← Book details Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 86

Sashe 84

Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

___________________________/___/
Time É—in da Abban su ya shiga É—akinsa, yayi tunanin zai ga junaid a kwance yana sharar bacci, amma sai yaga wayam daga blanket sai pillow asaman gadon, abun ya É—aure masa kansa, aransa ya ce "meyasa Junaid bai zo ya kwanta bane wai, ko dae yana a bedroom É—insa bara dae na canza kaya naje na duba sa,"
Shaf shaf ya cire kakin dake jikinsa, ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ya zura jallabiya fara, sannan ya fice daga room É—insa izuwa na junaid dake a upstairs,
Yana isa ya tura kopan ɗakinsa abun mamaki babu junaid babu alamarsa, har toilet ɗinsa ya duba babu Shi saboda tsabar ruɗu har cikin Laundry basket ɗinsa ya duba da cikin Wardrobe ɗinsa don yaga ko ya 6uya aciki 😂
Amma babu shi, aikuwa hankali atashe abban su ya fito ya wuce part ɗin sgr, ya shiga har ɗakinsa ya bubbuga masa jikin ƙoparsa,
Sgr dake kwance natse saman gadonsa yaji knocing É—in da abban ke masa,
Janye bargon jikinsa yayi, sannan ya tashi zaune yana kallon Abban nasu daker yake buÉ—e Eyes É—insa saboda bacci,
A sanyaye yace "Abba me ya faru ne? Kai ne da kanka?
"Ina fa lafiya babu junaid fa acikin gidan nan"! Jin hakan yasa sgr yin saurin haurowa ya sauko daga saman gadon, jikinsa na sanye da night dress riga ce dai dai guiwarsa ta tsaya babu dogon wando sai dai shorts acan ciki,
Cikin ruÉ—u yace "Abba kamarya? How za'ace junaid baya cikin gidan nan!!!? ya tmby yana kallon abban nasu dake a tsaye,
"Nima bansani ba, dawowa ta kenan, gsky akwai matsala,'
Fito wa su kayi atare shida abban suka bi sauran bedrooms É—in sauran saboda su duba su gani ko ya kwana a É—akin sauran saboda yana yin haka in rigimarshi ta tashi sai ya za6i inda yake so ya kwana ko É—akin waye kuma dole abarsa ya kwanta,
Duk wanda akayi wa knocing ya buɗe daga yaji cewa Junaid ake nema sai kaga ya wartsake daga baccin da yake yi, hankalin kowa ya tashi matuƙa,
Gaba É—ayansu duk suka hallara a babban falon in ka cire Marshal saboda basu tashe shi ba tunda shi ranar ya dawo baisan wainar da ake toyawa ba Sai haroon,

Duk sukayi tsaye cirko cirko sai faman hammar bacci suke yi,
"A cikin ku wayasan inda Junaid yaje !!? Abban su ne ya tambaye su,
Kowa sai faman murxa ido yake yana hammar bacci,
HaÉ—a baki su kayi wurin cewa "Abban bamu San inda yake ba wlh,"
Tsawa sgr ya daka musu har sai da suka É—an firgita yace "wannan wane irin shashanci ne ace junaid yabar gidan nan batare da kun sani ba har yakai wannan time É—in a waje baku lura ba,!"?
Murya na rawa Su twins suka haÉ—a baki wurin cewa "Junaid fa baya zuwa ko'ina kowa yasani yana cikin gida kullum sai dae wani abun daban,"
"Nima a iya sani na kenan gsky akwai matsala* acewar fawan
Jabeer da Irfan suka ce "mun fa lura baya cikin gidan nan, amma gaba É—ayanmu munyi tunanin yana É—akin Abba yana bacci shiyasa mukayi shiru,"
Bin su da kallo kawai sgr yake yi suma kallon shi suke yi suna kora bayani,
"Yakamata ajaraba kiran layinsa mana aji inda yake" acewar Khaleed, cikin sauri kanal yusif ya zaro wayarsa dake cikin aljihun wandon baccinsa,
Contact ya shiga ya dubo numbar junaid wadda yayi saving da *Last Born* Ya danna masa kira ta soma ringing,

Gaba É—aya koya ya saurara yana jiran amsa kira daga junaid, 3 times tana ringing junaid bai É—aga ba,
Hakan yasa kanal yusif yin amfani da wayarsa wurin duba location É—in Inda wayar take,
Gaba É—aya kowa na jiran tsammani, kanal yusif yace "kai ! Location É—in fa ya nuna cewa wayar tana acikin gidan nan that means junaid yana acikin gidan kenan ko yabar wayar tashi a bedroom É—insa ne,

cikin hanzari su fawan suka haye upstars shi da su twins domin su duba É—akin junaid koyana nan,
A tsiyace suka tura ƙopan ɗakin suka shiga cike da tsammanin ganinsa amma sai suka ga wayam, sae wayarsa dake ajiye saman Pillow bisa gadonsa, hakan na nufin gida yabarta,
Duk basu ji daÉ—in hakan ba, jiki amace suka sauko down É—in har haÉ—a baki suke keyi wurin tambayar Su ina junaid É—in ? Suka amsa musu da cewa basu ganshi ba sai dae wayar shi kawai,
"I know u will not see him cos i ave checked his bedroom already ya Ilahi," acewar Abbansu ya faÉ—i cikin tsananin damuwa,
Hankalin kowa fa ya tashi, bazaman lpy ba Romeo ba junaid ba last born, ba shagwa6a boy Ba dole kowa ya rasa natsuwa,
"nasan inda yake ni,"
Atare suka É—ago don suga wanene haroon ne wanda fitowarsa kenan daga shi sai gajeran wando ajikinsa,
Har haÉ—a baki suke yi wurin cewa "Yana Ina!?
"Abada cin hanci a É—auko muku shi," kai kana ganinsa kasan yasha ya bugu idon nan sunyi jawur kamar na mujiya sai tangyaÉ—i yake yi,
Tsoki suka ja atare,
Abbansu ya daka mishi tsawa "Haroon kadaina mun wannan wasan kasan inda yake ne ko baka Sani ba _"!!!
Haroon yace "Billahil Azeemu na tsarance da rabbus sama'wati wal'ard nasan inda junaid yake, in ku kayi haƙuri kuka sa salama azuciyarku yanzun nan zan ɗauko muku shi,"

gaba É—aya mamaki ne ya kamasu su kace shikenan "Muna jira,"

Juyawa haroon yayi ya nufi hanyar É—akinsa yana faÉ—in "saboda wannan É—an shilan duk kun bi kun tashe mutane Fil laili..........
Shigewa bedroom ɗinsa yayi yana ƙunƙuni,
Su kuwa zama su kayi suna ta faman jiran haroon ya fito musu da junaid,"
Jimmm kaɗan sai gashi ya fito hannun shi ruƙe da Pillow yana tangal tangal,
Zuba ido su kayi suna kallon ikon Allah, haroon na ƙarasowa ya shiga ƙoƙarin tu6e rigar pillown yana cewa "Yawwwa ynx zaku ga shegen ya faɗo daga cikin pillown ae nan cikin ya 6uya ja'irin,'
Rai a6ace har haɗa hannu suka yi Babban yaya da Abbansu suka sharara mashi zafafan maruka , daga shi har filon kowa yayi ƙasa baje,
Ihu haroon yasaki tare da cewa "Eeeeeeee !!!huuu!!!huuuu !!! waman ƙadarallahu haƙƙa ƙadrihi yanzu abba daga abun arxiki zan nuna muku inda junaid ya 6oye sai kawai naji saukar maruka? Yaron nan fa akan idona ya shige cikin rigar filon nan ya 6uya amma shikenan bakomai,'
Abun haushi abun takaici, banza kowa yayi dashi suka shiga tattauna yarda za'a yi a nemo junaid,
Kanal yusif yace "ina ga bari naje na sanarwa Azmee wata'ƙil tasan inda yake,
"A'a bana tunanin hakan, kwarama wannan mai aikin tukur raina yana bani cewa suna shiri sosai da junaid wata'ƙil shi yasan inda yake tunda kusan shine tsaransa," acewar Abban su

yace hakan ne saboda abunda yagani wato da Junaid yyai ma sehrish magana ƙasa ƙasa lokacin da suna Cin abinci dama abbansu shine ya lura da hakan,
Cikin sauri Fawan yace "Bari naje na tambayesa,'
Yakama hanya da sauri ya nufi wurin É—akin azmee don yana da tabbacin É—akin tukur yana kusa dana Azmeee
Sehrish na zaune idanu duk sun kumbura, taji bugun ƙopa da ƙarfi jiki na rawa tace "Wanene," a tsorace ta tambaya,
Muryar fawan taji yana faÉ—in "Fawan ne, Fito maza ina son magana da kai,"
Cikin sauri sehrish ta kimtsa ta mayar da gashin bakinta, ta gyara É—aurin kanta,
Sannan ta taso ta buɗe ƙopan cike da mamakin ganin fawan tabbas kam akwai matsala,
"Gani," ta faÉ—i a raunane,
Fawan yace "Kana da masaniyar inda JUNAID ! Yaje !?
Zaro ido tayi gabanta na faÉ—uwa aranta tace "Ina junaid yaje har daren ne bai dawo ba ake nemansa,'
Cikin sauri tace "a'a gsky ban da masaniya akan hakan,"
"Ka tabbata'?
"Eh wlh," ta bashi amsa
jiki a mace fawan ya wuce izuwa falon,

Shigewa cikin É—akin tayi gabanta na faÉ—uwa sai lokacin ta tuno da cewa É—azu junaid ya sanar mata da cewa su haÉ—u a garden After magrib,
. "to kodai yana can ? May be ya jira ni ne yaji shiru banzo ba bacci ya kwashe shi Acan, kai anya kuwa !? taya ma zai zauna tun bayan magrib zaman jira na har yanzu kusan ƙarfe 1:00 na dare bai shigo ba, gsky bana tunanin hakan,
Haka sehrish ta rinƙa tunane tunane aranta, har ta samu wuri gefen gadon ta tazauna zuciyarta ta saƙa mata cewa "Junaid fa rigimamme ne zai iya yiyuwa yana can ya dage akan in banzo ba ba zai bar garden ɗin ba, kai gsky fa haka nake tunani hankali na bazae kwanta ba har sai naje na duba garden ɗin can, tana faɗin hakan ta miƙe .................................................

Wannan kenan 🙌

Keep sharing it everywhere pls 🙏

Boss Lady 💝

Masu son yi mun Comment ba hali ga Phone no ɗina Only message kuma mata kaɗai (08103884440)*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*🔥The Father Of Soldiers🔥*

*Na*

*Hafsat Bature Moh'd*

~BossLady~

🔔🔔🔔

_nataƙaita littafin Abban sojoji yanzu yakoma part one and part two only duk mun yawansa zai ƙare a part 2, namai dashi yanzu muna a part 1 sai ya kai 100 pages cuf, sannan part 2 zai shiga, sannan kuma yanzu free pages ne_💔👌

Page 94-95
Chapter 84 · 0% Book details