bayayi suka sashi a wani d'akin daban.
Chapter 13 · 0% Book details