← Book details Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 86

Sashe 57

Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

At same time heart ɗinsu ke beating da karfi, ya jima yana mamakin wata zararriya ce wannan ta faɗo masa a ƙirjinsa haka, this is d first time da mace ta faɗa masa a jikinsa, wadda ba muharramarsa ba, babban abunda ya ɗaure masa kai yadda yarinyar ta ƙanƙamesa bama Alamar zata sake shi, yana jin duk wani moving ɗinta ajikinsa, hatta numfashi ta dake fita cikin sauri sauri, kamar jinjira haka ta kwanta masa luf tana sauke ajiyar zuciya, Mutanen dake wurin kowa yayi zuru yana kallon ikon Allah, wasu kam sai godiya suke wa Allah daya kawo masu sauƙi, har aka amshe gun ɗin dake hands ɗinta, Jahad kam wadda ke cikin matsanancin tashin hankali, ganin bala'en da hosana ke ƙoƙarin ja musu, cikin yanayi na firgici ta ƙarasa inda hosana ke jikin bawan Allahn nan ta ruƙo hannunta da ƙarfi ta fisge ta daga jikinsa tana cewa "Dan Allah kayi Haƙuri bawan Allah, ba da sanin ta tayi hakan ba, she did it unintentionally, tana da ta6in hankali ne.....' muryar na rawa Jahad ke kora masa bayani, Har time ɗim bai cire face mask ɗinsa ba, kuma bai janye idonsa daga na Yarinyar ba, "Ki rabu dani !!!!" honasa ta faɗi tare da cire hannunta daga na Jahad ta matsa wurin mutumin nan, da ta faɗa mawa ta sa hannunta cikin nasa ta riƙe kam tana kallonsa cikin muryar kuka tace "dan Allah ka rabamu da waɗannan masu baƙaƙen kayan wlh sun takurawa rayuwarmu, duk inda mu ke bin mu suke yi, wlh ba mu bane muka kashe ta ba, mun faɗa musu sunki yarda, ni dai kace su rabu ni in ba haka wlh zuciya ta bugawa zatayi na mutu kowa ya huta.....' "Hosana !!! Ba ki da hankali ne !! Kinsan wanene shi ki !! meyasa ki ke tona mana asiri ne agaban mutane," jahad ce tayi maganar ranta a 6ace ta janyo hosanar da karfin gaske ta dawo gefenta, Su dae mutanen dake tsaye tare da police ɗin sun zuba ido suna sauraron su, Rai a 6ace hosana ta sake fisge hannunta daga na Jahad cikin ƙunar rai tace "ki rabu dani, ki ƙyale ni nace !!! meyasa kowa bai son mune !! Laifin me muka aikata, babu mai ƙaunar mu wlh Jahad ba zan koma cell ba sai dae a shigar da gawa ta, amma bani ba,' tana gama fadar hakan ta koma wurin mutumin nan dae dake a tsaye, ta zura hannunta cikin lallausan tafin hannunsa ta rike gam, ta marairaice masa da kyawawan idanuwanta tace "Dan Allah ka tafi dani,ka da kabarni anan, bana son ganin waɗannan masu fararen kayan (wato likitocin dake tsaye da nurses ɗin dake wurin) kuma bana son waɗannan masu bakaken kayan," ta faɗi tana nuna ƴan sandan dake tsaye baki asake suna kallonta, kwantar da kanta tayi a damtsen hannunsa, sannan tasanya dukkan hannayenta ta rungumo nashi, (mutu ka raba kenan) Lumshe idonsa yayi a hankali, sai lokacin kallon police men ɗin dake tsaye a wurin yace "wane irin shashanci ne yasa ku kabar yarinya harta kwaci bindiga daga wurinki!!"? Ya tambaya yana kallonsa, Rai a6ace wani inspector yace "kaga malam ka iya bakinka, mu jami'an ƴan sanda ne munsan me muke..." tunkan ya ƙarasa major ɗin dake bayansa wanda ya fusata rai a6ace yace "Ka iya bakin ka !! Kasan wanene shi!!!"? "maganar wanene shi bata shafe mu ba, mu dae a bakin aikin mu mu ke," wani inspector ne ya bashi amsa a yayn da ya fiddo da ankwa alamar zai sanya masu hosana, Itakam ƙara kanƙameshi take yi, gaba ɗaya ta gama kashe mishi jikinsa, daurewa kawai yakeyi, "Laifin me suka aikata"? Ya tambaya yana kallon ƴan sandar, Wannan copral ɗin ne yayi saurin cewa "ana suspecting ɗinsu da kisan wata tsohuwa wadda take riƙonsu," Shiru ya ɗanyi tare da jinjina kai, kafin yace "Cancel the case (akashe case ɗin)" ɗagowa su kayi jami'an ƴan sandan suna kallonsa cikin mamakin jin abunda yace, a fusace wannan inspector ɗin yace "malam wai wanene kai !! dame kake taƙama ne !! kaga ka kama gabanka kawai cikin salama, in ba haka ba, zamu haɗa dakai mu tafi police station.....' Jikin major ɗin dake bayansa har tsuma ya ke yi wurin cewa," Shut Up Stupid !!! ka iya bakin ka ƙaramin ƙwaro ko kuma nayi ƙasa ƙasa daku a wurin nan....' cikin hanzari ya dakatar dashi tare da cewa "i did not allow u to talk again, last warn,' Shuru major ɗin yayi sai faman huci yake yi tamkar zaki, rai a6ace ya wurgawa ƴan sandar bindigarsu ƙasa, Matsawa Inspector ɗin yayi da nufin yasanya wa hosana ankwar dake hannunsa, amma sai mutumin ya dakatar dashi da cewa "karka kuskura !!! domin ban bada izini atafi da yarinyar nan cell ba, kamar yadda ta roƙe ni cewa bataso ta koma, daga nan ba inda zata je," Mamaki ne ya rufe ƴan sandan, inspector ɗin yace "idan ka cika shisshigi zamu sa bindiga mu kashe ka !! A wurin nna," Jinjina kai mutumin yayi tare da cewa "idan kuka kashe ni, ba hukumarku kaɗai bace zata shiga haɗari ba, gaba ɗaya sai an tada nigeria saboda raina kawai," Kansu fa ya gama ɗaukar zafi kowa mamakin wannan mutumin ya keyi, ganin ya toge yaki bari su ta6a yarinyar dake kwance ajikinsa yasa inspector ɗin cewa "wai dan Allah wanene kai!!"? "Yanzu naji bayani" acewar mutumin bayan ya faɗi hakan ya zura hannunsa cikin aljihunsa ya zaro ƴar waya nokia, ya yi dialing wasu numbers da basu fi 5 digits ba ya miƙa wa, inspector ɗin wayar yace "Ka kira numbers ɗin dana sanya ka tambaye su*WANENE MARSHAL OMAR* za ka samu amsar da kake so," Jikin kowa yayi sanyi jin ance marshal, shi kansa inspector ɗin yana ɗan sauko, hannu yasanya ya kar6i wayar, ya danna call tare da karawa a kunnansa, one bugu on ɗauka, cike da kwarin guiwa ɗan sandar yace "WANENE MARSHAL OMAR, cikin harshen turanci yayi tambayar yana jiran amsa daga cikin wayar, tunkan ya cire wayar a kunnansa, wasu irin jibga jibgan motoci ne suka soma antayo wa cikin asibitin aguje masu ɗauke da fusatattun sojoji zafafan gaske, runduna guda kamar a filin yaƙi, zaro ido su kayi gaba ɗayansu cikin tsananin mamaki, kowa dake kallon wannan al'amar tsantsar mamaki ne a fuskarsa, Da gudun gaske sojojin nan suka shiga dirowa daga saman motocinsu kowanne riƙe da manyan bindigogii, da gudun gaske suka tunkaro inda Marshal omar yake sukayi masa ƙawanya, tare da buga ƙafa suka sara mashi sannan suka haɗa baki wurin cewa "We're waiting for your command Sir !" (Umarninka mu ke jira yalla6ai) 😳 Gaba ɗaya hankalin kowa yayi mugun tashi, sun tsorata ainin ganin sojojin ma ba na nan qasar bane, Black americans ne masu wata irin ƙira ta zakuna, kai kana ganinsu ba ɗigon Imani a fuskarsu, umarninsa kawai suke jira, koda hospital ɗinne su tada gaba ɗayansa 😳 Cikin rawar murya ɗan sandar nan wanda yaci ka zaƙe wa yace "Yalla6ai, dan Allah wanene kai"? "dan Allah ka miƙa masa wayarsa, salin alin mu tafi," acewar wannan copral ɗin daya gama tsorata, Hosana ta firgita sosai, amma maimakon ta cire hannunta daga nasa, sai ma ta ƙara ƙanƙamesa sosai, duk yana jin motsin hannun yarinyar acikin nasa, ita kuwa jahad ƙiris yarage tasaki fitsari don tsabagen tsoro, gashi tayi tayi da hosana ta janye hannunta daga nashi amma taƙiyi, Hankali fa ya tashi, kowa da ke wurin so yake yaga fuskar marshal Omar, sun jinjinawa ƙarfin ikonsa, . "Yalla6ai! dan Allah ka karbi wayarka, wlh zamuyi biyayya akan abunda kace," acewar wannan copral ɗin,' sai lokacin Marshal Omar yasanya hannu cikin natsuwa, a hankali tare da zame face mask ɗinsa, Wow zo ka ga ido Cikin wannan Cool voice ɗin tasa yace "Sunana Marshal Omar, U.s Army ni ɗane ga Chief of Army staff wato Abban sojoji,' tunkan ya idasa maganar tasa gaba ɗaya police ɗin dake wurin suka sara masa, hatta sauran mutanen dake tsaitsaye a wurin duk suka sara mashi jin sunan daya ambata, "Nayi muku uziri ne, saboda na lura bakusan koni wanene ba, duk da nayi mamakin hakan," Sauke hannayensu su kayi, Tabbas sai yanzu suka shaida shi, abunda yasa suka rikice sun san cewa Marshal Omar ɗin da su ka sani suke yawan gani tare da SGR ba anan suke zaune ba, kuma basu ta6a tunanin zasu ganshi ido da ido ba, sun saba ganinsa a kafafen sada zumunta, shiyasa su kayi tsammanin ko raina musu hankali zaiyi, gashi kuma yayi hiden face ɗinsa da mask sannan, babu uniform ajikinsa shiyasa komai ya shige musu, "Ynz yalla6ai ya zamuyi kenan? Domim Case ɗin yaran ya kai har wurin commissioner of police, cikin week ɗin nan ma muke shirin miƙa su court don gudanar da shari'a, rashin lpyr yarinyar ne ma ya dakatar da komai," inspector ɗinne ya kora masa bayani, "Ku bar komai a hannu na, zan yi magana da commissioner ɗin, zaku iya tafiya," ya basu umarni Yayi magana tare da amsar wayarsa daga hannunsa, ba musu ƴan sandar suka kama hanya tare da barin asibitin suna masu tsananin mamakin ƙarfin ikon Marshal Omar lallai shi ba ƙaramin jan wuya bane 💪💪💪 (Yanzu shikenan an kashe case ɗin su Hosana da jahad kurmus ya mutu) 😁😬 Mutanen wurin gaba ɗaya murmushi kawai suke saki, kamar a shirin film haka suke kallon lamarin, haƙiƙa marshal Omar ya gama tafiya dasu, Ajiyar zuciya kawai Jahad ke saki tarasa me zatayi don farin ciki, sam bakinta taƙi rufuwa (shin bana faɗa muku ba? Cewa dukkan tsanani yana tare da sauƙi? Sannan bawani yanayi na arayuwa da yake kasance wa na dundundun ba? this is an example) 💞😊 Murmushi kawai hosana ke saki, sam taƙi barin jikinsa har sai da yace "My hand" sannan ta janye jikinta, daga nasa tana zazzare masa waɗannan kyawawan idanuwan nata, sai faman murmushi take zabga mashi, shi kam binta kawai yake yi da kallo, "Kowa ya koma bakin aikinsa!!" Marshal Omar ya faɗi yana kallon jama'ar dake wurin, cikin sauri doctors ɗin dake wurin da nurses ɗin da other peoples ɗin suka watse, Ajiyar zuciya yasaki tare da mayar da eyes ɗinsa akan major ɗin dake bayansa yace
Chapter 57 · 0% Book details