← Book details Auren Chochi Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 29

Sashe 26

Auren Chochi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mommy datake Zaune tanajinsu Bayan sungama wayar,tace"Daddy Anya mundauko hanyar bullewa kuwa?gaskia yadace musanar DA Halil gaskia Duba DA yanda yakeson Auta kaga Kar nan Gaba inmunxo rabasu tashafi lfyrshi.

Kasanfa shikan yariga yagama sakan kancewa DA yasamu matar aure.

Kuma abunda Na Lura ita kanta Radiyar Yau DA gobe yasa tafara sakewa DA Halil din Wanda gareshi Gani yake soyyrshine yasamu guri ya zauna axuciyar Radiyar,alhalin ba haka bane tunda koni DA ita munyi mgn Kan Halil din sbd Karta ki kulashi yaki Zaman schl.

Daddy yace "hakane Bt Koma mezai faru mubari yagama schl din yadawo Nigeria Sai asanar dashi nafi kowa sanin matukar yaji mgn sabanin Wanda muka dauraashi Akai tsab xai dawo Kasar nan.

DA wannan mgnr Daddyn yakashe Wutar mgnr DA Mommy takawo.

Wata guda cur DA Fara zuwa schl Na Radiya,AUREN Mardiya yazo,Duk inda Radiyar taso tazo bikin Hakan Bai damuba sbd rashin lokaci Domin karatu suke gadam gadam hasalima ranar auren wato Friday ranar Zata Fara jarabawa.

Saidai Aunty Saada ita DA aunty Suwaiba sune suka Zo jukun auren,tare da gudunmowa Mai yawa Na kece raini Kama Daga tv fridge harma DA Injin wanki,Shiko Babah kayan Gara suka kawo mishi Sai kudu Mai yawa DA suka bashi.

Mardiya DA umma Ammi bakaramin murna sukayiba,Dan Daman Cikin kayan auren DA Baba yasaya baisayi abunda su Saada suka kawoba.

Itama radiyA tabada nata gudunmowa Naira 30,000 akawowa Mardiya Tare da Bada Amminta atamfofi uku Cikin Wanda Mommy tasai Mata.

Ya Ib Sai nan nan yakeda su Saada DA Suwaiba Dan neman gindin xama Ko zasu shawo masa Kan Radiya.
Saada dariya tana fadin"Ya IB shagaki.

acikin zuciyarta tana fadin Auta tayi Maka Nisa fiye DA Nisan Nigeria DA bangon Duniya Dan tasan mgnr DA sukayi DA Baba abune Mai wuya DA zaiyi kaffara Kan rantsuwar Shi game DA fasa auren.

Kwanan su aunty Saada biyu ajikin suka dawo Garin lagos cike DA tsaraban 'kauye,Ya IB kuwa Shima tsaraba sosai yayiwa Radiya Yace akawo Mata Aunty Saada takarba tana fadin Auta ta gode.

Ranar DA suka dawo weekend ne Radiya tana gida,Cikin ihu DA kewan 'yan uwanta ta rungume su Duka sbd aunty Suwaiba itama direct gidan saadar ta tawo Sai dare Zata wuce gidan Daddy.

Radiya DA Mai aiki sune suka gabatar musu DA spcl food DA suka musu,dr David shikan Yana like ajikin matarshi Yana fa'din yayi kewanta musamman Dan bbyn Shi dake Cikin Saada Dan wata biyu.

Radiya tace"Yaya David Dan Allah kabar aunty tabani lbrn Babana DA biki Dana amminah.

Dr yace"Ankidin Barni ingama ganawa DA bbynah yafa'da t
Yana dago Saada tsaye Babu Kunya suka wuce daki sukabar su Radiyar afalo.

Radiya ta turo Bakinta tana fadin "aunty subina Sanar Dani kinji! Subi tace" o.o Aida bakisan daniba Saida aunty big ta tashi Dan haka Anki afadan.
Radiya ta shAgwabe fuska tana matsan hawaye tare da fa'din" ayyya Aunty subina kiyi hkr mana.

Aunty subi DA Yar aikin Saada sukayi dariya,Radiya tace"shkkn ma tafa'da Zata tashi awajen aunty subi tarikota tace"Dawo autanmu wlh Kowa lfy Baba Ammi dasu Yaya IB Har amarya since agaisheki Kinga GA sakonki can Na tsaraba inji Baba harma DA ya IB tafa'da tana Mata nuni DA kayan DA suka dawo dashi dake zube afalon.

Aunty subi tacigaba DA Mata bayani tana fa'da Mata irin tarban DA suka samu wajen mutanan gidan musamman Baba,sbd tarba Mai kyau Baban yamusu.

Radiya tayi dariya sbd Jin da'din kowa Yana lfy,Dakin Radiyar suka wuce DA subi tayi wanka ta canza Kaya kafin suka futo falon Dan cin abincin DA aka shirya musu Akan dinning table.

Sai dare Direba yamaida aunty subi gida sbd gobe Monday zAta wuce aiki shiyasa Bata kwanaba.

'karfe biyu saura minti ashirin Radiya DA kawayenta biyu suka futo Daga klass,Radiya sanye take DA Riga DA Wando bakin jeens Sai Rigar material fari Wanda yasauko Har guiwanta bakin gyale tayafa akanta Dan siriri,Sai brief case Mai kyau DA Halil yaturo Mata Daga Kasar waje Wanda iri dayane Sak DA nashi Wanda yake Shiga schl jakar Taji kyau Duk Wanda yagani saiya Fadi kyau nata, Some times Radiya takan riko jakarne sbd ajiye Dan littafi Ko hijab inhar bata Saka hijab dinba ajikinta.

Hannunta rike DA takardu guda biyu handout.
Sai Yar yatsanta dake sanye DA chasbi counter.

Radiya Mai kyauce tayi Sawai gwanin shaawa,Sukansu kawayenta tunda tazo suke fa'din Radiya Jamil kinyi kyau wlh.

Dariya Radiyar tayi,Cikin Rigimah Wanda yanxu Yaci uban Nada sbd anxamo 'yan Aji 'daya a uny tace tenchu my Pple.

Masallaci suka dauki hanya,
Kasan cewan Dukkansu musulmai ne yasa Duk DA yinwar DA sukeji Amman suka wuce masallaci Dan Fara gabatar DA farali wato sallar azahar.

Ahanya suka hadu DA wasu en Klas nasu,Jabira khabiru tace"Radiya Jamil Maryam Abdullahi Lallai kuntaka zero,Maryam tace"Zero kanmene ?Tace"Wlh bohal na bangaren Mata ya lalace kinga Muma munfutone musayo ruwa sbd alwala.

Radiya tayi caraf tace"sbd Allah Duk bangaren masallaci arasa Ruwan alwala?Jabira tace"Ohh musu kikeyi?Shkn jeki xama kidawo Radiya tace"adallah mujenku Nasan iskancin jabirane sbd Allah qi akwai abangaren Maza.
Jabira tace"taff Nibaxanje canba sbd ruwa tunda DA'yan kudadena acikin jaka.

Mitsw Radiya taja tsaki tana fadin "banxa Talaka wayasani mako Yar ta sayan Ruwan gareki Kunga muje Maryam Abdullahi.

Masallacin suka wuce itama Jabira wucewa tayi xuwa sayo ruwa tana dariyan Mgnr Radiyar sbd tsokanar datayi Mata.

Koda sukaje masallacin dagaskene Ruwan bayixuwa sbd lalacewa Daga Saman bohal.

Jakarta tamikawa maryam,Buta uku tadauka tana fadin barin samo ruwar.

Kai tsaye ta xaga ta Baya tayi bangaren Maza,Sbd Tuni an idar DA Sallah yasa Babu mutane DA yawa awajen Radiya Tabude famfon Maza ya'divo ruwa Buta uku.

Saidai wajen daukane takasa hadosu Duka uku.

Hakan yasa tayi kundunbala tahado Duka Duk, Ahankali take tafiya dankar su zube.

Dr Obinna DA futowarshi Kenan Daga masallaci Tabaya yazago sbd Lokacinshi yakare futa xaiyi yawuce gida Hakan yasa yabi shortcut.

Tundaga nesa ya hango Radiyar Kuma Sarai yaganeta itane Bata ganshiba,Gud yafa'da aranshi sbd Shiba manjwa bane yaukan ya tabbtr Radiya musumace bt as how?

Aranshi yace"Kamar yadda kafuto Kai kadai agidanku Muslim,Wannan yasa ya kawar DA mamakin Shi tare day Dan Daga kafa sbd Sauri yakeyi xai wuce Wani waje.

Itakan Radiya Tfyr datake ahankali sbd Kar Ruwan yaxube shine yabashi Daman isowa kusa DA ita Yana zuwa Kai tsaye yawuce abunshi

Kirjintane yayi mummunar bugawa Sbd Jin kamshin turaren Dr Obinna,Idontane yabi mutumin daya wuce gabanta Aiko shidinne tagani tafe Cikin takunshi Mai daukan hankali inda yake tfy anutse Yana Sosa kunnanshi DA car key.

Radiya batasan lokacin DA Taji jikinta Yana rawaba,kafin ta Ankara butocin Ruwan dake hannunta Duka uku sunxube ixuwa kasa.

Plx my Frnds share ND comments.

Taku Har akullum matar Faisal Zakhari.

*Phone number is 08100044786.*
*AUREN CHOCHI.*

*Book one.*

*By Sayyada tahir Matar Faisal.*

*Littafina Na kudine sbd masoyana masu kaunar book dina Na mayar DA complete 1 kyauta bt 2 kadai Zaku biya kudinshi Cikin farashi Mai sauki only 300 Naira.ga Mai bukatar Shiga group Na Auren CHOCHI just call me.08100044786.*

*Page 60&61*

Wani sanyine Mai tsananin dadi yaziyarci zuciyar Radiya,Idonta taware sosai tana karewa dr kallo ta Baya son Ranta Sosai Shigar jikinshi ta geznah hap Jamfa jajaxur tai mishi kyau kafarshi sanye yake DA Jan Takalmi Jan hulah.

Haka kawai Radiya Taji tana kaunar bin Bayan dr,Dan Bata koshi DA ganinshiba.

Batayi wata wataba ta bi bayanshi,Saida taga ya nufi motarshi Honda Hala JA itama kafin tayi ajiyan zuciya tana fadin "Dr Obinna he is spcl Evin his dress r spcl,I rilly rilly like him tafa'da aranta.

Ikon Allah tunda tazo schl din take Raba idanuwa Ko Zata Ganshi sbd tana DA labarin Anan yake Pat time Daga bakin dr David sbd time DA suke xaryan cuku cuku dr David din yake sanar DA ita sbd abokinshi dr Obinna tasamu Har dr David din Yana fa'din ashema kinsanshi Wanda kukaje gidansu.

Radiya tace aranta Sani Kan ba sanin shanuba, Amman afili tace "eeh naganeshi.

Saidai tunda tazo schl din Basu taba haduwaba Duk irin nema DA baxa idonda Radiyar takeyi kullum Dan kaunar ganin kyakkyawan fuskar tashi.

Saiyau Allah yamata gamon Katar DA ganin fuska Mai tsada fuska Mai sanyata nishadi Duk ranar DA taganshi.

Daga nesa yahango futar dr Obinna Cikin second get din schl din,Dan first get Yana can farkon shigowa,Saida motarshi yabacewa ganinta kafin taja ajiyan zuciya.

Tsit Tsit tafarajin ruwa Yana xuba Tacikin panties nata wannan ya tabbtr Mata Tayi Nisa wajen tunanin dr gashi tajawo wa Kanta Abunda always yake faruwa Duk lokacin DA ta tsananta tunaninshi.

Radiya Taji Wani kasala DA mutuwar jiki,yayinda matsanancin ciwon mara Yafara muntsininta.

Ahankali tadaure tajuya
Maimaikon Takoma wajen butocin data Bari ah ah zagawa tayi Takoma bangaren Mata Dan tasan lallai Sallah yaharamta gareta harsai tasamu tsarki.

Wani hawayene Mai dumi Taji Yafara zarya Akan fuskanta,Na tausayin Kanta Kan soyyr Wanda Yafara xame Mata jaraba ya salam.!

Hawayen tayi Sauri ta goge sakamakon hango su Maryam Daga nesa Suna alwala,wannan yasa tadanji sanyi tasan sunsamu nafuta Kenan Na Ruwan alwala

Koda ta dawo wajensu,su Maryam din Sai masifa suke Mata Wai ta shanya su Badan Wani Dan ajinsu yakawo musu ruwaba DA haryanzu ita suke jira.

Batace dasu komaiba tamikowa Maryam hannu,Tana fadin"Bani ajiyata xanwuce gida tafa'da tana cixan baki,Maryam da safiya sukace"Lfy Radiya Jamil?,Radiya Cikin karfin Hali tace"Marata.

Ayya sannu sukafara Atare,Jakar nata Maryam rataya akirjinta tare darike Mata takardun nata, tana fadin" Daman tundazu Naga direbanki yazo muje inmiki Rakiya Sai indawo inyi sallah.

Har Mota Maryam taraka Radiyar tana Mata sannu,Radiya Kai kawai take dagawa takasa mgn Shima Direban sannu yake ta Mata Har suka Isa gida.

Ko agidan kwanciya tayi takasa komai sbd Maran Babu abunda takeso DA kauna aranta irin sake ganin fuskan dr Obinna.

Gashi gidan Babu kowa aunty Saada DA dr David Suna wajen aiki,Mai aiki kadai itace Ke aikinta akiching Sai karfe wajen uku kafin Cikin ya Lafa mata,Sai Alokacin tasamu Daman yin wanka tagabatar DA sallahr azahar tana idarwa Babu jimawa akayi Kiran sallar laasar batare DA Bata lokaciba tagabatar.

Dr Obinna Sarai yaji lokacin DA butan hannun Radiya yafa'di.
Still yanajin time DA take bin bayanshi,Aranshi yake fa'din wannan daya kuwa?
Chapter 26 · 0% Book details