← Book details Auren Chochi Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 29

Sashe 12

Auren Chochi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali dr Yafara cin indomie din Yana Danna chasbin counter dake yatsan Shi,Ko Rabin indomie din Bai cinyeba Aka Kira sallar AssalAtu Hakan yasa Dr ya matsa DA fulet din indomie din gefe Goran Ruwan yadauka Yafara sha Ko acup din Bai saba, haka kawai jikinshi yabashi ana kallon Shi Hakan yasa dr yadan Dakata DA Shan ruwan.

tabbas yaji JIN motsi akunnan Shi wannan ya tabbatar mishi akwai Wani Afalon, Ido Yafara bazawa Dan son tabbatar DA Hakan saidai sanin akwai mutane Yau agidan nashi Hakan yasa Yatabe baki Yana Daga kafa'da alaman oho Duk radiyA tana kallon shi,shikan dr Goran Ruwan DA fulet din ya'daga yamaida kiching baifi 2minutes ba yafuto DA Sauri kofar futa tanufa yabude anutse Yafara takawa xuwa masallacin dake kusa DA gidan Shi.

radiyA ta fashe DA Kuka tare da Faduwa Kan kujera,haka kawai takejin inhar batayi kukanba Zata iya Suma sbd abunda yafaru DA ita akan dr,Tunda take iyakar rayuwarta Bata taba Jin irin abunda takeji Akan. WAannan bawan Allah ba Ko Yaya IB da Zata aura Bata taba Jin feeling akanshi irin wannan ba,Dan bazata mantaba tunda aka Saka aurenta DA Yaya IB aunty kubra kawar Ammi Ke tsumata da mgnin Mata Kuma sau biyu tana Tambayar ta Ko tana ganin ni'Ima ajikinta kasan cewan aunty kubra wayayyar mace Yar gayu shiyasa take fahintar DA radiyA Kai tsaye amfanin Jin ni'imar sbd shine darajan mace Kuma itadin de tanunawa Radiyan Jin Hakan balaifi bane Saima San barka.

Cikin Kuka radiyA tace" ya Rabbi help mie help me, I don't know wht is wrong with me,I knw u knw all my problems,,plx God help me, help help tafa'da Cikin Kuka akalla batasan minti Nawa tashafe tana Kuka DA sambatu afalon ba.

Ko kadan bataji motsin dawowar Shi ba,Saijin tattausan muryanshi tayi Yana jefo Mata tambaya! You again? Problem girl, wht is wrong with u?

Dip dip radiyA ta shanye kukanta Cikin Tsoro DA razana tafara Kokarin mikewa zata gudu,saidai Ina dr ya Sanya kafarshi ta dama yamaida ita Kwance, Cikin 'Bata Rai tare da zura Mata fararen idonshi yace"Waya kawoki gidana?radiyA Cikin in inah tace moo moooo Mitsw Dr yaja tsaki tare da fadin "Always Cikin Kuka Kuka saikace jaririya Oya jeki Karki fasa Mun kunne DA cry. yafa'da Yana Bata hanya, Aiko DA gudu radiyA ta wuce Dakin Anitha shikan DA ido yabita Yana mamakin ganinta agidan Shi saidai shigarta Dakin Anitha wannan ya tabbatar mishi tare sukazo.

Cikin Sauri ya Haye Saman Dakinshi, direct wanka yashiga baijima ba yafuto agaggauce yashirya yabar gidan sbd Yau asabar aiki gareshi DA yawa gashi zaije daurin auren dr David.

Itakan radiyA Saida tayi tsarki tasake dauro Alwala kafin tagabatar DA Tata sallar Hakan yasa tana idarwa Bata jimaba bacci yadauketa sbd jiya Bata samu ishesshen bacciba.

'karfe 8 Na safe Halil yayiwa gidansu Dr Obinna kawanya sbd dauko Radiya,Har falon gidan Momcy tasa Anitha tashigo dashi lokacin dukansu Suna Kan dinning table Suna break fast radiyA kadai Ke wanka sbd bata Jima DA tashi abacci ba.

Anitha tagabar wa Halil break fast Amman fur yakici,Suwaiba tace"Rabu dashi sis Bari Auta tashigo I knw zasuci tare Momcy tace"To aishkn Daman Yanxu nake Shirin mishi dura inbashi DA kaina,Shikan Halil rAnsane ya'baci yayinda Duk faraar dayazo dashi yabata afuskan Shi,sakamakon ganin tafkeken photon dr Obinna afalon wannan ya tabbtr mishi gidansu Gayen jiya radiyA ta kwana.

Hakan yasa yayi Kicin Kicin DA fuska Tuni Kishi DA bakin ciki takamashi, Koda radiyA tafuto falon Ko gaisuwa basuyiba bare yabari taci abinci yace DA ita"muje gida radiyA DA Suwaiba suka kalleshi Atare Shiko Cikin fa'da yace Zaki wuce mujene kosai Na biyoki DA kayanki ?ba Radiyaba harta Momcy mgnr tabasu mamaki Suwaiba Itace Tamike Cikin turo baki tace barin dauko jakata muwuce Momcy Karki damu zandawo nan Gaba,Itakan radiyA Batace komaiba waJen Momcy taje tana gaisheta sbd Basu gaisaba Momcy ta Amsa DA kulawa tana Tambayar ta Kafarta, radiyA tace" DA sauki mommy.

Umurni Momcy taiwa Hellin Kan tAhada komai nA breakfast din basket Sbd radiyA ta wuce dashi,radiyA tace"Dama kinbarshi Momcy Momcy tace"shiiiii my Dota ai gidankune nan.

Cikin wannan Hali Suwaiba tafuto DA Jakarta DA mayafin radiyA Sallama sukayiwa momcy,Momcy tace jirani dotas shikan Halil tuni yafuce waje Momcy ta'dauko rafar 50k tabasu tace su Sai swt. Godiya sukayi wa momcy Anitha DA Rahap sukace Sai sunzo anjima itama Momcy Hakan tafa'da Cikin Jin dadi suka rabu.

DA misalin karfe 1 Na ranar asabar Manyan pastoci DA Manyan Matan xumunta iyayen ango Dana amarya suka shaida daurin auren Saada DA dr David,Amarya tayi Alkawarin rike ango Amana mutu karaba.

haka Shima angon yayi Alkawarin Hakan, Duka agaban iyayensu DA shaidu Saida ango DA amaryan kowa ya dam'bara Hannu Kan takardan yarjejeniya, Zobuna biyu Na gwal uwar ango ta miko ango yarike yatsan Saada yasa itama tariko tashi yatsan tasaka Cikin murna suka rungume June.

Dr Obinna shine daf DA ango haka Suwaiba Itace kusa DA amarya,Sai shigewa dr takeyi tana iyeyi, ana Gama daurin aure.

Rap rap akadauki tafi, take Mai kidan gangan chochi yasaka Sauti,yayinda masu photo da video Ke aikinsu, Habawa Amarya DA ango suka Fara rawa Suna Kissn juna, 'yan uwa Suma rawan suka Fara Suna taya amarya DA ango murna.

radiyA sosai abun ya burgeta burgewa Mai sosai,Musamman DA taga Harda Ammi DA Baba wajen Taron daurin auren,bugu Da Kari GA Dr Obinna awajen Itakan buya tayi Bayan Amminta tana Kare mishi kallo Dan jitake aranta Yau watakila shine kallonta Na karshe dashi sbd tasan dole Babah DA Ammi zasu wuce gida DA ita.

Hawayene yafara zarya Akan fuskanta Na tausayin Kanta DA rayuwarta,Itakan datasan halinda Zata Shiga Kenan Bayan xuwanta Lagos DA batayi garajen xuwaba! ahankali hawayen Ke tsiyaya Wanda batasan Lokacin DA Hakan yafaruba Charaf Idonshi yahango masa ita dafe ajikin wata mace Mai kama DA ita tana sanar ta wato Kuka,Ko kadan Itakan batasan Yana kallontaba saidai Ankara datayi Kuka take Hakan yasa tasanya Zara Zaran yatsunta tafara share hawayenta.

Wht is wrong with her?dr yafa'da acikin zuciyarshi,saidai sanin Babu Wanda zaibashi amsa yasa yashare yacigaba DA Gudanar DA abunda yakawo Shi wajen.

'karfe biyun Rana Baba DA Ammi harma DA radiyA suka futo Dan Gabar DA sallar azahar, Radiyane tace Bari ta Nemo ruwa aciki Baba yace"Tabari Bari ya sayo musu awaje.

Daga nesa Baba ya hango dr Obinna Yana alwala DA Ruwan faro,Baba yayi mishi sallama abun mamaki saigashi dr Obinna ya amsa Cikin sakin fuska Baiyi kasa aguiwaba ya gaishe DA Baba.

Baba ya amsa Cikin faraa kafin yace"Dan Allah yaro inazamu samu Ruwan Sayarwa?Dr yace No problem akwai amota barin baka,Baba yace Kai ngd sosai saidai Bani dayabane mu ukune yafa'da Yana nuna su radiyA dake can Baya atsaye,Shikan dr Bai Kalle wajenba motar yabude Yana murmushi Laidan Goran faro guda yadauko Mai dauke DA Gora 12 yace gashi Baba hop wannan Zai Isa?

Baba yace sosaima yaro Kai ngd sosai Allah yasaka maka da alkairi Allah yasa kagama DA Duniya lfy.

Aminn aminn dr yace Cikin Jin dadi adduar Baba.

Babbar darduma yadauko abayan motarshi yace DA baba" kuyi Alwalan ga abun Sallah innayi zanbar muku Anan,Baba yace Kai sannufa sannu DA kokari.

radiyA Daga nesa take kallonsu,sosai farin Ciki yakamata ganin irin taimakon DA dr yayi wa Baba wannan Yara mishi kima a Idonta.

Shikan dr Ko kadan baisan tsohon waye ba bare harma yasan akwai wata radiyA acikinsu,Koda yayi Sallah cewa yayi da Baba inkin gama zaka iya barimin darduman Kan Mota sallama yayiwa Baba dake alwala yawuce abinshi.

Albarka Dai DA godiya Baba yakuma mishi.

Daurin aure DA shagali Bai tashiba Sai karfe 5 Na yamma,dr Obinna yaukan Bai tafiba dashi Ake komai,Haka su radiyA Duk Suna wajen Basu bar wajenba Saida akagama Taron haka Momcy dasu Anitha Duk sun samu xuwa daurin auren.

DA karfe 8 nadare aka Kai amarya gidanta dake Cikin anguwar Festactown

Gaskia gidan amarya ya hadu Babban gidane Mai tsananin kyau Mai dauke DA manyan Falo Biyu Sai dakunan bacci manya manya guda 5, Wanda Duk kofifinsu suke Cikin Babban falon Sai katuwar dining table Kai komaifa sambarka Duka dakunan kowanne akwai manyan gado Na Bacci.

Haka Duka falon akwai manyan kujeru masu daukan hankali komai Na gidan Daga waje Daddy yayi order.

Plx my Frnds share ND comments.

If u need my complete book jst call me.

08100044786.
*AUREN CHOCHI.*

*Book one.*

*By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari.*

*Littafina Na kudine sbd masoyana masu kaunar book dina Na mayar DA complete 1 kyauta bt 2 kadai Zaku biya kudinshi Cikin farashi Mai sauki only 300 Naira. Gamai bukatar Shiga group Na Auren CHOCHI just call me.*

*08100044786.*

*Page 33&34.*

Halil tunda su Baba sukazo yake hidima dasu Ina kasaka Ina ka ajiye, gareshi neman gindin Zama yakeyi wajen Iyayen radiyA sbd shifa kaunar Radiyan yakeyi bilhakki DA gaske.

Daddy Okapo wato maaifin Halil shine yasamu Baba DA mgnr Halil din Kan radiyA,Baba yayi murmushi irin tasu ta manya kafin yace"radiyA DA Halil Duk 'ya'yanane Dan haka inhar aure ya tabbatar atsakanin su dazanfi kowa murna Kuma hankalina Zai kwanta nabada 'diyar 'dan uwana wacce itadin amanace agaren xuriar DA nasan zasu mutumta ta sbd ba hango soyyr radiyA wajen Duk ahalin gidan nan Bama Halil kadaiba.

But Addinin mu ya haramta auren radiyA da HaliL bisaga Hukunci.....dalla Dalla Baba yayi bayani a addinince Yanda musulci yace sannan yace DA wannan dalilin nake Baku hakuri Allah yabada Halil macen kirki,Daddy ya gyada Kai Cikin jimami yace shkn Alhaji Auwal nayarda DA hujjanka kuma Na gamsu bt don Allah karka sanar DA Halil wannan mgnr sbd Yana shekaran karshe akaratun PHD nashi baniso yasamu matsala sbd wannan mgnr,Baba yace"Babu komai wlh ai mgnr kaidashi yadace kuyi Bada niba.

Halil ne yashigo dakin, ganin Baba adakin yasa ya nutsu sabanin DA data shigo Dakin DA shagwaba wa Daddy nashi,Cikin ladabi yagaida Baba. Baba ya amsa Cikin faraa tare da Tambayar Shi lfyrshi Shima Halil yace"Lfylau Baba Ganin Halil yashigo yasa Baba yamike Yana fa'din barinje masallaci anyi kusan Kiran sallar laasar.
Chapter 12 · 0% Book details