← Book details Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 18

Sashe 6

Zurfin Ciki Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kuma da kin
kwantar da hankalin ki ummi fa ba wai tana sona
bane, ita fa an matsa ma tane, kuma su umma da
kike zagi na rantse miki masoyan kine.

Ta ce
tokai kana son ummi ne ?

Ya dan yi jim, sannan
ya ce ai dai kin san yanda auran namu da ita
yakasance bagatatan bai dace ace kinma tsaya
yin wannan tambayar ma.

Tadan yi shiru, zancen
nan ya shige ta bakamar yanda ta zata da farko
ba, ko dadin baki zaimata?

Sannan ta tuno da
ranar da fati tazo.

Ta labe taji koza suyi
zancenta sai taji suna ta hirarsu, acikin harar fati
ke cewa wai kuwa ya kuka kaya ne ummi?

Nasan
yanzun ai kin warke, kema kin goge.

Ta ce
damefa?

Fati tace, a'a ki gane mana, batun
kwanciya.

Ummi tace, kin san cewa yaya Abba ko
gadona bai taba kwana ba?

Fati tace kai haba?

Ummi tadinga yimata rantsuwa, tuno da wannan
sai bishira ta yarda mijinta ma baya son ummi,
don haka sai ta saki murmushi.

Yace, tunanin me
ki ke yi?

Tace da ina ga kamar dadin baki kake
min, amma dana tuno naji ummi tana fadama fati
wai baka taba ko kwanciya a gadonta ba, bare ka
hada jiki da ita sai na yarda.

Abba ya zaro ido, a
ina kika ji suna zancan?

Ta ce, a'a tazo mata
rakiyane naji suna maganar a soro.

Abba ya
girgiza kai.

Bishira tace, kuma da gske hakane,
yakai hannu yakama nata tafin hannun, wannan
wani sirri ne tsakanina da ummin.

Ynda ba zan
fada mata komai tsakanina dake ba, haka itama
zan sakaya nata sirrin, tadai fahimci hakane, don
haka sai ranta yayi mata dadi har ma ta baiwa
Abban kanta a daran.

Ynda taga yna rawar jiki ya
tabbatar ma ta ba wani angwanci da yayi, don
haka zuciyarta fes ta wayi gari.

Duk da cewa
abba ya tashe ta cewa taje tayi wanka harda
Allah yahadata amma tayi niyar baza tayi hakan
ba sai gari yayi haske.

Ummi ta fito don tanuna
mata cewa Abba ya kwana da ita.

Bishira an dafa
ruwan tea an kai falo sai wannan rawan kai ake
yi.

Sai data lura ummi ta dauko tsintsiya tasoma
sharar gidan kamar yanda tasaba, sannan tafito
da buta aka nufi bandaki, kai ko dankwali babu
aka yiwanka aka fito.

Gashi yna ta digar ruwa,
ummi ta fahimta kuma tagane cewa tayi hakan
don ta nuna mata ne.

Kuma taji zafi aranta
kamar ynda bishiran taso, ta amma azuciyar ta
sai tace na banza jiya nan yakora miki mari.

Lokacin da abba ya shigo gidan tagama shara
tana kwashewa, bai ko dubeta baya shige falon
bishira, kan ummi yasake daurewa, me yake
faruwane haka da zafi?

Ta tambayi kanta.

Data
koma daki tagumi ta zabga tana tunani ita da
suka yi kaca-kaca ma sun shirya bare ni?

Kamar
tabi shi har falon bishiran ta gaida shi, amma sai
tafasa.

Tazuba ido taga zai bar gidanne ba tare
daya leko dakinta ba?

Sun gama karin
kumallonsu tsaf yayo wanka don tafiya gurin aiki,
sai dai kayan dazai saka suna dakin ummi.

Ya
fito yanufi dakin.

Ciki- ciki yayi sallama ita kam
tsoro ne ya tsirga mata, tasake tambayar kanta
mekuma yafaru?

Ta amsa tare da gaida shi.

Nan
ma a ciki ya amsa, yadauki kayan sai dazai fita
sannan yace ba kya bukatar komai ko?

Tayi
karfin halin cewa sugata ceta kare.

Ya dube ta
furka tsuke me yasa baki fada minba?

Ta ce, na
manta ne, yace to sai kije gurin bishira da dibar
miki inzan dawo na siyo.

Ba kya neman komai da
rana ko?

Tace a'a sai nama kawai ya daga
murya, kullum ne ya zama dole a saka nama a
abinci?

Jikinta har bari yake don tsoro, ta ce a'a
yaja tsaki ya fita.

Ummi tasaka kanta cikin cinya
tana furta 'inna lillahi wa inna ilaihir raji'un.'
hawaye suka soma yi mata sintiri.KI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 11
ZURFIN CIKI book 4 part 11
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 01:57
Dadi tamkar yakashe bishira don tna labe tana
jinsu afalon ya saka kya yashirya tsaf, sannan ya
nufo dakinta don dauka jakar laptop dinshi.

Jin
sallamarshi tayi mza tashare hawaye sannan ta
amsa, yshigo ya dauko dari biyu ya aje mata
akan gdo, ga kudin maman nan kura, kada fati
tzo kifada mata baki kudin nama kullum tunda
har kin iya shaida mta cewa ban tba kwana
agadonkiba.

Kin kosa inkwanta dakene?

Yadauki
jakar yarataya sannan yayi mata wani kallo sama
dakasa, to banga gurin kwana agadon naki ba.

Hakanan banga abin kwanciya ajikinki ba, yafice
yabar ummi tsaye tazaro idanunta cikin matukar
al'ajabi da kunya.

Ina ya Abba yaji zancen nan?

Kodai fati ceta fada masa?

Wata zuciyar tace fati
baza ta iyayi masa zancan nanba saidai in
ummarsu tafada mawa ita kuma tafada masa.

Inko hakane fati batayi mata adalci ba, ai hira ce
irinta aminta tsakaninsu, gashi ta bata kunya har
tasa ya Abba naganin tazaku.

Tokuwa tasha
alwashin nuna mishi bahaka take nufi ba, afili
tace Allah yabamu rai da lpy.

Sai kuma tasoma
kuka.

Bishira tafadi kan dadi ashe gara data fada
masa zancen dataji suna yida fati, gashi yanzun
yayi mata rana.

Lallai labe yayi mata amfani sai
kawai tasabi 'yarta tazari mayafi tafice makota,
yau kan tana da labari mai dadi sai yawon raba
shi take bata manta ko kalma daya.

Sannan
darana tazo tahau kici-kicin dora girki, lokacin
ummi tafito don yin alwala, ita ko karyawa batayi
ba don tawuni da takaici ya Abba.

Tana kallon
yanda bishira tazubu kayan miya tana jajjagawa
batare data wanke ba hancin kawai ta cire.

Ummi
tayi alwala tashige daki, ranar har dare ummi
bataci komai ba, duk da tanajin yunwa.

Zantukan
abba kawai kemata yawo a kwanya.

Tayi kuka
harta gaji fuska ta kumbura.

Tun uku yadawo
baiga ummi ba, bishira tagabatar masa da abinci
dakyar yayi cokali uku.

Dama yazo dafura, yasha
sannan yanufi shago, yini yayi yana tunanin
kamar bai kyauta ma ummi ba, amma yana
mamakin yanda ummi ta iya cewa bai hau
gadonta ba.

Kenan inyahau din dakuma abinda
yabiyo bayan hawa gadon duk zata ringa fesarwa
ne?

Kai yafaji haushin abu biyun nan dacewa
bada sonta aka daura masu auran suba dakuma
fada ma fati sirrinsu.

Saidai duk dahaka zuciya
da idanunshi suna matukar kewar ganin ummi,
sai shida yadawo gidan.

Ruwan wanka ya diba
yanufi bandaki, man shafawarshi dasauran su
suna dakin ummi, don haka yakalli bishira.

Bari in
dauko kayana can dakin ummi kozaki dauko min?

Tace, bazan jeba kaje da kanka.

Tana kwance
kan doguwar kujera lokacin kanta yana matukar
sarawa, don kuwa yanda yayi sallamar da kyar
itama dinda kyar ta amsa.

Saidai ita badon
wulakanci tayiba, saidai don yanda take jin
jikinta.

Yashafa mai tare da feshe jikinsa da
turaruka.

Idanunshi suka sauka kan darinshi biyu
daya aje mata.

Yakalleta, ke ina abincin da kika
dafa?

Batare data dubeshiba tace, bandafa ba.

Yace sbd me?

Tace banjin yunwa, kaikuma naga
ba anan kake ba, baki ya taba yasa kaya yafice.

Har tayi sallar isha'i lokacin tasoma jin jiri, amma
bata da niyar shan ko tea tanajin ya shigo ya aje
mata ledar ta kusan minta 30 kafin tataso tazo
tatura kofarta.

Sannan taduba ledar, nama ne
balango yaji albasa da tumatiri, sai sugar da
madara, nan ta aje su tayi kwanciyarta afili tace
natabbata kurar kenan indai naci maman nan.

Bacci yadauketa can kusan ukun dare fa yunwa
fatakai yunwa, kowa yasan yunwar dare yanda
take jigata bawa, a gigice ummi ta tashi tahada
tea tahau sha da gaggawa.

Tagama kamar taci
naman sai kuma tafasa ( tamiko min ninkuma
nayi fuska nacinye au namanta madawani azumi
lolx) ta kauda kayan ta koma ta kwanta, aikonan
fa cikinta yahau hautsinawa.

Dagudu tatashi
tanufi fita tana bude kofa kafin takai bandaki
tasoma sheka amai, tun bude kofarta abba
yafarka dasauri yafito.

Riketa yayi ganin yanda
take sheka amai kamar zata amayar da hanjin
cikinta, sai sannu yake mata.

Data gama yajanyo
ruwa ya wanke mata fuska ta kuskure baki.

Yawanke gurin gurin tana gefe tsugunne, cikinta
da kanta sai ciwo sukeyi tana mikewa sai jiri.

Nan tafadi ragwaf, shine yadauketa tamkar ya
dau jaririya don rashin nauyi yace duk kece kikayi
makanki sanadin wannan matsalar.

Don kina
fushi saiki yiwa abinci yaji, ai gashi nan kema
kina ji ajikinki, kan kujer yadorata ya cire mata
siket din atamfar dake jikinta, don duk sun jike sai
na ciki.

Yajuyata zai zage mata zif din rigar tana
son ta hana amma bata dawani karfin hanawa.

Tanaji tana gani abba yacire mata riga, gashi ko
best bata saka ba sai breziya.

Takai hannuwanta
tarufe kirjinta.

Shikam ganinta ahaka yasa tsigar
jikinsa tashi, tun daga karamin yatsansa har
tsakiyan kansa ruf da ciki ta juya tayi, shi kuma
ya kunna mata fanka yafita.

Zaune ya samu
bishira atsakiyar gado, ta kalle shi da tuhuma, me
kaje yi dakinta?

Yce amai naji tanayi shiyasa
nafita, bta dlpy ne, tsaki taja sannan ta kwanta.

Shi kam bai runtsa ba, kunnanshi da hankalinshi
suna can, dga bisani madayaga baccin yaki sai
yatashi yayi alwala yasomayin nafila.
Chapter 6 · 0% Book details