part dinta ba a zuciye ta wuce fuuuuuuuu
Cutar Kai Part 1 Complete Hausa Novel · about 49 min read
tana
jin haushin kanta da tasan baya part din ma bazata zo ba ya shiga dakin kisna
ya rikota ta fixge "ka rabu dani daman zakin bakin banza kake min
alhalin kana zuwa kana fadawa wacan matar wai ina zuwa dakin saurayi ta karasa maganar
tana kuka da karfinsa
ya janyota
ya zauna tare da zaunar daita a kan ciyarsa yana shafata
yana rarrashinta "wallahi ki yarda dani ban fada mata komai ba yadda bansan inda kika san mamarta nada
karkatacciyar kafa ba haka itama ban san inda tasan wannan maganar ba amman na
auki laifina kiyi hakuri ,hakurin duniya kisna
taki yarda
,ya rasa yadda zai yi
shawo kanta
ta hakura duk inda yayi ta
batsare
masa
...."
Karfe tara
ya shigo part dinsa dake cikin na
nawal sai dai har shadaya bata san ya shigo ba ya tashi ya shiga
akinta ya iske har lokacin kuka take ya zauna yana rarrashinta kamar yadda yayiwa kisna
amman sam taki sauearansa har shabiyu ya gaji ya
tashi ya koma d'akinsa ,bata
biyosa ba
bare tasan anan ya kwana ko a bangaren kisna ,ranar batayi bacci
tana tunanin hanyar bi dan mallakar muradi ita kadai kuma ko ta wani hali a cikin satin nawal ta zamo customer malamai taje nan ta mika kudin ta taje can ta mika kudinta , kowani malami
na cin rabonsa tare da girba mata karya ta kashe kudi ba ka
an ba sai
dai
babu wata biyan bukata me makon ta hakura ta natsu ta kwantar da hankalinta tayi hakuri tayiwa mijinta biyayya sai ma wani salon iskanci ta dauko
rikici yaki karewa case fa
har gurin
dady
babu
wanda bai yi dariya
ba daga ya badamasi har aunty ummi mumy ce ta hade rai
shi kansa dady dannewa yayi
dan idan yace zai yi dariya lallai abun zaiwa
nawal yawa, ya numfasa bayan wannan zagin da kisna tayi min dady har da kwanana yake dauka ya kai mata
muradi ya zabga mata wata
atuwar
harara "ban nemi iznin agurinki ba
ki fa shiga hankalinki kin dai san na fiki iya abinda kike yi ?dady yayi saurin daga masa hannu "magana ta natsuwa za'a yi ba fada ba "wallahi dady sai dana nemi izininta kuma da kanta ta amince "shinkenan ya isa gbdy sukayi shiru suna sauraron dady
a natse ya soma magana .
"Allah subhanahu wata'ala ya farranta adalci akan miji wanda ya auri mace sama da daya, koda guda dayar ce Allah yace dole yayi mata adalci kuma ya riketa da amana ,idan kuma mace tafi daya biyu ne uku ne ya zama wajibi yayi musu adalci kan rabon kwana ciyar dasu abinci tufatar dasu da kuma gurin da zasu dinga kwana wannan dole ne sai namiji yayi adalci atsakanin
matansa ,wajen kwana kar yace zai je kwana biyu a
gurin daya ita kuma dayar yake mata kwana
aya sai dai idan da mincewar daya wannan ya hallas a Shari'a amman ban da tillasta wa sai tare
da amincewarta
,ta amince yayi kwana biyu a dakin yar'uwarta, ita kuma
yayi mata kwana
aya koma ya koma
yana kwana a dakinta gbdy muddin dai itace ta amince da haka babu matsala haka ma gurin cin abinci abinci da kabawa waccan shi zaka bawa dayar ya zamonto komai daya babu wani bambanci dalili akan haka kuma
Allah subhanahu wata'ala yana fada acikin Alqur'ani
Idan
kukaji tsoran bazaku iya adalci a
tsakanin matayenku ba to ku auri guda daya da kuma abinda zaku mallaka na kuyangi
wato bayi kenan idan mutun yana da mata yana da
baiwa to bazai yiwu ace duk abinda mutun yayi wa matarsa ta aure shi zai yiwa baiwar
ba,
ita din ba dai
dai take da matarsa ba, idan
yana jin tsoron
bazai iya adalci a tsakanin mata biyu ba kuma yana bukatar ya zauna da mace sama da daya yaje ya nemo baiwa sai ya zauna daita
, dady yayi shiru tare da
nunfasawa
yana dubansu daya bayan daya "dan haka kayi
iyakar kokkarinka kayi adalci a tsakanin matanka a karshe ya hadasu yayi musu nasiha sannan kisna tace "dady ni ba'a yi tawa maganar ba ina son naji a ina taji ina zuwa dakin
saurayi
kafin nayi aure idan ba haka ba rigima bazata kare
ba ? ta fada hawaye na zubo mata aunty ummi ce tayi magana wannan karon" ke nawal waya fada miki ? wannan ne ya fada min gashi nan idan karya nake ta nuna muradi , gbdy suka zaro ido suna kallonsa shi kuwa dafe qirjinsa yayi yana kallon nawal "Inna lillahi ya furta a fili "wallahi aunty ummi bani na fada mata ba kinji na rantse ke kuma idan baki fada musu wanda ya fada miki ba zan katse igiyoyin aurenki dake kaina ya k'arasa maganar yana nunata , dady yayi saurin cewa" a'a muradi shi hukunci ba'a yanke sa cikin fushi , sannan ya kalli kisna yace "mamana kinsan abinda nake so dake ?,ta girgiza masa kai "kiyi hakuri ki bar maganar nan kuma bana son ki sake tayar daita har abada idan kika yi haka kin gama min komai yana gama fadar haka ya
sallamesu
koda
suka fito nawal ta shige gaban mota ta hakince
tana zagin kisna tana mata habaici so take ta tanka mata a gidansu amnan kisna bata ce mata komai ba ta bude gidan baya ta shiga ta
zauna har sanda muradi ya fito yayi mamakin ganin nawal a gaba ,sai dai shima bai ce mata komai ba ya shiga suka wuce har suka gida bai ce kowace acikinsu qala ba dan ransa a bace yake ."
*******
Ranar wata Laraba nawal
na zaune
muradi
ya shigo
bangaren
bakinsa dauke
sallama
Assalamu
alaikum
yana
kallon
fuskarta
tayi
masa banza
tamkar bata san da tsayuwarsa
ba dan har lokacin fushi take dashi ganin take baya mata adalci yafi son kisna akanta shima fushin yake daita sai dai ya danne nashi saboda yana son sanin wanda ya fada mata kisna na zuwa dakin saurayi kafin aurensu da har tace shine ya fada mata ya lumshe idanunsa yace "amman dai kinji nayi sallama kou?duk fushin da kike ai bai kamata kiyi
watse da rahma da kuma aminci Allah a gareki ba, tsaki taja aranta sannan ta dauki wayarta tana
dubawa ha
e da
mikewa tsaye ya janyota jikinsa ya makaleta da hannunsa daya yace " Please nawal banason muyi irin wannan rayuwar ki dinga hakuri
kina
saka fahimta
acikin zamantakewarmu
shinkenan bazaki min uzuri ba
"kada ka fada min komai dan banason jin komai daga bakinka dan duk kalamanka na yaudara ne a gareni ka tafi kawai ka cigaba da son zuciyarka Kayi abinda
Kaga
dama yayi shiru yana tunani dan shi da biyu yake lalla'bata
"kina ji ko ina son ki fada min wanda ya fada miki cewar kisna na zuwa gurin saurayi ?
"bazan fada ba ,ni kuma muddin baki fada min ba bake ba zaman lafiya a cikin gidan nan bare wani adalci da kike magana akanshi "kome zai faru ya faru Amman bazan fada ba , cikin
haka wayarta
ta soma ringing
ta duba sunan fedy ta gani yana yawo akan screen din wayar hankalinta kwance ta danna silet
ta cigaba da fidda numfashi tana hura hanci yaki sankinta haka zalika
kira yaki daina shigowa
wayar "wake kiranki da kika ki dauka ?tayi shiru "bani wayar sai lokacin ta d'ago ta zuba masa idanunta "saboda me zan baka ki bani wayar nace yayi maganar a dan tsawace ,bazan bayar ba tunda ba kai ka siya min ba ta nawal ya fada a karo na biyu, zuciyarsa cike da tashin hankali ya ajiye system dinsa ya mika mata hannunsa yana firfito da kwayar Idanunshi nan take jikinta yayi sanyi dan sam bata tsamaci zai matsa ya amshi wayar hannunta ba, yana amsa kiran fedy na sake shigowa ya danna koren madanin tare da sakawa a handsfree
batare da yayi magana ba "nawal kiyi hakuri na bata lokaci kou wallahi na
tsaya amsar address din malamin nan
ne amman gani akan hanyar zuwa nan da minti goma kacal zaki ganni a kofar gida hope kin gama shirinki jin shiru yasa fedy furta hello !!! nawal kina jina zan tsaya a kofar gida kinsan me gadi baya barin na shigo da kinga kirana ki fito kawai still shiru taji hakan yasa ta katse kiran ya tsaida Idanunshi sosai akanta yana dubanta a wulakance
bai
ji abun ya taba shi ba saboda daman yasan da komai tunda
suka fara
shirinsu
guri
ya samu
zauna ya kunna
system
dinsa
ya shiga wani bangare ya soma dube dube har ya shigo inda yake bukata , yayi shiru ne jin
nawal
din
taki amincewa
da shawarar fedy
shi
yasa ma
bai tunkareta da maganar
ba ko a kwanaki
da yaji wayarsu sam bai damu ba dan ganinsa sai fedy ta samu damar shigowa gidan zata
fita zuwa wani
guri byn kwana biyu ya daina jin wayarsu yayi tunanin ko sun bar komai ne ,a natse ya d'ago Idanunshi batare daya kalli inda take tsaye tana rawar jiki ba , ya ciro wayarsa ya kira mai gadinsa tare da bashi umarnin idan fedy tazo ya barta ta shigo inji madam mai gadi yace amsa masa da "okya sir ."
"kin bani mamaki nawal duk abinda kika fada min kafin aurenmu bashi na gani ba , kenan yaudarata kika yi kou ?ban yaudareka ba kai ne sanadin canzawata wallahi ba halina bane wannan fedy ce ta kai ni ,me kike son nayi miki nawal iya kokari ina yi amman bakya gani kina tunanin na tare agurin kisna ne saboda tayi min asiri kou?
ki sani ace kisna ke yin abubuwan da kike min wallahi da iyayena bazasu barta ba , ke bama zatayi abinda kike min ba , sannan duk abinda ke yi wallahi nasani a tunanina idan Kinga babu riba zaki hakura a she wani lasisi kika samu na baje kolin bin mlm ko daren dana zo na fada miki kisna bata da lafiya duk abubuwan da kika binee acikin gidan na gani kuma ni nan da kaina na cire
,ke kanki baki yarda cewa za kiyi
nasara akanmu ba bare ni dana nasan karya kawai malamai suke miki kudinki kawai suke ci , duk abinda zakiyi ya tsaya iya kaina saboda ni na auroki karki yi kuskure da zai shafi kisna dan ita agurinta dake da babu duk daya ne
na gode da abubuwan da kika min
Allah ya saka da alkhairi
suna zaune sai ga fedy ta shigo tana cewa "kawa da alamun aikin wancan malamin ya fara aiki naga har ....
turuss tayi gabanta na faduwa ganin muradi zaune ya daura kafafunsa akan center table yayi crossing dinsu idanunsa na kallon system ta dan juya a hankali inda nawal ke tsaye babu laka ajikinta ta tsira mata ido ,muradi ya rufe system dinsa ya
tashi "ki tattara komai da kika san naki ne ki bita har sai na nemeki ,ya soma
arin barin falon ta durkusa bisa gwiwowinta tana kuka dan Allah kayi hakuri ka min rai wallahi bazan sake ba ya fixge karsa ya fice ta kalli fedy ta sake rushewa da kuka "kinga abinda kika janyo min ko kin bani muguwar shawara sai da zuciyata ta haneni amman Kika rinjayi zuciya
gashi kin kaini kin baro dukab yaushe nayi auren da har zan koma gida surutai kawai take fedy na bata hakuri da kyar ta samu ta lalla'bata ta dauki abubuwanta suka fito suka shiga mota suka wuce gida tana zuwa gidansu da kuka ta karasa shiga hankalin mahaifiyata ya tashi ta dinga tambayarta dalilin kuka "na shiga uku fedy ta kai ni ta baro tasa muradi ya kareni "me tayi tukunna take ta fada mata komai "bar shege zai dawo da kansa yace bai fada ba daman duk jinin tsiya sai ya nuna rashin arziki da daddare mahaifinta ya kira layin muradi sai dai yaki dauka har ya gaji ya hakura ya zubawa sarauta Allah ido
kuma cikin satin muradi ya soma ciku cikon barinsu kasar
cikin sati biyu
komai ta kammala kisna taje gida dan yin sallama duk anan suka hadu da sauran yan'uwanta anan ne ma take jin nawal din tana gidansu shine fa ta fara basu labarin fadansu ai babu wanda bai yi dariya ba aunty mufeeda tace" ke kuwa a ina kika samu labarin uwarta na bin bokaye ?babu wanda ya fada min kawai ha
awa nayi na hada da
kafar uwar , ta taba zuwa tunda dana
ji kara jiniya
da shigowar hillus na biye da
motarta kuma har sanda aka fito aka bude mata nasan uwarta ce ga tsantsar kama wallahi kudi ne kawai Amman kafarta a karkace take suka sake kwashewa da dariya har muradi ya shigo suna labarin ya bala'in hade rai kafin daga baya yayi mata gargadi da Idanunshi nan take tayi shiru ta shiga hankalinta suka canza hira ."
Bayan kwana uku
kisna da muradi suka bar kasar
zuwa cairo a can suka ci-gaba da rainon cikinsu da
gudanar da soyayyarsu
cike da kulawa da juna sam idan kaga muradi bazakace shine wannan miskililin ba komai shi yake mata ya dawo tamkar bawanta watanin sunja sosai
har sun share
wata bakwai
batare daya waiwayi nawal ba a
lokacin cikin kisna
ya fito sosai
mahaifin
nawal
da mahaifiyarta suka
samesa da kansa a cairo sun jima suna tautaunawa akan nawal a karshe uwarta
cikin fushi tace" idan bazaka dawo da nawal
ba ka sakar min
yarinya
ta cigaba da
rayuwa
muradi yaji haushin maganarta
sosai
dan haka a zuciye yace "zasu ga sakonsa a
cikin
satin
mahaifin nawal bai so ta fadi haka Amman babu yadda zai yi an fi karfinsa sai abinda hjy mardi tace da shi yake aiki aiko cikin satin ya tura mata sakon sakinta daya."
" ai nawal na gama karanta sakonsa ta zube kasa sumammiya sai farkawa tayi ta ganta a gadon asibiti satinta daya aka sallamota ta dawo gida
damuwarta ta karu
, cikin kankani lokacin ta fita haiyacinta ta zamo kamar mahaukaciya tayi ta ihu
tana sambatu kiran sunan muradi
tayi baki ta rame mahaifiyarta kamar ta hadiye zuciya ta mutu
dan bakinciki ita kanta ta zabge ko bacci bata iyawa kuka kuwa tayiwa nawal har ruwan idanunta na neman tsiyayewa , ga surutun danginta dana mijinta
dake yawo cikin kunnenta
mijin nawal ya tafi da uwar gidansa
ya bar nawal ga kuma saki wasu nacewa ai
mugun kishin uwarta data dauko ne yasa ta kasa zaman aure
har zuwa suke gidan gulma
duk wanda ya shigo ya iske hjy mardi
ta dinga zage zage kenan da maseefa wai muna furci ne ya kawosu
bayan anyiwa mijin yarta asiri ne ya saketa
shine dan munafurci ake zuwa ganinta."
cikin kisna na shiga wata takwas
ya tattarata
sukayi london
sakamakon yana da buga wasa kuma anan kasar yake son ta haihu
bayan ya gama abinda ya kai shi yace suje su kara siyan kayan baby amman kisna taki dan gbdy a tsorace take kullum da tunanin haihuwa take kwana take tashi barin ma da likitoci suka tabbatar mata da bazata iya haihuwa da kanta ba
,kullum muradi cikin rarrashinta yake ya kwantar mata da hankali "wannnan bazakiyi doguwar makusa ba tunda ansan cewar bazaki iya haihuwa da kanki ba edd dinki na cika za'a cire miki babyn ki huta ai kuwa
wata tara daidai aka shiga dakin tiyata da
kisna tare da muradi, yana tsaye akanta akayi mata komai aka gama
aka ciro mata
diya
mace mai kama daita
sak sai dai farincikinsa bai bayyana ba har sanda aka fita da baby dan gyarata dan gbdy hankalin muradi baya ga bby yafi son yaga farfadowar matarsa sannan yaji da bby washegari ta farfa
o har tana tambayar bby girl dinta tunda daman an fada mata abinda zata haifa nan farinciki muradi ya bayyana ya riki hannunta "na gode matata Allah yayi miki albarka , Allah ya bar mu tare muddin rai acikin satin
mumy ta sauka a london cikin tsananin farinciki akayiwa bby huduba da sunan mumy wato
saliha nan take kisna ta sanya mata mother....."
******
Muna saida ingantattun maganin mata masu kyau da nagarta wanda ko da kudinka sai da rabonka tsimi , zumar Mata, gunba, gari insertion,kaza,zakara ,
jigida dadai sauransu.
1.Tsumi Yana saukarwa mace niima Kuma bazataji wuyar jimai ba.
2. Zuma Tana taimakawa wurin Jin sha'awa Kuma itama Tana taimakawa wurin jindadin jima'i.
3.insertion( Dan matsi) daban dabanne akwai Wanda ke matse mace kuma yake saukar da ruwan ni'ima sannan akwai na mallaka , idan ana bukata a tuntubi wannan number
234 815 945 0159..
Mmm Sudais
[7/19, 5:33 PM] +234 803 631 5951:
CUTAR DA KAI
Page 70 last page
~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne ,mai bukata karanta shi zai tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number alert +234 803 238 4602 domin tabbatar da an tura , ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 ,kada ayi vtu a number MTN sannan kada a Kira number mtn ba'a kira dashi only chart ne . "domin sauraran littafaina sababbi da tsofaffi za'a iya tuntu'bar Channel dina ta Hausa bakwai,sannan muna bada sarin Lagos lace da kamfala ,Lagos rapa , jaka da takalma, getzner na cotonou da chiganvy, voil lace duk akan farashi mai sauki ,ga mai bukatar siyan
aya ko sari yayi magana ta wannan number 08059623096.
Mumy tayi rawar gani sosai wanda komai hassadar mutun sai ya yaba mata ,idan kaga yawan kayan baby , da irin hidima data yiwa kisna sai abun ya baka mamaki ,zaka dauka bata ta
a haihuwa da kuma samun jika mace bane sai lokacin kusan akwati shida shida shake da kayan baby dana kisna haka nan dan ta nunawa diyarta da takwararta gata da soyayya , bayan sati uku sai ga muradi ya turo kofar d'akin da kisna take zaune tana kallon fuskar kyakkwar babynta dake bacci da nashi kyautar , ya k'arasa shigowa a natse bakinsa dauke da sallama ya ajiye takardun dake rike a hannunsa akan cinyarta ta d'ago idanunta a hankali ta amsa masa sallamarsa kana ta tsura masa idanunta tana kallonsa cike da matsanancin qaunarsa, shi din ma ita yake kallo a natse ta dauki takardun tana dubawa muryarta a sanyaye tace "wadan nan takardun fa na menene world best ?.
"naki ne baby love na mallaka miki su duniya da lahira , tsaye tayi tana kallonsa tsabar mamakinsa tasan yana da niyyar yi mata kyauta amman bata dauka kyautar zata zamo mai girma haka ba ,takadun gidan mansa ne guda biyu dana supermarket dinsa dake nigeria wanda suke dauke da sunanta , iya sunanta kadai ma daya sanya musu tasan babban kyauta ne bare ya kai ga mallaka mata su , a hankali yaga hawaye sun biyo fuskarta zuciyarsa na dokawa ya dinga girgiza mata kai alamar karta yi kuka hannunshi yasa ya share mata hawayen fuskarta ."
cikin tsananin murna ta rungumesa ajikinta tana fashewa da wani sabon kuka , ya zagaye waist dinta da duka hannuwansa yana cewa "ki daina wannan kukan Please bana son ganin zubar hawayenki matsayinki ya zarta wannan kyautar "na gode world best !!! amman ba sai ka mallaka min wannan qadarorin ba ni kai karan kanka nake nake so , ka soni ka kula da rayuwata ya fiyye min wadan nan qadararon ,naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana share mata hawaye ,kula da rayuwarki dole ne baby love Koda kuwa bana sonki bare kece mahadin rayuwata , cikin Muryar kuka tace "to ka ha
a dana gurinka na barwa yaranmu " kada ki kara cewa komai baby akan wannan kyautar dan soyayya ce idan baki amsa ba zanji babu dadi araina wata naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana zare jikinta ta tsura masa ido zatayi magana ya kai wa bakinta kiss .." kisna taja hannunsa suka shiga d'akin da mumy take tana nuna kyautar muradi "mumy ki tayani godiya abbansu aryan ya mallaka min gidajen mansa guda biyu da supermarket dinsa ,mumy tayi murmushi tana dubansa tare da cewa "ban san abunda ke burgeka atare da kisna ba da har kayi mata irin wannan kyautar? kisna tayi murmushi tana dubansa , shi kuwa a ransa cewa yayi mumy bazaki fahimta ba ni kadai nasan yadda nake jin hajiya kayi a raina da ina da ikon mallaka mata rayuwata zanyi ."
wata biyu da haihuwar kisna suka tattara suka dawo cairo tare da mumy cikin tsanani farinciki , duk wani gata da kulawa muradi na bawa kisna kamar zai mata numfashi ,wani lokaci haka zata zuba masa ido tayita kallonsa mutumin data tsana ada shine yanzu ya zamo farincikin rayuwarta ,shi ke mata komai kafin mumy ta tashi a bacci ya hada mata ruwan wanka ya bata abinci sannan ya fita zuwa office ,sai idan mumy ta tashi ne tayiwa baby wanka , renon mother ya koma hannunsa dan ba karamin qaunar yarinyar yake ba musamman ma da tayi kama da kisnarsa , yanayin zamansu da muradi a yanzu ko ba'a furta mata ba ya tabbatar mata da cewar taso *cutar da kanta* a baya allah da tsayayyun iyayenta suka taimaki rayuwarta da yanzu tana can gidan musa tana shan wahala kamar yadda taji ance byn fitowarsa a jail bakar wuya yake ci ga babu tsayayyen aiki ga shaye shayensa yafi na da , har sata yake da zarar yaga wayar mutane zai yi gaba daita ya cefanar ya siyi kayan maye ."
a yanzu wani irin so take wa muradi fiyye da lokacin dawowarsa ta farko daga cairo , zamansu lafiya babu fada ko sa'insa a tsakaninsu sannan babu rabuwa suna tare har abada dan shi kansa wata zazzafar qauna mai tsayawa arai yake mata kamar yau ya fara saninta diyya mace ,ashe samun mijin na garin shine babbar dace da sa'a a duniya Allah ya sakawa iyayenta da mafifi alkhairi domin sune suka yi tsayin daka akan rayuwarta da muradi ,lallai rayuwarta ya zamo izina ga yara masu irin halinta na baya, su farga su gane zabin iyaye shine zabi kuma abun farinciki da alfahari domin kuwa duk wanda yayiwa iyayensa biyayya zai ga farinciki a rayuwarsa wanda yaki binsu kuwa karshensa wahalar rayuwa dan ita sheida ce Allah ya hanata auren musa ya bata muradi domin son ganinta cikin farinciki ita kuwa me zata ce wa Allah daya wuce godiya wani hanin ga Allah baiwa ,kwance take ajikinsa a falo akan kujera manne da juna yayinda mumy ke daki tare da mother ya shige jikinta sosai yana shafata yana mata magana a shagwabe " baby love ki duba lamarina mana gurin wata wata uku kenan ina zaune haka kinsan fa hakurina bai ka haka ba , Allah idan ban ci ba yau komai zai iya faruwa dani "haba aliyu muradinah ka dan qara hakuri wai so nake cike 3 month kaga dai aiki aka min kai kuma abu ba ka
an ba idan kayi min shigar sauri fa zan iya mutuwa yayi saurin zaro mata Idanunshi yana toshe mata baki da bakinsa sai da yayi dogon zango sannan ya cire ya busa mata numfashinsa "shinkenan na hakura dan bazan juri zama a duniya babu ke atare dani ba, ta kashe masa ido tana kising bakinsa "nima hakan take gareni da kai kadai zan karasa rayuwata kiss daya tayi masa amman shi yayi mata ya kai goma gbdy a hannu yake "to kiyi min dabara na dan samu natsuwa suna rungume da juna mumy ta sanyo kai da sauri ta juya qirjinta na bugawa da matsanancin karfi duk da ba wani abu taga suna yi ba iya kiss ne a ranta tace "kai gara nazo na tattara na bar kasar nan da alamun dai yaran nan sun gaji dani ".
*****
bangaren nawal dai abubuwa sun cigaba da rikicewa dan tana gidansu zaune har lokacin bata ga tsuntsu bata ga tarko , bata ga aikinta bata ga komawa gidan muradi duk da tana samun biyan bukata daga iyayenta amman da kaganta kasan bata da natsuwa da kwanciyar hankali, kullum cikin kuka da damuwa take ta damu iyayenta akan suje gurin dady ko mumy tasan muddin suka je zasu saka baki magana daya zasuyiwa muradi zai maidaita gidansa cikin wannan lokaci mumy ta koma Nigeria tace sa biyota a baya dan bazata iya da rashin kunyarsu ba a fili suke nuna maitar junansu mumy na barin kasar
suka bude sabon babin soyayya tare da diyarsu mother suna son mother tamkar basu ta
a haihuwa ba ,soyayyarta ta zarta tasu aryan watanta uku a duniya amman sarai take ganin mahaifinta da zarar taji muryarsa ko baya nan ko ta cikin waya ne aka saka handsfree yanzu zaka ga tana raba idanu a haka lokacin yaci gaba da tafiya al'amura na cigaba da daidaituwa cike da qaunar juna dan gaban kowa muradi yake nuna ma kisna soyayyarsa tana tsaye goye da mother tana jijigata ya shigo ya tsaya bayanta yana kallon fuskar diyarsa mafi soyuwa a rayuwarsa sannu da zuwa tayi masa ta amshi briefcase dinsa ta nufi d'aki ya biyo bayanta yana cire yar saman suit dinsa , ta kwanto mother ta kwantar daita akan gado ,hajiya kisna sannu da hidimar gida data mamana ,hajiya ? ta furta a kasan ranta a zahiri kuwa cewa tayi " yau kuma salon sakonar ta nan ka bullo ? "
"Babu wani tsokana daga yau kin tashi da zallar kisna ko baby love kin dawo hajiya kisna ko hjy baby love ki shirya bana damu za'a sauke farali nan da 2 week's Kuma zamu bar kasar nan zuwa saudia muyi umara idan mun gama daga nan zamu wuce Nigeria dan daga nigeria zamu dawo aikin hajji cike da farinciki ta rungumesa ajikinta , muradi ba dai zurfin ciki ba sam baya fadan abinda zai yi sai idan lokacin yayi ya aiwatar , wannan na cikin abinda yasa yake qara samun matsuguni a zuciyarta addaur ta shiga yi masa shi da mahaifiyarsa cike da kulawa da qaunarsa sannan ta tayashi cire kayansa ya shiga wanka kafin ya fito, ta fito masa da kayan shan iska farare sol wando da riga ta feshesu da turare ya fito daure da towel tana ganinsa ta karaso garesa ta dauki karamin towel tana goge masa jiki "kina ji dani sosai fa wanda hakan ke
ara min soyayyarki ,"dole naji da kai, kai din dan lelena idan ina tare da kai komai nice zan maka bazan yarda ka sha wahala ba , bayan sati biyu suka ziyarci kasa me tsarki zuciyoyinsu cike da farinciki mara misaltuwa ,
suna kare umara kisna da muradi suka fara shirin dawowa kasar haihuwarsu lokacin diyarta nada wata shida a duniya ."
kwanansu hudu da dawowa nigeria amman har lokacin suna fama da 'yan taya murna, satinsu biyu suka gama watstsake gajiyarsu suka ware sati daya don ziyarar yan'uwa da dangi da abokan arziki kowa ya gamsu sai yayi farinciki sun zaga dangi sosai cikin yan kwanaki inda suka yada zango a gidan aunty ummi ,aunty ummi taji dadi cike da farinciki ta mika wa kisna hannu "babu ruwana daku ku bani mamana mu gaisa tukun dan fushi nake daku dan wulakanci nice karshen zuwa kawowa ziyara bayan da kuka dawo nice farkon zuwa "kai aunty ummi ni dai kina da fushi dani dan ba laifi bane laifin dan'uwanki ne shine yace abarki a karshe ta karasa maganar tana mika mata mother tare da gantsarewa sakamakon mintsinta da muradi yayi mata a bombom dinta ta juyo tana kallonsa kamar bashi yayi ba ta sakar masa harara shi kuma ya kashe mata idonsa
aya aunty ummi ta nunawa takwarar mumy soyayya wuni guda sukayi sannan suka baro a gidan akan hanyarsu ta komawa gida taga muradi ya tsaya a bakin titi ta kalleshi domin jin karin bayani sai gani tayi yayi warning glass din motar bangaren da yake "kalli can kiga wani abu ya nuna mata hannun da yake nan take idanunta ya sauka akan musa yayi baki sosai yayi muni idanunta sanye da farar jallabiya oversize gbdy taji ta muzanta agurin "ga naki baby love ....." shiru tayi kawai tana kallon musa tana tsanar kanta da irin rayuwar data yi dashi abaya tafiya yake cikin maye yana cilla
afarsa duk inda yaga dama yana surutai da alamun ma brain dinsa ya fara samun matsala da sauri ta dauke kanta akanshi zuciyarta na wani irin tsinkewa muradi ya rufe glass yaja mota tare da daure hannunsa akan nata batare daya ce mata komai har suka karasa gida kuka take sosai tamkar wacce akayiwa mutuwa da misalin karfe takwas na dare muradi ya shigo ya tsaya akanta "wai kukan na meye hk ?ta girgiza masa kai alamun babu komai ya zauna a gefenta ya kamo hannunta ,"ko kina bukatar taimaka masa ne ?,ni ba wannan ba rayuwarsa ta bani tausayi ta k'arasa maganar tana kuka, ki daina kuka saboda shi din ba abun tausayi bane abinda ya shuka yake girba ko hakin yaran daya bata wa rayuwa bazai barsa yayi rayuwa me dadi ba kin manta abinda ya faru jiya ki fuskanci yau ya karasa maganar yana rungumota jikinsa yana shafa bayanta
..."
muradi ya shawarci samir domin su ginawa iyayensu sabon gida , da fari yaso ya gidana shi kadai ne ,sai kuma ya ga gara suyi tare tunda komai nasu tare suke babu mutsu samir ya bada tarin kudi masu yawa suka siya makeken fili a abulegba aka fara ginawa mumy da dady cikin lokaci muradi da kisna suka tsallake zuwa kasa me tsarkin dan sauke farali suka bar mother gurin mumy , cikin wata uku kacal akayi komai aka gama mumy ita kadai sai mijinta da yan jikokinta suka tare acikin tamfatsetsen gidan da
anta suka mallaka musu shi kuma tsohon gidan mumy tace a gyara a rufe kofar da zata kai mutun bangaren ya badamasi sai a zuba mutane marasa karfin babu bata lokaci suka aiwatar da umarnin mahaifiyarsu tun da kisna tazo taya mumy murna tarewa a sabon gida taki komawa gidanta yan'uwanta duk sun koma ranar data cike sati daya sai ga muradi da daddare yazo ,ta kallesa ta kunshe dariya dan daman jikinta ya bata tana kokarin shiga dakin mumy yayi wata super ya cafkota ya had'eta da jikinsa "wato ke kinsan ta kan mugunta kou ai kuwa zaki jiki wallahi "am really sorry daman gobe nake cewa zamu dawo, kinsan Allah daga nan bazaki ko'ina ba sai gida dan na gaji da zaman kadaici ni kadai a gidan kamar wani maye ko'ina yayi min shiru babu dadi ko ka
an ,ta kwashe da dariya" to ka bari na shiga na dauko mayafi na ya kalli kan kujera inda hijab din mumy yake ya nuna mata da baki "to bari nayi wa mumy sallama "shi kuma rantsuwar da nayi fa babu yadda ta iya ta dauki hijabi din mumy ta zira shi kuma ya saba mother a kafad'ansa ya kwashi iyalinsa sai gidan suka bar mumy dasu aryan dan suma yanzu basu qaunar barinta suje wani guri ko sunje kuwa basa iya bacci sun fi so sujisu a karkashin kakannensu kamar yadda ta sabar musu ."
gida daga su sai mother hakan yake basu damar cin karensu babu babbaka dan kullum ganin junansu suke tamkar sabon ango da sabuwar amarya Allah yayi musu kyakkyawar turba, a yanzu kisna ta zama mudubin gidan muradi baya ganin kowa a gabansa sai ita bama gidan ba hatta family dinsu kowa cikin qaunarta yake daman ita ce damuwarsu , yanzu kwanciyar hankalinta ya kwantar da nasu ,
kullum cikin sa albarkar iyaye take musamman mahaifinta ji yake kamar ya bata rayuwarsa a dalilin farinciki da take bawa muradnsa mahaifin nawal ya kira muradi yafi sau babu adadi amman bai daukan
kiransa
nawal ta fashe masa da kuka dady "nace maka ka nemi iyayen goyonsa wallahi nasan zai maidani nifa da shi kadai zan iya rayuwa idan babu shi mutuwa zanyi tunda mahaifinta ya runtse Idanunshi bai bu
e ba yana taya diyarsa bakinciki da jimami
yana matukar son nawal a rayuwarsa
kasamcewar ita
kadai ce lafiyayyen acikin yaransa babban dansa nakasashene komai sai an yi masa diyarsa ta biyu halima ta dade da mutuwa gurin haihuwarta ta biyu sai nawal shiyasa ya dauki dan duniya ya daura mata sam baya son damuwarta yaso ta hakura da muradi ne ta samu wani ta amman tunda ta nace babu yadda zai yi dole ya nemi alhj realwan ."
a lokacin mahaifin nawal ya nemi dady domin ayi sulhu yace babu komai komai ya wuce ta shirya dawowa d'akinta cikin satin waya kawai dady yayi wa muradi yace babu komai ya amince amman yace ya tainakesa
ya fadawa
kisna da kanshi
dan shi bazai iya
fada mata ba "kenan tsoronta kake ji ?"a'a dady bana dai son ganin bacin ranta ne to shinkenan kazo min daita yau da daddare suna gama waya ya kira afra yace tazo itama
yana son ganinta ."da misalin karfe takwas
suka kamo hanyar zuwa gidan dady ,kisna ta kalli muradi taga duk baya cikin farinciki ransa a hade "wai lafiya kuwa tun d'azu nake kallon yanayinka wani iri ?,babu komai ya fada yana damke hannunta cikin nashi
ya
an waigo inda take ya sakar mata laulausan murmushi suna zuwa suka iske ya badamasi zaune yana jiran fitowar dady hannu muradi ya bashi suka gaisa cike da girmamawa haka ma kisna ta gaishe dashi suka zauna byn kmr minti biyar sai ga dady ya fito sanye da jallabiya gbdy suka hada baki gurin gaidashi ya amshi mother yana mata wasa ko cikakken minti goma dady bai yi da zama
ba sai ga afra duk ta rame tsufa ma
ya fara
bayyana ajikinta ,nan take ta sha jinin jikinta ta durkusa har kasa ta gaishe
da dady suka gaisa da kisna batare da sun gaisa da ya badamasi da muradi ba a ganinta tunda basa sonta meye amfanin gaisawa dasu ? ."
Falon ya dauki shiru can dady ya kalli afra "kenan har yanzu bakwa gaisawa da yanuwanki?shiru tayi ta kasa cewa komai numfasawa yayi kana ya kwantar da mother akan kujera a nan kusa dashi saboda bacci ya soma
aukarta ya kalli ya badamasi da muradi sannan ya fara magana a natse cike ban tausayi " hakuri dai da
kuke ganinsa wani abu ne da yake da falala a addinin musulunci , kusan babu abinda ya kai shi falala saboda Allah subhanahu wata'ala da kansa yana cewa "
Lalle masu haquri za'ayi tacika musu ladansu acikin mizanin batare da hisabi ba, duk lokacin da wani bala'i ya fado wa mutun ko kuma a kayiwa mutun wani abu mara dadi amman ya mallaki zuciyarsa yayi hakuri kuma yayi hakurin nan saboda Allah to zaayita rubuta masa lada har iyaka yadda Allah yaso shine abinda Allah subhanahu wata'ala yake nufi me hakuri kadai yake samun irin wannan ladan babu wani aiki da mutun zai yi da za'a yita bata shi lada batare da lisafawa ba ,badamasi ka duba kaga muradi bani na kawo shi duniya
ba yau an wayi gari na kiransa
umarni na bashi na
ya maida matarsa nawal kuma kai tsaye babu ja inja babu jayayya yace min to amman Kai dana haifa yau tsawon shekaru hu
u kenan ina binka tun daka saki afra amman daidai da rana daya baka taba amsa min da zaka mayar daita shin byn laifin data maka akwai wani laifi ne ?yayi shiru yayi
kasa magana " kisna ta kalli muradi da sauri fuskarta da alamar
tambaya da kwayar Idanunshi yayi mata magana ta zagmasa harara tana kawar da fuskarta "ko kisna da tayi
mana laifi ta 'bata mana rai
ta musguna mana ta nuna mu din ba komai bane,
ta wulakanta mijinta ta tozartashi yau gata a karkashin mijinta sun cigaba da rayuwa me yasa bazaka yafe mata ka dawo daita ba ?dady ya karasa maganar yana
arin zubar da hawaye atare suka dawo gabansa gbdy suna kuka har afra "kayi hakuri dady ka daina masa maganata wallahi na dade da cire zan sake zaman aure da ya badamasi ,dady ya shiga girgiza masa kai "yana tausayinta yana tausayawa iyayenta shekarunta na tafiya duk sauran yan'uwanta suna gidan
mazajensu "ni dai nafi qaunar ganinki a karkashin ikonsa idan har zai iya min wannan alfarma" zai mayar daita a gobe nan
tunda haka shine farincikinka numfashi dady ya sauke sannan ya mike yana cewa kisna ta biyosa , ta shiga d'akinsa ta gansa zaune a bakin gado ta samu guri ta zauna a kasa qirjinta na luguden bugawa
"kisna mijinki zai dawo
da nawal sai dai yace yana gudun damuwarki to karki yarda ki nuna masa bai isa ba a gidansa, kada ki kawo masa hayaniya ko tashin hankali ki zauna lafiya da abokiyar zamanki ,idan ma bata biki ba ke ki bita ku zauna lfy ba wani abu bane duniyar ma guda nawa take nasiha sosai yayi mata mai ratsa jiki tana kuka har da shesheka ita ba dawowar nawal din ne bata so ba tashin hankali take gudu dan sam bata ga ta inda take son su zauna lafiya ba , gashi ita yanzu ta saba da rayuwa ita kadai da mijinta .."
acan falon ma muradi tashi tayi ya shiga dakin mumy ya bar afra tana kuka ,ya
badamasi ya
tsira mata ido yana kallonta
tana kuka ",kin cire rai da zaki sake zaman aure dani saboda
bakya sona ?'ta d'ago idanunta a hankali ta tsura masa sai dai ta kasa bashi amsa illa ta mike ta juya ta fice a falon yana zaune yana kallon bayanta dan dole zai maidaita ko babu darajan Iyaye shi kansa danne zuciyarsa kawai yake amman akwai soyayyarta
me karfi
a cikin zuciyarsa ."akan hanyarsu kisna ta komawa gida kuka kawai take muradi na rarrashinta tace"
taji amman kafin nawal ta dawo ya gyara mata saman gidan ta koma yace an gama ranki shi dade duk abinda kika ce shi za'a yi ko cewa kika yi baza'a dawo da nawal ba dole ne
a bi dokar uwargida sarautar mata
"ka jika kamar idan nace zakayi
ne ?,zan yi mana me zai hana da a min rikicin gangan gara nabi doka da oda
cikin satin yasa aka gyara mata sabon bangarenta itama nawal ya gyara mata part dinta na da ranar lahadi aka tsara zaa mayar da
auren nawal da muradi ya bada da afra amman sam afra taki sai na nawal da muradi aka mayar
kuma
a ranar ta tare da Ahmed dan yayarta
sai
dai ta dawo gidan ne da shirin zama na dindindin babu tashin hankali har gida mahaifin nawal yazo yayiwa
dady
godiya bisa karamcin da yayi masa dady yace ",babu komai ai an zama daya nawal diyata ce har abada Allah ne ya hadasu da dana dana fi so kuma take qaunarsa kaga dole ne nima na sota." Haka ne Allah ya sake ha
kansu sai abu na gaba
Ina neman wata alfarma mahaifin nawal ya fada dady ya fuskancesa ,
akan maganar aikin nawal kayiwa yaron magana domin itace ke kula da wasu daga cikin kasuwancina na kasashen duniya
shiru dady yayi har sanda
ya dasa aya sam baya jin muradi zai amince dan ko kisna da take gabansa a yanzu
bai ji yana maganar zatayi aiki da takardunta ba bare aikin kasa da kasa ,bari dai
na kirasa inji cewar dady
nan take dady ya kirasa yayi masa bayanin komai shima muradin shiru yayi yana mamakin hauka
irin na mutumin sai daya numfasa sannan yace "dady zamuyi magana da nawal din abinda ake ciki zata masa bayani ya tsaya sai dady
kashe
wayar
tukuna
yana jinsa yana yiwa mahaifin nawal bayani
a hankali ya
shiga part
din
nawal
jikinsa sanye da wando jeans baki da riga dark green yayinda kafafunsa ke sanye da takalmin canvers baki haka ma kansa facing cap ne baki
tana
ganinsa ta soma bare baren neman gindin zama ya zauna yana
dubanta
ta tsiyaya masa
ruwa acikin glas cup ta mika masa bai ki amsa ba,
sha
mika mata
"da zamuyi aure a tun farko
munyi
alkwari dake cewar zaki ci gaba da yawo kasashen duniya ?tayi saurin cewa a'a ,to me yasa yanzu mahaifinki yazo wa dady da batun ?gaskiya ban sani ba amman zan kirasa ,well wanan ya rage naki idan zaman aure zakiyi idan yawon kasashen duniya sai ki zabawar kanki
yana gama fadar haka ya mike ya fita ta sauke naunayen ajiyar zuciya gara tayi zaman aurenta ya fiyye mata alkhairi dan babu komai acikin yawon zuwa kasa da kasa sai zubar da mutunci ka dinga cudanya cikin maza zuciya kuma bata da kashi
nan take ta kira mahaifinta ta sheida masa ita zaman
aure
zatayi
ga lawan idan ya qara tasawa ya maye gurbinta lawan dan farin yayarta halima ne yana daf da karasa karatunsa a London ."
****
Babu
laifi kisna ta dan sakarwa
nawal
fuska, nawal na zuwa saman kisna itama tana zuwa nata sai dai ita kisna bata fiyye zuwa ba gaskiya sannu a hankali suka ci-gaba da rayuwarsu tana jan su aryan ajiki sosai a duk sanda suka zo gidan zata dinga haba haba dasu tana nuna tana bala'in son su din nan, barin ma idan akwai idanun mahaifinsu haka ne yasa muradi ya fahimci sauyawarta kuma yayi farinciki , duk kuma lokacin daya shigo da mother zata amshi yarinya tana mata wasa idan yana bangarenta tare zasu wuni itace komai nata muradi ya cigaba da daukar nauyin karatun
Ahmed dan shekara bakwai yana
mata fatan samun nata , tafiya tayi tafiya shekarar
mother biyu
kisna ta samu ciki wanda ita kusan bata so haka ba sai dai tayiwa kanta alkwarin bazata sake cire ciki ba haka zalika bazatayi planing ba zata haifi abinda Allah ya qaddaro mata dan tasan mutuwa da rayuwa duk na Allah ne , ai
nawal na
fahimci tana dauke da ciki nan kishinta ya motsa ta soma shan kamshi , ta daina zuwa bangaren kisna
a lokacin data fi bu
atar taimakonta
ko haduwa sukayi sai tana jiran
kisna ta gaisheta ita kuma idan tayi yau tayi gobe sai tayi mata ba sai hakan na neman ya kawo gaba a tsakaninsu amman hakan kisna ta
dauke kanta ta cigaba da tsagoginta dana mijinta dan gbdy ta gano abinda yasa ta sauya har ma akan yaranta idan sun so idan babu idanun ubansu ko kallo basu isheta ba Amman da zarar ta gansa zata fara rawar jiki ."
akwana a tashi babu wuya har cikin kisna ya kai wata
shida alokacin ta dan
samu lafiya ,ya fito
abin sha'awa sai yayi mata mugun kyau yayinda nawal kullum idan ta kalli kisna da ciki sai zuciyarta ta motsa
tayi
kukan zahiri dana bani di, cikin take so ta kowani hali
amman yaki zuwa wata kanwar mahaifinta ce ta samo labarin me magani haihuwa a Sudan ta hanyar wata kawarta dan haka ta sanar da mahaifiyarta nan fa suka sheidawa muradi bai hanasu ba dan shima yana son Itama tasamu nata
, sun isa lafiya ta sha magani iri iri an basu wani da alkwarin tana dawowa sai ciki satinsu biyu suka dawo da takamar nan da wani lokaci zata haihu sai dai har wata uku wanda yayi daidai cikin wata tara
bata samu
Cikin ba ,cikin kisna ya tsufa
sosai suna jiran edd dinta sai dai a daren wata laraba ta tashi ciwon nakuda daman tun magrib tana jin ciwo sai dai tunaninta ai lokacin da'aka bata bai yi ba shima gogan yana lura daita idan yaga ta cije sai yace "yaya dai baby love kodai zamu hospital ne ?sai ta yatsina fuska tace babu komai fa ta tashi da kyar ta sauko daga kan gadon ya tashi shima ya taimaka mata ta sauko yace ",ina zuwa ?fitsari zanyi ya riketa suka shi ga toilet tana tsugunawa taji kamar an sauko mata da ciwon duniya ta hau nishi nan muradi ya rikice ya fita aguje ya kira aunty ummi
ya shiga ya taso nawal
ta tashi
Itama a rikice ta biyosa yaje ya fito da mota shida nawal suka riketa
suka sata a mota duk dauriyarta sai da hawaye ya zubo mata tana salati tana cewa akira mata mumy da dady shima idanunsa ya fara cikowa da hawaye sai zabga gudu yake yana mata sannu gudu yayi sosai atare
suka isa asibitin da aunty aummi
ai yana gama parking ya fito
sai
aukarta yayi dan kasa tafiyar tayi dan kafafunta sun rike sai ciki a gaba daya sauko kasa aka shiga daita labor room
mintina Kadan doctor ta fito dake sun san aiki za'a yi mata suka fara shirin aiki ana aka mata shirin aiki ai ana shirin shiga dakin tiyata daita tayi wani nishi sai ga kan da karasa shiga daita akayi ta haihu da kanta likitoci kansu sun jinjina wannan
girman al'amarin na
Ubangiji
murna kuwa agurin muradi kamar ranar aka fara haihuwa a gidansa kudi masu yawa ya dauko ya bawa nurse din data masa wannan albishir nan ya zaro waya yana fadawa mumy , madala mumy tayi a waya tana wa Allah kirari tace gata nan zuwa yace mumy shabiyu
dare yayi tace" kai gafara can in samu jika kace min inyi jinkirin zuwa cikin minti talatin direba ya kawo mumy alokacin har an gyara kisna tana dakin hutu ita da kyakkyawar diyarta sannu da kokari baby love Allah yayi miki albarka abinda muradi yake fada kenan ita dai sai murmushi take ita kanta cikin tsananin murna take ta haihu da kanta "..
washegari gari aka sallameta byn an tabbatar da babu wata matsala da sassafe sai ga su aunty
mufeeda
ta zo tare da aunty Zahra har ma da afra
kafin yamma gida ya cika makil
da dangi ranar suna kowa yayi tunanin sunan mahaifiyarsa zai sa wa baby sai kawai sukaji sunan aunty ummi Aisha murna har da rafka buda tayi ,suna na kece raini akayi kuma me kayartawa
kaya iri daya muradi yayi musu ita da nawal byn suna kowa ya watse aka bar aunty ummi sai da tayi sati sannan ta koma gidanta
haka da rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi da kwanciyar hankali agurin kisna ,kisna ta gina gidanta cike da ni'imar qauna soyayya da kwamciyar hankali wanda kula da junansu da kulawa da soyayya shine ya haifar musu da haka kowannensu na kokarin sauke hakin dan'uwansa tare da kyautatawa , duk abinda kisna tagani na maza muddin yayi mata kyau zata siya ma muradi
tunda yanzu da kudinta wanda kasuwanci ke kawo mata ga gidan mai ga supermarket da mijin kwarai ya mallaka mata
har karshen rayuwarta babu shakka mijinta kyautar Allah ne
shekarar Aysha daya da rabi ta sake haihuwar namiji shima da kanta yaci sunan Aliyu suke kiransa da papi nawal ta dauki soyayarsa papi ta saka aranta komai ta samu papi ne ita kuwa kisna ido ne nata duk har cikin ranta bata son nawal din na shiga tsabgar
anta tunda ta lura soyayyar bata Allah bace ta ganin ido ce ."
Bayan shekara shida a lokacin kisna nada ya'ya biyar aryan arif ,mother da aisha mai sunan aunty ummi papi mai sunan muradi ga wani sabon ciki ajikinta yayinda har lokacin ko batan wata nawal bata ta
a yi ba kullum dai tana kan yawon neman maganin haihuwa bata hospital bata ga na gargajiya
muradi ya tabbatar mata lokacin ne ta kwantar da hankalinta muddin tana da lafiya kuma spam dinsa ke dinga ya'ya a cikin kisna itama zata haifi nata duk sanda ya fada mata haka jinsa kawai take dan gani take bai damu da rashin haihuwarta ba tunda yana da wasu ya'yan .
Ranar wata laraba aunty zee tazo duba jikin kisna dan laulayi ya fara sakata gaba suna zaune tace "ke dai kisna abun yayi miki yawa ga laulayi ga wahalar nakuda ,to ya zanyi aunty zee?
qaddarata kenan Allah dai yasa muci amfanin ya'ya ameen aunty zee ta amsa ya kuwa zamanku da nawal babu wata matsala ko ?,to gaskiya dai matsalar da sauki sai dai ta iya makirci ni kuwa bana ma son na iya ,ai makirci bai yi ba a zaman aure ace sai da makirci ai mugun abu ne kowa dai ya zauna da halinsa ,ato zan zauna da halina bazan koyi halin banza ba sbd wata
kishiya yanzu ko bako mukayi zai dauka nice mara kirki ni muguwa ce ina mata mugunta sai ka karanci halinta tukun zaka gane ta ko abu ta siyawa yaran bata bani ba sai taga idanun mijinta zaki ganta ta shigo suki suki cike makirci a hau basu ,
Kinga last week muna zaune ya tambaya ko yaran suna da sababbin kaya da wanduna ingaya miki kafin nayi magana ta tsigil " wai suna dashi akwai waondunan da basu saka
ba ,na
kalleta na hade rai nace" ni dai babu wandunan da basu saka ba duk sun gama sakawa
sai cewa tayi "Ahmed dai na da wanduna
sababbi ina
kallonta ta gama kirge kirgenta
dana ga zata bamin lokacin na barta ita dashi
na wuce ina zan iya ga magana kmr aku kuturu ga makirci
"Allah
ya kyauta yasa ta gane ,ameen suka ci-gaba da hirar duniya wata tara kisna ta sake haihuwar namiji yaci sunan ya samir aunty ummi ta
saka
masa
mahbub
amman ita
kisna dan uwa take kirasa
*******
Kisna
na zaune a falonta sanye da riga da wando na
bakistain farare sol kanta babu dan kwali gashin kanta dake cikin gyara kullum sun zubo bynta , yayinda mahbub ke kwance a gefenta
yana shan hannu ,sauran yaran suna
kasa suna wasa sai mother dake gefenta tana nuna mata assignment sai
ga nawal ta shigo
kamar zata fashe
tana kunfar baki
"nace a kawo min mahbub
kince kar akawo min Allah yasa dai ba cinyasa zanyi ba sannan ba wani abu zan masa ba bare kince kar akawo shi ,ni bansan kince a kawo miki shi ba amman gashin nan yanzu idan zaki wuce ki tafi dashi inji cewar kisna ta fada tana dauke kanta ta maida kan assignment din da takewa mother ,
"bazan tafi dashi ba me gindin haihuwa dan na lura baki qaunar ganin yayanki angurin Allah yasa ba wani mugunta nake masu tsam mother ta mike ta shige dakinsu ta kulle dan sam kwakwalwarta bata son hayaniya haka bata son ana ihu
brain din zafi yake mata."
kisna tace
"naji ni me gindi
haihuwa
ce idan fitsari banza ne kiyi mana ko ni na saki shan maganin kwayoyin hana daukar ciki da kike yawon kasashen duniya , ki haihu mana ko na
hanaki
ne ,Allah ne ya bani kuma kema zai baki idan kin tsarkake zuciyarki
kin cire mugun nufin dake ranki ,kaji min shegiya munafuka makira mata
duk yadda nake kauce miki sai kin nemi sani magana, ban san me kawo
wannan kananan maganar bare har kice
min me gindin haihuwa yaro ne
nace gashi nan idan zaki tafi ki wuce dashi ko bashi kenan ba amman dake ke din makira ce sai da kika nemi fada min magana duk take taken ki fa
ina sane fa kawai dai na zuba miki ido dan bani da lokacinki, Idan kinga miji ki dinga nan nan da ya'ya kina nuna wai ke kina sonsu alhalin ba haka bane acikin zuciyarki daga yau ma karki kara taba min ya'ya muna fuka kawai wahalalliyar sai faman lashewa miji takashi kike amman bakya gabansa suna cikin haka muradi ya shigo aiko nawal na ganinsa ta
fashe da kuka tana cewa "daga abun arziki zai zama na tsiya norr kaji fa daga na aiko ta bada mahbub
akawo min shine tace...."shine nace me ?
ki shiga hankalinki
nawal , haushi ya kama kisna ganin tana kukan makirci daga yau kika sake jefa min magana sai na miki rashin mutunci na cire miki bakaken hakoran nan me katon baki kawai
aiko
nawal ta sake rushewa da wani
kuka kamar wacce akace uwarta da ubanta sun mutu kisna ta bude baki kenan zata sake wanketa muradi yayi saurin daga mata hannu a tsawace "karki sake cewa komai anan ya isa .
ya kalli inda nawal dake tsaye tana kuka "ke kuma idan daukarsa zaki yi daukesa ki wuce tsabar mubafurci irin na nawal nan take ta hau goge hawayenta tasa hannu ta dauki mahbub
dake kwance
ta fice muradi ya k'araso ya riko kisna ya manneta da qirjinsa yana tafiya daita a hankali ya nufi d'akinta daita yana shiga ya zagaye hannuwansa a cikinta yana magana kasa kasa kmr me koyon mgn "haba kisna ban sanki da haniya ba banason kina yiwa nawal iyaka da yaran nan ita din abar tausayi ce ki dinga mata uzuri kinji , koda nawal ta girmeki amman kece babbar acikin gidan nan kin fita experience din rayuwa saboda kin haihu ita kuwa duk girmanta bazata qarar da wani abu daya danganci hakan ba , amanar gidana tana hannunki ko ina nan ko bana nan duk abinda nawal tayi miki ki sanar dani kafin ki dauki mataki , shiru tayi kawai tana sauraronsa ya numfasa tare da juyo daita
suka fuskanci juna ya tsira mata ido yana kallonta cikin tsananin qaunarta ta bala'in hade rai kamar an aiko mata da sakon mutuwa har tasa gabansa faduwa sai dai haka yayi karfin halin cewa"ko babu komai hayaniyar nan zatayi affecting din mamana tana ina banganta ba ?da kyar ta bude baki" tana dakinsu ki qara hakuri akan wanda kike yi .
Ya zauna tare daita
"idan kin gama abinda kike
ki shiga dakina akwai wasu kayana da'aka kawo daga gurin wanki ki kai min part din nawal tafiya ta kamamu gobe zuwa spain nida samir gobe 12:dot jirginmu zai tashi yace ta kai wa nawal ne dan part dinta yake itace ya dace ta ha
a masa kayansa har ya gama maganarsa bata ce masa qala ba ganin taki cewa komai yasa shi juyawa ya fita zuwa dakin su mother tana kwance ta takure jikinta guri daya ta toshe kunnenta da hannuwanta tsura mata ido yayi na wasu mintuna yana matukar qaunar diyarsa zai iya karar da rayuwarsa akanta gyara mata kwanciya yayi sannan ya sauko
ya shiga gurin nawal
ta kwantar da mahbub
tana wani irin kuka idanunta yayi ja saboda zagin da kisna tayi mata Ahmed yana zaune yana
goge mata hawaye ta kamosa ta rungumesa ajikinta muradi ya k'araso cike da sanyi jiki ya zare Ahmed ajikinta "ahmed jeka falo kayi kallo kaji
yaron ya fita daga dakin muradi ya zauna a gabanta
"haba nawal menene abun kuka nasan kina kuka ne
dan baki haihu ba
kiyi hakuri kema inshaallahu naki yaran na zuwa nan kusa , zaki haifa min mace zaki haifa min namiji komai lokaci ne amman ki daina fadawa kisna duk maganar datazo bakinki saboda kinsan bazata kyakeki ba tana da hakuri da kawaici amman bata daukar irin wadannan abubuwan ya k'arasa maganar yana rungumeta har magarib ta shigo suna tare yana rarrashinta da fada mata kalamai masu kwantar da zuciya suna zaune a falon suka ji knowcking "waye? inji cewar nawal kisna tayi shiru, har nawal
ta mike tsaye muradi yace ta koma ta zauna ya mike ya bude kofa kisna ya gani tsaye cikin
riga da wando
ba irin wacce ya gani d'azu ajikinta ba , sai kamshi take tana sheki
,nazo daukar yaro na
ne tunda ba'a ga ya dace akawo
min shi ba."
Muradi
yayi shiru yana kallonta kafin daga bisani ya juya ya daukosa ya saba a kafad'ansa nawal na ganin haka ta fahimci kisna ce ta ta'be baki a ranta tana cewa" aikin banza
kawai
ki dai bari na fara haihuwa zaki sha mamaki ,muradi ya fita ya mika mata mahbub
har ta juya ya janyota ya rungumeta tare da yaron ,"dan Allah ki
an saki ranki mana kin fa san idan akwai abinda na tsana bai wuce fushinki ba Please baby love
ki saki ranki ,naji ta fada a takaice tana zare jikinta
ya manna mata wani hot kiss guda biyu sannan ya saketa ta juya yabi bayanta da kallo har sai daya daina ganinta
Washegari karfe tara
ya fito daga part din nawal cikin shirin tafiya ya shiga na kisna lokacin tuni yaranta sun wuce school ta gyara ko'ina sai kamshi airfresner yake tana sanye cikin dinkin atama riga da siket puppy
da ratsin fari jikinta sai wani sihirtaccen kamshi yake fitarwa tana ganinsa ta mike tsaye ta rungumesa tana sakar masa Kukan shagwa'ba zuciyarta tayi matukar rauni dan bata so abinda zai nisanta ta dashi , ta kasa sabawa da tafiye tafiye da yake duk sanda zai yi sai taji wani iri a zuciyarta
kissing dinta ya shiga yi babu kaukautawa ,baby I will miss you ,"I will miss you too ta fada ranta a jagule ji tayi kamar ya fasa tafiyar , dan Allah ki daina kukan nan idan kina zubar da hawayenki zan tafi zuciyata cike da damuwa wayarsa ce ta dauki kara ya ciro ya duba sunan Samir ya gani ya mayar da wayar ya
auketa
cak bedroom dinta ya nufa bisa gado ya shimfideta sannan shima ya hau gadon ya daura kanshi akan cinyarta yana shafa yatsun hannunta" zanyi kewarki baby love
irin sosai din ko zaki shirya mu tafi tare bana son nayi nisa dake ina tsananin qaunarki burina mu kasance tare a kowani hali ?ta sauke numfashi tana daura hannunta daya a sumar kanshi yayinda d'ayan hannunta ke gadon bayansa sai dai har lokacin bata daina masa kukan shagwa'ba wanda yake sake rirkita masa lissafi tun samir na kiransa har ya gaji ya daina dan yasan karsheta yana can gaban kisna yana faman aikin rarrashinta tunda ga nawal nan har ta fito masa da jakarsa."
ya cigaba da fada mata kalamai masu sanyi har sai daya ga babu hawaye ko daya a cikin idanunta sai dai hakan bai shi tashi daga kan cinyarta ba , daga qarshe ya tsurawa kwayar idanunta nashi idon cikin tsanani tashin hankali ''anya baby love ba haqura zanyi da tafiyar nan ba Samir ya tafi shi kadai ? ''da sauri ta girgiza kai tana cusa hannunta cikin sumar kanshi '' gara ka tafi tunda nasan abu ne me mahimmanci nayi maka alkwarin idan zaka sake tafiya zan bika ,Ina bazan yarda da wannan wayon ba
koda yaushe haka kike fada min 'dariya ya bata "shinkenan ka tafi da nawal ,okay haka ma zaki ce shinkenan bari naje nace ta ha
a kayanta kawai mu tafi tare ? ai tana jin abinda yace ta sake sakar masa kuka yayi saurin tashi yana hade hannayensu''is Okay ! ya fada yana kallon fuskarta yadda tasha kuka sai yayi sha'awar tsokanarata
'"ga tsoro ga ban tsoro ta baba me gadi
kina mutuwar son muradi kina wasa dashi ta kaiwa qirjinsa dukan wasa tana cewa"
kai ko Allah sai na fada wa dady ,tunda dai ba granny zaki fadawa
ba ai da sauki dan itace zata hadiye zuciya ta mutu tsabar kishi ta matsoshi sosai kamar zata shige jikinsa , Allah zanyi kewarka ,nasani baby love rabuwa da masoyi akwai ciwo Amman karki damu 2 0 7 muna tare akan waya
idan kuma na kira ban sameki ba shinkenan na hakura tayita kiran nawal muna shan soyayyarmu ''yayi maganar cikin salo tsokana ,tashi tayi
ta fara bubbuga
kafafuwanta cikin shagwaba, baya ya dan ja kana ya kama baki ''eyeeee naga fa alamar matar nan kina kishin wannan abar over fa ya fada still cikin tsokanarta yana shafa gaban wandonsa ,anya da gaske bazan fasa tafiyar nan na zauna mu cgaba soyewa ba ?haka yayita tsokanarta sam ya manta wani samir na jiransa ta fada jikinsa cike da kukan shagwa'ba ,shima bai
tsaya wata wata ba ya rungumeta tsam yana jin duminta da qamshin azababben turarenta mai tsayawa arai ".
"ki daina wannan kukan baby love Allah yana bala'in kashe min sana'ar jiki har yanayina ya fara canzawa tana jin haka ta zame jikinta ta fara share hawayenta yana tayata sai da yaga fuskar ta tayi fes sanann ya fara kising every part of her da kyar ta kwaci kanta ya kamo hannunta ya dauki hijab dinta ya saka mata sannan suka fito ta shiga kitchen ta dauki karami jaka wanda fararen roba ne set uku aciki dauke da cinci da dambun naman rago ta fito suka sauko tana kan kafad'ansa hannunta rike da karamar jaka suka jero har harabar gidan inda Samir ya cika yayi bammmmm kamar zai fashe ,bai damu da securities dinshi ko nawal da Samir dake tsaye ba ya sake kwakwame kisna
babu kunya kisna ta motso shi a haka har suka isa jikin motar da zasu tafi airport acikinta batare da ya kalli
Samir dake tsaye shida nawal ba yana zabga masa harara , sake janyota yayi ya mata kiss a kumatu da goshinta nan fa zuciyar nawal ta shiga rawa
kamar ta buga tsabar
bakinciki ruhinta yayi baki idanunta suka ciko da hahaye a hankali muradi ya saki kisna ya karaso
inda nawal take ya rungumeta ,yasa
an yatsansa yana
auke mata hawayen da ya fara silalo mata''no baby karki min hasarar hawayenki ya janyota gefe guda samir ya sake zabga masa wata
atuwar harara ya sakar masa murmushin gefen baki ,kisna ta hadiye wani abu taji ya tsaya mata arai ta fuskanci samir tare da juya masu baya dan bata son ganin irin sallamar da zai yi da nawal .."
"My baby nawal
karki karya min kwarin gwiwaa ,ki bar kukan nan haka, bari na gaya miki abinda zaisa ki yarda dani
'bakinsa ya sanya a kunnenta cikin kashe murya da iya salon magana tare da sace zuciya yace''ina sonki har yanzu kina cikin zuciyata burina na karshe yanzu bai wuce ki haifa min me sunan mahaifiyata ba.."wayyo Allah dadi kamar ya kashe nawal taji wani irin farin ciki ya mamaye ruhinta tasan muddin Allah ya amshi addu'ar sa ta haifi uwar masu gida soyayarsa gareta zata ninku ita dai burinta ya sota fiyye da kowa da komai,
ta daura kanta kan kafadarsa tana sakar masa dariyar farinciki ''na gode na gode!!
my norr wallahi ruhina yayi haske Allah ya amshi addu'arka itama tayi masa mgn cikin nata salon ,"ki sha kuruminki Allah ma ya amsa lokacin kawai muke jira ki hafawa hajiyarmu jikoki masu tsananin kama dani ''inshaallahu ta karasa maganar yana kissing dinta ''kaga malam ,idan ka fasa tafiyar nan ne ka gaya min na kama gabana , banza yayi masa yana sake bata hot kiss wanda
yasa Samir dauke kansa
kana ya kama hannunta yana fadin''ki kular min da kanki, zanyi kewarki sosai ''kai take daga masa tana murmushin farinciki har ya juya ya soma tafiya ya kawo daidai inda kisna ke tsaye ta kamo hannunshi ta sumbata , ita dai kisna na tsaye bata ce komai ba sannan bata sake yunkurin isa garesa ba dan ita bata cikin matan nan masu gasa da kishiya, dan ciwo taji ciwo a ranta tunda tana son mijinta kuma tana kishinsa ya kai bakinsa
daidsi kunnen kisna " zanyi kewarki bayan tafiyata ki kular min da gidana amanar komai tana hannunki "
har ya shiga mota shi da samir motocin suka ka yi gaba suna kokarin ficewa daga gidan
me gadi
na kokarin rufe get din gidan amnan
tana tsaye rungume da hannunta duk a qirji
ta kai minti goma tsaye sannan ta juya domin
komawa ciki
karaf idanunta suka sauka akan nawal tana sakar mata murmushi sam hakan bai dameta ba kuma bata jin zai zama hujja da zatayi fushi da miji
ba dan wani lokaci ka dauki lamuran makirci da kishiya take ka saka a ranka sai ta ha
aka da miji kuzo kuna samun matsala tana gefe tana muku dariya.