← Book details Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 86

Sashe 70

Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A tsiyace ya shigo da motar layin gidan a dai dai gate É—in gidan ya dakatar da ita, ya shiga buga uban horn kamar zai tada motar gaba É—aya saboda karar da take yi,
"Kai!! uban waye ke mana horn haka,"? É—aya daga cikin sojojin dake gadin gidan ne ya tambaya da É—aga murya, akwai yasamu amsa dai dai dashi sai ji yayi ance "Ubanka ne kazo ka duba,"
Abun ya basu mamaki aiko afusace sojojin nan suka tunkaro motar kamar wasu zakuna har haÉ—a hannu suke wurin buga glass É—in motar tare da cewa "Come out !! ,"
"Ae basai kunbar umarnin na fito ba, É—an tasha ne ni dai dai daku,"
Zuge glass ɗin motar yayi tare da sa hannu ya cire ƙumeman glass ɗin dake manne a face ɗinsa yace "Akwai magana,"?
Shiru su kayi dama ransu ya basu cewa shegen ne, ae duk duniya ba mai musu haka sai shi tantirin É—an duniya,
Bama cikin hayyacinsa yake ba ae mafi yawancin lokaci a buge yake yasha yasha har takai masa karo,"
dogon tsoki ya buga tare da cewa "abani hanya na wuce kona bi takan mutun ba ruwana, kuma in na kashe mutun na kashe banza abanzance,"
Ransu yayi mugun 6aci a dole suka matsa mishi ya shige babban gate ɗin gidan da motarsa yana raira waƙa,"
Parking ɗin motarsa yayi sannan ya fito hannunsa riƙe da kwalbar giya, jikinsa na sanye da t-shirt baƙa sai wando crazy jeans ɗinnan ne, wani irin ɗan iskan aski ne akansa na shaiɗanu jigunannun ƴan duniya gefe da gefe an aske sumar kan, tsakiya kuma an mikar da wata tsaye ba ladabi, wuyansa na sanye da sarƙa yayin da kunnansa ke manna da earrings kai kace ba musulmi ba, saboda kwata kwata bai kama da musulmai ma, don kyau fa akwai kyau kana ganinsa ka ga bafullatani sak, duk da ba fari bane sosai amma yana da hasken fata mai kyau, yana da tsaga ta fulani agefen fuskarsa,
daker yaja ƙafarsa izuwa cikin babban falon gidan babu kowa aciki wayam, ɗaga murya yayi yadda kowa zaiji sa yace "NADAWO !!!! Hhhhhhhhh Woooo !! Yaro ya dawo gidan Ubansa !!! Abba !! Gani fa nadawo !! ɗanka HAROON ya iso dira ta kenan na ƙaro sabon wulaƙanci buhu buhu hhhh,

Gaba É—aya hayaniyarsa ta cika musu kunne kamar zararre haka yadinga sambatu,
Ba arziƙi suka soma fitowa kowa jikinsa sanye da kayan bacci kanal yousouf ne yafara fito wa yana buga tsoki sai Khaleed da jabeer da irfan kowa ido cike da jin bacci ya katse musu baccinsu, atare twins suka sauko daga upstairs hannunsu cikin na juna sai hamma suke yi,,
Abba ma tare da junaid suka fito sanye cikin phyjamas hannunsu cikin na juna, kowa sai faman buga tsoki yake yi a ƙuntace, tun da suka ga Commender haroon gabansu ya faɗi hankalinsu ya tashi ainin, sam babu mai farin ciki da zuwanshi duk da kasancewarshi ɗan uwansu na jininsu amma munanan ɗabi'unsa da halayyarsa tasa sun tsane shi sbd mugune na bugawa ajarida,
Cike da takaici suke kallonsa kwashewa ya sake yi da dariya tare da cewa" ƙananin ƴan iska sun bayyana ga kuma fararen balbelu," yayi maganar yana nuna su Twins da fawan da hannu ɗaure fuska su kayi har time ɗin ba wanda ya tanka masa binsa kawai suke da ido,

"Kutmelisiiii! Ni kuka maida shashasha ina magana kowa ya zubamin ido wato ga zautacce ko?baku farin ciki da zuwana ne, ae nayi tunanin ina zuwa zaku watso aguje kamar karnuka ku rungumeni ku sunbace ni muuuaaah a baki na,' cike da futsara Haroon ke musu magana baya jin kunyar Abbansu,
Gaba ɗaya duk wannan suratan da Haroon yake yi a kunnansa kaf ya gama fusata yagama hasala, aiko a harzuƙe ya ƴunkura tamkar zaki yabi ta gefen Sehrish ya wuce ita kanta ta tsorata sosai ganin yadda Sgr ya fusata,
A wani irin slow sauri sauri yake tattakowa izuwa downstairs É—in, yana idasa sauko wa kai tsaye inda haroon yake tsaye riqe da beer a hannunsa ya tunkara,
Kanal yousouf ne kawai ya lura dashi wani shu'umin murmushi yasoma saki saboda yasan mai zai faru,
Haroon na cikin wannan sambatun baiyi wani aune ba yaji saukar wasu zafafan maruka ajere saman kuncinsa,

Sai gashi ƙasa baje saman tiles idonsa na facing sama, wato wasu irin black stars yagani a ƙwayar idonsa masu wutsiya, kowa dake wurin bakinsa kumshe da dariya,

Sgr kuwa kara naÉ—e hannun rigarsa yake yi,
daker haroon ke kallonsa muryarsa na rawa yace "Ya Allah ka yafemun in zunubi nayi ka haɗani da wannan Ifritun minal jinnin, wlh danasan cewa kana acikin gidan da ba abunda zai kawo ni, Abba mai yasa baka sanar dani cewa Babban yaya na cikin gidan nan ba...? Yayi tambaye agalabaice har lokacin bai samu ya miƙe ba yana daka kwancen yake sambatun nasa idonsa na kallon ceilling,

mayar da hannu Sgr yayi ya damƙi wuyan rigar haroon da hannu guda ya ɗago shi tare da Buga shi ƙasa ya ƙife a susuce, shin wai ina kwalbar giyar dake hannun haroon ae tuni tayi gefe guda ta tarwatse,
Ganin Sgr na ƙoƙarin sake kai hannu yakaiwa haroon wani naushin yasanya abban su cikin sauri ya riƙo hannusa yana cewa "Ya isa haka pls rabu dashi ae yaji jiki,"
Jinjina kai Babban yayan yayi yana cije lips É—insa da ace abba yabarsa wannan naushin da yaso yakaiwa haroon da to tabbas sai yayi jinya a gadon asibiti,
ɗagowa haroon yayi ido luhu luhu yana kallon babban yayan nasu murya na rawa yace "Yanzu babban yayan mu don rashin imani ka daddage ka dunkule wannan hannun naka ƙirar samudawa da adawa bakaji komai ba ka jibge ni agaban ƙanne na,"? yayi maganar akasalance yana kallonsa,
Wato bai daddara ba rae abace sgr yace "kai wai waye ya kawo wannan É—an iskan acikin gidan nan !?
"Da ƙafafuna nazo," haroon ya bashi amsa a raunane, mayar da idonsa yayi akan haroon yana huci in ya biyewa haroon to tabbas zai iya halaka shi a wurin nan, don shi bakinsa bai mutuwa ana bugunsa yana magana sai dae akashe shi,

In kina so ki gode mun kiyimun share na novel ɗina 🪩 Kar a Manta da Comment 👍👏🤝*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ❤️💋

*Episode 83-84*

*Hafsat Bature Moh'd*

Meaning of Name Rafayet, arabic name ne, kuma sunane na Mace da Namiji both suna amfani dashi, Ma'anarshi *Ur highness*👑,*sublimity*high rank*,
*power*💪
Chapter 70 · 0% Book details