← Book details Auren Chochi Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 29

Sashe 13

Auren Chochi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Futar Baba keda wuya Halil yamatso Jikin Daddynshi Cikin Sauri yace Daddy hop kayi masa mgnr Beauty Na?Daddy ya shafa Kan Halil Yana kokarin danne damuwar Shi Cikin Dariya yace "sosaima nayi mishi Saidai yace abari kagama schl saimu tsaida mgn,Halil yayi Ihun murna tare da rungume Daddy Yana fa'din "tnz somuch my everything Daddy kagama Mun komai Dagudu yafuta adakin Dan xuwa shafawa Mommy labari Yayinda daddy yabishi DA kallon tausayi,Afili yace Halil Kai kadaine 'dana Dan haka Bazan taba amincewa sbd mace kabar addininka ba Sbd haka dole wannan Karon inhanaka abunda ranka keso Badan inason hakanba saidan tsira DA addinin DA muka Gada iyaye DA kakannu.

Aiki sosai Yau sukaci agidan Domin hidiman biki DA akayi sosai gidan yayi kaca kaca Dan ma masu aiki Suna iyakar kokarin su wajen Gyara DA Anbata zasu Gyara,Sai Bayan sallar azahar kafin suka samu Hutu Bayan sungama aiki.

Zaune suke adakin radiyA Ammi DA aesha Ammi Suna Hira,Sbd gidan Yafara watsewa tunda angama biki Aeshace Tamike sbd Kira DA Mommy taimata tasata Wani Dan aiki futar aesha Kenan.

Ammi tace "DA radiyA tashirya kayanta jibi zasu wuce radiyA tace Shkn Ammi Daman ina sane DA Hakan tunda kafin inxo Baba yace dakunzo zamu wuce, sbd Hakama Tuni nafara shirya kayana insha Allah gobe Zangama Hada sauranma sbd inaso inbada wanki.

Ammi, ta Bata Rai Cikin Tsare gida tace "DA radiya menene alakarki DA 'dan gidan nan Wanda Har kika cire kunya Taki ta 'ya mace Kuma diyar musulma kina rike hannunsa Cikin mutane? Ammi Tacigaba DA mgn Cikin fa'da Ko kindauka Bani ganinkine? Aiko Bani ganinki Allah Yana kallonki wlh Allah ne yataimake ki Baku kwana agidan nanba dasai Na Sassaba Miki kamanni Doluwa kawai.

radiyA tafashe DA Kuka Dasauri tasauko Daga Kan gado ta durkusa agaban Ammi Cikin Kuka tace"Yi hkr Ammi wlh tlh Nima Bani kaunar abunda yakemun Allah shaidata dole yamun,radiyA tacigaba DA Kuka tana baiwa Ammi hkr.

Ammi tasake fuska cikin kaunar 'diyarta 'daya 'daya aduniya tace"shkn koba Akan Halil ba Karki sake Dan ba tarbiyan DA muka baki ba Kenan,Kuma ba tarbiyan diyar musulmai ba kenan Alhmdullh komai ma aitazo karshe tunda kina dap da barin Garin Ammi tafa'da tana Jawo Radiyar jikinta sbd kukanta Yafara damunta.

Aiko radiyA ta kwanto Jikin ammin tana murmushin yafiya DA Ammin Tamata,Ammi tace"Kifita shaanin Halil tunda Addininku ba dayaba sanin kankine Babu aure tsakanin mace musulma DA namiji Kristan Allah DA mazan sonsa sun haramta saidai macen kiristan kadai Allah ya yarda musulmi namiji ya aura,radiyA ta gyada Kai tana nuna gamsuwa DA mgnr Ammi saidai bakaramin mamaki Radiyar tayiba Jin Ammi batai Mata fa'da Kan Ranar auren Yaya IB dake kantaba tunda kowa yasani haramun ne nema Cikin nema musamman Wanda aka tsaida Rana.

Daren ranar radiyA tana tare da Baba DA Amminta Cikin Dakin DA akaware musu masauki Hira sukayi sosai Na yaushe gamo,Anan radiyA Ke Tambayar meyasa baazo DA Mardiyaba tayi zaton zaazo DA ita,Baba yace dawai niyace Mai yawa GA Kuma gudunmowa shiyasa Amman tunda 'yan uwane wata Rana mardiyan Zata kawowa Saada ziyara.

Suwaiba DA aeshane suma sukazo Dakin akacigaba DA hiran dasu,
Sai karfe 12 Na dare kafin dukkan su suka watse kowa ta wuce Dakin baccinta.

Washegarin DA misalin karfe 10 Na safiya Suwaiba DA radiyA aesha DA Halita suka shirya Dan xuwa gidan Sis Saada su Dan kintsa Mata gidan sbd tun jiya Saada tace dasu lallai gobe suzo,kasan cewan weekend ne Babu aiki yasa Har Suwaiba tashirya Dan sutafi tare, Halil chiwgam Yana Manne DA radiyA Duk inda take Yana tare da ita,Shima Cikin Shirin tfy yafuto Dan tare zaaje dashi Ababban motar mommy Mai Suna range roba suka tafi Halil Ke tukin motar radiyA agaba Sauran Abaya saidai yaukan fir radiyA ta Tsare gida inda tahana Halil tabata shikan gareshi San bayason bacin Ranta shiyasa yabari bawai Hakan laifi bane gareshi.

Niko nace Wani laifi Bayan bakasan Allah DA manzonmu annabi Muhammadu rasulillahi s.a.w.

Mamakine yakama radiyA ganin Baba afalon Saada gaban Shi cike DA kayan chi itako Saada DA dr David Suna Zaune kasa DA alaman mgn suke,radiyA Cikin dariya tace "Kai Baba Ashe Daman nan zakazo shine Baka Bari muka tawoba? Baba yayi dariya Yana" fa'din Afuwan 'yar Baba tfyrce takama shiyasa nazo Dan DA banxoba 'yar uwankine DA Kanta datazo Niko bazanso hakanba sbd amarya Bata Yawo.

Aesha DA Suwaiba sukace "hakane Baba shikan Halil Kasa yaduka Yana kwasan gaisuwa awajen Baba Kamar ba dazu suka rabu agidaba,Baba yariko hannun Halil sukayi musabaha Yana fa'din "Allah yamuku albarka no barin wuce Sai kundawo Ko? radiyA tace"o,o, Babana kawai katsaya muyi Hira kaga Sai mutafi tare tafa'da Cikin Sakalci ,Baba yayi murmushi yace"Ah ah 'diyar Baba kuyi xamanku Ni tfy zanyi sbd inason Inga Garin lagos sosai kafin jibi muwuce gobe muwuce sbd anjima baagamu ba.

Halil yace"muje inkaika Baba,Suwaiba tace "Kai Yaya Halil bakaga Direban Daddy awajeba Inaga tare sukazo Baba "yace kwarai kuwa suwaibatu tare muke.

Har Mota dukansu suka raka Baba Aunty Saada Sai godiya take mishi Shima dr David godiyar yake take tayiwa Baba saikace Baban yamusu gagarumin kyauta.

Bayan tfyr Baba Raba aikin sukayi wasu suka Shiga Kiching Daura girkin Rana wasu Kuma suka Fara hyran daki Daga inda me gidan DA angonta keso,Harta Halil kiching yashige wajen radiyA kusan tare suke aikin komai,Halil yamatso kunnan radiyA ahankali yarada Mata wata Rana iwar haka Suna nasu gidan Yana tayata girki,radiyA tayi dariya Mai Sauti batare DA tace komaiba Itakan yanxu tausayi Halil din Ke Bata Domin tayi imanin Babu digon soyyr Halil acikin Ranta hasalima daurewa takeyi wajen biye mishi suyi muaamala albarkacin 'yan uwanshi dake nuna Mata zallan 'kauna.

Sai Bayan sallar magriba kafin sukayi sallama DA Saada zasu wuce gida, gabaki dayansu sun shiga Mota radiyA kadai Bata shigeba sbd kukan rabuwa DA take DA saada,itako Saada hannun Radiyar tarike tana murmushi Daga baya Jikin motar ta leko tace DA Halil"broda kuje kawai Zan kawota DA safe,Halil yace"Ah ah wlh baki isaba Ni inyi Yaya Bayan yaune zamusha hiran ban kwana saikuma naje garinsu Yafa'da Yana balle Murfin motar.

Saada tace"Allah bazata bikuma kawai kuje inkuma kunki Sai inhadaku DA baba Dr DA tunda suke mgnr baisa musu bakiba shima yace "barin ma Kira Baban Aiko wayar yasa ahandsfree yakira Baba saijin mgnr Baba sukayi yace", Assalamu alaikum likita Dr David yace" Baba Sunki barin radiyA ta kwana Baba yace "Bani Radiyar Aiko Dasauri Radiyar tace"Hello Babana Baba yace "'diyata subarki wajen 'yar uwanki zamuyi mgn gobe insha Allah.

Badan Halil yasoba sukayi sallama DA radiya saidai yace wlh kaisu Suwaiba gida zaiyi yadawo suyi Hira dr David yace"Imma kwana xakayi Muna DA masaukin baki.

Daki guda Saada ta Kai radiyA Cikin Lallashi tace Nan shine dakinki autana,radiyA Cikin share waye ta gyada Kai Domin San Bata DA karfin guiwar Bude baki bare Har Tayi mgn,acikin Ranta damuwa Goma DA ashirin Ke damunta Babbar itace zatayi kewan fuskan dr Obinna ba biyu haka kawai takejin inhar Bata ganin fuskanshi xata iya Rasa Duk wani farin Cikin Ranta,Saada tace"Auta kukan ya Isa Dan Allah ki Shiga bayi kiyi wanka gobe DA safe zanmiki albishir Mai ban mamaki Kuma ki tanadamun tukuici Mai tsoka Dan nasan tsab zakiyi farin Ciki DA abun,radiyA tazaro ido waje tana kallon Saada tare day fadin"Kai aunty big?Saada tayi dariya Tana Shirin barin Dakin Saida tazo daf DA futa tajuyo tace DA radiyA Yes Hannu ta Daga alaman bye bye tajawo wa radiyA Dakin,radiyA tabita DA kallo Ko kadan batajin albishir din Zai Mata dadi. Tunda goben zatayi ban kwana DA farin Cikin rayuwarta Hakan yasa Dasauri takarasa Jikin kofar ta Danna key Gadon ta Haye tafashe DA marayan Kuka Mai tsuma Rai.

Plx my Frnds share ND comments.

*Taku Har akullum matar Faisal Zakhari.*

Gamai bukatar Shiga group Na Auren CHOCHI just call me.

*08100044786.*
*AUREN CHOCHI.*

*Book one.*

*By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari.*

*Littafina Na kudine sbd masoyana masu kaunar book dina Na mayar DA complete 1 kyauta bt 2 kadai Zaku biya kudinshi Cikin farashi Mai sauki only 300Naira,gamai bukatar Shiga group Na Auren CHOCHI just call me.08100044786.*

*Page 35&36*

Meyasa zakamun haka Baban radiyA Ammi tafa'da Cikin tsananin Kuka,mgn Tacigaba dayi Cikin fada,gaskia innace dakai naji dadin abunda kaimin lallai naimaka 'karya,Mgnr gaskia iyakar zamana dakai Baka taba batamun Rai irin nayauba habawa habawa tafa'da tana rike kirjinta dake barazanar fashewa sbd tashin hankali.

Shima gabaki daya jiyayi jikinshi yamutu yayinda nadamar abunda ya aikata ya zuyarci Cikin zuciyarshi,saidai sbd Karya tunzura zuciyar Ammi yasa Baban matso gAreta dad DA juna,Hannu yasa yariko Ammi jikinshi Cikin sigan lallashi yafara mgn"Yi hkr Aminatu Aminatuna kiyafeni Na tuba bansan amincewar Zai zamo tashin hankali gareki hakanba DA ban aikataba,saidai yanxu Kan lokaci yakure Duk bakin DA yace ehh Babu Girma yazo yace ah ah Dan girman rabbil alamin Aminatu ki muntuntani Karki SA inji kunya wajen wannan bayin Allah Wanda nake matsayin UBA agaresu.
Aminatu kiyarda Dani wlh tlh mafi rinjayar amincewar tawa Yana DA alaka DA kwanciyar hankalin Radiya, nafarko bazanso Takoma wajenmu tasakanta adamuwa sbd fasa aurenta DA IBrahimu ba nabiyu Naga Yanda 'yan uwanta Ke kaunarka ta soyy Mai tsabta,Itama daalamun Zama dasu shine farin cikinta sbd Na Lura tunda akafara mgnr tfyr Duk jikinta yayi sanyi, Kiyafemin Aminatu Baba yafa'da tare da yunkurin durkusawa agaban Ammi.

DA Sauri Ammi tasa Hannunta 'daya Na dama tariko Baba Tana share hawayenta DA dAya hannun Cikin Jan majina tace"Dan Allah karka durku samin Baban radiyA Wlh rainane ya'baci,da jimami Dan kwata kwata zuciyata Bata kwanta Kan Zaman radiyA Cikin kafurai ba Amman tunda Har kabaiwa Saada Daman rikonta aishkn Mgnr tawuce Bazan Baka kunyaba girman kane isarkane kayi Yanda kaso Dani bare radiyA 'diyar ka Na halak Malak,Baba yaji da'din mgnr Ammi Cikin faraa yace"Yawwa Aminatuna ngd Miki sosai Allah yamiki albarka Daman nasan matar kwarai irinki bazata ba'dawa mijinta 'kasa acikin Ido shiba Ngd ngd yafa'da Yana Murmushi.

Ammi tace"Ngd Baban radiyA kaga mu kwanta karmu makara Tfyr namu akwai Nisa dole Sai muntashi DA wuri,Baba yace"Hakane matar kirki wlh Nima Duk damuwar rabuwa DA 'diyata yahanani Zama lfy Kinsan Allah Aminatu Ammi tace "sosaima nasan Allah ubangiji buwayi gagara misali,Baba yace sadatki.
Chapter 13 · 0% Book details