← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 17

Sashe 10

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fu ad wan da ya hada Kai da gywa sai rusa kuka yace ga littafin yayi kaca kaca Sabi da hawaye musamman ma yadda yaji asalinsa sai hakan ya Kara bashi tsoro,jikin Adeena na rawa Tace "yanzu Yaya Maine amfanin rayuwar mu?" Daker Fu ad ya iya bude manya manyan idanuwan sa yace "Babu amfani Adeena ,wallahi Adeena aranar lahira akwai kallo, Mai nayi musu, da ce ZAN hadu da mahaifiyata sai na yimata tambaya Akan mantawa da rayuwa ta da tayi har soyayya ta rufe Mata Ido ta haifeni ba ta hanyar aure ba, n'a tsani wanan rayuwar wallahi an cutar da mu komai ya kare, gwara na mutu na huta ,ya dauke wata Yar karamar wuka a gefansa wadda ya Sha kankana da ita, yace "Baki da nakasa kokad'an Adeena ke yar sunna ce sabi da ko Babu komai da aure Aka haifeni ,idan Har Zaki iya zaman wanan duniyar Mai cike da son abin duniya da kizauna gaki Nan kizauna tare da su walalhi Yaya Abeed yaso kanshi yamanta da Ni idan natashi Yaya za a kirani, ayanzu mutuwa kawai nake bukatar nayi ,sai dai na fahimci bazata dauke niba gwara na rage Mata wahala, ya daga wukar zai cakawa kansa Adeena ta rike tana kuka,

Dan girman Allah Yaya kada ka aikata Haka ka yadda da kaddara ,daman allah ya tsara Bata hanyar aure za a haife kaba kuma Allah ya tsara Dole Yaya da kanwa ne zasu haifemu n'a rokeka kada ka kashe kanka, idan ka mutu kamutu dan wuta fa yaya!" Wani huci fu ad yayi Yana kokari karbar wukar daga hannunta cikin nutsuwa Dan karya yanketa ,sai kuwa itama ta hanashi ,Nan take suka Fara rikici garin kwatar wukar Adeena ta soka Masa batare da ta Ankara ba, wani uban ihu ta kurma Hadi da sakin wukar Fu ad yayi baya ya Fadi a kasa......

Juyi tashiga yi a d'akin tana kuka tana dawowa tama rasa mai zatayi akai, ga shi tana ji tana gani jinin Dan uwanta sai zuba yake akasa, dawowa tayi gaban da ta durkusa a cikin jinina tashiga jijjiga shi tana kuka tana cewa " Dan girman Allah Yaya kada ka mutu kabarni, dan Allah ka tsaya narokeka "murmushin karfin hali ya Soma sakar Mata cike da kwarin gywa ya Soma magana da ker Yana cewa "babban burina shine na jini a karkashin kasa nagaji da zaman wannan duniyar Mai cike da bakinciki da danasani, wallahi Adeena idan har kema kina son kisamu farinciki ki biyoni mu mutu tare ,kada kizauna a gun wadannan mutanen domin wata Rana kema sai sun kashe ki" jijiga Kai ta SHIGA Yi Hadi da ware manyan idanun ta a kansa Tace "a,a Yaya ayanzu bani da wani buri da ya wuce karayu inason mu gyra komai ,mutaimaki mahaifin mu Yaya idan ka mutu shima mutuwa zaiyi wallahi, shikkenan yazama na bani da kowa ku danake gani nake samun farinciki narasa ku, bani da tabbacin mahaifiyar mu tana Raye balle nace watarana idan n'a hadu da ita zata tallafeni ta goge duk wani zunubi da suka aika ta, n'a rokeka ka yafe musu bakasani ba ko Bata rayé ,yaya karka jawa mahaifiyar mu wata sabuwar azabar agurin ubangiji" numfashi fu ad ya Soma ja ,har lokacin jininsa Bai daina zubaba kuma wukar tana jikinsa har yanzu, ganin Haka yasa Adeena ta gigice ta futa a guje falo tana rusa ihu, Abeed ne yasoma ganin ta jikinta duk jini ,a razane ya Mike hadi da cewa "innalillahi wa'inna ilaihirraju un ! Adeena mai yafaru? Jinin Mai nake gani ajikin ki Ina Fu ad?" Da gudu Adeena ta zo ta fad'a kirjin Abeed tana kuka ,Allah sarki take yaji zuciyarsa ta karye, Bai taba tunanin akwai ranar da zatazo yarannan Susan su Suwanee Kuma su sake rabar Saba ,bakinsa da jikinsa narawa yace "Adeena lafiya Maine yafaru ,Dan Allah kiyi magana Ina Fu ad?"

Cikin kuka adeena ta ce "yaya fu ad Yana can a kwance zai mutu ya barni " ai abbansu Bai jira abin da zata sake cewa ba sukayi cikin daki da gudu har suna gware tsakanin ammi da Abba, suna shiga abbansu ya rikeshi Yana kuka, Fu ad har lokacin Bai daina motsiba muryarsa da ker take iya fita yace "abbanmu ka cikani kadaina tabani ,bana son ganin ku natsane ku dukkanku" fu ad Bai karasa magana ba Abeed ya shigo hankali a tashe hawaye na zarya a kuncinnsa, batare da ya tsaya wani tunanin ba, ya sa hannu ya ya fincike wukar daga cikin Fu ad ,Dan kwalin Adeena ya fincike ya daure gurin dashi ,sannan ya Sabi Fu ad a kafada ya fita a guje, Yana tafiya hawaye na zarya a kuncin sa, tsabar tashin hankali ma ya manta da wata mota a gidan su, dan gani yake idan ya tsaya kunna mota zai iya mutu wa, dan Haka ya fita a kafa, Yana kudu Yana haki ,duk inda ya wuce mutane na kallonsu, zuciyar Abeed na suya da zafi ,burinsa kawai ya ceci rayuwar fu ad kada ya mutu, allahu Akbar yadda zakusan iyaye soyayyarsu da tamu ba daya bace, yadda zakusan iyaye sun fita daban da sauran iyaye jigone sannan gatane, Babu wan da yakaii iyayanka sonka, yau na tabbatar ,Abeed gudu yake dauke da Fu ad a kafadar sa Amma ko ajikinsa kallon mahaukaci akemasa duk inda yazo hucewa Sabi da ko takalmi Babu a kafarsa shidai burinsa kawai ya samiwa Dan sa lafiya, ana Haka saiga abbanan ya tuko mota, saï da yaje daidai inda Abeed yake sannan ya dakata ya bude kofar Abeed ya shiga ,suka cigaba da tafiya har suka Isa asbiti....

💔 _____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 25*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK TWO✌️*

*Chapter 25*

*UMMA*

"Ke sumayya n'a lura wannan mutumin ya raina mini hankali ,Dan uwarsa Ni zai rainawa hankali ,Sabi da Ina son kudi a wajansa sai yayi ta Raina min hankali ,wayar tawa ma ya daina dagawa ,zai ci uwarsa kashe shegiya zanyi n'a huce haushi, gaba daya ya batamin komai "yan kudaden dana tana da duk yasa na kashe su wajan siyawa yarinyar Nan kayan sawa ,to wallahi akan ta Zan huce" "umma akan ta kuma? Mai zakiyi Mata bayan kinsan baba Yana Raye ,ai wallahi yun farko kece bakyason shawara da tuni kin Gama da ita, sai da nace Miki ki dauki yarinyar Nan ki hurgar yadda ba Wanda zai zargeki kika ki, yanzu baga shinan ba mun rabu da zaidu cikin sauki ,amma ita kin tsaya kina jiran wannan mutumin watakila ma aljanine ba mutum ba, Dan wallahi wannan kyau nasa baya rasa nasaba da jinsin aljanu" zaro ido umma tayi Tace "ke sumayya ! Aljani fa, kinsan wane aljani kuwa? Daina janyo Mana masifa ,idan aljanine asbitin Nan ai baza su dauke shiba Kuma taya za ai muyi video dashi ya fito a camera"

"Hmm umma kenan wallahi kina Wasa da aljanin yanzu ,kedai kawai tun da ya daina daga wayarki mu hurgar da shegiya mu huta ,idan kuwa ba Haka ba bazaki taba sun damar cin wannan gold din ba ato" ",tab dijan aikuwa haka za ayi Bari muga ,Amma to ya zamuyi da malan kenan" tabe Baki sumayya tayi Hadi da murmawa Tace "uhm umma kenan da bakin ki kika ce kashe shi zakiyi ki huta sai muje musake sabuwar rayuwa da wadannan kudaden ko" tabbas kuwa haka zamuyi yanzu maza tashi kisayo min maganin bera a shagon muntari" jikin sumayya ne yadan yi sanyi kuma da kamar Tace tafasa sai Kuma ta Mike tace, "umma kawo kudin kafin ya dawo" tsaki umma taja Tace "metsamtssss yanzu ke Ina samarin naki shashasha sai dai kowanne yazo ya tafi hannu na dukan cinya Babu Mai ko sirin da zai iya Baki kudi shsha Sha, gashinan sai kije ki sayomin Kuma Kar ki dade, Kuma wallahi duk ranar da nazama hajiya Kar naganki da ko Dan minister Sabi da kin fi karfin ajinsa banza kawai wadda batasan irin wadan da zatana kulawa ba, ke kowana gaja so kike"

Ita dai sumayya duk abin da ummanta take fad'a Bata ce komai ba saï dai taji zafin maganganun da ta fada mata sosai, daman tana kare mutuncin ta ne shiyasa Bata yadda subata kudi, Dan a zamanin Nan duk wan da zai baka kudi kaima saï ka bashi wani abun ,ba kowa bane mai tsoron allah wan da zaizo da niyyar son ka da gaske, Nan take sumayya ta kudiri aniyar sai ta riga samun kudi a gurin samari Kota wanne hanya ce,

Uhm Niko nace Allah ya rabamu da iyaye irinsu umma.

*Mujahid*
Chapter 10 · 0% Book details