← Book details Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 86

Sashe 41

Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri ta shiga toilet, wanka tayi sannan ta fito, jikinta na ta faman rawa, kayan nan da tafara zuwa aiki dasu gidan at her first day, su ta É—auko, wato burgujejan wandon nan Falazu,
Wanda ƙafar mutun 5 sai ta shiga ciki ba tare da ya matse su ba, pink colour sai riga ta maza launin ruwan madara (milk) mai ma6allai dayawa ajikinsu da aljihuna, ta gyara gashin bakinta ya zauna raɗau, sannan ta nannaɗe sumar kanta kamar yadda ta saba,
ta aza hukar nan, yar tashi da kwakwa sannan ta aza kuma mayafinta launin wandon daga saman hular ta naÉ—e shi,
sai da tatabbatar da komai ya zauna raÉ—au,
Sannan ta fito gabanta na faÉ—uwa saboda taji alamun bakin nan fa sun iso, suna cikin gidan batasan ya zasu kalleta ba, ko'ina na jikint rawa yake yi saboda zazza6in da take ji,
tun daga inda take ta hango su a zungureran table din, binsu da kallo tayi, musamman aunty babba da Amani da tagansu Æ´an larabawa, ga kuma su ishaq da abbas da abuhaisam da sauran duk batasan su ba, amma kamanninsu ya tabbatar mata da cewa yayyansu Kanal yusif ne,
"To fa wanene wannan kuma, baƙon saurayi ku ka yi ne:? .
Sai da sehrish ta firgita jin maganar aunty azeema, lokaci guda kowa ya ɗago yana kallonta 👀
Cikin sauri azmi dake tsaye akansu suna saving É—insu dasu chef ummu tace "he's our new house boy, tukur yana taimaka mun wurin aiki sosai,"
Jinjina kai azeema tayi tare da cewa "that's gud"
ƙarasawa azmi tayi ta ruƙo hannun sehrish tare da janta izuwa kitchen suka tsaya, sannan ta kalle ta tace "meke damunki ƙanwata na shiga na Same ki jikinki zafi baki lafia ne,"
Hawaye ne suka soma zubo ma Sehrish cikin nuna tsananin damuwa tace "aunty azmi dan Allah ki taimake ni, ke kaÉ—ai ce zaki iya taimako na a halin yanzu, ina cikin tashin hankali...'
"tell me whats happening wit u? Azmi ta tambaya,
"Aunty azmee ina ji araina cewa Æ´an uwana suna cikin mawuyacin hali, inaso naje nagansu, dan Allah ki taimakamin naje katsina na duba su koda kwana É—ayane ina tsoran na rasa su bani da kowa sai su..... .....'
kuka ne yaci ƙarfinta ta gaza ƙarasa maganar, azmi ta janyota jikinta tare da hugginta ɗinta tightly a jikinta tace....
"I feel your pain sehrish,ina mai takaicin sanar dake cewa bazai yiyu ba hakan!
É—agowa sehrish tayi daga jikinta tana kallonta ido jawur, cikin muryar kuka tace "meyasa aunty azmi"?
"Banso na sanar dake ba amma ynx dole ne kiji, sehrish kuÉ—in da na baki na aikin Æ´an uwanki, bana salary É—inki bane kawai, hada kuÉ—aÉ—en dana jima ina tarawa domin na yi amfani dasu, na haÉ—a miki duka sbd na tausayawa halin da ki ke ciki sosai, salary É—inki bazasu isa ba dole saina cika miki, a yanzu haka da nake miki magana nikaina banda kosisi domin duka na tattara miki su...."
Shiru ta ɗanyi tana wani tunani idonta akan sehrish, ita kuwa jikinta yayi sanyi ba don komai ba sai don jin cewa Azmee hada kuɗinta ta haɗa mata don ta biya kuɗin aikinsu husna, sai taji ta ƙara ƙaunar azmi sosai, tana da matuƙar tausayi, ga kyan hali
"ki daina kuka sehrish, duk kan tsanani yana tare da sauƙi, ki daina sa damuwa aranki, insha Allah ba abunda zai sami ƴan uwanki, Allah yana tare dasu, maganar zuwanki wurinsu zanyi ƙoƙari akan hakan amma ba yanzu ba,'
cike da rashin kuzari sehrish tace "shikenan aunty azmee, nagode sosai bansan da wasu irin kalmomi zan gode miki ba, narasa mahaifiyata amma gashi Allah ya bani ke alokacin da nake cike da jimamin rashin wani nawa akusa dani mai sharemun hawaye na,
Murmushi azmee tayi kafin tace "samu wuri kizauna, me kike so na kawo miki ki ci? tun da safe baki ci komai ba,' tayi mgnr cikin nuna damuwarta,
"Aunty azmee i cant eat anything now, zuciya ta tashi take yi bani da kwanciyar hankali,'
dafa shoulder É—inta tayi tace "Calm down your mind reeshi na, just ave a seat, bari na haÉ—a miki abu mai daÉ—i mana ki ci, zaki ji daÉ—i,'
Ajiyar zuciya sehrish ta saki, wuri ta samu a saman dinner table É—in dake a kitchen É—in ta zauna, tana jiran azmi,
a tray ta shirya mata abun tattaunawa, ta ƙaraso da murmushi ta ajiye mata tana faɗin"Ina mai tabbatar maki cewa indai ki kasa wannan Cheese burger ɗin abakin ki sai kin manta da duk wata damuwa da ki ke ciki, musamman in ki ka haɗa da Cornflakes ɗin Zan haɗa miki ynx da madara haɗi na musamman ,'
Wani irin sanyi ne ya ratsa reeshi haƙi ka azmi ta musamman ce acikin na musamman, cikin sanyi murya ta furta "thank u aunty azmee kina ji dani sosai, only God can rewards you,'
"Don't worry your self reeshi i just wanna see you always in happy mood, bana so naganki cikin yanayi na damuwa,' ta faɗi hakan a yayin da take ƙoƙarin juyawa,
Murmushi sehrish tayi ta zuba wa tray ɗin ido, Cheese burger ce aciki tare da hot dog ga sandwhich, lumshe idanunta tayi aranta tana tunanin me ƴan uwanta suka ci su 😥
ruwa azmi ta ɗebo a Dispenser mai zafi cikin tea cup, ta haɗa wa sehrish cornflakes yaji madara da sugar, tasan cewa sehrish akwai son zaƙi shiyasa ta zuƙa mata shi,
Ƙaraso wa tayi ta jiye mata shi a gefen tray ɗin, sannan tace "ko kina buƙatar wani abu ne?akwai sauran abubuwa da muka haɗa masu daɗin gaske,
yar dariya sehrish tayi ganin yadda azmi ke treating É—inta sai kace Æ´ar masu gida,
"oh dariya na baki?dama dariyarki nakeson gani kuma gashi naki har dimple É—in nan naki ya lotsa,'
azmi tayi maganar tana kallonta, cikin jin daɗi sehrish tace "daga ynx zan rinƙa yin dariya aunty azmee tunda kina so insha Allah,'
hannu azmee tasa tare da jan kumatunta tace "yawwa haka nake so my daughter, bari na shiga ciki, keep enjoying ur meal banda loma,' .
ta faÉ—i hakan cikin zolaya kafin ta fice daga kitchen É—in,
tana fita sehrish ta fashe da wani irin matsanancin kuka ba don komai ba sai don, tunawa da ƴan uwanta, kuka take bil haƙƙi da gaske hawaye na sintiri a face ɗinta, Allah sarki baiwar Allah, aduk lokacin da taga abu mai daɗi agabanta zata ci sai ta tuna da ƴan uwanta, wane hali suke ciki? shin sun samu abunda zasu ci kuwa, in ta tuna hakan sai taji ɗaci aranta, maganar oummansu ta tuna a inda take cewa

_sehrish ke ce mai wayau acikin ku, dan Allah duk runtsi duk wuya kada ku rabu ko bayan raina, ku haɗa kanku ina son ku sosai ƴa'ƴana rabin raina_ 😭

Hafsat Bature

*page 51 to 52*

Abban Sojoji

*💋romantic love story btwn Sehrish & Surgeon General Rafayet💋*

_Heart touching story abt a Triplet_😢

mamaki ya ke ganin taƙi ɗauke eyes ɗinta akansa, kuma bata da niyar daina kallonsa, hannunta har rawa yake yi wurin ajiye spoon ɗin da ta ɗauko,

Lumshe idanunsa yayi a hankali yana ƙare mata kallo acikin zuciyarsa yana cewa "Ya Allah ka mallakamin wannan baiwar ta ka,'

A yayin da sehrish ke cewa"
_tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan kyakkyawar surar Junaid duniya ne_💋

_shigowar azmee ne ya dawo dasu daga wannan tunanin na ƙurawa juna ido kowa ya waske_

cikin fara'a azmee tace" junaid me ka ke bukata ne na kawo maka? naga baka ci komai ba,

A cikin zuciyarsa yace"kallon ta danake koshi nake Aunty azmee"

A fili kuma yace" nima cornflakes É—in zan sha, a haÉ—o mun da fresh fruits'

"Junaid ba ka son cin abinci ko? Kafi son Æ´an lashe lashe kamar Tukur"?

Wani irin murmushi ya saki jin abunda azmee tace har time É—in idonsa nakan sehrish wadda ta mayar da idonta kan cheese burger É—in dake gabanta so take ta É—auka taci amma zuwan junaid yasa duk ta dabarbarce sai Æ´an kame-kame take

"Aunty azmee ae we are the same ni da shi,'

Azmee tace "gsky saina haÉ—a maka da farfesu mai zafi zaka ji daÉ—insa,'

Junaid yace "its ok am waiting,

zuciyarta sai faman É—ar É—ar take yi mata, kamar mara gsky koda yake ba gaskiyar ae,

Shi kam ya zuba mata ido yana kallonta, yarinyar ta kwanta masa a heart ɗinsa, just he is affected 💘

Azmee ce ta ƙaraso hannunta ɗauke da plate wanda ta zuba masa farfesun ganda aciki, ajiye wa tayi a gabansa, sannan ta koma ta Kawo masa fresh fruits ɗin daya bukata acikin wani haɗaɗɗen round tray,

sannan ta koma ta kammala haÉ—a masa corn flakes ta kawo masa,
A hankali ya furta "shukran aunty azmee'

azmee ta juya ta fice tana ɗan murmushi bata ta6a sanin cewa junaid Romeo bane na gaske sai da ya gane cewa reeshi maca ce ba namiji ba, ❣️

Ƙamshin farfesun gaban junaid ne ke ta faman kai mata hari, ɗagowa tayi tana satar kallonsa,

A hankali yake sa hannu yana ɗaukar gandar ta dahu tayi tubus taji kayan haɗi na kamshi, irin wadda daga kasa a baki zata dagargaje😋

A hankali yake turawa abakinsa yana tauna, ganin bai kara É—agowa ba yasa tayi saurin wawurar burger É—in tana turawa a baki,

Muryarsa ce ta katse ta "Ki ci a hankali," ya furta yana É—an smiling ashe ya É—ago bata sani ba

kaÉ—an ta gutsara ta maida ta ta ajiye, hot dog É—in ta dauka tana ci,

a yayin da shi kuma ya É—auki spoon yana shan cornflakes É—in da azmee ta kawo masa,

Wani tunani ne ya faÉ—o masa aransa a lokacin da yake kallon sehrish wadda take ta faman Æ´an kame kame,

Bin ta da kallo yayi aransa yace " Wani abu na ban mamaki nikam, ko ya aikai take matse boobs É—inta, suyi flat tamkar babu, dama Allah yasa su 6ace muga yarda zata yi........

Shi kansa baisan dariya ta kubuce masa ba, har ya fetsar da cornflakes ɗin dake bakinsa, zuba mishi ido sehrish tayi gaban ta na faɗuwa tsoranta kada ace wani abu junaid ya ganu wanda zaisa ya gane cewa ita maca ce,😳
Chapter 41 · 0% Book details