← Book details Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 86

Sashe 51

Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙiris ya rage azmee ta fashe da dariya, wannan fadancin na fawan ya bata mamaki,
Bin su ya ke da kallo ɗaya bayan ɗaya, bayan sun gaishe shi, kowannansu ya shiga taitayinsa, don sun sani sarai bayason hayani ko kɗan, hakan yasa suka rage ƙarar spoon ɗin da hannunsa daga wannan sautin kwas kwas da ya ke yi,

Hannun sa ya miƙa acinkin wani empty bowl, azmee tasanya masa ruwa ya wanke, kafin ya tsoma hanun acikin naman, tsoka ya ɗauke ya jefa a bakinsa, a hankali yake taunarta, yana ci yana binsu da kallo One by one,

Ƙasa ƙsa da murya irfan yayi shi dake kusa da jabir yce "wannan kallon da babban yaya yake yi, bana lpy bane, duk ƴan ciki na sun kaɗa , jabir ya ɗauki cup of tea ɗin dake front ɗinsa ya kare fuskarsa dashi kamr zaisha, sannan yace "kai kenan ma, wlh jiki na kamar na mai zazza6i don fargabansa,'
Khadeel dake sauraronsu ya ce"jikin wasu na ƙaiƙayi da alama,'

Sun gane me ya kenufi cikin sauri suka ja baki su kayi shiru,
Kowa tsit kamar mutuwa ta gifta, sautin ƙarar cokulan da hannunsu twins yake yi ne (kwas kwas) ya cika masa kunne, ɗagowa yyi ya aza eye balls ɗinsa akansu, zo ka ga tashin hankali, bakomai ya haddasa hakan ba, face kermar da jikinsu ke yi,
mirya na rawa ayaan ya ce "mun shiga uku, idon babban yaya akan mu jahan,'

"menene" ya tambaya a É—an firgice suka É—ago suna Kallansa, ya sake cewa "are u not feeling well ? ganin yadda jikinsu ya ke rawa,

Ido luhu luhu Jahan yace" Ba mu jin daÉ—i ne, ni da ayaan, "

É—gowa yusif yyi yana kallansu, jin zasu ja masa bala'e, tun Kan big bro yace wani abu, yusif yayi hnzarin cewa "but why u didnt tel me about ur sick ? ya tambya yana kallansu,
cikin sauri ayan yace "dama tun jiya da dare ne,
"Atlease u should inform me abt ursick, ko ƙarfe nawa ne zan duba ku ae,? shiru su kayi shi dae Rafayet binsu da kallo kawai ya ke yi kafin ya dakatarsu da cewa "its ok, after we finish the breakfast, yusif makes sure that u check them well,'
".Insha Allah babban ya ya" zuru su kayi jin za'a duba su, Bayan sun san cewa lfyarsu lou,

Mayar da idonsa yayi kan Junaid wanda ke ta faman murmushi, kamar zautacce, ada sun yi tuanin cewa yaron ta6in hankali gare sa, amma da aka bincika sa sai aka tabbatar da cewa haka Allah ya haliccesa wit smiling face,

ɗagowa junaid yayi suka haɗa ido da babban yayan, cikin sauri ya sunnar dakai yana ci gaba da murmushi, Shifa kallon dollar $ ya ke ma yayan nasu, shiyasa murnarsa ta ƙaru in ya kallesa $ kawai ya ke gani a fuskarsa, ya riga da ya kammala lissafin nawa zai amsa da nawa zai kashe wa sehrish ɗinsa 😥

.................SEHRISH........................

A 6angaren sehrish kuwa, zarce wa tayi da bacci, na ɗan mintina ta farka tana sauke ajiyar zuciya, sunan shi ne kawai zuciyarta ke ta faman ambato, idonta takai kan agogon bangon dake manne, ƙarfe 12:30am, ynx sun isa kammala breakfast ɗin,

tashi tayi ta kimtsa, ta fita taga me ke wakana, basa nan ciki duk sun fita, wayam kuma azmee ta gyara ko'ina yayi fess, a kitchen ta same ta, tana wanke dishes É—in da su kayi amdani dashi,
"Aunty azmee sannu da aiki," da fara'a a face É—inta tace "Yawwa Sehrish ina fata kin washe yanzu,"

Murmushi sehrish tayi tare da cewa "eh Alhamdulillah da wani aiki da zanyi yanzu?. ta tambaya tana kallonta,
Azmee tace "a'a yau fa hutu ki ke hajiya sehrish, na ma kammala komai sai zuwa anjima zamu shirya dinner atare amma pls karki maimaita shiriritar É—azun,"

Ƴar dariya sehrish tayi kafin tace"Insha Allah" ta ɗan yi shiru tana so ta zuba abinci, taci amma ƙunya take ji saboda 6arnar da tayi na zubawa farfesu abun wanki,"

"Ke bakya jin yunwa ne wai? kullum sai na ce ki zuba abinci ki ci, ko saina fara sa miki bulala ne?

Azmee ce tayi maganar cikin zolaya, dariya sehrish tayi da cewa "dama ynx nake so na zuba ne,"
ƙara sawa tayi ta ɗauko tray,
Bin ta da kallo azmee tayi ganin ta jera pancakes, ga sandwich ta kuma haÉ—a da scrambled eggs, duk a ciki a haka bai ishe ta ba sai da ta hada da fried chicken, taje ta ajiye ta kuma dawo ta haÉ—a cornflakes a cup ta zazzaga uwar madara, ta tsula sugar,
Zama tayi asaman dining chairs ɗin na kitchen tana kallonsu, tunani take da me zata fara, muryar azmee ce ta katse ta da cewa "Sunyi miki haka? Ko zaki ƙara da wani abu ne? 😒
sunnar da kai sehrish tayi cikin jin kunya tace "sun isa haka," Wato su sehrish banza ta samu, dama talaka bai iya samun wuri ba, ni bama wannan ba, Soyayyar babban yaya tasa ta manta da halin da su Hosana ke ciki, ada in zata sa abu mai daɗi a bakinta sai ta tuna dasu tayi kuka sosai, amma ynx ba wannan mgnr, *BABBAN YAYA* kawai 😥

Sandwich ɗin tafara ɗauka tana ci, tunanin ta nakan *RAFAYET* azmee na lura da ita duk wani motsi da sehrish zatayi murmushi take yi, hankalin azmee bai kwanta da irin wannan zauce war da Sehrish tayi ba akan Babban yaya, tabbas soyayyace mai ƙarfin gaske take masa, tunkan tasa shi ma a idonta, da jin sunansa kawai ta faɗa tarko, balle ynx da tasa shi a ido? hakika jikin azmee yayi mugun sanyi tunawa da Junaid, bawan Allah wanda kullum burinsa ya ga yarinyar cikin farin ciki,
Babu wanda yasan da zaryar da junaid ya ke yi izuwa ɗakin azmee, kullum roƙonta ya keyi akan dan Allah taba sehrish kulawa ta musamman, komai sehrish take buƙata, tagaya masa zaiyi mata,
Junaid ba ƙaramin so ya ke mata ba, 😿
(Tabbas akwai tashin hankali, ni babban damuwa ta, waɗannan zuciyoyin guda biyu ❗‼⁉

Wane hali zuciyar sehrish zata shiga ita da ta kwallafa rai akan mutun da ya kasance misoganist ! ya ƙi jinin mata, baya sha'awarsu basa gabansa, balle ma maganar aure, shin wane hali zuciyar junaid zata shiga ❓shi da bashi da ƙoshin lafiya, ga soyayyar wadda bashi ke gabanta ba, yayansa take so ❗ wane hali hosanna da Jahad zasu shiga in suka amince da bukatar Inspector Eesha!? shin za'a yanke musu hukuncin kisa ne, ko zasuyi zaman gidan yari ne ⁉ 😭😭😭
Me zai faru idan su Aunty Babba Suka ziyarci Bokan nan na dajin enugu wato baba Iblis wanda muddin yayi asiri sai ya ci mutun jazamun, in ba wani iko na ubangiji ba 😿 dole fa ku gyara zama domin yanzu cakwakiyar ta soma 🔥🔥🔥

"Idan kin kammala cin abinci, inaso mu zagaye gidan nan tare dake ki ƙara ganin haduwarsa sosai," murmushi sehrish tayi wadda tuni cikinta ya fara birkice mata dakyar ta iya cewa "tom aunty azmee, amma sai na fara shiga toilet shaf shaf,'

Azmew tace "dama nasan wannan jazamin ne ae, zuba miki ido kawai nayi Allah, ni zan shiga ciki, in kin kammala ki same ni a bedroom É—ina, kyau ma mu fara sallar azhar naga time yayi,"

Sehrish ta amsa da toh, cikin sauri ta kammala, sbd dama a ƙagare take ta zagaye gidan, ta gaji da zama wuri ɗaya, daga bedroom sai kitchen, shaf shaf ta wanke kayan da ta 6ata, sannan ta wuce ɗakinta toilet ta shiga, bayan ta fito da alwalarta tayi sallah, sai wurin addu'a ta tuno da su hosana, tayi musu addu'a sosai, kafin ta cire hijab ɗin ta tura a wardrobe, dama already dress ɗinta na maza ne ajikinta, gashin baki kawai ta aza, tagyara sumar kanta, ta naɗe ta cikin hularnan tashi da kwakwa, daga sama ta bi da mayafi ta yi kamar turban, ta saki jelar mayafin gefe,

A tare da azmee su ka zagaya, sehrish tasha mamaki, ganin haÉ—uwar katafaren gidan, ko'ina take bi da kallo kamar wuyanta zai 6alle, muryar azmee ce ta katshe ta da cewa "kin ga nan, wurin motsa jiki ne wato gym, bi da kallo sehrish tayi an kawata abun wurin da komai na motsa jiki, kamar ta shiga ta jaraba itama haka taji, amma taci alwashin watarana sai ta shiga ciki tayi gym itama,

gaba su kayi suka sake zuwa wani room ɗin, "nan kuma ɗakin bincike kenan ," jinjina kai sehrish tayi ganin wasu matsiyatan Computers gava ɗaya na'urori ne a ɗakin ke sarrafa komai, wurare daban daban ta nuna mata Hada weapon's room ( ɗakin ajiye makamai) , hada haɗaɗɗen parlor wanda suka ware domin yin kallo acikinsa, an ƙawata shi da faskekiyar plasma tv, ga speakers na sauti, ga ƙawatattun kujeru aciki da sauransu,

daga nan suka fita can harabar wajen, sehrish tasha kallo sai taga kamar tabar 9ja ne, saboda cikin gidan duniya ne, bakomai ya ƙara burgeta ba face swimming pool ɗin da tagani, mai faɗin gaske ruwan ciki yayi blue sky, daga gefe a hada kujerun shakatawa da table, bata ga komai ba sai da su ka shiga garden Aljannar duniya, juyawa tayi ta kalli azmee tare da cewa "har yanzu muna cikin nigeria"? dariya azmee tasaki tare da cewa "of course," jin jina kai tayi wasu komai na cikinsa kore ne 🌲, sai aka ƙawata shi da Red & yellow flowers 🌹🌻, ga wani tsaftataccen ruwa dake guda na (waterfalls) yana gangarowa daga jikin dutsi zuwa ƙasa ya taru acikin pool yyi kamar lakes, Bakomai ya burge sehrish ba face agwagin dake ciki suna yawa farare,

"Aunty azmee gaskiya gidannan ina kokwanto anya ba hotel bane, girmansa da haÉ—uwarsa yayi yawa," tayi maganar tana kara bin ko'ina da kallo, azmee tace "haryanzu fa akwai sauran wuraren da baki gani ba, ynx dai na gaji mu zauna mana,
Chapter 51 · 0% Book details