← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 17

Sashe 7

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga lokacin kuwa bani da kwanciyar hankali farinciki ya bace daga gareni Jin dadi kuwa kamar ba Dan gidan A k FADAMA ba, duk wannan tarun dukiyar da muke da ita Gaba daya bana jin dadi ta, gidan ya komamin makabarta narasa Mai zanyi nasamu Salama a zuciyata, nan take wata da bara ta fadomij, oga atiku, Shugaban masu gudanar da harkalar Kayan maye n'a farin adamawa, Babu shiri nasa daya daga cikin masu gadin gidanmu suka nemomin shi, Nan take muka Saba da oga atiku aduk sati Ina shanye giya tafi guda dari ,kullum cikin bacci da maye nake gaba daya gidanmu suka rasa gane kaina, bakoma mashayin gida da kwayoyi sak, n'a daina wanka n'a daina sallah ,saï dai idan bukata ta zomin Ina jin sha,awa n'a yiwa zarah duka sannan nayi amfani da ita amatsayina na mijinta, komai ya karenin rayuwata ta koma maye sak, duk asanadiyyar kiyayar da abbanmu yakemin ,inason in manta dadamuwa dan tayimin yawa.

Fu ad ne ya tsaya da karanta littafin ya goge kwalla, cike da tausayin Abeed ya kalli Adeena yace "gaskiya abbanmu Bai kyau taba" sannan ya cigaba da karatun littafin.....

To yau kamar kullum Ina zaune a dakina cike da damuwa na tusa kwalbar giya a Gaba saï sha nake, Gaba daya na fita daga hayyacina na koma kamar wani Mara hankali, zarah ce ta shigo d'akin fuskarta dauke da murmushi, Bata karasa takowa in da nake ba zuciyarta tashiga bugu bakinta na rawa idanta duk suka cicciko da kwalla Tace " innalillahi wa'inna ilaihirraju un nashiga uku ! Yanzu yaya Abeed abin da kakeyi kenan, daman Kayan maye kakesha meyasa zakayi Haka eh dan Allah ka Bari, "tayi maganar Yana karasawa in da yaje "haba yaya yanzu Har ka manta da Allah shi yake komai? Ka manta da cewa shi ne ta jarrabemu da kaddara ,wannan abin da kakeyi zunubi kake karawa kanka komai kagani allah ya tsara shi tun kafin a haifi Dan Adam ,to Mai yasa baza kayi imani da shi ba" ta Kai hannu zata Kar'be kwalbar, Abeed ya fincike ,tare da mikewa kamar zaifadi Sabi da maye, da baya da baya zarah ta Soma ja ganin yadda yake nufota Yana lumshe Ido, Bata an karaba taji kwalbar guyar a kanta jikake kwall ,Nan take kan ya fashe jini ya Soma zuba ,ihu zarah ta kwalla ta fadi a gurin,

Duk da wannan abin da Abeed ya aikata Bai hakura ba ya cigaba da cewa "Dan ubanki nizaki rainawa hankali ,kicemin kaddarace shegiya, kizo har gidan ubana ki batamin rayuwa sannan kirinka Kiran tun kafin a haifeni aka rubuta, to ubanki ne da yasa ki yi cikin dani, wallahi saina karkasheki, wawuya kawai Mara hankali, kinzo kin rabani da iyaye.... Kafin abin ya karasa maganar da yake su ammi sun turo kofa da gudu, domin suna falo suka jiyo karar zarah ,cike da rashin hankali Abba yace "innalillahi wa'inna ilaihirraju un Abeed ! Kasheta kayi, abba ya gigice ya kasa tsinana komai tsabar tashin hankali,"shikkenan munshiga uku! Nidai Ina tsammanin banine mahaifin ka ba wallahi zaliha ta cuceni ,data shigomin da cikin wani gidana, dan ni wallahi ban haifi mazinaci Dan iska irinka ba, natsaneka wallahi, allah ya tsi..... Kafin ya karasa ammi tayi saurin rufe Masa Baki tana girgiza Kai ,kukan tane ya Kara karfi tana cewa "haba abbansu Bai kamata ace da girmanka da hankalinka kayi Masa Baki ba, kaduba kagani fa halin da yaronan ya shiga Sabi da Kai ,Kuma batun da Abeed dankane duk da cewa mahaifiyar sa munyi kishi da ita bazan so ka aibatata ba ,ko kayar da ko karka yadda Abeed jininkane ba canji Kuma aka maka a asbiti ba, Kai ka canza shi, Sabi da Kaine baka yafiya ,narasa dalili ko annabi Yana yafe Mana idan mummasa laifi Amma ban da Kai ,ace ka fifita agola Akan dan cikinka, kafin zuwan yarinyar nan Abeed ba Haka yakeba amma yanzu jibi duk sabi da ku, kullalata rayuwarsa l'un Bata komai, wallahi ko Mai Abeed ya aikata kana da kaso acikin zunubansa ,Sabi da Kaine baka jashi ajikiba ,Kai Abeed yake gani ya ji dadi Kaine Wanda kake rayuwa dashi mahaifiyar sa Bata gidannan, kazamar masa gata komai idan yatashi abbansa yake cewa, hatta so yafi sonka fiye da komai ko bacci baya iyayi sai ya ganka, shine Kuma yanzu zaka juya Masa baya kace ya zauna lafiya, bazai taba yuwuwa ba, yakamata kasan laifinka ne ba nashi ba" Ammi ta fada cikin bacin rai da damuwa.

Yazeed ne ya ce "abbanmu ! Ka barni wayarka nakira doctor mansur tun kafin yarinyar Nan ta mutu" mikamasa wayar yayi batare da cewa komai ba ya samu guri jiki a sanyaye ya zauna bakin bed din, shikuwa Abeed jirine ya Soma daukansa take ya Soma ganin dishi dishi Basu Ankara ba sukaji shi akasa ya Fadi sumamme.

Doctor kuwa tun da aka kirashi Bai wani Dade ba ya karaso, yana zuwa yashiga duba zarah ,anci da a Bata mutuba tsorata ce kawai tayi ,,saï kuma jinin da yake zuba ,Babu wani Bata lokaci doctor ya gyra komai itama ta farfado, ananne likitan yake yimusu albishir da tana da shigar ciki har na wata hudu ,nikuwa innan a kwance Rai a hannun Allah ,bayan doctor ya Gama dubata kaina ya dawo ya shiga dubani ,zaro Ido yayi sosai tare da cewa "subahanallahi alhaji garinya akayi Haka ,ya akai wannan yaron duk abubuwan dake cikin sa suka tabu? Gashinan duk sunyi Baki Sabi da Shan Kayan maye ,ayan Zuma illlah suka Soma yimasa shiyasa ya Fadi, idan har Baku kula da shi ba wallahi cikin kwana uku rak zai iya rasa ransa, ga zuciyarsa yadda take bugawa bakamar ta kowa ba a ko da yaushe xata iya samun matsala daganan kuma ta buga Sabi da damuwa , please idan ma akwai abin da ake Masa adaina Dan numfashin sa Yana barazanar d'aukewa " abbanmu ne ya dafe Kai hade da runtse idon domin yasan komai ya faru shine sanadi, da ace ysyarda da kaddara hakan bazata faruba ,Amma sai ya ki ya nunamin tsana da takura har najefa kaina cikin wannan masifar tabbas ko a lahira Allah saiya yimana hisabi Dani da abbanmu ,

To kwance a tashi a gurin Allah babu wuya kullum ammi cikin kulawa take Dani ,hakan yasa na Dan rage damuwa da Shan Kayan maye, itakuwa zarah kamar mayya kullum kamar kara mata soyayyata ake a zuciyar ta gabaki daya takasa hakura dani ,tacemin ko kasheta zanyi sai dai na kasheta Amma bazata hakura Dani ba,shikuwa abbanmu ganin yadda na tsani kaina yasa ya Dan Soma sakkowa ya fara rage tsanar da yakemin da koin kula, Har cikin zarah yakai Watan haihuwa.

_____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 22*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK TWO✌️*

*Chapter 22*

" Innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! Innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! Innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! Yau itace ranar da bazan taba mantawa da ita acikin tarihin rayuwata ba, yau ce ranar da mahaifiyata tazo gareni da wata mummunar magana wadda ta sa dukkan family na fadama tarwatsewa ,yau itace ranar da tazamar min masifa da bala'i yau ne nagane irin soyayyar da zarah takemin Ashe ba iya soyayya bace ,ayaune naji kamar Zan mutu, naji a duniya komai yamin zafi abbanmu Kuma ya koma tamkar mahaukaci Dan damuwa, ayaune zarah tasa kafa ta gudu tabar ak fadama Sabi da tashin hankali da damuwa Akan abin da taji, lallai muncuci kanmu Haka zalika Abbanmu ya cucemu innalillahi wa'inna ilaihirraju un! Kaddara tayinana kamun kazar kuku, narasa yadda Zan Kira wannan abin shin zunubine muka aikata allah ya jarrabemu ko me? Kokuma ya Mana hakane domin yaga zamu iya daukar kaddarar batare da zuciya ta tubzuramu mun mutu ba...wannan tashin hankalin ko ku idan kuka ji sai kunji ranku ya soso, Kuma bansan Yaya zaku dau abin idan n'a fada ba .....

_____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 23*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK TWO✌️*

*Chapter 23*
Chapter 7 · 0% Book details