← Book details Depression Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 17

Sashe 15

Depression Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Munira na fita daga d'akin tasaki murmushi Hadi da tauna lebe, Tace "yanzu nasan sunacan suna tunanin sabuwar da barar da zasu bullomin nikuma kafinnan Bari nayi sauri Kar Abba yagaji da jirana" tana Gama wannan tunanin, ta fada dakin mahaifiyar su da sauri Amnaa tana bacci ta dauketa tare da dorata a bayanta ,sannan ta saka hijabi, ta huce d'akin abbansu, kamar yadda ya fada mata Haka tayi, durowarsa ta bude ta daga kasan kayansa, saiga wasu Damon takaddu a leda baka, duk da bata San komai ne ba amma dai tana tunanin kudadene da yawa Haka, batai wata_wata ba ta dauki ledar ta fice daga gidan, shima Mai gadin Tun da safe Abba ya sallamesa Hadi da bashi kudi masu yawa ya ce yatafi gida zai nemesa, aikuwa mai gadi Tun safen aranar ya tattara kayansa ya tafi batare da umma ko sumayya sun sani ba, munira kuwa tun da ta fita take zuba sauri har gudu gudu takeyi Sabi da sauri Kar su umma su Ankara su biyo ta, har ta karasa bakin titin garin adamawa, a daidaita ta Tara tashiga Tace ya kaita Tasha kamar yadda sukayi da mahaifin ta ,Babu musu Mai adaidaita ya Soma tafiya cikin mintina kalilan ya Isa Tasha, kamar kuwa Abba yaga shigowar su ya Mike daga inda yake a zaune yazo ya biya kudin adaidai tar daga Nan Kuma ya kalli munira tare da sakar Mata murmushi yace "'yar albarka harnaji tsoro nazata sun kamaki" "a,ah Abba ai Allah bazai Basu nasara akan mu ba, musamman ma tayadda mukeson mu ceci marainiyar allah wadda Bata jiba Bata gani ba" "hakane 'yar nan yanzu ina akwatin da kika dakko a dakina?' zaro ido munira tayi Tace "Abba wane akwati Kuma ba kudi kace na dakko ba? Yar dariya Abba yayi yace ai ba kudi bane 'yar Nan akwati ce a tsakiya abin da yasa kikaga nasaka kudi a sama da kasan ta kar mahaifiyar ku ta ganine, kinga yanzu kuwa da nayi Haka ai gashi mun fito da ita cikin sauki" "Kai abba kardai wannan akwatin da umman su zaid ta bawa ummanmu Tace tabawa su zaid in sun girma?" " Ah itace Mana yar Nan idan ba ita ba to wacce ?" "Kai alhamdulillah Abba kaga shikkenan mun samu hanyar da zamu iya nemo adresse d'in gidan batare da baci ba , yan Zu dai Abba muyi sauri mu gudu tun kan su Ankara Dan wallahi umma Bata da imani zata iya aikata komai Akan kudi" "uhm munira kenan nasan mahaifiyar ku ciki dabai saidai Allah ya shirya kawai yanzu dai Ni na tsira nasan Banda kinji suna maganar kin zo kin fad'a min tuni yaune sadakar ukuna ko" dariya munira tayi Nan take kewawan hakoranta farare Tass suka bayyana Tace "Abba ga motar Nan airport zata ko zamu shiga takaimu in yaso sai mu tafi wata kasar batare da sun ganmu ba" "eh to kin kawo shawara babbama kuwa Allah yamiki albarki ,kin ga sai mutafi America ko? "Eh Abba "suna Gama fadin Haka Abba ya biya kudin motar suka Shiga suka dauki hanya .

*Faransa*

Tun da su doctor suka fita zuwa d'akin Abeed Dan suga mainene yake faruwa har gware suke a tsakanin su , Fu ad ne ya Soma karasawa bakin gadon idonsa cike fall da hawaye, hannunsa kuwa jini ne yake zuba Sabi da kalular da ya fincike a hannunsa, ya fad'a gaban mahaifinsa tare da Dora hannunsa dukka biyun a kirjinsa yana kuka Yana jijjiga shi, shikuwa Abeed Allah sarki Yana kwance so yake yayi Masa magana Amma Babu Dama, saï wani irin numfashi ne yake fita daga bakinsa ,bama ya iyayin numfashin ta hanci sai dai ta Baki, idanunsa Babu hawaye Amma sun kada sunyi jajur kamar garwashi, gangar jikinsa kuwa sai rawa take Rana wani irin jijjiga kamar Mai farfadiya, kuzo kuga tashin hankali gurin Abba da sauran mutanen dake cikin d'akin, doctor imam kuwa yama rasa abin da zai Masa Domin ya fahimci ciwan Abeed yafi karfinsu sai an dangana da kasar waje.

Kuka Fu,ad yake kamar zai shid'e Bai na damu da jininsa dayake zubaba shi dai kawai ta lafiyar mahaifinsa yake, ana Haka kamar an dauke ciwan sukaji Abeed tsit yakuma daina jijjigar, saurin matsowa doctor yayi ya tura gadon suka Shiga dashi dakin gwaji, Har da Fu ad Dan ya ki cikashi, anyi anyi ya cikashi yaki, sai Dole aka hakura aka shiga dasu subiyun,

Mintina kalilan ba jimawa doctor ya fito Hadi da furzar da iska ,Fu ad bin da yayi abaya Yana cewa "Uncle ya jikin abbana dan Allah kada kacemin bazai tashiba ,kada ka fadamin Haka Dan Allah" abba kuwa cike da tsoro da fargaba yake kallon doctor ,sanyi lokacin ga AC tana Yi a asbitin Amma shi Abba gumi kawai yakeyi Yana sauraron abin da doctor zaice , doctor imam kuwa bakinsa da ker ya iya budewa yace "innalillahi wa'inna ilaihirraju un ,wannan wace iriyar masifa ce ,abbanmu ina mai baka hakuri sai dai muyi hakuri da Abeed domin abubuwa sun Masa illa da yawa ,daga wannan sai wannan dafari zuciyarsa ce ta tabu, yanzu Kuma munsake gano wata matsalar daban, order sa duk guda biyun sun tabu Sabi da kayan mayen da ya jina Yana Sha, sai dai daya tafi Taya tabuwa ,alissafin mu da tunanin da mukayi akai ,da ker ne Abeed ya Kai jibi bai mutu ba, duk da dai bamune masu daukar ran ba amma dai yanayinsa yanuna abba" wani irin kukan kura fu ad yayi Bai San lokacin da ya cafko wuyan doctor imam ba, Sabi da Gaba daya ta fita daga hayyacin sa, surutai ya somayi ta inda yafi ta ba tanan yake shiga ba yace "wallahi karya kuke bazai taba yuwuwa Yaya abeed ya mutu ya barni ba, bazai yuwuba wallahi, abbana bazai mutu ba ,duk ma yadda za ai kucetomin ransa kada KU kashemin shi Dan Allah..... Fu ad ya fad'a zuciyarsa na tafasa, daker amaar da abba suka kwaci doctor daga hannun Fu ad, shi kansa doctor ya tsorata Sabi da idanunsa duk sai da suka firfito waje, dabadan su Abban ba inaga saidai ya mutu kafin akawo Masa dauki,

Fu ad ne ya cigaba da cewa "idai order ce wallahi nayarda na amin ce Zan bawa mahaifina yawa dukka Ni na mutu shiya samu farinciki ,Kai zuciyarma ma da ana cirewa zam iya cire tawa na bawa wannan bawan Allah, nidai burina Dan girman Allah uncle imam kada kabari abbana ya mutu, narokeka" Fu ad ya hade hannayensa duka biyun tare da durkushewa a kasa Yana zubada hawaye Yana ruko kafafuwan doctor .

Tsananin tausayin sa ne ya Kama doctor Bai San sanda hawaye shima suka wanke Masa fuska ba, sannan ya durkushe a kasa ,tare da Kama hannun Fu ad yace "Fu ad kayi hakuri kaji komai kagani yafaru daga Alla ne, shi tasa kaddarar kenan ,wallahi da Ina da damar ceton rayuwar mahaifinka da tuni na cecesa to Amma abin da wahala Abeed ya ra..... Saurin daga masa hannu fu ad yayi yace "kada ka fadamin Haka Uncle ,nayi imani da Allah sannan nayi tawassali ga Wanda ya kawomu duniyar ya halicceta Baki daya, kamar yadda Allah ya dorawa mahaifina wannan kaddarar ,nasan yanaji Kuma Yana gani ,allah bai dorawa wani bawa cuta ba sai da yayi maganinta ,Dan Haka mahaifina ban karaya ba zai tashi da izinin Allah, Kuma muyi rayuwa tare cikin farinciki, Dan Allah doctor kataimaka muje kacire tawa order asakawa abbana ,na rokeka" jikin doctor yayi masifar yin sanyi hakama Abba musamman yadda sukaji yaro karamin Yana irin wadannan kalaman, saï lokacin shima doctor yasamu kwarin gywa akan Abeed bazai mutu ba zai tashi Dan Haka yace "duka ordar sa ta tabu Koda anyi dashen guda daya Dole datar zata Kara lalata dayar, Dan Haka Nima Zan cire tawa guda daya kaima sai a ciri taka guda daya saï a dasa Masa dukka biyun" kukan farinciki ne ya Soma zuba daga idon abba saï lokacin wasu hawaye masu dumi suka Soma zuba daga idonsa, Haka ma fu ad baisan lokacin da yasaki murmushin farinciki yace "nagode uncle Allah yasaka maka da alkairi ya biyamaka abin da kakeso duniya da lahira" uhm Fu ad kenan Babu komai kaima da kake yaro matashi ka yarda zaka zauna da ordar daya balle kuma ni ,ai Babu damuwa tsakanin ka da amaar Babu maganar godiya mahaifinka ya dauki anaar tamkar dansa nasan Nima danine nake cikin wannan yanayin abin da yafi wannan Abeed zaimin ".

💔 _____*DEPRESSION*_____💔
(DAMUWA)

*#CIN AMANA*💔
*#JURIYA*💔
*#SOYAYYA*💔
*#DAMUWA*💔
*#HAKURI*💔
*#YAFIYA*💔
*#KYRA*💔

*Chapter 30*

TO😌 TO😌 TO😌💪💃💃💃💃💃 DA KARFIN SA YAKE TAFE SHIN KIN SAN YADDA AKE TSANTSAR CIN AMANA KUNSAN YADDA AKE NUNA TSANTSAR SOYAYYA KARYA? KO KUNSAN YADDA ZUMA DA MA'DACI YAKE ,TO ALBISHIRIN KU MASU SAURARO MUTANEN ALKAIRI ,INA SON KU GYRA ZAMA DOMIN RAKASHE NI SHADIN GWANGWAGE KARATUN WANNAN LITTAFIN MAI TAKEN DEPRESSION (DAMUWA) 'YAR UWA KADA KIBARI ABAKI LABARI WANNAN SALON NA DABANNE DOMIN 'YAR'UWA💃💃💃💃💃💃

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼
_*DEPRESSION*_
*damuwa*
_*BY*_
_*HAFSAT UMAR ƊAN GORO*_
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

_*JARUMAI💪🏻WRITER'S ASSOCIATION📚*_

_*Marubuciyar*_
1- Burina Mu'azzam
2- Ba Mahaifiyata bace
3- Babana ne sila
4- Ummu Amani
5- Amatullah
6- Zuciyarta
7- Mace Rayuwa
8- Rayuwar Ƙasƙanci
9- Mar'atussaliha
10-Babbar sakayya
11-AFNAN
_And now_
💔_*DEPRESSION*_💔
*damuwa*
*BOOK TWO✌️*

*Chapter 30*

*Adamawa*

Tun da su umma suka Gama sabuwar kullinsu da zasu bullowa munira da da mahaifinsu ,suka Shiga shirinsu,Dan har lokacin umma Bata lura munira Bata nan ba, saï da ta Shiga dakin ta taga Babu Amnaa Babu labarinta sannan ta fito hankali a tashe Tace "sumayya waikuwa bakiga Amnaa ba nafa duba ko ina Babu Amnaa Babu munira ga malan haryanzu shiru.....
Chapter 15 · 0% Book details