← Book details Auren Chochi Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 29

Sashe 8

Auren Chochi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan rasuwar maaifiyar Shi Anan yagaji arziki kasan cewan shikadaine 'danta Bayan rasuwarta Bada jimawaba maaifinshi yabita wato Shima Rai yayi halinshi Hakan yasa Gadon maaifiyar Shi Dana maaifinshi Duka yazamo nashi, Barrister Yayanke shawaran yin karatu Mai yawa tunda akwai kudinyin Cikin yardan Allah yasamu futa Kasar Chaina yayi karatu Bayan yashafe wasu shekaru masu yawa Yana karatu yayi nasaran gamawa DA nasara Mai yawa Hakan yasa Kasar Chaina tarikeshi sbd yamata aiki,ganin baida uwa DA UBA dazai dawo dominsu Hakan yasa ya amince.

Barrister yazauna tsawon 7yr Yana aiki DA Kasar Chaina Anan yayi gamon Katar DA matar aure Wanda takasance itama Yar Nigeria Yar jahar Bayelsa saidai itadin Cristian ce,batare DA Bata lokaciba ganin ba haramun bane amusulunci yasa barrister Ra'is ya auri Uju,Dangin maaifinsa Dana maaifiyar Shi Ko kadan Basu soba saidai ganin shidin marayane yasa Basu tauye mishi hakkiba Hakan yasa sukayi ruwa sukayi tsaki Har auren Barrister DA Uju ya tabbata.

Bayan anyi auren Anan Nigeria Cikin Jahar Bayelsa DA kano,Bada jimawaba barrister Yadauki matarshi suka koma Chaina.

Aurensu uju DA barrister Ra'is,DA shekara 'daya chip Uju ta aifo danta namiji fari TAS Kamar yadda take Fara tas irin farin IGBO wato inyamurai, jariri tubar kallah Dakagan Shi kaga ruwa biyu Igbo DA Hausa fulani wato Yaren Uwa DA ubanshi.

saidai hanci Kan DA tsawo Na maaifin shine, DAn Uju guntuwace saidai itama akwai kyau Babu laifi, Akan sunan yaro ansha artabu DA Uju inda tadage sunan kiristan zaasa Amman Ra'is yaki Daga bisani Ra'is yaradawa 'danshi Suna amasallaci Ahmed itakuma Uju ranar Suna tara'dawa 'danta Suna Obinna.

Ahmed Ra'is Obinna shine sunan DA yake rubuce Jikin takardun aihuwan Shi,Uju DA 'yan uwanta sukan kirashi DA Obinna Daddyn Shi Da 'yan uwanshi sukan kirashi DA Ahmed,Bayan Aihuwar Ahmed Saida yayi 6yrs aduniya kafin Uju takuma aifo Ibrahim Wanda Shima take kiranshi DA Abraham,Bayan Abraham taaifo Rahap Sai Auta Anitha,Uju tayi kokari sosai wajen ganin yayanta sundauko addininta yayinda Ra'is Ke kokarin yayanshi su kasance musulmai.

Akwan atashi Har yaransu suka Girma, Obinna Shikadai yakasance musulmi yayinda Duk 'yan uwanshi suka kasance kiristan,Lokacin DA Obinna yafara karatun jamiane Alokacin Daddynshi yayi ritaya yabar aiki DA Kasar Chaina inda ya tattara yanashi inashi yadawo Nigeria DA Zama saidai Maimaikon yakoma Kano Ina Ibadan yayada zango sbd Harkan kasuwanci daya fara.

Barrister Ra'is Wanda yazamo dattijo ayanxu Kuma Daddyn Obinna, shida iyalinshi
Dukkansu suka dawo ibadan, Obinna kadai akabari achaina sbd karatun likita dayafara.

Ahmed RA'Iz Obinna,shine cikekken sunan DA yake amfani dashi Ko aschl,saidai tuni abokai DA lecturer sun dauki sunan 'karshen DA ita suke mishi inkiya wato Obinna Cikin yanaki harya Fara Amsa sunan tunda yasan bazasu dainaba.

Cikin Ikon Allah dr ObinnaHar yagama karatun Shi tuni yasamu shaidar Zama cikekken ghanicologys Dr.

Dr Obinna
matashine kyakkyawa,son kowa kin Wanda yarasa, Mai tausayin na 'kasa dashi bugu Da Kari Allah ya 'daura masa kaunar addinin shi ta musulumci, Hakan yasa yake matukar kiyaye dokan Allah aduk inda yake, Haka family nashi Na uwa DA UBA ba karamin 'kaunar dr sukeba sbd always Yana Cikin musu alkairi, Momcy ND Dad DA Kannan Shi uku Wani madaran 'kauna sukewa Dr 'kauna bilhakki DA gaske,Shima dr Sosai yake fama DA 'kaunar family nashi infact Jiyake Zai iya sadaukar DA Duk arzikin daya mallaka sbd family nashi suji da'di.

Koda dr yagama schl Bai zauna Kasar Chaina ba tuni ya tattara komanshi yadawo Nigeria, dr kememe yaki Zaman Ibadan yace wa Daddyn Shi Lagos yakeso Abunka DA 'dan Gata Kuma 'dan gidan masu Hannu DA Shibu, nan DA nan Daddyn yasai mishi katuwar gida alagos Cikin anguwar Victoria Island.

Dawowar Shi keda wuya Daddyn yasai Babban Fili nan Cikin Garin lagos batare 'bata lokaciba akafara 'daura ginin asibiti,Wata biyu cur aka kammala Gina asibitin Daddyn Shi yagaiyaci manyan attajiran gwannati DA 'yan kasuwa aka bude katuwar asibitin Dr Obinna Mai Suna Wumen ND children Hospital, Asibitine Mai kyau Mai matukar Girma,Wanda Daddyn yazuba mishi kayan aiki masu kyau,Ko Acikin Lagos ba kowani asibiti suke dashiba,dr Obinna ya dakanshi yadinga intabiyu wa nurse DA doctors Dan tantance masu aiki bilhakki DA gaske tunda abune DA ran 'yan Adam,Bayan yagama 'daukan maaikata tuni yafara aiki Cikin asibitin Shi.

kwarewan dr Kan aiki shi, tare da tausayi DA kaunar Shi GA patients shine silan DA yasa sunan shi DA Asibitin Shi tayi kaurin Suna Cikin kankanin lokaci agarin alagos,Kafin kace me manyan asibiti Na gwamnati sun Fara Ko Karin kwaceshi sbd yayi aiki dasu.

Amman fir Ahmed yaki saidai atare DA Hakan dole ya amshi tayin aiki Cikin general asibiti sbd taimakon takawa,Wanda yake xuwa asati sau biyu kacal, Dr yazamo ficeccen likitan Mata Wanda yasan matsala ciki DA waje Na Mata, Hakan yajawo mishi Tarin masoya cikin,ciki DA wajen lagos.

Nan Cikin gidanshi dake Lagos nan take DA Zama iyakarshi DA Ibadan saidai yaje ganin family nashi,Dr da Kanshi yace DA Daddy Zai dauki Anitha tazauna wajen Shi sbd yaga rawan Kanta yayi yawa bugu Da 'kari Anitha akwai son Shigar banza GA Sakalci irin Na Auta tun dawowarshi Daga Chaina yafahinci Yarinyar tana bukatar settings shiyasa Duk DA Momcy bataso dole ta hakura Domin Daddy yabashi goyon Baya Kan daukan Anitha, Anitha Takoma gidan dr DA Zama ganin haka yasa Momcy tabada dr amintacciyar 'yar aikinta Hellin sbd tasa Ido sosai Kan Anitha Domin tanajin tsoron Kar Dr yarinjayi Anitha Takoma Kan addin Shi wato Addinin gaskia musulumci.

Itako Hellin sosai zuciyata Ke 'kaunar Dr Obinna,turota gidan Shi Da Momcy tayi ba karamin farin ciki tayiba wannan yasa ta kudura azuciyanta DA wannan dama zatayi amfani ta rinjayi dr Saidai Momcy Taji lbrn Zasuyi aure wannan Kenan.

Satin Momcy 'daya gidan Dr Obinna itada yaranta suka koma Ibadan,sbd Jikin dr DA sauki tuni yatubure yacigaba DA futa aikinshi, ganin weekend ne yasa Anitha tariko Dr Kan zatabi mommy jibi xata dawo,dr Yace "Kuje jibin zanxo Nima Anitha tayi ihu tanajin da'din barinta DA dr yayi Dan batayi xatoba tunda tasan taurin Kanshi,Hellin Tayi murmushi acikin xuciyar ta da'din tfyr Anitha Taji Hakan yasa Cikin faraa taraka momcy dasu Anitha Har Mota.

Shima dr motar Shi yashiga yawuce asibiti,Wuni zubur dr yayi bayi gida Sai 'karfe biyar Na yamma dr yadawo gida, gidan shiru Babu kowa Hakan yasa ya yada zango Afalon 'kasa Cikin gajiya yazauna Kan 2siter,Hellin DA tin shigowa DA motar Shi gidan Taji Dagudu Takoma dakinta dress ta canza izuwa Na Bacci kananun Kaya tasaka Mai showing body Ahankali tafara takowa xuwa falon Cikin Maye Kamar ta tashi abacci tafara Hada hanya,Dr San Bai Lura DA itaba harsaida tagama futowa Cikin falon Kallo daya yamata Yakauda Kai Tareda cigaba DA Danna laptop dake jikinshi,Hellin tayi hanyar Dinning table abinci tafara hadawa Saida tagama ahankali tafara juya duwaiwanta izuwa mazaunin dr Cikin turo kirji Kamar karuwa tace"Uncle Ur fud is ready.

Mitsw dr yaja Babban tsaki Cikin kaushin murya yace "Ke meye Hakan Ashe kema shegiyace dubeki Sai kace karuwa Dalla 'bacemin Anan.

Hellin Duk DA Taji ciwon mgnr dr Amman haka tadaure,Cikin Kirsa tace Yi hkr uncle bacci nake Jin dawowar Kane yasa natashi, Dr yace"Get out b4 in babballaki Jahila kawai yafa'da DA ihu,Dagudu Hellin tabar falon Cikin Jin Tsoro Domin sosai Dr ya'bata Tsoro Bata taba ganin bacin ranshi irinna yauba,dr yaja tsaki Cikin Jin zafin Hellin Yadauki jakarshi yahaye Sama side dinshi.
*AUREN CHOCHI.*

*Book one.*

*By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari.*

*Littafina Na kudine ban yarda Wani Ko wata ya karanta batare da kunbiyani hakkina ba.08100044786.*

*Haryanzu Dai Muna nan afreepage.*

*Page 23&24*

Duk wani shirye shiryen auren Saada ya kanka ma,Kama Daga dangin amarya harma DA dangin ango David,uncle nasu Saada Wanda suke Kira da Daddy Tuni yagama sayyan kayan daki yadawo Nigeria, Hakan 'ya'yan Daddy dasuke karatu awaje Duk Suna Shirin zuwa halartan auren Saada, Halita itace tafara isowa Daga Kasar New Delhi,Sai HaLIL DA Yau yake hanya Daga Kasar Afghanistan.

Radiya kafa DA sauki Har anfara dagata tayi tfy,ranar farko Kuka wiwi Tasha sbd azaba Amman Hakan bai Hana Dr ILIYASU dagewa saita takanba, Cikin Ikon Allah washegari DA Kanta tafara takawan Bayan ta dafa Jikin Dr din.

Shiko dr Obinna tuni Takoma aiki Cikin kirjin Na damunshi harya warware Ras,Duk DA yaso yakoma Duba Radiya DA jiki Amman lokaci DA aiki Bai barshiba saidai yakan Tura Mata DA sakon gaisuwa time to time awajen dr David.

Dukkan su Yau Suna Kuching Kama Daga
Mommy DA 'yan aiki Halita bakuwar new Delhi Harda ita kanta amaryan duk kansu Suna Kuching wajen Hada delicious Na tarban firstborn Na Daddy wato Halil, Yanda Ake Shirin xuwan nashi kadai shine Zai Tabbatar muku lallai wannan ba'ko Na musam man ne awajen iyayenshi.

Harta Radiya DA Ke dingisa kafarta sbd ciwon kafar yaukan tuburewa tayi Harda kukanta itama zatayi aikin,Momy tace"Share hawayenki my Auta Cak mommy tadauki Radiya zuwa Kuching Kujeran roba tadaura Radiya akai Cikin dariya tace zauna nan kitayamu surutu,Saada DA masu aiki sukayi dariya Suna fa'din"Momy Ashe kina dakarfi tunda kika iya dauko wannan katuwar.

Radiya tayi narai narai DA ido zatayi Kuka,"Mommy tace rabu dasu autana Duk bakinciki sukeyi sunga nafisonki sbd kece auta,Halita tayi dariya"Itama Cikin 'kaunar Radiya tamkar jininta tace Swt Autanmu Barin Fara zubo Miki girkin broda kifara tabawa rabu DA Saada.

Radiya tayi saurin mayarda kukanta Cikin Jin dadi tace"Yawwa aunty Halitana much love, Halita tace "mie to my autas, Radiya tace Aunty sauri kizubo Mun girkin Daman tundazu 'kamshin girkin yafara cikamun ciki,Halita tace" Ohh autan Kwadayi, ungo Ta mikowa Radiya fulet Mai dauke DA Cake Tare da Goran 5alife Aiko Radiya takarba tana dariya tace tnz Auntyna tnx somuch.

tana zaune Duk DA ba tayasu aikin takeyiba saidai surutu,yayinda takecin cake dinta tana santin da'din cake, Daddyne yashigo Kuching din Cikin Shirin futa ,Radiya tace" Barka Daddy Shima Daddy Cikin kulawa yace"Radiya hardake akiching Baki gudun sufama Miki ciwo?Mommy tace"Ah ah bamai taba Mun autana Hira kawai take tayamu itama Radiya tace"Daddy Bazasu fama munba Daddy yace to ai shkn Allah yasauwake.
Chapter 8 · 0% Book details