← Book details Auren Chochi Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 29

Sashe 4

Auren Chochi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

IB yacigaba da mgn Cikin zafin Rai,Wlh tallaci Baba Jamilu yacucemu Cuta Mai yawa Sbd DA Allah ace Duk Tarin Matan dake Cikin Hausa fulani yakasa aura harsai yaje ya'divo mana maguxawa dangin tsinannu, Tsakani da Allah fa, Yau maigari yawaya yamutu yabarmu da jaraba yamutu ya'bata mana zuria,Kallesu fa Tsinannun arna shaidanu,haba saiyau nasake tabbatar da Ashe shaidanan Radiya Akwai ayar tambaya Kan Baba Jamil...tas tas tas Baba Auwalu daya shigo Dakin Babu zato Babu tsammani yawanke fuskan IB da Mari dama da hauni,Cikin bacin Rai da zafin xuciya irin tasu tagado yafara mgn"IBrahimu Yayana kake zagi acikin gidana agaban Matata da 'diyata sannan akan kunnenah,yafa'da Yana numfarfashi Kamar zai mutu.

Ba IB Hatta umma saida Taji tsoron ganin mijinta Cikin wannan Hali,Hakan yasa Cikin Kuka tafara bashi hkr Babah yasaka mata tsawa Tare day fadin"Dakata abida Bansan bani da mutumciba wajen keda 'diyarkiba saiyau Dan haka bani bukatar Jin Kalmar bakinki saidai kisani inhar nine Maaifi wajen IBrahimu Na haramta mashi auren Radiya,Kuma Ngd da cin mutumci da zagi Nida 'dan uwana Jamilu.

Baisaurari Jin mgnrsuba Yafuce adakin Cikin tashin hankali, Ammi dake Alwalan sallar azahar tanajinsu Kasan cewan Baba yadaga murya ,hawayen takaicine yafara wanke fuskanta sosai Taji zafi Kan Abunda IB yafa'da Kan tsohon mijinta,ganin Baba Auwalu Yana Hada hanya Kamar zai Fadi shine yasa Dasauri tabar Alwalan tariko hannun Shi zuwa dakinta, tnz God ma Babu kowa Dakin nata Radiya tana Wajen 'yan uwanta.

Kamar 'karamin yaro Baba Auwalu yafashe da Kuka,itama Ammin kukan take Tana Kara lallashin mijinta saida yaji anshiga Sallah kafin yafara tsaida kukanshi Cikin kulawa da 'kaunar Ammi yace" shkn Amina mgnr tawuce Kuma nasan kobaki fadaba kinji mgnrmu dashashan Yaron nan shida uwarshi Dan Allah kiyi hkr karkisa damuwa aranki nariga Nayanke hukuncin da Dole suyi Dana sani.,Ammi yagya'da kai Shkn Baban Radiya Allah yasa Hakan yazamo alkairi.

IB hawaye masu zafine yacigaba da zuba akan kuncin Shi,bahawayen Marin da Baba yamishi shine matsalan ba illah Jin furucin Baban Kan mgnr auren Shi da Abun son Shi Radiya,tsakani fa Allah IB sosai yakejin soyy Radiya musamman da Yau Baban yace yafasa bashi aurenta Jin kanshi yake Kamar zai rasu sbd soyyr Radiya, Umman Shi Dae Mardiya Suma kukan suke sosai suka Shiga damuwa sbd ganin 'bacin ran Baba,Mardiya tace"Kaico kaiconmu Umma Yau munyi sanadin 'bata abunda akayi shekaru ana ginashi Wayyonie inama banga wannan ranaba,Umman tarungume ltama tana Kuka Mai tsuma Rai tasan lallai ita Mai laifina Garin Yaya tabiyewa shaidan Kan son 'ya'yanta Har yazamo silan tsananin 'bacin ran mijinta,Ganin kukansu yayi yawa yasa IB yafuce adakin Dafe da kirji Wanda yakeji Kamar zai fashe.

Karaf suka ha'du da Radiya dake rike DA kwanukan abinci zatakai Kuching cikin Jin zafinshi ta Danna mishi harara Shiko Wani tsananin 'kaunarta da son aurenta yaji Kamar yasaceta yagudu Ahaka yafuce agidan Shagon Shi yashiga yadanna sakata taciki tare da fashewa da Kuka Mai tsuma Rai.

Bayan sunga cin abinci sukan Hiransu sukaci Gaba dayi,tuni soyy DA 'kaunar junansu ya'bula Ko Ina ajikinsu even David angon Saada sosai yakejin 'kaunar 'yar Kanwar tasu aranshi, Anan Saada kesanar da Radiya tagama degree hartayi Mastas Har tagama PHD,yanzu itadin maai kaciyane Ababban banking Nigeria wato first bnk dake reshen Ibadan,itama Suwaiba tuni tagama schl itadin dr tace Tare suke aiki asibiti 'daya da mijin Saada David, David din shine yanema Mata aikin Bata Jima da farawaba aesha Kuma itama yanxu haka tagama degree tana service acikin jahar Kaduna.

Allah sarki Wani Dadine da farin ciki kefasa zuciyar Radiya,Yayin da takeji inama itama tasamu daman cigaban karatu Ko 'yar diploma ta Daura,Saada tace"Auta Kefa a Ina kika tsaya aschl Domin Naga kina da ilimi Duba da yanda turancin ki yake DA kyau.?Radiya tace"Aunty iyakata secondary Shima last yr nagama tafff shine kike Shirin aure?"Saada tafa'da Radiya tace"Uhum Uhum aunty ai ai,shiru tayi sbd Jin sallamar Baba Sannu da zuwa Baba Duka suka fa'da atare Baba yawashe baki Kamar baida damuwa yace"Yawwa my Dotas hop kunci abinci kun 'koshi?Yes suka fada saidai Radiya Kallo 'daya tamishi tagane akwai damuwa Hakan yasa Cikin dabara tazame ajikin Saada Jikin Baban Takoma Daman itadin 'yar shagwabane tasaba da Langwabewa Babanta, Cikin Magana kasa kasa tace meyasamu Babana Na hango damuwa afuskan Babana.

Wani sanyine gami DA 'kaunarta yalullube Baba sosai wannan dabiar nata na damuwa da Duk wani farin cikinshi yake burgeshi, Radiya tarigada tasan farin ciki da bakin Cikin Babah habawa dole yaso Radiya sbd itama tana sonshi,Baba yarike hannunta Cikin kulawa yace 'yar Baba lfylau kawai natuno da 'dan uwanane wato maaifinku sbd ganin jinin Shi,Radiya tayi narai narai DA ido zatayi Kuka Baba yace"ah ah Radiyan Baba Yaya Jamil addua yakeso shine gatanda zamu nuna mishi yanzu.

Saada tace To Baba muzamu wuce,inasu broda da sauran matan gidan muyi sallama sbd tfyr karmuyi ta dare kaga amota mukazo,Duk Da haka saimun kwana ahanya Saidai yanxu Abuja muka nufa gobe mawuce lagos,Babah yace "Hakane ngd muku sosai Saadatu Dan Allah karku sake wannan jimawan bakuzoba Kuma yanzuma baxaku wuceba muje kugaida 'yan uwa nakusa sbd insunji lbrn kunzo bakuje kungaisaba bazasu dadiba.

Saada tace"To Baba Kuma Dan Allah Baba innatafi kazauna da brother kafahintar dashi Kan mgnta sbd inganta rayuwar aura,Baba yayi murmushin takaici Yana fadin"bakomai Saada tuni Na gamsu da mgnrki David yace"yawwa Baba Mungode sosai Kuma sister zatazo kafin biki Ko?Suwaiba tayi charaf tace"Dan Allah Baba Kabamu ita muje tare sbd tela ya auna dinkunan ankonta Domin Muna zuwa zamu Saya Mata.

Radiya tayi dariya itadai Batace komaiba,Haka kawai Baba yaji ya amince suwuce da Radiya inyaso tunda zaixo bikin inyaso Sai sutawo tare,Ga mamakin su saiji sukayi Baba yace Radiyan Baba Jeki hado kayanki kadan kuwuce inmunje biki madawo tare,Tsalle Saada da suwayba sukayi sunajin da'din Karancin Baba itako Radiya tausayin Baban ne yakamata Dan tasan Ko kadan Baba bayason nesa da ita,Shima Baban baiso hakanba saidai bazai raba Radiya da 'yan uwantaba shekaru dayawa basusan junaba Sai Yau awani 'bangare kuwa jiyake kota nan zai hora IBrahimu dan yasan Yana son Radiya,saidai Ya rantse da Allah Radiya tayi mishi Nisa.

Ammi Badan tasoba tabi umurnin Baba Radiya tabi 'yan uwanta,Umma Kan da Mardiya Kuka sosai sukayi lokacin da Radiya tazo musu sallama itakanta Radiya tayi mamakin yawan kukan saidai Abunda Bata saniba kukan matsalan su sukeyi Bana rabuwa da itaba, tsaraba sosai Suwaiba da Saada suka kawo wa Babansu tare da Kudi Mai tsoka Baban yaso yaki karban kudin Amman suka nuna inbasu mishiba mawa zasuyi aysu yanxu Allah ya azurtasu tahanyar karatu da uncle nasu yadage sukayi Dan haka yakarba su basuda matsalan Kudi,Baba dole yakarba tare dasaka musu albarka.
*AUREN CHOCHI.*

*Book one*

By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari.

Freepage.

*Page 11&12.*

Ayyuka sunyi mishi yawa shikan Shi yasan Yana bukatar Hutu,Daga Daren jiya zuwa wayewar Garin Yau sosai kanshi kemishi ciwo.amatsayin shi Na likita yasan tabbas Sitres yamashi yawa lallai Yana bukatar Hutu, Duk Da yaudin weekend ne saidai Babu halin Hutu gareshi,sbd Daren jiya yayi CS wa Mata modan 5 Kuma yasan Suna bukatar sake Duba lfyrsu wajenshi, Dr YAYI karamin tsaki Cikin kasala Dauriya yamike tsaye Jirine yadebeshi yuuu yakoma yazauna saura kadan yafa'di kasa,Zaman minti uku yayi Dan samun nutsuwa Hakan yamike Domin yakudura aranshi lallai zaishiga asibiti, Wannan tsarin rayuwar shine Bazai taba ganin 'dan Adam Cikin ciwo yabarshi sakaka Babu taimako ba Hakan yasa Dole yashige wanka, Yadauki lokaci Yana Kwance Cikin Ruwan wankan kAfin yafara durje lallausan fatar jikin Shi da zallan sabulu, Tsab yayi wankan Shi yafuto By time din yaji 'karfi sosai ajikinshi Agurguje Yayi Shirin Shi Cikin Shigar Shi maikyau Na Suite baki da Jan Takalmi,Masha Allah sosai yayi kyau Cikin Shigar tashi Abunka DA farin fata Bakin Glas Mai Babban fuska yadauka yasaka Cikin Idonshi ahankali Yadauki key Na Mota Tare da 'karamin jakarshi ta aiki yafuto aside 'din nashi.

Gud mrng uncle OBi Budurwan tafa'da tana Gyara dinning table,Dr Ya amsa Mata "How yhu,5n uncle tace dashi Cikin Jin da'din ya amsa gaisuwar ta sbd tasan miskilancin dr ba son mgn CE dashiba Evin gaisuwan Saiyaso yake ansawa,Kujeran Dinning table din yajawo Baya yazauna Cikin sauri Budurwan Tafara bude Plaks Na Abinci Soyyn Planten Tazuba mishi tare da fefesun Kan say, Wani fulet tajawo tabude Soyayyan doya da kwai Zata zuba mishi,Dr ya 'daga Mata Hannu Baice komaiba yafara cin planten din Cikin Yanga Itako doya da Kwan tarufe Domin tagane Maanar 'daga hannun wato Baya bukata.

Baiwani ci breakfast din da yawaba Yajawo tishu yagoge bakinshi,Karamin Cup yadauka yatsiyayi Ruwan Lipton Yafara sha Ko Suga Babu, Itakan Budurwan Tuni tawuce Kuching Saidai 'buya tayi Cikin farin ciki tana kallon Fuskan Dr Yayinda takejin tsananin 'kaunar Shi aranta Kamar tasace Shi tagudu,Ganin Dr yamike Daga kujerar yasa tafuto DA sauri Cikin Faraa tace uncle harka Gama?Dr ya dauki jakan Shi Saida yayi Taku biyu kafin Taji yace"Wannan yarinyar Bata tashiba? Baijira Ansar taba yacigaba da tfy Hakan yasa tarufa mashi Baya tana fa'din "ANITHA Bata tashiba kasan Yau Babu schl.

Wuni zubur yayi asibiti bashi yashigo gidaba Sai 6:pm, Ahankali yarufe Mota Bayan yayi parking Anutse yake takawa harya shigo falon gidan nashi,Zaune yasame su Afalon Duka biyu Suna buga wasan Game atv,Cikin sallama dr yashigo falon, ANITHA Dasauri tamike oyoyo Uncle,Dr yace" Kishirya zamuje weekend saura Kuma kije kibatamin lokaci tfy zanyi inbarki,hehehe ANITHA tayi ihu tana Jin dadi Dasauri tafuta Dagudu zuwa Dakinta Dan shiri,itako Hellin Mai aiki Sannu da zuwa tayiwa Dr cike DA iyaye tana Wani turo kirji Dan son Burge Dr saidai Ko Kallo Bata isheshiba Dakinshi yawuce Ko ansa gaisuwar nata baiyiba,Hellin tayi 'kwafa Cikin Jin zafin Ko inkula da Dr yake Mata tabar falon tawuce nata Dakin dake gefen Na ANITHA.
Chapter 4 · 0% Book details