← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 17

Sashe 17

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Bayan su malan sun sauka a kasar America sai ya zamana duk kudaden da suka ruko ya kare, sai Abu daya dayayi ragowa shine akwatin gold dinnan, zama suka samu guri sukayi a airport din America ,malan Yana tunanin yadda zasuyi, munira ce taga yananin mahaifin nata , dan Haka Tace "Abba kada ka damuwa dan bamu da kudi allah bazai hanamu gurin da zamu kwanta ba" ana Haka saï ga wani jirgin ya sauka, kurawa jirgin Ido munira tayi har mutanen dake cikin girgin suka fito, abin mamaki wani kekkewan saurayune sai dai ya Dan manyanta ,sai Kuma wasu yara Mata guda biyu masu Kama da mahaifiyar su, sai yaro guda daya namiji daga gani shine babba, Yana biye da mahaifin nasu abaya, wasu masifaffun motocine masu tsada da kyau n'a hango ya nufesu masu take masa baya suna biye dashi, Har ya karasa jikin motar, mikewa munira tayi da sauri ta karasa inda yake Nan take aka dakatar da ita, rokonsu ta farayi su barta tayi magana dashi Amma suka ki, aleem wan da shine babba ,a 'yayan alhaji yazeed ,shine ya fito ya musu magana Akan su barta tayi magana da mahaifin nasa, Babu musu kuwa suka kyleta, tana karasa inda yake ta tsuguna har kasa tashiga gaishesa, cikin fara,a ya amsa Hadi da cewa "lafiya yarinya Naga kin zo gurina?" "Lafiya ba lafiya ba alhji Dan Allah sonake ka taimakeni dani da mahaifina yanzunan muka saika a garinnan bamu da kowa kuma kudinmu ya kare shine nakeso katainake mu ko aikine zanyi muku ,nidai burina ku bamu abinci da gurin kwana" murmushi alhaji yazeed ya saka cike da mamakin yarinya karama Wai tasan ta taimaki mahaifinta, hakan da tayi bakaramin burgeshi tayiba dataje tayi bara tazabi tayi aiki a biyata, "yarinya muna da masu aiki a gidan saidai kamar yadda kikace na tainaka muku Zan Tai makeku nabaku gurin kwana da abinci har zuwa lokacin da zaku koma garinku kinji Maza kije ki kirawa mahaifin naku" murnace lokaci guda ta kafa munira batasan lokacin da ta durkusa tashiga yimasa godiya Har da dafa kafarsa, kana ta juya gurin Abba Wanda tun tashin munira ya saki Baki ya kurawa sarautar Allah Ido Dan yaga Mai zatayi, tana zuwa tace" Abba bana fadamaka na Allah basa karewa ba gashi Har na samamana inda zamu zauna kataso mutafi" "a,a munira bazamu ba kina ganin mutumin Nan yadda yake da kudi kinsan da sake, haka kurum muje Dan yankan Kaine" "haba Abba ka saka allah a ranka kawai insha Allahu yadda kake tunani ba Haka bane" "to shikkenan yarnan muje ko" munira ta dauki amnaa suka karasa gurin alhaji yazeed,

Wani irin bugu alhaji yazeed yaji kirjinsa yayi adi da zare glass din idonsa, ya Kara kurawa amnaa Ido bakinsa nason fadin wani abu Amma ya kasa, lokaci daya zuciyarsa tashiga bugu kwakwalwarsa tasoma tunamasa kamannin ta , "innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! Nashiga uku masifa da bala I, wannan wace ?" a tsorace munira Tace "kanwa tace" "kanawar ki Kuma ? To ki maida ita indai Zan taimake ki sai dai idan Babu wannan yarinyar a hanninki" zaro Ido malan yayi munira Kuma ta cigaba da kallon alhji yazeed cike da mamaki......

Coming soon ✍️

Safhat ce.... Muhadu a Book three

Paid book 700# duk Wanda ya karanta batare da ya biyani hakkina ba Allah ya Isa ban yafe ba.
Chapter 17 · 0% Book details