← Book details Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 86

Sashe 2

Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Sannu da dawowa hajiya, wallahi barci ne ya yi awon gaba da ni da ma na sha maganin mura saboda ta takura mini."

Tabe baki ta yi ta ce, "Ni fa ban yarda da ke kullum shan maganin mura anya ba shaye-shaye kika fara ba?" Cikin zolaya ta yi maganar tana kallon ta,

Dariya Larai ta yi ta ce, "Haba hajiya Allah ya tsare ni dayin shaye-shaye tsofai-tsofai da ni."
Murmushi hajajju ta yi "Ya yi kyau! Yanzu dai akwai abinci gidan na zo da yara ne daga kauye."

Girgiza kai larai ta yi, "A'a hajiya sam ban yi tunanin yau za ki dawo ba ai, da na girka muku abinci."

A jiyar zuciya ta saki kafin ta ce, "Koma mene dai laifina ne da ban sanar da ke cewa yau zan dawo ba. Yanzu dai na san muna da bread, ko shayi ne ki hada musu da indomie."

Amsawa ta yi da, "To hajiya!" sannan ta juya ta nufi hanyar kicin din.

Hajiya ta nufi dakinta saboda tana bukatar ta d'an watsa ruwa ta canza kayan jikinta.

Rokon Allah yarinyar take yi a cikin zuciyarta, Allah Ya sa ta samu wannan aikin ko ta samu ta taimaki 'yan uwanta wadanda suke cikin wani mawuciyan hali, muryar d'aya daga cikin 'yammatan nan ta jiyo tana mata magana, "Ke kin iya kunna kallo ki kunna mana mu kalla."

Girgiza kai tayi alamar a'a, ba wai don ba ta iya ba sai don tsoron kada hajajju ta yi mata fada har ma ta kore ta ta hana ta samun aikin. Tana jin su suna cewa, "Karyar banza babu wani ta iya kawai ba ta kunna mana ne 'yar bakin ciki."

Dagowa ta yi ta kalle su harara ta watsa musu ta ce, "E na iya ba zan kunna ba ne ba ku da hannuwa ne ku?" Tsit suka yi ganin yadda ta daure musu fuska sun yi tunanin 'yar shiru-shiru ce, ashe ita ma ta iya fada. Fitowa hajjaju ta yi jikinta sanye da kayan barci, riga da wando ruwan madara, ta daure gashin kanta da ribbom, hannunta rike da waya kirar Infinix Hot 10, suna ganin ta suka gyara zamansu cikin natsuwa.

Wuri ta samu ta zauna a saman 3 seater, yadda za ta ji dadin yi musu magana, yarinyar na jingine jikin 2 seater wadda ke bangaren dama su kuma suna duban ta ta sashen hagu.

A nutse ta soma magana, "Ku na riga da na yi muku bayanin komai ko?" Da'ga kai suka yi alamar e.

Ta ci gaba da cewa, "Yanzu abin da ya rage mini shi ne na koyo muku yadda za ku gudanar da aikin naku don ba zai yi yu ku je gidan mutane a matsayin 'yan aiki ba, a haka kaca-kaca da ku ba tsafta ba. Dole ne kusan yadda za ku tsaftace kanku, da tsaftar muhalli da kuma yadda za ku tsaftace abincin da za ku girka. Kuna bukatar sanin abubuwa sosai daga wajena, kuma insha Allah zan nusar da ku."

Ta mayar da idonta kan yarinyar ta ce "Yammata kin yi shiru ga shi ni ban san ki ba amma yanzu ina son na san me yasa kike nema na ne?"

Bude baki ta yi za ta fara magana amma ganin yadda 'yammatan kauyen nan suka zuba mata ido kamar zomaye, hakan ya sa ta kakare ta kama in ina.

Muryar hajjaju ce ta sa su janye idonsu akanta, "Ku fa matsalarku ke nan sai shegen kallo salon gulma ko?" Sunkuyar da kansu kasa suka yi amma kunnuwansu na bude don su ji me za ta ce?

Cikin sanyin murya ta soma magana, "Da ma na ji an ce kina taimakawa ki sama wa yara aikatau shi ne na zo ni ma ki taimaka ki samo mini don Allah!"

Dafe kai hajju ta yi da hannunta na hagu ta ce "Kash! Da na san wannan ya kawo ki da tun dazu na ce ki koma gida saboda yanzu babu wadanda suka yi mini magana akan na samo musu 'yar aiki, wad'annan 'yammatan da kika gani su ne kawai suka rage na mika su ga wadanda na yiwa alkawarin zan sama musu 'yan aiki amma yanzu babu wani da ya yi mini magana. Ki yi hakuri 'yata!"

Tamkar an d'aga guduma an buga mata a kai haka ta ji, jikinta ya yi mugun sanyi tuni kwalla ta ciko mata a idonta, saboda ba karamin wahala tasha ba, kusan kullum tana fama zaryar zuwa gidan matar neman aiki, tunanowa da ta yi da halin da 'yan uwanta ke ciki ne ya sa ta ji ba za ta iya hakura ba komai zai faru sai dai ya faru, amma ba inda za ta je sai ta samu aikin da za ta samu kudi, saboda ta san ba wanda zai taimake ta ya ba ta kudi haka nan don Allah face ya nemi wani abin daga gare ta.

Tamkar za ta fashe da kuka ta ce, "Don Allah ki taimaki wallahi ko wane irin aiki ne zan iya yin sa. Ki taimaka mini 'yan uwata na kwance asibiti ba ta da lafiya kuma aiki za a yi mata, kudin da doctor ya fada ba mu da su kuma ba mu da wanda zai taimaka mana ni ce kawai nake fafutuka akan yadda zan samu na biya."

Ganin yadda yarinyar ta bi tana rokon ta cikin lallami ya sa ta ji tausayin ta ya shiga ranta, "Ya isa haka, share hawayenki. Nawa likitan ya ce kudin aikin nata?"

"Dubu dari takwas ne." Ta ba ta amsa tana kokarin goge hawayenta. Jinjina kai hajjaju ta yi jin kudin, "Da a ce ina da su da na taimaka da wani abu amma halin da muke ciki yanzu komai tsada hakan yasa kudi ba sa jimawa a wurina. Amma yanzu abin da nake so na sani ina ne gidanku saboda dare ya yi sosai, na mayar dake gid, idan kuma za ki tsaya nan is shike nan in yaso gobe sai ki koma ko?"

Cikin sauri ta ce "Zan tsaya a nan, ba kowa gidan suna asibiti kuma na yi sallama dabsu babzan sake komawa ba har saibna fara biyan kudin aikin, babzan iya jure ganin su cikin mawuyacin hali ba!"

Hajajju ta ce "To shike nan amma gobe zan bincika kuma za mu je asibitin tare saboda ba na daukar yaro ba tare da iyayensa ko wani nasa ya sani ba!"

Yarinyar ta amsa da, "To!"

Larai ce ta shigo dauke da faranti, ta jera sinkin bread guda 3, sai jug mai dauke da tea da kananan kofuna, a jiye masu tayi sannan ta koma ta dauke sauran abin da ta hada musu a kicin.

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_Hafsat Bature_*
~(Boss Lady)~

Page 3-4

Tun da y'ammatan nan suka ga bread suka gaza samun natsuw, sai kokarin zura hannu suke su dauka, ganin haka yasa ta taso da kanta ta rarraba musu ta bawa kowa nasa, dawowa larai tayi dauke da karamin tray wanda ta baza musu taliyan a ciki ta ajiye masu, zama sukayi suna ta aikin ci, ita dai a hankali take ci tana kallonsu hannu baka hannu kurya suke cunkusa wa a bakin, bakomai yazo mata a ranta ba face y'an uwanta, in ta tuna irin wannan yanayin sai taji komai ya fita ranta.

Bayan sun kammala ci , hajjaju ta kai isu zuwa bedroom din da ta ware domin irinsu in ta dauko su anan suke kwana sannan ta yi masu sallama ta fice, tana fita y'an matan kauyen nan suka haye saman bed din dake ciki kuma shi kadai ne, bin su da kallo tayi ganin yadda suka wawware kafafunsu saboda kar tasamu wuri tace zata hau.

Murmushi tasaki, "Allah sarki rayuwa ni ina ne bazan iya kwana ba, bed is ur problem, Sisters dina sune damuwata,
Cire hijab din dake jikinta tayi, wardrobe din dake manne a bango, ta bude babu wasu kayan kirki a ciki, zannuwan atamfa ne kawai, saka hijab din tayi ciki ta rufe,
toilet din dake ciki ta shiga, komai na ciki a tsaftace yake, fari kal! Gaban mirror ta karasa tana kallon fine face dinta, fanfo ta kunna ta tarba hannuwanta tana wanke fuskanta, bayan ta gama tasa hannu ta cire head din dake kanta, ta yi holding dinsa a hannunta tana kallon doguwar kitson kalabar da akayi mata guda biyu ta zubo tun daga head dinta har zuwa west dinta, tana da Yalwatacciyar sumar kai dark brown colour very smooth ga kwantaccen saken gefen fuska.

Fitowa ta yi daga toilet din, samunsu tayi sai minshari suke ja tamkar raguna, wardrobe din ta sake bude wa daya daga cikin zannuwan da ta gani ciki ta dauko, ta shimfida a kasa, ta kwanta
Washe gari tunda sassafe suka fita, hajajju ce ke driving yayin da yarinyar take a gefenta , sai kalle kallen hanya take ta glass din motor, hajajju ta ce "Har yanzu baki fadamun sunanki ba ! da age dinki yakamata nasani ko"? tayi maganar ne a lokacin da take kokarin juya sitiyarin motar wurin canza hanya tabi titin da zai kai ka har izuwa asibitin.
Chapter 2 · 0% Book details