Sashe 8
Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin yanda mahaifiyarshi tashiga gidan cikin
hanzari haka shima agurguje yafada gidan, ranshi
yayi mugun baci yanda yaga gidan cike da
jama'a.
Ga bishira mutum biyu sun rike ta tana
zambarmar asake ta ta lallasa ummi, ga ita kuma
ummi tsaye akofarta kanta babu ko dan kwali ta
sha gajeren wando ya dan gota gwuiwarta da 'yar
riga tana maida martani.
Yace ma matan dasuka
rike bishira, ku saketa suka sake ta ya daka mata
tsawa da karfi, duk ku fice min daga gida,
magulmata tunda duk yawanku kun kasa sasanta
su.
Sum-sum suka wucesuna tabe baki, duk
dahaka bishira bata daina magana ba.ZURFIN CIKI book 4 part 16
ZURFIN CIKI book 4 part 16
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:14
Haka umman bashar batasan yarda komai ya faru
ba.
Amman ta shiga zagi da tsine ma ummi har
da ce mata karuwancin ne ya motsa, ai dama
nasan tun kafin kixo gidan nan kinsan maza.
Bishira ta ce umma wllhi ga babban mai laifin
nan, muna funtata sukeyi duk ire ire wadannan
kayan na jikinta shiya sai mata su, ni bai siyo
min ba.
Na gaji da hakuri ana cutata gwara
yaban takarda ta.
Umma tace daina fadin ya baki
takarda insha allahu saidai ita ya bata, Abba
yayima bishira wani kallo tare da cewa ki tafi
mana sai me?
Yarda kika gaji da ni nima Haka na
gaji da ke, ya kalli ummi yace ke kuma mi nake
fada maki kullum?
Itama cikin fushi tayi magana
toh shikenan saita ta zagina tana ma ummata
sheri don ita kake so?
Bishira ta cafke dama ai
ya fadaman baya sonki.
Ummi ta kalleshi ko zai
kare kanshi, amman baya kokarin Haka saima
kara zaro mata ido da yayi yana cewa.
Ni kike ma
ihu ummi?
Zuciya tazo mata wuya nata ganin an
daketa ne kuma an hanata kuka.
Shi kanshi ya
tozarta ta da ya fadama kishiyarta baya sonta.
Duk da tasan da haka ta kalli bishira cikin daga
murya tace, an fada maki na damune don baya
sona bana son ya soni don nima bana son Shi....
Mari Abba ya sakar ma ummi da bayan hannu,
kalmar da ya tsana kenan, zafi yakeji a Zuciyarshi
ko tunowa yayi da ummi bata sonshi.
Daki ummi
ta fada, ta fada kan gado tana kuka, ya kalli
bishira kije gidan ku sai nazo, umman bashar
tace ba inda zataje kuma in ka sake na samu
labarin ta tafi saina debe maka albarka.
Tasa kai
fuuuu ta fice, tunda ka dauki hukunki mai kyau ka
duki marar kunya ai naji dadi.
Bishira ma taji
dadin haka, Shi kuwa ba don su yayi ba zafin
furta bata sonshi ne yasa ya daketa.
Yana shiga
dakin ummi lokacin ta mike tana kuka, ta dauko
zane ta daura tana kuka sosai.
Ta zari hijabi ta
zura zata fita, yace ina zaki?
Taki sauraronshi
zata fita ya rikota, ina zaki nake?
Tayi magana
cikin daga murya cikin muryar kuka tace gidan
ubana kai kuma ka zauna da warda kakeso,
tunda ya mareta nan ya gane bai kyauta mata ba,
don yasan ba dole bane ta fahimce Shi, sai ya
samu kanshi da jawota ya rungume.
Duk da suna
cikin bacin rai Duk kansu saida sukaji wani irin
yanayi.
Yace kada kiyi yaji ummi kinsan dai koh
kinje su umma fada zasu maki.
Cikin sanyin
murya yayi maganar, kan ummi ya sara, ta kwace
daga jikinshi ta sake fadawa kan gado.
Sabon
kuka ta saki, ya zauna bakin gado ya kamo
hannunta ta sarke ya tsunshi da nata ya dan
matsa, ummi!
Ummi!!
Tashi kiji, cikin kuka tace
mi zanji yaya Abba, kawai ka rabu dani, ni baka
man adalci ba.
Ya za'a yi kaje kana fada mata ni
baka sona kasa tana man gori, umman bashar
harda ceman wai ni nabi maza.
Ya sake kwantar
da murya yace ki yarda ni ban fadama bishira
cewa bana sonki ba, kuma batun umma kisashi a
gefe kawai don ni nafi kowa sanin halinki.
Nafi
kowa sanin tarbiyar umma na...
Duk da haka ai
baka kare kanka ba lokacin da take fada ba,
ummi ta katse kiran da yake mata, yasan ummi
sarai yanzu kam bazata saurari komai ba, koma
ta saurara zata ta kalubatanshi ne, don haka sai
yace to Tashi ki bani abinci.
Kin Tashi tayi don
kanta jinsa take kamar ya fado, mi kewa yayi ya
fita, ya rasa sukuni, koda yaje shago kasa yin
komai yayi, sai murza hannunsa da ya mari ummi
yake.
Ya ciro wayarsa ya kira ummin tayi ta
ringing kusan sau 3 kafin ummi ta daga yace
haba ummi, inata kira kayi banza dani?
Shiru dai
tayi bata tanka ba, ummi cikin disashiyar murya
tace, dama haka ne, sai an kwance ma mutum
zane kasuwa azo gida ace za'a daura masa.
Sai
ta kashe wayar.
Daga nan gidan umma ya nufa,
tace anya Abba lafiyarka kuwa?
Naga Duk ka ya
mutse.
Ya zauna suka gaisa yace umma ina fa
lafia, dazun bayan sallar jumma'a ina iso wa gida
da yunwa sai kurum na samu gidan tam d
jama'a.
Ummi da bishira na tarar suna ta zage
zage har aka samu wata shedaniya taje ta kira
umman bashar.
Umma tace subhanallah!
To ya
akayi yanzu?
Yace tarwatsa taron nayi, nasan
koda ban tsaya bin bahasi ba ummi ce mai
gaskiya.
Domin bata kula bishira, Duk yarda akayi
ta kure ta ne.
Tsohuwa daga can gefe tace, wai
bayan zuwa na gidan sukayi fadan?
Abba yace
oho ni ban masan mafarin fadan ba.
Umma tace
kai wannan abu allah ya dai dai ta maka su.
Amman kyanshi kana zuwa ummin ya kamata
kayi wa fada, koma ka zane ta, don itace karama.
Abba har suna hada baki da Tsohuwa gurin fadin
"Haba dai".
Abba yace umma in itace da gaskiya
kuma ai na zalinceta, yanzun da haka fushi take,
Duk na tsorata bana son fushinta, sai taki cin
abinci.
Don allah umma bari in kira maki ita ki
bata hnkr, umma tace ba zan bata hnkr ba, abinci
kuwa kada allah yasa taci.
Sai dai ayi tunanin
abinda ke cikin ta, Tsohuwa tace, wannan
sakaryar matar taka dama na lura fada takeji.
Sanda nayi sallama tana zaune amman amsawa
ta gagareta, don haka ma ko gaisheta banyi ba
na wuce.
Ita kuma takwara ka hanata saka
wadannan kayan na arna.
Abba yace, su ake yayi
Tsohuwa, Tsohuwa tace, tafdi lallai yayi ya zama
banza.
Abba yake cewa Don allah umma ga nmbr
bari in saka maki a waya, ya dauki wayar umma
ya saka mata lambar wayar da ke hannun
ummin, yace umma na roke ki lallasheta ba wai
fada zaki mata ZURFIN CIKI book 4 part 17
ZURFIN CIKI book 4 part 17
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 02:17
Duk jumma'a abba yana dawowa gida
musamman in ranar girkin ummi ne don cin
abinci na musamman.
Jumma'a biyu kenan bata
fado kanta ba sai wannan, don haka tun alhamis
taje ta yarfo kitsonta, ta biyo ta gidan su gurin
tsohuwa tazo.
Don haka suna gaisawa da umma
tace gurin tsohuwa nazo.
Suka shige daki tace da
tsohuwa nazo ne indan samu dan wani sirrin.
Tsohuwa tace, name ummi?
Ta ce na gyaran jiki
mana.
Fati tace min kwanaki kin fada mata wasu
abubuwa.
Tsohuwa ta ce, ja'ira, kinga uwar bari?
Dama nace zaki same ni ina kyakkyawan zamana,
bada ina fada miki kina sharewa ba?
Ummi tace
haba tsohuwa banaso aji mu yanzun dai ki bani
shawara sannan ki fada min abinda zanyi inja
hankalin mijina.
Ta ce, toda farko ki dinga kula da
jikinki ta hanyar rufe shi ruf, kada kibar kofar
iska.
Banda tafiya ba takalmi, iska tana shiga
tanan kuma mace narage ni'ima banda zama ba
dankwali inso samu ne hatta tsarki ki daina yi da
ruwan sanyi, ki dinga yida ruwan dumi.
Sannan ki
amshi bagaruwa gurin ummarki ki dinga shiga
inkin tafasa da alif dakuma saiwar mata, sannan
inkinyi al'ada kin gama kinyi wanka toki dinga
matsa farin miski a ehem dinki.
Sannan ki samu
saiwar kankana, saiwar zogale, kanunfari,
mazarkwaila dazuma amma kisa kanunfari
dayawa sai ki dafa su su dafu kullum kisha kofi
biyu safe da yamma.
Sannan ki aya garinta,
kwakwa ma kiyi garinta, dabino ma kiyi garinsa,
sai ki dinga diban cokali bibbiyu ki zuba amadarar
ruwa sannan ki zuba zumarki mai kyau kisha, sai
ki samu kuma gwanda, kankana, abarba, zogale,
citta, lemun tsami, ki markada su kisha.
In anan
maki katsaya yarinya zakiji ki kin cika cindum
daruwan ni'ima sai kin samu martaba ta
musamman agurin miji dan zaijiki kin fita daban
da dukkan sauran mata.
Ki hada da biyayya
tsafta da kuma iya tsara girki mai dadi.
Ummi
tace, toni yanzun yaya zanyi nasamu saiwoyin
nan?
Tace, bari zanba matar ado dake yawan
zuwa kasuwar qauye zata zo miki dasu.
Amma
su gwanda gasu nan bakin titi ko shi sai kice ya
siyo miki, zogale kuwa baki rasa shi gurin
ummarki, har da cittar da alif din da bagaruwan.
Ta ce to, ta tafi gurin umma ta amsa har taje
gida bata daina mamakin tsohuwa ba, ya akayi
tasan duk wadannan hadin matan?
Tun ranar
alhamis din ta soma aiwatar da darussan da ta
debo daga tsohuwa, safiyar jumma'a ranar zai
bar dakin bishira.
Ya fito tana sharar tsakar gida
ta gaidashi, ya amsa da fara'a, tare dawani kallo
mai fassarar in ba keba.
Cikin muryar data adana
don shi kadai tace, ya abba ina son in je ayi min
zanen fulawa.
Yace jiya kin fita yau kam a'a.
amma ki aika akira mai zanen tazo ta miki.
Ta
marairaice, towa zan aika yaya abba?
Yace aike
ni, ina ne gidan?
Tace layin su umma ne yace to
za'azo ai miki.
Bishira tafito daga daki tazabga
ma ummi harara, Tare dacewa kisisina.
Abba
yakalleta, kema sai tayi miki.
Tace bana bukata,
aikin banza, shikam yafice.
Ummi kuwa tace gaba
da aikinta, ita ko sai tasa kujera tazauna tana
sakin zantuka, eh don kwalliyar tabanzanta tunda
ba a iya biyawa miji bukata.
Allah dai yasa ya
fada min komai, to ni me zai dame ni don 'yar
aiki kawai na dauki yarinya.