← Book details Auren Chochi Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 29

Sashe 2

Auren Chochi Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaman minti uku yayi Cikin office din yamike, 'daya Bayan 'daya yakebin dakunan marasa lfy Yana dubasu, tare da Bada taimako wa marasa lfyn Kamar inda yasaba 'ban garen Yara yawuce Nurse uku nabiye dashi rike da kayan aiki, Aiko shigansa bangaren yaran Yasa yasaki fuskanshi da tunda yazo yake murtuke Kamar boss,Cikin faraa yafara Duba yaran Yana tambayan lfyrsu,Suma yaran Cikin farin Cikin ganinshi suka Fara bashi amsa dasauki Dr Hannu yasa Cikin aljihunshi Na farin rigan aiki yafara Basu minti swty thanks thanks shine yaran kefa'da yayinda Iyayen yaran suke masa godiyar dawayniya da yaran nasu,Dr YAYI MURMUSHI tare da fa'din "No problm ix my duty.

Wannan dalilin yasa mutane dayawa keson asibitin nashi musamman Iyayen Yara 'kananu Domin 'karyane Kaje asibitin nashi batare da Kayabi irin tsari da Bada patients kulawa irin nashiba,Suma nursing da sauran doctors dasuke aiki tare sosai sukejin da'din aiki dashi,Hakan yasa 'yanmatan nursing dayawa Ke 'kaunar Shi sbd Kyau ku'di dakuma Ajin dr Obi.

'karfe 12, daidai na rana,dr yakoma Cikin office nashi sosai yakejin gajiya ajikinshi,Hannu yasa yadanna madanni Dasauri Wani saurayi yashigo sanye da farin kayan aiki ajikinshi, gd evening my boos yafa'da Cikin girmamawa Dr Obi yakalleshi da shanyeyyen Idonshi Cikin yatsina fuska yace"evening, prepare me a breakfast,okey my boss.

Cup din shayine ahannuna Shi Yana kur'ba Sai Cake guda biyu dake Cikin karamin tangaran Na glass agaban shi,Juyi yakeyi Kan kujera Shi ta office Mai jijjuyawa Yayinda yake lumshe Idonshi Yana taunan cake din Kamar Bazaiciba wannan dabiar shine yin komai anutse harta cin abinci Hakan yakeyi anutse Kamar bby, Cup din shayin taajiye Tare da 'daukan Wayarshi daya dake zube gabanshi Kan table, Swthrt shine number dayayi calling,Kamar shitake jira ringing 'daya ta'daga wayar Hello my Bby! Yes Mah Dr yafa'da Cikin Shagwaba Hakan yasa Duk zafin dake Kanta game dashi tare da jin takaicin rashin kiranta Na 3days yabar zuciyanta sbd Jin dadda'dan muryanshi,itama Cikin kulawa tare da soyyrshi Mai 'karfi tafara mgn" I MISS YOU MY Baby ND whr do u Hide ??? murmushi yayi Mai Sauti harsaida Taji 'karan tawaya kafin yace" I miss u too my swt Mah, am there bt just dat am to busi wt work, double sorry Mah,Dariya tayi sbd Jin da'din muryanshi Kafin tace"Issoryt my swthrt bt the work busy is getting too much dat u are not having our time, I ,daddy ND the other members of the family.Awkhay mah,I will try my best in seeing how I can adjust my schedules.

Daz my swthrt,Yep mah,Hiransu suka cigaba dayi maicike da 'kauna tsakanin dr da maaifiyar Shi,Sai karfe 1saura kwata Na Rana sukayi sallama sbd yaji Kiran Sallah Daga Cikin masallaci dake asibitin, Hannu yasa yacire takalmi cobashu dake kafarshi gami da cire safan kafarshi Flat Shue yajawo dake Cikin durowa dake gefenshi yasaka kafin yashiga toilet nashi dake office nashi,alwala yadauro Yafuce zuwa masallaci.

Up up up masoyana kugarxayo kuyi payment naku,Cikin sauri Dan samun Shiga group Na Auren CHOCHI I knw zai kayatar daku fiye da Sauran book dina.

Gamai bukatar Shiga jst call me,08100044786.
*AUREN CHOCHI*

*Book one* freepage.

By Sayyada tahir Matar Faisal Zakhari.

Tsokaci! 'daukaka Yana Daga rabbil alamin,ya Allah Ina rokonka da sunanka Mai tsarki Allah kabamu Ikon rubuta abunda al'ummar annabi s.a.w. zasu amfana tare da kasuwa Mai albarka while rabbi kamu 'daukaka fiye da Tsofan marubutan mu ameen.

*Page 5&6.*

Radiya itace tafa'da Maka Hakan???IB yashafa gemu Yana sunkuyar dakai Kamar Yana gaban al'kali,Tambayar yakuma maimata mishi Enye nace Radiyar ce tafa'da Maka Hakan???Akaro nabiyu IB yagyada Kai tare dacewa"Eeh Baba Hakan tafa'da Kuma mgnr bayau tasomaba tuni tajima tana fadin haka,sodayawa nakan yi zaton wasane Ko shirme irin nata saidai tunda akasaka ranar auren nan kusan kullum saitayi wannan mgnr Yau kamma tabbatar mun tayi inhar ba achochi zaa'daura aurenku ba Tofa....'karasa mana kayi shiru Baba yace" IB yacigaba "Tace saidai afasa auren yafa'da Cikin takaicin karasa mgnr.

Baba yayi murmushi tare da Gutsuran Goro "shkn Zanyi mgnr da ita danjin tabbacin mgnr,GA mamakin IB Ko ajikinBaba bare afuska baiga alaman damuwa wajen Baba Kan mgnr Shirmen Radiyar ba,Duk da yasan Baba bayison laifin Radiya Kuma akwai soyy Mai 'karfi tsakanin Radiya da Baba baiyi xaton nuna Ko inkula wajen Baba Kan Wannan mgnrba musamman da mgnr tashafi aure harma da addini,Kana iya tfy Muryan Baba yadawo da IB Daga mgnr zuci dayakeyi, Cikin ladabi yace "Ngd Baba barinje sainaji Daga gareka.

IB takalmin Shi yasaka 'dakin Umma yawuce Duk jikin Shi yayi sanyi sosai yaji karayan xuciya Kan Wannan mgnr da Baban yace, da sallama yashiga Dakin umma Sa ilin umman itakafaice Kan darduma tana sallar nafula IB yanemi'daya Daga Cikin kujeru guda uku dake 'dakin umman yazauna Dan jiran umman ta idar da Sallah.

Baijima da zamaba umman ta idar da Sallah,gajeruwar addua tayi sbd sanin IB Yana jiranta, Umma takalleshi Cikin kunyar 'dan fari tace" Babana Lfy daiko?IB yagyara Zaman Shi Kan kujera Yana fa'din "Lafiya Umma Daman kan mgnr dashin nanne Nawa Jiya Yahya yabani Kinsan Daman nace Miki nafison Na 'karshe sbd fitina,yasanya hannun Shi Cikin aljihu bakin laida yaciro gashi yamika Mata dubu Darine cus Sai kisamu Ammi Kutsara yanda zaayi inyaso Sai insa usaini da Yahya sumuku rakiya Cikin jalingo kuhade Sauran kayan akwati, umma tace "Madallah Hakan yayi kyau Allah yasanya alkairi yasa zaayi damu Hannu tasa takarbi ku'din tana sanya mishi albarka,IB yace aminn Ummah "nibarin koma shago sbd Masu ciniki To umma "tace dashi.

Taraba state, Cikin Babban birnin Taraba state ' wato jalingo karkashin 'karamar hukuman manbila, 'kauyan jukum take.Garine Wanda yake ha'de da musulmai da kiristan,hasashe yanuna Cikin Garin jukum kirista sunfi musulmai yawa nesa ba kusaba, masu 'kabilan jukun Hakan shine sunan 'kabilar Wanda suka kasance kiristan wasunsu bakakene wasuko fararene Kamar fulani sakamakon auratayya da 'kabilar jukun da Hausa fulani dakeyi tsakanin junansu,akwai Zaman lfy sosai tsakanin musulmai da kiristan Na 'kauyan jukum.

Alhji Jamilu da Alhaji auwal haifaffun 'kauyan jukum ne Cikin 'kabilan Hausa fulani,Bakaken fulanine kyawawa masu hanci dogo Kamar biro Wanda yake ha'de da manyan idanu farare tas Kamar Madara,Alhji Jamil da Alhji Auwal uwarsu 'daya ubansu 'daya Suna da arziki daidai misali saidai Alhji Jamil yafi Alhji Auwal arziki saidai dukansu biyu sunje makka sun sauke farali,Alhji Jamilu shine babba kafin Alhaji auwal, tun fil azal iyayensu sunjima darasuwa Hakan yasa subiyu suke rayuwarsu Cikin family house nasu Sai dangin kusa Dana nesa dasuke Kan xumunci dasu.Alhji Jamilu Yana da macen aure biyu Amina itace uwar gida Sai Grace wacce takasance kirista Wato 'yar 'kabilan jukum mace kyakkyawa Mai sanyin hali, grace itace tafara aihuwa wa Alhji Jamilu sbd Amina uwar gidanshi Allah baibata aihuwaba, 'ya mace grace taaifo Ranar Suna yarinya taci Saadatu Bayan Aihuwar Saadatu grace Takuma aifo suwaiba Aliya,saidai Duka 'ya'yan grace sunkadance kiristan wato sunbi addinin iyayensu Suwaiba kadai takasance musulma.

Amina Bata samu aihuwaba Har grace taaifo 'ya'yanta hudu, Cikin Ikon Allah saigashi Allah yabata ciki, Bayan wata Tara Amina ta aifo diyarta mace inda suka aihu Rana 'daya da matar 'kanin Alhaji Jamil wato Alhaji auwal Wanda tuni yariga yayan nashi aure Shima Yana zaune Cikin family house, Matar Alhaji auwal saida taaihu kafin Alhaji Jamil ya'kara aure haryafara samun zuria inda itama take da 'danta namiji Mai Suna Ibrahim Bayan Ibrahim ne Bata Kuma aihuwaba saida Amina tasamu ciki Suka aifo yaransu Rana guda,dukkan su Mata Hakan yasa family din sukayi farin ciki sosai ranar Suna Yara sukaci Radiya da mardiya.

Haihuwan Amina da kwana 46 chif Gobara yatashi Cikin family house 'bangaren gidan Alhaji Jamil kafin afarga gobaran tayi Nisa Cikin tashin hankalin mutane suka kaimu 'dauki saidai Kash Sanadin wannan Gobara Alhaji Jamil da matar Shi grace da 'diyanta Aliya Suka Kone kurmus! Suwaiba da sauran 'yan uwanta sune Basu koneba saidai Suma sunji jiki Cikin gobaran, itako Amina da 'diyarta tuni sunfuce lfy Ko hayaki Bai musu illaba.

Wannan mutuwa ta Alhji Jamil da iyalanshi yadaga hankalin Amina Iyayen grace da Alhji Auwal, Suma 'yan uwa da abokan arxiki sunji mutuwan Alhji Jamil da zuriarshi sosai Baran Ibrahim yayi Kuka sosai sbd lokacin Yana da wayo akallah yakai 11yrs.

Bayan mutuwan Alhji jamil, Alhj Auwal shine yacigaba da 'daukan 'dawayniyar Amina da 'diyarta, tuni anraba gado qnbaiwa kowa nashi Amina dakanta ta danka Gadon diyarta wa 'kanin mijinta Alhji Auwal Domin tasan zai rike Amana,suwaiba ko da sauran 'kannanta biyu Tuni family Na grace sun karbe tasu Gadon tare da dauke su Duk da Alhji Auwal baisoba haka suka dage saida suka karbesu.

Bayan Futar Amina takaba Anan ne Alhji Auwal yabijiro da mgnr son auren Amina sbd yarike amanar yayanshi Amina batakiba Domin tasan halin Alhji Auwal nakwarai Hakan yasa batare da 'bata lokaciba Akadaura auren Amina fa Alhji Auwal, Radiya da mardiya suncigaba da Zama 'bangare daya Daga Alhji Auwal Har iyalanshi sunrike amanar Amina da Radiya.

Tsananin soyy Alhji Auwal keyiwa Radiya fiye DA 'ya'yan cikinshi sbd 'kaunar dake tsakanin Shi da Margayi Alhji Jamil, ko kadan Alhji Auwal bayi kaunar Jin kukan Radiya Hakan yasa take da Sakalci sosai da Neman mgn Amminta Duk Da Bata son Hakan itama Hakan take kauda Kai sbd tausayin 'yar marainiyar Allah, RADIYA da Mardiya suntaso Kamar 'yan biyu akwai shakuwa sosai atsakanin su Inba Wanda yasaniba xakayi xaton sudin 'yan biyune Radiya tafara schl Tunkafin Mardiya tafara wannan araayine Na Alhji Auwal sbd Radiyan akwai wayo fiye DA Mardiya saida Radiya taje aji biyu A primary schl kafin Mardiya tasamu shiga.

Ibrahim Wanda suke Kira da Yaya IB tun Radiya tana yarinya yake 'kaunarta,Cikin ana ganin abun wasane Har Radiya tafara Girma Yana Kan Nuna kulawa agareta IB yayi karatu iyakarshi secondary sbd Yafi kaunar kasuwanci Kan karatu Babban shago yakedashi Na saida kayan marmari akofar gidansu tare da Provision.

Radiya Tacigaba da schl itada Mardiya Har suka Gama jiniyo,Mardiya Bata cigaba ba sbd Samari da sukayi musu cha itada Radiya kasan cewan Radiya itada Yaya IB Suna soyy Hakan yasa Itakan tacigaba da zuwa makarantar ta ta Boko, Akwan atashi hartagama schl dinta itako Mardiya Babu schl din Kuma Babu mgnr aure.
Chapter 2 · 0% Book details