← Book details Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 86

Sashe 21

Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

yayi wani irin ƙwaƙƙwaran juyi ya haɗa da ita duka ya rungume ajikinsa kuma ruƙo bana wasa ba, 😳 Allah kaɗai yasan tashin hankalin da sehrish ta shiga, zuru zuru tayi da ido, hancin ta na shaƙar ƙamshin turarensa, lokaci guda ta shiga cikin yanayi, ganin bata da wata hanyar tashi yasa ido ya raina fata, bin wuyansa tayi da kallo gwanin kyau, ji take kamar ta gartsa masa cizo a wannan lallausar fatar tasa ko ta samu ta tsere, tashin hankalin da ba'a sa masa rana, ga azmi na jiran ta a kitchen saboda safiya ce akwai aikin haɗa breakfast, da sauran aikace aikace, ga junaid ya maƙale ta a jikinsa ta rasa yadda za'ae ta fita, tana cikin wannan tunanin na yadda za'ae ta raba jikinsa da nata, ya ƙarayin wani kwakkwaran juyi, atare suka mirgina ƙiris ya rage su faɗo ƙasa, saboda tsabagen ƙiɗima tuni taji fitsari ya zo mata, komai ya tsaya mata cak, bugun zuciyarsa kawai take saurara, Sun ɗau 30 mins a haka, ta ƙura masa ido yayin da shi baisan meke wakana ba, Wayarsa ce ta soma ringing da ƙarar gaske, wannan sautin ne ya dirar masa a tsakiyar kunnansa, nan ya soma nuƙu nuƙu buɗe ido, tsananin tsoro ne suka bayya na a fuskar sehrish, yana ƙoƙarin buɗe idonsa, cikin sauri ta janye hannayensa daga jikin ta, ita kanta batasan ta iya wannan ƙarfin halin ba sai yau, juyi tayi da ƙarfi ta sulale a ƙasan bed ɗin ta durkushe a ƙasan, hankali a tashe kamar mafarki haka junaid ke kallon lamarin, tabbas ya ga gifcin mutun daga jikinsa, amma sai ransa ya basa cewa duk cikin bacci ne abunda ya gani, hannunsa ya kai tare da ɗaukar wayar tasa dake ta faman buga ringing, tare da karawa a kunnan sa cikin shagwa6a ya ce "Assalamu alaikum babban yaya na, am angry wit u cos i ave been waiting for your call since yesterday night, " ya yi maganar tamkar yana a gabansa, Sehrish da ke zuƙunne kasa cikin tashin hankali, tabaza kunne tana sauraron wayar da junaid ya ke yi, jin ya ambaci sunan babban yaya yasa ƴan cikin ta ƙadawa, sam tarasa dalilin daya sa in aka ambaci sunan nan take jin faɗuwar gaba, ganin yayi nisa a wayar tasa ne yasa tayi tunanin ta rarrrafe ta fi ce daga ɗakin, don haka ta soma tafiya a ɗurkeshe a ɗurkushe, cikin sanɗa take rarrafa wa, Ko waiwayen bayanta bata yi burin ta ta fice daga ɗakin before ya ankara, junaid kuwa dake maƙale da waya yana zabga wa yayan nasa shagwaba sam bai lura sai da yayi wani kwakkwarn juyi yana faɗin "just come back home i wanna see you serious..." bai ida maganar ba karaf idonsa suka sauka akan ɗan aikin nasu wanda ke tafiya cikin sanɗa yana rarrafawa zai fi ce, Ƙura ido 👀 junaid yayi yana kallon ikon Allah, acikin ransa yana cewa" lallaima wannan ɗan rainin hankalin wato raini ya fara shiga tsakanin mu, bari in tsara in ga ƙarshen game ɗin, sam batasan ya ganta ba,lokacin da ta isa ƙofan ɗakin ta saki wata irin ajiyar zuciya, maimakon ta fice ba tare da ta waiwaya ta kallesa ba, amma ina ranta ne ya bata ɗan juya mana ta kalle sa tun da ta tsira, juyawa tayi a hankali tana sauke ajiyar zuciya, karaf idonsu ya shiga na juna, ganin dagaske ita yake kallo ido cikin ido ya ganta asiri ya tonu, hannu ta shiga tafawa da yake ta kware wurin iya fauzewa sai kawai ta 6a66ake da dariya hhhhhhhh kamar mahaukaciya, Tsananin mamaki ne yasa junaid yin kasaƙai yana kallon ikon Allah, bata dakata da dariyarba cikin salon wayau da dabara ta fice tana tikar dariya, hada janyo masa kopa da rufe wa, tana ganin ta fito ta tsagaita da dariyar tare da aza hannunta a saitin zuciyarta tace"wai Allah na tsira" da gudu ta sauka kasa ta wuce kitchen, har ynx junaid bai dawo daga duniyar mamakin da ya tafi ba, tunda ya ke a rayuwarsa ba'a ta6a raina masa wayau irin na yau ba, ya ma rasa mai zaiyiwa ɗan aikin nan nasu, wane hukunci zaiyi masa, "Zamu haɗu" ya fada a fili, kafin ya tashi ya shiga cikin toilet, gaban wash basin ya tsaya, yakai hannu ya ɗauko toothbrush ɗinsa, ya matsa maclean a jikinsa, ya shiga goge hakoransa,a hankali yake komai saboda tunanin mai aikin nan nasu daya tsaya masa aransa, Bayan ya kammala ya kunna mixer tap ɗin ruwa ya soma zubo wa wanke mouth ɗinsa yayi sannan shima brush ɗin ya wanke sa ya mayar dashi cikin holder dinsa, wanka yayi shaf shaf ya dauro towel a west ɗinsa, ya fito yana matse sauran ruwan dake ɗiɗɗiga a sumar kansa da hand towel, a gabn mirror ya tsaya yana kallon zunzurutun kyansa, a nan ne idonsa yakai saman fatar wuyansa, wani dogon gashi ya gani siriri mai tsayin gaske, tsananin mamaki ne ya kamasa, a cikin ransa ya ke faɗin "ynx duk wankan danayi amma wannan gashin bai bar jikina ba kodai har yanzu ban iya wanka bane haba junaid be a big man mana kana abu sai ka ce na ƴara," hannunsa yasa a hankali ya tsafko gashin, ya ɗago sa izuwa saitin eyes ɗinsa yana kallo, sai lokacin ya lura cewa tabbas wannan gashin mai tsayi bana sa bane to na wanene !!!! 😱 Sannu da zuwa mlm tukr, acewar azmi wadda ke magana tana kallon sehrish dake shigowa cikin kitchen, ɗan murmushi tayi tare da cewa ........................ Page 23-24
Chapter 21 · 0% Book details