← Book details Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 86

Sashe 65

Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Miƙewa tayi tare da cewa"Bari na kawo maka snacks da abunsha," dakatar da ita yayi da hannunsa yace"No need thanks" Murmushi ta ɗan yi tare da komawa ta zauna, tana ci gaba da kallon fuskarshi, kafin ta mayar da idonta kan surar jikinsa tana haɗiyar yawu, "Banason Kallo," ya faɗi yana ci gaba da dannar wayarsa, cikin jin kunya Amani ta janye idonta, tana mai mamakin taya akai haryasan tana kallonsa, Cikin kashe murya tace " Babban yaya ae dole na kalle ka, kai fa abun kallo ne, kuma ni ban ta6a ganinka ba ido da ido, shiyasan ya,' ta ƙare maganar tana cizon pink lips ɗinta alamar ya cije ta, shi kuwa ba ta ita yake ba, burinsa yayansa Abbas ya ƙaraso, su ga juna, yayi kewarsu sosai, Muryarta ce ta ƙara ratsa shi "Babban yaya, ko dae baka farin ciki dani ne amatsayina na matar yayanku ishaq,'? ta yi maganar tana kallonsa, "Why'? ya tambaya har time ɗin bai ɗago ya kalleta ba, gyara zama tayi tare da cewa "to naga u don't even want to look at me, atlease u should put ur eyes inside mine," Amani ba ƙaramin takura masa tayi ba, ji yake tamkar ya tashi yabar gidan, don baisan nacin magana, "Plsss babban yaya," dogon tsoki yaja tare da cewa "becareful with me," gabanta ne taji ya faɗi jin gargaɗin da yayi mata, tabbas mace bata gabansa, Jiki a mace Amani tabar falon, cikin bedroom ɗinta ta koma, jiki na rawa ta ɗauki phone ɗinta dake ajiye asaman pillow ta dannawa AUNTY BABBA kira, Ringing 3 ta ɗaga kiran bayan sun gama gaisawa cikin zumuɗi Amani tace "Aunty ko kinsa cewa SGR na cikin gidan nan yanzu haka? tayi maganar da murmushi a face ɗinta, A can 6angaren kuwa cike da mamaki aunty babba tace "Are you serious? shi da kansa kuma"? dariya Amani tayi tare da cewa "wlh kam,baki ji yadda naji ba dana gansa duk da rashin maganarsa, yaci ka ji dakai wlh," Aunty babba ta fashe da dariya ta cikin wayar tare da cewa "ki barshi zai zo hannu ne yanzu dai ya maganar Ziyartar wurin bokan nan baba ibliss? kin sama mana kuɗin? Ajiyar zuciya amani tasaki tare da cewa "tukunna dae auntyna, ina nan ina tarairayarsa, ina so nabi komai a sannu, insha Allah nan ba da jimawa ba, zaki ji daga gare ni, da kaina ma zanzo kd na kawo miki ziyara," Aunty babba tace "To shikenan, Allah ya kaimu lpy, shiri na musamman zamuyi, domin ganin munci nasara akan waɗannan zafafan guda biyu," sun jima suna waya a tsakaninsu, agame da yarda zasu ziyarcin wurin hatsabibin bokan nan Baba iblisssss 👹 A can ciki kuwa, dirar Abbas kenan fuskar nan dauke da fara'a kamar gonar auduga jin cewa Sgr ya kawo masa ziyara da kansa, sanye yake cikin kakinsa na sojoji daga headquater yake, yana shiga falon Rafayet ya miƙe fuska a sake suka rungume juna sosae, kamar karya sake shi haka Abbas ya ji, "Am really glad to see u bros, nayi kewarku sosae kamar kamar me," abbas ya faɗi hakan cikin tsananin farin ciki, ruƙo hannunsa yayi suka zauna a mazauni ɗaya, suna kallon juna cike da kewa, Cikin sanyin murya babban yaya yace"Nayi kewarku sosae, har ma bazan iya faɗa ba," ƴar dariya abbas yayi tare da cewa "Wake koya maka hausa ne? nayi mamakin jinta raɗau abakin ka duk da har yanzu da sauranka, last time da kazo daker kake fahimta in anyi magana," Jinjina kai Babban yayan yayi tare da cewa " bana so nazo ƙasar nan ne arinƙa gulmata bana ji, that's why na dage na koya saboda su Ammi," Dariya abbas yayi sosae jin abunda Rafayet yace, a wasa wasa shima ya iya zolaya in yaso , bayan abbas ya tsagaita da dariyar ne yace "Am wai baku gaisa da Amani ba? naga ko abunsha ma bata kawo maka ba," "No tazo mun gaisa, ni nace bana son komai shiyasa," Jinjina kai Abbas yayi tare da cewa "meyasa baka son shan abu ko cin abu in kazo gidan mutanene nifa ɗan uwanka ne jinin ka, shikenan nima duk ranar da kayi aure nazo gidan ka, matarka tayi mun tayin abinci bazan ci ba," wani kallo babban yayan yayi masa tare da ɗan ta6e baki kafin yace "NEVER," wato bashi ba aure har abada, Murmushi abbas yayi yana kallonsa yace "hmmm haka dayawa irinka suke cewa but at the end sai ga lamarin ya sauya, irin ku ma mace tafi juya ku, sannan maza irinku da basa ra'ayin mata ko aure wlh basu iya faɗawa tarkon so ba, haukace wa suke yi idonsu ya makance lokaci guda," . Abbas ya ƙare maganar da zolaya yana kallon fuskar Sgr, wanda ya tamke fuska yana sauraran bayanin yayan nasa," . Miƙe wa yayi tare da cewa "Ni zan wuce," "Haba Babban yayansu, nasan magana tace tayi hurting ɗinka am sorry 4 that, it was a joke," Abbas ya faɗi tare da miƙewa shima ya ruko hannunsa cikin lallami,' "Ba abunda kake tunani bane yaya abbas, time ɗin tafiyana ne yayi, saboda ko wane lokaci na rayuwata yana da amfani, kuma a ƙirge yake" Murmushi abbas ya saki yana jinjina kai yace "kuma fa hakane, na tuna da wannan, ae nama gode ssae da ziyarar da ka kawomin, Allah yabar zumunci," ya faɗi hakan a yayin da ya matsa suka sake hugging junansu, sannan su kayi sallama, ........................SEHRISH............................ Bayan sallar La'asar wuraren ƙarfe 5 na yamma, suna kitchen ana ta faman girke girken abincin dinner, ƙamshi ya gauraye ko'ina, tana tsaye tana yayyanka kayan lambu a saman chopping board, fuskar nan a washe abubuwa biyu na mata yawo aranta, na farko shine wanene wannan wanda xata haɗu dashi yau a garden wanda yasan cewa ita maca ce, na biyu kuma shine new phone ɗin da aunty azmee tace an bata kyauta, bakomai take ɗauki da wayarnan ba fa ce shegen son kallon fina finai dake gare ta, ga son sauraron music gata mayyar selfy kamar hafsat bature 😇 "Ji mana, ki dubamin girkin nan , ynx zanje na dawo," azmee ce tayi maganar a yayin da take fi ce daga kitchen, .. Cikin sauri sehrish tace "To aunty azmee," Ajiyar zuciya tasaki tare da cewa "ko ƙarfe nawa yanzu i ave to check the time, ina da baƙo fa," ta faɗi cikin zumuɗi tana kallon agogon dake manna a bagon kitchen ɗin, shida saura murmushi tasaki tana faɗin "lokacin haɗuwa ya kusa Ya Allah ka bani ƙwarin guiwar tunkarar koma wanene wanna," ta faɗi tana nuni da knife ɗin da ke hannunta, Azmee kuma da ta fice bedroom ɗin junaid ta wuce, domin ta ƙara tunasar dani haɗuwar da ta shirya musu da sehrish," Sai faman knocking take yi, amma sam baiji ta ba, yana tsaye riƙe da ƙugu gaban closet ɗinsa ya buɗe yana kallon jerin kayansa, yama rasa wanne zai sanya domin haɗuwa da sehrish ɗinsa for the first time, sai zabga murmushi yake yi ba magana, tun da azmee ta sanar mishi da haɗuwarsa da sehrish yarasa tsaye ya rasa zaune, sai rawar kai da zumuɗi yake, kamar sabon ango 😌 daga shi sai short ajikinsa, sai da azmee ta ɗaga murya da cewa "Junaid ka buɗe aunty azmee ce inason magana da kai," Ae yana shaida muryarta a kunnansa jiki na rawa, yayi hanzari zuwa ya buɗe mata kopan, yana sakar mata murmushi, "Ango kasha ƙamshi," azmee ta faɗi cikin zolaya, "Ka ce ka shirya haɗuwa da amaryar taka kenan,"? Cikin ɗan jin kunya yace "Kai aunty azmee, nifa kunya nake ji," yadda yayi maganar da shagwa6a yasa ta yin ƴar dariya tace "uhm junaid kenan Romeo shugaban ƴan soyayya yau zai haɗu da juliet ɗinsa akaro na farko, yakama ka rubuta wannan a diary ɗinka saboda tarihi," . ɗagowa yayi da dariya a fuskarsa yana kallon azmee jin abunda yace, "Insha Allah aunty azmee, dole na rubuta wannan, saboda rana ce ta farin ciki da bazan ta6a mantawa da ita ba arayuwata," cikin sanyin murya junaid yayi maganar, alamar yana jin abun aransa sosae, Azmee tace "hakan yayi kyau, ynx dae ni zuwa nayi na ƙara karfafa maka guiwa kasan kai mutumina ne, inaso ka saki jiki sosae, sbd rishi yarinya ce mai shegen tsoro, tana da wani hali dana lura dashi yanayin yadda mutun ya tarbe ta itama haka xata kar6esa, i mean yadda kasakar mata fuska haka itama zata sakar maka tata, kuma zata saki jiki da kai sosai kamar ɗan uwanta, Junaid nasan baka da ƙanwa mace, gaba ɗayanku maza ne, to inaso ka ɗauki sehrish amatsayin ƙanwarka, kai kuma ka zama tamkar yayanta mai share mata hawayenta, kuma abokin shawararta," natsuwa junaid yayi yana sauraran maganar azmee har cikin ransa bayaninta ya kwanta masa aransa, Bayan ta kammala maganarta ta tace "Junaid ni zan koma kitchen, nasan gobe akwai labari mai daɗi daga wurinka, zanji ya haɗuwarka da juliat ta kasance," Dariya kawai junaid yake yi, yana faɗin "insha Allah aunty azmee, ngde ssae ke ce silar farin ciki na," Murmushi azmee tasaki tare da juyawa ta fice tana cewa "Karka manta kaifa ɗane a wurina junaid, cikina ne kawai baka zauna ba, amma ni na shayar dakai ina alfahari da hakan," Rufe door ɗin yayi, tare da daka uban tsalle na murna, runtse idonsa yayi tare da dunkule hannunsa yana faɗin "Can't wait to seeeeeee you Sehrish My dreamy Girl............. koma wa kitchen ɗin azmee rayi suka ci gaba da aiki, tana lura da sehrish cikin sauri take yin aikinta fuska ƙumshe da murmushi, ba don komai ba sai don tayi saurin taje tayi wanka ta kimtsa bayan sallar magriba ta wuce garden wurin wanda aka ce zata haɗu dashi 😘 💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕 ..............Twins.................................... kwance su ke rungume da juna a katafaren ɗakin da suka ɗauka na hotel ya haɗu iya haɗu, da alama sun gama biyan buƙatar junansu ne bacci ya kwashe su, sam babu sutura ajikinsu zir suke manne da juna kamar tip da tyre, Wayar Jahan ce dake saman bedside table ta soma ringing taken waƙar Shape of you ta Ed shareed," Almost 3 times tana ringing an rasa wanda zai ɗauka cikinsu saboda daɗin bacci, har calling ɗin yayi rejecting, wani
Chapter 65 · 0% Book details